Showing 6001 words to 9000 words out of 52375 words

Chapter 3 - KISHIYA KO BAIWA BY REAL ESHAA.txt

06 Mar 2025

3303

damar yanke duk hukunci daya so akanta,Dan Allah kibar maganan,'daya daga cikin Aminan Ummi ne wato mahaifiyar Sofi'a me suna Hjy Amina tace"hakane Aliyah kibar maganan kawai.Kallon ta Ummi tayi tace yanzu kitashi kuje Gidan kiduba duk abinda beyiba se kugyara"mikewa Aunty Aliyah tayi suda wasu kawayen Ummi suhudu suka tafi Gidan Ahmad...
Tunda suka shiga compound din gidan sukajin kida natashi kamar ze tsaga gidan,tsaki Aunty Aliyah taja aranta tace lalle wannan yacika Mara mutunci wato yabar matarsa tayi abinda taga dama can kuma yahana ayi taro saboda rainin hankali dasamun waje irin nasa,wajen tanufa kasancewar sashen Nadiya Dana Sukainat ahade suke corridor kawai ya banban tasu" A?Kanabin Corridor zesadaka dasashen nasu"Tsayawa sauran matan sukayi suna gaishesu anma daga Nadiya har kawayen ta basu San Allah yayi tsiron hallittarsuba,aunty Aliyah kuwa takaici ne yacikata dan haka batace komai ba tayi wufewarta direct sashen Sukainat,danyi abinda yakawo su.Harsukayi aikin suka gama ko ruwa ba akawo musuba bare kuma abinci,lokacin dasuka fito kawai se Nadiya suka fashe da dariya tare dacewa se ayi mugani intusa zehura wuta"kojuyawa Aunty Aliyah basu yi ba bare sukanta musu...koda Aunty aliyah suka koma gida direct dakin Ummi ta shiga inde tasame ta da aminiyarta wato mahaifiyar Sofi'a, Rai abace aunty Aliyah tace agaskiya yaya wannan matar Ahmad din ba yar mutunci bace..kai Ummi tadafe tace Aliyah rayuwar nanfa hakuri akedashi dan Allah kibar wannan maganan banason abin fitina ki kyaleta duk abinda tayi kanta tayiwa"Shiru Aunty Aliyah tayi domin baki 'daya hakurin Ummi Sukainat ta'dibo...
Da daddare kamar yanda Ahmad yafada misalin karfe 9:00pm yazo daukar matarsa,lokacin duk anwatse se 'yan uwa dakuma bakin dasukazo daga nesa suka rage.
A parlour Malam Ahmadu aka sauki Ahmad badadewa aka kawo Sukainat daketa kuka"Da Addu'a Malam Ahmadu yabude taron sannan yafara yimusu nasiyya meratsa jiki bayan yagamane Ummi da Hjy Amina sukayi musu nasu nasiyyar meratsa jiki" aunty Aliyah ce karshe cikin yanayin ta na zafi tace toh Ahmad ga amanar Sukainat munbaka ita karkaci amanarta ko kuma kazalunceta kasane muddin kazalunceta Allah baze barka ba domin Sukainat nitsatstiyar yarinyace munsan da ikon Allah bazata bamu kunya ba sannan kazamto me adalci a tsakanin matanka kada kazalunci kodaya acikinsu...Cike da ladabi yace insha Allah zakusameni me rikon amana zan kula daita dakuma tarbiyanta,mikewa Malam Ahmadu yayi yarike hannunta sannan yariko na Ahmad yace kuje Allah yabaku zaman lafiya medaurewa" 'kan'kame hannun Malam Ahmadu Sukainat tayi tafashe dakuka metsuma zuciya cikin muryan kuka tace dan Allah Abba karku bari yatafi dani ninafasa auren banason rabuwa daku,Rarrashinta Malam Ahmadu yayi tayi da 'kyar akasamu akafita da ita akasanya ta amota tawani irin kuka metsuma zuciya.....








