Showing 18001 words to 21000 words out of 52375 words

Chapter 7 - KISHIYA KO BAIWA BY REAL ESHAA.txt

06 Mar 2025

3314

kin kai waje!? insha Allah daga yau keda waya sede kigani ahannun wasu anma ba ahannunki ba bare harkisamu daman 'karya,dakuma koya miki munafurci yanagama fa'din haka yajuya afusace zefice"rigansa tarike tabaya tace kabani wayata nagaji nagaji da Wannan cinkashin da ake yimin acikin gidan ka kowa yatashi se ya yimin cinkashin dayaga Dama Har matanka nacewa saboda kudin ka na aureka ina...wani wawan mari ya kwasheta dashi yace aibakarya akayi mikiba dan kudina kika aurene kokina zaton bansan yanda kika yadawa duniya kancewa zaki aure me kudi megida da mota zakihaifi yara dankici gado,keda kwa'dayayyun iyayenki,toh ni dukiyata banaki bane gwanda ma tun wuri kisani kikuma gyara niyarki danyin rayuwar aure me tsafta.Cikin wani irin fusata tamike tunda Ahmad keyi mata rashin mutunci bata ta'ba jin Wanda yatunzura mata zuciya ba irin na yau iyayenta yake kira da kwa'dayayyu"Hannu tasanya tashake wuyarsa,cikin karaji tace mekakedashi matsiyaci irinka butulu Wanda besan alkhairi wlh baka da dukiyar dazesa in aureka kokuma iyayena subakani iyayena dattijan arzikine Wanda Sam abin duniya berufe masa ido kaima kuma shedane domin basu taba zuwa wajen ka domin katemaka musu da kobanka"kansa yanuna da hannu yace nine matsiyacin Sukainat nikika kira da matsiyaci?yafada yana pointing din kansa da hannu.Cikin hargagi da rashin tsoro tace "eh" Kaine matsiyaci kuma makaskanci mayaudari azzalumi nafa'da cemaka akayi ni baiwace dazakayimin cin kashin dakaga dama,kana gadara da dukiyar da ko zakkan wani bekaiba tafada tana fashewa dawani matsanancin kuka me ratsa zuciyar duk Wanda yajishi...Fincike hannunta yayi daga jikinsa zuciyar sa natafarfasa lalle sukainat tacika tacacciyar mara kunya,yarasa meze mata hakan yasa shi fita daga dakin domin yasan muddin yatsaya ze aikata aikin Dana sani sede yayi alkawarin daga yau zenuna mata kuskurenta daga yau zefita ahanyarta daga yau zata fuskanci wanene shi da Wannan tunani yafice daga gidan baki daya zuciyar sa na tafarfasa.....










_VOTE_ โœ…
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_










*_ESHAA CE_*๐Ÿค™๐Ÿป
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_


*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*




*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*PAGE 25&26*๐Ÿ–Œ๏ธ


________________________๐Ÿ“–Sukainat naganin fitarsa ta durkushe awajen tare da fashewa da wani matsanancin kuka me ban tausayi,shin wannan wace irin rayuwace duk wulakanci da Ahmad da matarsa ke yimata be ishesuba harse ya ha'da dacin zarafin iyayenta hakika kodashi ne autan maza bazata zauna daahiba muddin zeci zarafin iyayenta.Tana cikin wannan yanayi taji dariya da shewa akanta,kai ta'daga dan ganin wacece?!Nadiya tagani fuskarta na bayyanar da farin ciki,du'rkusawa tayi agabanta tace, hausawa sunce idan kaga mutum ze hadiyi gatari to kari'ke masa 'kota"wannan Karin maganar tasu haka yake babu shakka acikinsa!,tun kafin kishigo gidan nan nafa'da miki cewa se kin gommaci zaman prison da zaman Cikin gidana, domin babu macen data isa tashigo gidan amatsayin matar Ahmad kuma tasamu kwanciyar hankali babu wannan matar aduk fadin duniya.Duk da ire iren tarin kashedi dana miki haka kikasanya 'kafa kika shure kika maida magana ta tamkar tatsuniya,kina tunanin zakishigo muzama daya saboda 'kwa'kwalwar kifi gareki.Har yanzu baki fara kuka da danasa ni, acikin gidan naba"tunda harzu wannan lokacin baki fara shirin barin gidan da kafafunkiba.Ina so in tabbatar miki cewa kishi da ni, ba Abu bane mai sauki kamar yanda kike zato,Murmushi tayi tace hakika kinbani tausayi shiyasa zanbaki shawaran daze anfaneki ,tunfasawa tayi kafin daga bisani tace" tunkafin dare yamiki kitattara inaki inaki kibar min gidana nida 'ya'yana,tun kina da sauran karfin ki dakuma kuruciyarki domin kar 'karfin ki da kuruciyat ki sukare abanza batare da kin moraba."Sukainat takasa koda furta kalma 'dayane banda hawayen dake malala daga idanunta"Wannan hawaye bakaramin sanyi sukewa Nadiya a zuciyar taba domin barin ta bewuce taga Sukainat na wahala ba.Seda tagama ya'ba mata ba'ka'ken magana kafin tafice tana karairaya tare da 'yan wa'ke'kenta.Sosai Sukainat tayi kuka da danasa ni,wanda bata ta'ba yiba irin na wannan rana.Wannan kukan datayi shi yajanyota mata matsanancin zazzabi da ciwon kai 'kyar ta iya Jan kafarta takwanta akan gado...


Da yammaci bayan tafiyar Hjy kultum badadewa hema tazo"Kafin Hjy kultum tatafi seda tajawa Nadiya kunne kan karta ragarwa Sukainat intayimata Abu kar tabari se Ahmad yazo tadauki matakin daya dace dakanta.Sosai Nadiya taji dadin wannan magana na Hjy kultum danhaka tayita zabga mata karya da gaskiya abinda kefaruwa tare da yimata godiya kan shawaran data bata.Lokacin da hema takaraso bakaramin farin ciki Nadiya tayiba tarungume ta tayi, tace gaskiya nayi farin cikin zuwanki kawata domin ina bukatar ki"Kallon ta hema tayi,tace kai 'kawata kina sha'aninki bakyajin garin sekace kece Amaryan?:dariya Nadiya tasheke dashi tace nice mana