YANZU AKAFARA LABARIN








_VOTE_ βœ…
_COMMENTS_
*And*
_SHARE_














*_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_


*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*




*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




```Wannan page din kyauta ne agareku Kishiya ko baiwa Fan's hakika inajin dadin comments dinku"Masoyan Sukainat wannan page din kuma kyauta ne agareku.


Teemah😘
And
Mmn mardiyya 😘
Kuma wannan page din kyauta ne agareku kuyi yanda kukeso dashi son so fisabillah😘```






*PAGE 9&10*πŸ–ŒοΈ


________________________πŸ“–Ba abinda ketashi acikin motar banda shesh'she'kan kukanta"Ahankali yarage gudun motar tare da sanya hannunsa 'daya yari'ke nata,yana murzuwa alamar tayi shiru,Cikin lallashi yace kukan ya isa haka mana Amarya ta koso kike nima inyine?, yafa'da yana langwa'bar da kai"Banza tayi dashi tare da cigaba da kukanta batare data kallesaba" ganin bazatayi shiru bane yasanya shi maida hankalinsa kan tukin insunje gida yayi lallashin dazatayi shiru.Suna zuwa kofar katafaren Gidan sa ya danna hong dasauri gate man ya wangale masa gate din,ya cilla hancin motarsa ciki"yana parking yamaida hankalin sa kanta ganin harzuwa wannan lokacin batabar kukan ba,bece da ita komai ba yabude motar yafito sannan yazagayo gefen datake yabude,kifito yace da ita yana me gyara tsayuwarsa bamusu tasanya kafa tafito fuskarta alullu'be"Hannunta yakama suka nufi sashen Nadiya "Tun sanda sukashigo gidan take hangosu ta window dakinta wani malolon bakin cikine yatokare mata zuciya ganin yanda Ahmad dinta keta rawan kafa akan wata ba itaba" Jin alamar shigowarsu parlour yasa takoma bakin tangamemen bed dinta dasauri ta kwanta tare da lumshe idanunta kamar me bacci.Da sallama dauke abakinsa ya shiga parlour ganin bega Nadiya a parlour ba yasa shi zaunar da Sukainat adaya daga cikin manyan kujerun dake cikin parlour,kallon ta yayi da Har izuwa yanzu batabar kukanba yace kiyi shiru barina kira Nadiya yanagama fadin haka yashige Ciki yana gyara malun-malun dinsa"Da sallama dauke abakinsa yashiga yana washe fararen hakoransa,bakin gadon yakara sa tare dazama agefenta hannu yasa yashafa fuskarta Cike da zumudi yace my Queen harkinyi bacci ne bakijirani ba?,Banza tayi dashi tanajin zuciyarta na ingizata anma haka tadanne dan intabiyashe zata fallasa kanta"sake shafa fuskarta yayi akaro nabiyu yace dan Allah My Queen kitashi baccin yayi wuri haka.
'Bude idanunta tayi tana mutsikawa tamkar me baccin gaske sewani ta'be baki tayi,murmushi yayi yamikar da hannunta tare dacewa zomije 'kanwarki najiranki, bamusu tamike hannunta yarike suka fito parlour,kan daya daga cikin kujerun sukazauna kamar zata shiga Cikin sa" gyaran murya Ahmad yayi Cike da nutsuwa yabude taron da Addu'a, kana yamaida kallon sa kan Nadiya data wani makalesa tamkar zata koma cikin sa"Cikin Nutsuwa yace Nadiya takanki zanfara ga amanar Sukainat nabaki ina kuma fatan zakikar ba kikulamin da ita domin nayaba da nutsuwarki dakuma kalamarki"Murmushi tasaki mecike da ma'anoni masu yawa tace bakada matsala Honey wannan me saukine anma fa bazan karbi amana ba sede zankula maka da ita"Alhamdulillah daman nasan baza'asamu matsala daga 'bangarenki ba domin nafi kowa sanin wacece ke Allah yabada ikon kula wa da ita Uwar gida sarautar mata"Banza tayi dashi batace komai ba domin duk abinda takeyi daurewa kawai takeyi anma jitake tamkar tashakesa yamutu dan jin zuciyarta take kamar zefashe.