tunda se yanda najuya kambu na acikin gidan ta'fada tana juya kananun idanunta,Dariya hema tafashe dashi tace baki da dama mutuniyar, bani insha yanda abin yafaru cikin sauki??!Zama Nadiya tagyara tace agaskiya yarinyar batada reni ko rashin kunya kamar yanda kika fada, sede matsalanta daya! batasan yanda zata min biyayya ba domin da ta iya yimin biyayya toh datasamu kan Ahmad" sede tacika taurin kai tafada tana yatsine fuska.Dariyar 'keta hema tafashe dashi tace aiduk Wanda yaci tuwo damu miya yasha waya fa'da mata muna zama dakishiya?Anma yabatun Wannan maganin hope yana aiki?Murmushi Nadiya tayi tace aikomai normal tunda nafara sanyawa acikin abincin kullum abinci cikin baci yake,arasa gane kansa da gindinsa,anma dayake yarinyar akwai shegen wayo shine tafaki idona tayi girki bansani ba"Ahmad naci yazo yana wani rawan kafa...duk de abinda yafaru seda tazayyanewa hema"aikuwa suka dinga dariyar keta cike da farin ciki hakarsu na cimma ruwa yanda suke bujata.Seda daddare mijin hema yazo yadauketa sukatafi"bayan sun sake shirya sabon manakisa ...
Koda Ahmad yadawo gida direct sashen Nadiya yanufa kasancewar ita ce da girki toilet yashiga yai wanka Kafin yafito yasanya jallabiya maroon megajeran hannu Wanda yaimatukar yimasa kyau kana yafeshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi"Koda wasa besanar da Nadiya sa'banin dayafaru tsakanin sa da Sukainat ba"se bayanda ya kammala shirin kwanciya yace da ita kar tasake baiwa suky abinci na tsawon kwanaki biyu,sannan koda wasa karki barta tashiga kichen tagirka komai harse nabada izinin hakan.koda tagama jin abinda yace se tace,haba Honey meyayi zafi haka hadda horon abinci? kasanfa Sukainat yarinya ce dole se anbita Ahankali??! Ta'fada cike da kissa.Shiru yayi yajuya mata baya batare daya bata amsa ba dan bejin ze iya magana a wannan yanayin dayake ciki.Jin haka yasa tasha jinin jikinta domin tasan tunda yajuya mata baya bazece komai ba,tsaki taja aranta tace mutum se miskilancin tsiya...
Kamar yanda Ahmad yafa'da hakan yakasance, Nadiya tahana Sukainat abinci natsawon kwanaki biyu,daman ya lafiyar kura bare tai zawo,dama kawai dama Nadiya kejira Wanda zata musgunawa Suky sekuma gashi tasamu cikin sauki yanda babu Wanda ze ga laifinta.
Atsawon kwanakin biyun nan baki daya Sukainat tarame ta lalace gawani zazzabi dake damunta duk Daren duniya bata iya bacci dashi take kwana take tashi ga horon yunwa sede tasha tea kawai,tarasa Wanda zata fa'dawa damuwarta,taji sanyi aranta,ga ba waya ahannun ta bare tasamu daman kiran mahaifanta. Ahmad yadena zuwa dakinta acikin kwanaki biyun bare tasanar dashi halin datake ciki, Nadiya kuwa tasan koda shure shuren mutuwa take bazata temaka mataba hakan yasa take zaune cikin kunci da bakin ciki.Seda tayi kwanaki biyu kafin Ahmad yasa Nadiya taci gaba dabata abinci,toh koda anbata abincin ma bata iyaci kasancewar batada cikekken lafiya,haka take wuni ko yaushe acikin dakin daga Nadiya Har 'ya'yan ta babu me shiga inda take....


****
Tun daga Wannan lokaci Sukainat tashiga rayuwar 'kunci da ba'kin ciki,duk wani aikin wahala da bauta acikin gidan itace,Nadiya tadena komai,saboda tsaban mugunta irin nata ga injin wanki anma bazata yi dashi ba sede ta tattarowa Sukainat nata dana 'ya'yan ta tayi musu haka zalika wanke wanke, moffing sharan compound din gidan,duk wani aiki me wahala itace zatayi Ahmad kuwa yagoyi bayan matarsa acewar sa aikin yakamaceta"shiyasa suke mata duk lulakancin dasuka ga dama ita da 'ya'yan ta batada ikon tankamusu tun da mai gidan yagoya musu baya.Tsakanin ta da Ahmad kuwa wani irinin zama suke mecike da ban tausayi,Sai ranan girkinta ne ze shiga dakin ta,tsakiyar dare asbah nayi zefita bakuma za tasake ganinsaba se wani ranan girkinta, wani lokacin ma batasanin shigowar sa sede taga alamar mutum ya kwana adakin...Yauma kamar ko yaushe se misalin 'karfe biyu nadare yashigo dakin nata gani yayi tanata murkususu,A'kasan 'dakin tana shesshe'kan kuka,cike da rashin damuwa ya kwanta batare daya kalletaba yayi kwanciyar sa,yakai kimanin minti talatin bacci yaki daukarsa sakamakon sheshshe'kan kukanta"mikewa yayi yana Jan tsaki cike da takaici yace Dan Allah malama ki yimin shiru kinbi kin dameni da kananun kuka idan kuma bazakiyiba nabar miki dakin,ai wannan wulakanci ne kinsani gaba da kukan munafurci jarababbiya kawai yafa'da yana binta da mugun kallo....Kasa cewa komai tayi se kukan dake kara kufce mata ga wani azabebben zazzabi dake damunta shin wai yaushe Ahmad yakoyi rashin tausayi ne?tatambayi kanta"Jin taki yin shiru yasa shi yamike afusace yayo kanta hannu yasa daniyyan janta waje,Dasauri yajanye hannunsa daga jikinta sakamakon wani zafi daya gauraye ilahirin jikinta.. Zama yayi agefenta yana binta dawani mugun kallo,saboda tsaban bakin hali da munafurci baki da lafiya shine bazaki sanarmin ba,Inkin kashe kanki iyayenki kikayiwa asara baniba danni bakya gabana jarababbiya kawai yace da ita"ko Kallon sa batayiba domin ita tasan abinda kedamunta,seda yagama jifanta da mugayen kalamai kafin yajanyo hijabi yasanya mata, sukanufi asibiti lokacin uku da Rabi yayi ko acikin motar se hantaran yake tare da ya'ba mata ba'ka'ken magana...Suna isa asibitin aka shiga bata temakon gaggawa, gwajin farko aka gano tana dauke da ciki na tsawon sati shida,Bayani Dr yashiga yimasa na yanda yakamata abata kulawa sannan kartayi aikin wahala kokuma ta'daga Abu me nauyi,saboda zejanyo matsala,sannan sakamakon binciken dasukayi sungano akwai yunwa da damuwa atare da ita dole adena yimata abinda zesata cikin damuwa domin tana bukatar kulawa na musamman.Magunguna Dr yarubuta masula Wanda zatayi amfani dasu"Godiya Ahmad yamasa sannan yawuce masallacin dake cikin asibitin kasancewar ana kiraye kirayen sallah.Bayan ya idar da sallah ne yashigo,dakin datake Zaune yasameta tajinga bayanta da bango idanunta alumshe kamar me bacci,jin kamshin tularensa yasata bude idanunta tana Kallon sa cike da So, kawar dakai gefe yayi yana Jan tsaki"jiki asanyaye tayi kasa dakanta talura ko Kallon besonyi"wata noise ce tashigo hannunta dauke da Leda me tambarin asibitin da alama maganine aciki tabaiwa Ahmad,Kallon Sukainat tayi tace madam congratulations natayi murna Allah yaraba lafiya"Ameen ta amsa tana nazarin maganan, fuskarta da yakwateccen farin ciki tace ya Ahmad, ciki ne dani??Wani mugun kallo ya watsa mata yace, adakile"yece eh",bata damu dayanayinsa na halin ko inkula daya nuna mataba sema wani farin ciki daya mamaye mata zuciya,hannunta tadaura akan cikin tashiga shafawa tanajin wani yanayi me wuyar fassarawa atare da ita Ita ce ke dauke da cikin Ahmad ajikinta?,gudan jinin Ahmad ne ke kwance acikin mahaifarta,?zata haifawa ya Ahmad dinta yara kyawawa kamarsa?,wasu hawayen farin cikine suka shiga zubo mata afuska,Dawani irin sauri tadira akan gadon tarungume sa tana hawayen farin ciki....Rai abace yasa Hannu yafinciketa daga jikinsa yanabinta dawani irin kallo Wanda shika 'dai yasan ma'anarsa...