Kallon sa yamayar kan Sukainat dakanta ke kasa yace Sukainat kece karama inaso kibi Nadiya sauda kafa, nasan halin Nadiya macece megudun zuciya dasanin yakamata bazata taba yin wani abinda zebata miki raiba danhaka kema sekiki yaye duk wani Abu da ze bata mata rai ko kuma yakawo muku sabani,domin na fada miki tunfarko bawai tashin hankalin bane yasanyani kara aure sedan raya sunnar ma'aiki (S.A.W)
da hanka banason fitina sannan banason kawayen banza masu zugaki ko kuma sucanza miki hallaya ina fatan kin fahimta.
Gyada masa kai tayi batare datace komai ba"kallon Nadiya yayi yace My Queen kokinada magana??murmushi tayi tace bakomai aikagama magana,sede ka manta baka sanarmata dacewa kar tatakura maka yaya ba domin kasan wasu amaren basason yayan miji!!kai Ahmad yajinjina Cike da gamsuwa yace wannan hakane Amarya inafatan kinji abinda Nadiya tace ko? Duk danasan bakida wannan halin anma kikiyaye,Kai tasake gyadawa akaro nabiyu batare datace komai.ba dan haka Ahmad yarufe taron da Addu'a kana yamike tare da nufar inda Sukainat take yarike hannunta,yana me maida kallon sa kan Nadiya yace My Queen seda safe...Dasauri tamike tarike hannunsa tare da langwa'bar da kai tace kaje zankawo maka ita aibe kamatace ace bawanda yarakataba"Wani farin cikine yamamaye zuciyar Ahmad Cike da farin cikin yanda Nadiya kemartaba duk wani abinda yakeso danhaka yasake hannun Sukainat yace toh my Queen gdy nike da wannan karramawar.Murmushi tayi tarike
Hannun Sukainat sukafita shi kuma yazauna yanamejin farin ciki na mamaye kowani kungu da sako najikinsa.Bude kofar ma daidaicin parlour tayi Wanda yayi masifar kyau komai na parlour golden and blue ne direct bedroom din ta tanufa da ita agefen madede cin gadonta tazaunar da ita kana tasanya hannu tabude mayafin dake kan Sukainat ta tsareta da 'kananun idanunta, Ahankali Sukainat tadauke kanta daga fuskar Nadiya domin bazata juri kallon tsanan datake Binta dashi ba....Barka da shigowa gidana Sukainat hakika nayabawa jajurcewarki dakuma nacinki duk da kasancewar nayi miki kashedin karki yi gangancin shigowa Gida na domin mallakina ne nida 'ya'ya anma haka kikasanya kafa kika shure toh kisani bauta kikashigo yi cikin gidan domin nafada miki sekin gwammaci zaman prison da wannan gidan, domin babu abinda zaki tsinta banda bakin ciki da takaici dakuma kuncin rayuwa"tanagama fadin haka tajuya tafice,hartaje bakin kofa tajuyo tace
karki dauki maganata kamar barazana ko kuma cika baki domin muddin nace zanyi abu ba makawa senayi dan haka ina miki fatan alkhairi"tanagama fadin haka tafice daga sashen...
Da kallo Sukainat tabi kofar hartafi ce Wani irin kuka tafashe dashi me tsuma zuciya.Jin alamar shigowar mutum yasanyata saurin share hawayen ta tare da dago kai Ahmad tagani da Nadiya hannunsu sarkafe dajuna"Kafin Ahmad yace wani abin Nadiya tayi saurin katsesa tahanyar cewa Honey da alama wannan amaryar taka akwai Kewa atare da ita yakamata inbaku waje kasamu daman rarrashinta,Amarya inamiki fatan"Ficewa tayi tana sakin wani killer smile Wanda ita ka'dai tasan ma'anarsa.