_VOTE_ โœ…
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_










*_ESHAA CE~_*๐Ÿค™๐Ÿป
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_


*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*




*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*PAGE 27&28*๐Ÿ–Œ๏ธ


__________________________๐Ÿ“–Cikin kakkausar murya yace mehaka kikeyi?,bakida hankaline in wani yashigo yaganmu ahaka fa?!Wani irin kallo kike zaton za ayi mana ya fa'da yana tsareta da dara daran idanunsa"Cike da mamakin kalamansa take Kallon sa!,cikin sanyin muryanta tace nifa matarkace ya Ahmad meye aciki dan anganmu ahaka??batajira amsarsaba taci gaba dacewa Ya Ahmad farin cikine yasani rungumarka,nasan duk duniya bayanni babu Wanda yakaika farin cikin samun Wannan cikin, shiyasa nake ganin yadace innu nama farin cikine abayyane ya Ahmad duk abinda zanyi bazan iya fadan farin cikin danake ba sede in misalta..Hannu ya'daga mata yana ta'be baki, cikin halin ko inkula yace"Sannu Uwar iya tsara magana niba Wannan tsarin nace ki yimin ba.Saboda munafurci 'dazun kin langwabe kan cewa ke bakida lafiya anma dubeki yanda kike wani rawan kai dakikaji cewa kinada Ciki natsani karya da munafurci arayuwata, dubi yanda kika tashi kika kankameni wai farin ciki ya fa'da yana maka mata harara.
Asanyaye tace kayi hakuri in ranka yabaci wlh banyi hakan daniyyan 'bata maka raiba maganan cewa lafiya ta kalau kuma kaima kasan bahaka bane, kawai de ina farin cikin zanhaifi yara kyawawa kamar kane,sannan kuma zanhaifi yaran dasuka fito daga tsatsonka, inaji ajikina duk yaran da zanhaifa maka,zansosu fiye da komai arayuwa ta saboda soyayyar dana ke yimakane zedawo kansu, ina matukar kaunar ka arayuwa ta fiye da yanda uwa ke kaunar danta ina kaunar ka fiye da yanda nake kaunar kaina inayimaka son da banayiwa kaina,ban tabbatar da soyayyar danake maka na gaskiya bane se yau danake dauke da gudan jininka amahaifata"Dan Allah ya Ahmad kasoni koda Rabin soyayyar danake yimaka,soyayyar ka acikin jinina Allah ya halicceni dashi bana tunanin zan iya rayuwa batare dakaiba ya Ahmad Allah ne shedena kan irin soyayyar danake gwada maka.( _Ina Bukatarka acikin rayuwata Kamar yanda mutum ke bukatar abinci domin yarayu,Ina bukatar ka kamar yanda kifi ke bukatar ruwa domin yarayu,Ina bukatarka kamar yanda tsuntsaye ke bukatar fikafukai domin suyi rayuwa Kamar haka nake bukatar acikin rayuwa ta domin nayi rayuwa me inganci da tsafta)_ Hakika kazamto wani bangare daga jikina Wanda bazan iya rayuwa idan babushiba takarashe hawayen tausayin kanta nazuba daga idanunta!.Sosai kalamanta sukayi tasiri agaresa jiyayi zuciyar sa yakarye shi kansa yasan son datake masa korabi baya mata, hannu yasanya yarungumeta yana bubbuga bayanta alamar rarrashi"Wani irin sanyi taji yaratsa zuciyar sakamakon rungumar daya mata hakan yasa tasaka hannayenta biyu tabaya tasake rungumesa tana cusa kanta afaffa'dan 'kirjinsa tare da sha'kan dadda'dan kamshin sa."Nafa'da butulu azzulumi matsiyaci mekake dashi??"kalaman dasuka shiga yimasa suwwa acikin dodon kunnensa kenan jiyayi zuciyar sa yagaza juran kalamanta,finciketa yayi daga jikinsa atake idanunsa suka rine izuwa 'bacin rai,zuba mata idanunsa yayi cikin kunan zuciya da takaici yace me zakiyi da butulu azzalumi,kuma matsiyaci aganina bekamata kiso irin wannan mutumin ba kamata yayi kisamu Wanda bashida wannan soffofin baniba!!.kuka tafashe dashi tace kayi hakuri ya Ahmad idan muna tuna abinda yafaru abaya baza muta'ba yafewa junanmu ba hasalima idan kace zaka tuna nimafa kafada min kalamai masu zafi akan iyayena"bece da ita komai ba se juyawa dayayi yafice..zama tayi tare da fashewa dakuka me bantausayi....


****
Yana fita direct motarsa yashiga,driving yake anma baki 'daya zuciyar tsa cike da was-wasi yake yakasa nutsuwa zuciyar sa se sa'ke-'sake take masa gameda kalaman Sukainat yarasa wanne zeyi amfani dashi,!zuciyar sa yakasa hakuri da sunayen data kirasa dashi abaya.Yana isa gida yayi parking direct sashen Nadiya yanufa,harzuwa lokacin basu tashi daga bacci ba, tashinta yayi kafin yashiga toilet yawatsa ruwa cikin 'kan'kanin lokaci yafito yashirya cikin kananun kaya bakin jeans da White t-shirts bakaramin amsar jikinsa kayan sukayiba, dadda'dan tularensa yadauka yashefe ilahirin jikinsa dasu...Ido Nadiya ta'kura masa ko 'kyaftawa batayi, ganin irin kyan dayayi tamkar dan shekara ashirin da takwas" 'karasawa gabanta yayi da 'kayataccen Murmushi a fuskarsa yalakace mata hanci cike daso yace wannan kallon fa my Queen??, Fari tayi masa da 'kananun idanunta tace ina Kallon mijin dayafi ko wani 'da namiji kyau da aji je aduniya..Dariya yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoransa yakuma lotsar da dimple dinsa yace banda San Kai",ido tasake kuramasa ganin yanda ainihin kyawun sa yasake fitowa tace bawani San kai gaskiya nafada..Kallon ta yayi anutse yace shirya mutafi asibiti,dasauri ta kallesa tace waye ba lafiya Allah yasa de ba Hjy bace!!Baki ya ta'be yace Sukainat ce ba Hjy ba,yasalam meke damunta haka honey??Kede shirya mutafi,zatakara magana yadaga mata Hannu yace kije kishirya kizo mu je kigani.Jiki asanyaye tamike tashiga toilet. Batadau dogon lokacin ba tafito anma kafin tagama shiryawa se goma,Kallon sa tayi tace muje ko?,mikewa yayi batare dayace komai ba yanufi hanyar fita,hannunsa tarike tace honey haka zamuje ba komai ahannun mu??,Kallon ta yayi yace Kamar ya??breakfast tace dashi"Kai ya dafe yace na manta anma muje se musiya a restaurant kinga lokaci yawuce,kai ta girgiza tace no ba za'ayi ahaka ba, kabani minti ka'dan Yanzu zangama,bata jira jin abinda zeceba tawuce kitchen tabar sa awajen...Zama yayi yana latse-latse a wayarsa se misalin karfe,shabiyu tafito hannunta dauke da babban basket da warmers aciki.da Murmushi a fuskarta tace nadade ko Honey??, Kayataccen Murmushi yasakar mata yace no ai girki is not easy namaga saurin ki, muje ko yafa'da yana karban basket din hannunta, bashi tayi,tanayafa mayafinta, fita sukayi zuwa parking space key yasanya yabude motar, mazaunin driver yashiga itakuma tazagaya dayan side din tazauna key yayiwa motar suka nufi hospital...
Se misalin shabiyu da arba'in suka isa hospital din,bakinsu dauke da sallama suka shiga,tunkafin sukarasa shiga sukajiyo dariyan Sukainat natashi sama-sama"dasauri Ahmad yakarasa shiga dan ganin da wa take wannan dariyan".Sofi'a da mahaifiyar ta yahango sun sanyata atsakiya sehira suke cike da farin ciki,tsaki yaja aransa yana binsu da mugun kallo"Hjy Amina ce ta daga kai bayabo ba fallasa ta amsa musu sallaman tare da maida hankalin ta kan warmers din dake hannunta tana zubawa Sukainat peper soup din kayan ciki.murtuke fuska Ahmad yayi yayinda ya karasa cikin dakin,kujera yaja yazauna kafin Nadiya tashigo kusa dashi tazauna tana binsu da wani kaakantaccen kallo ta kasan ido,kamar Wacce aka tilastawa haka tagaishe da Hjy Amina "Amsawa tayi batare data kalletaba domin Hjy Amina irin matan nan ne dabasa daukar reni komai kankantarsa."Sarai Sofi'a taga irin kallon renin dateke binsu dashi anma se tadanne zuciyar ta tace ina kwananku"Daga Ahmad Har Nadiya babu Wanda yaimata amsawar mutunci,Musamman ma Ahmad dan wani irin haushinta yakeji, yafuskanci yarinyar batada kunya ko ka'dan" Juyawa bangaren dasuke sukainat tayi ba walwala a fuskarta tagaishesu.banza suka mata hakan yasa takauda kai suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login