Zama Ahmad yayi agefenta tare darike hannunta cikin sweet voice dinsa yace pls Sukainat kibar kukan haka,hannu yasanya yashare mata hawaye tare dacewa tashikije kiyi alwala kizo muyi sallah mungode wa ubangiji" ba musu taziro kafafunta masu 'dauke da zara zaran yatsu Wanda sukasha kunshi ja da baki,bayin tashiga tadaura alwala sannan shima yashiga yayi yafito.Sallah raka'a biyu yajasu sannan yadafe kanta yayi Addu'a" tambayoyi yamata game da addini Cikin ikon Allah tabashi amsar komai.gashash shiyar Kaza da freshmilk yadinga bata ka'dan taci tace ya isheta,ba yanda beyiba takara anma taki dan haka yakyaleta" yaci yakoshi sannan yariketa sukaje toilet sukayi brush,bayan sunfito yakashe wutar dakin yabar deam night.
Kusa da ita yamatso yace kirage wannan kayan yayi nauyi dayawa yafa'da yana janye mayafin kanta"ganin bata hana shiba yasan yashi fara shafata tareda wasanni da sassan jikinta yana romance dinta cike da zakuwa"tuni jikinta yafara amsar sakonnin sa masuwuyar fassarawa Cike da ficewar hayyaci takamo bakinsa tashga kissing dinsa cikin salon dabatasan ta iyaba sosai suka birkicewa junansu,ganin hankalin tabetare da ita yasa Ahmad rabata da kayan jikinta tare dacire nasa kana yafara kokarin Neman hanyarsa,jin haka yasa Sukainat tafara turesa tana rokon yakyaleta ina Ahmad bemasan tanayiba burinsa yajefa 'kwallo cikin raga"wani irin Ihu Sukainat tayi..Wanda yasani razana najefar da alkalamina🀭




Nayi waje daguduπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ




_VOTE_ βœ…
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
















*_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_


*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*



*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*PAGE 11&12*πŸ–ŒοΈ


________________________πŸ“–Bayan komai ya kammala ne Ahmad yaita lalla'ba Sukainat hartayi shiru,sannan yakaita toilet cikin ruwan zafi da gishiri ka'dan yasanya ta aciki bayan kamar 30mins yacireta sannan tayi na tsare tafito tana tafiya Ahankali simply gownt tasanya tada da sallah,bayan ta idar ne ta daga hannu bibbiyu tana rokon Allah yabata zaman lafiya dawwa mammiya da kwanciyar hankali me daurewa atsakaninta da mijinta, sannan yatsaresu daga sharrin makiya,tashafa lumshe ido tayi tana jin bacci nafusgarta"Bata ankaraba taji andauketa kan gado Ahmad ya kwantar da ita bayan yacanza bedsheets,din fuskarta yashafa yace sorry my suky na wahalar dake ko?kai tajuya Cike da kunya batare datace komai "shima murmushi yayi yashafa sajen fuskarsa"zuwa yayi yasanya jallabiya kana yatada salla bayan ya idar yaje gefenta ya kwanta tare da janyota jikinsa dahaka bacci me da'din gaske yayi awungaba da Ahmad yayinda Na wahala yadauki Sukainat....Se misalin karfe 9:45am Sukainat tafarka daga wahallen baccin daya dauke ta,'kura masa dara-daran idanunta tayi tana kallon lumsassun idanunsa dake lumshe ga sajensa daya kwanta luf-luf Wanda yakawata kyawun fuskarsa madede cin bakinsa takurawa idanu tana kallo yanda yatsukesu sun sake yin pinch color dasu" Hannu biyu tasanya tarufe fuskarta tana murmushi sakamakon tuna abinda yafaru atsakaninsu,jitayi anjanye hanna yenta dasauri taware dara-daran idanunta Wanda suka kumbura saboda kuka"Gani tayi Ahmad yakafeta da firgitattun idanunsa masu narkar da zuciyar ko wacce diya mace.Iskan bakinsa yahura mata a idanunta yace kallon ya isa haka mana yafada yana aika mata da wani irin kallo mecike da so"Sunkuyar dakai tayi Cike da kunya,'kafafunsa yazuro kasa yace bari na ha'da miki tea kisha sekisha pain relief ko?,"kai tagya'da masa alamar toh"Ficewa yayi yanufi corridor daze sadashi da kitchen dake tsakanin sashen nasu"Tsaye ya hangota tabaiwa kofa baya Arish din datake soyawa se konewa yake da alama batasani ba tazurfafa cikin tunani,cikin sauri yakarasa cikin kitchen din tare da kashe gas din.kafa'dunta yarike Cike da damuwa yace My Queen wani irin tunani kike haka dakikeson kashe kanki dasauri yaja baya ganin yanda idanunta suka koma sunyi wani irin jaaa dasu sunsake kankancewa gawani irin kumburi dasukayi.Tallafo fuskarta yayi da hannu biyu cikin dimuwa yace meyasa meki my Queen waya miki haka?,yafada yana bin fuskarta da matsanancin mamakin abin daya sameta daga daren jiya zuwa yau yanda suka koma haka...Itama ido tazuba masa Cike da takaicinsa jitake kamar tacika masa wuka awuya,koya yi zaton batasan abinda yafaru tsakanin sa da makirar Amaryarsa adaren jiya bane wai Ahmad ne ze Iya ha'da shimfida dawata kuma tana raye.Ka fadarta yajijjiga Cike da damuwa yace kibani amsa mana my Queen ina magana kinyi shiru."Dede ta nutsuwarta tayi tare da kakalo murmushin dole wanda bewuce saman la'b'ban taba tace calm down Honey am fine,nothing happen to me bleive me...be bari takarasa ba yakatsata dacewa taya zakice kina lafiya bayan banga alamar hakan atare dakeba.
Shitttt tace dashi tana daura hannunta asaman labbansa,alamar yayi shiru"kamar wani soko haka yayi shiru se ido dayake Binta dashi"talakace masa hanci tayi tace let me tell u exactly what happen:Kafin yace Wani abin tace, Ina cikin bacci da daddare nayi mafarki wai wata mata wacce bansan wacece ita ba tana zugaka kasakeni kancewa ni bamatar arziki bace kuma idan bakasakeni ba duk abinda yasameka kaikajawa kanka,ganin duk maganan data fada maka kaki yarda yasanyata kaika wajen boka",kasan meyafi girgizani acikin mafarkin ta tambayesa tana me kallon yanda yanayin sa yasauya baki daya zuwa tashin hankali"kai ya girgiza kai yayi Cike da damuwa yace a'a"Sukainat itace bokar kuma itake son rabamu,Wannan shine sanadiyyan dayasa kaganni awannan halin wannan abin bakaramin sake daga min hankali yayi ba ina tsoron tarabamu"ta'fada tana share hawayen daya zubomata.
Kamar saukan aradu aka haka yaji kalamanta,dan haka ya daure fuska yace kidena irin wannan kalaman Nadiya domin mafarki ba gaskiya bane saboda haka karki sake danganta Sukainat da boka sannan kirufe wannan maganar anan" nasan bazewuce sharrin shaidan bane anma taya Sukainat zataso rabamu"?rau rau tayi da idanu tace dalilin dayasa naki fada maka kenan anma kamatsamin tayaya kake tunanin nizan kwashi sirrinka infadawa wasu kada fa kamanta kamar 'kanwa haka nadauki Sukainat anma kaida bakinka kake fadin haka takarashe cikin rawan murya,Kai yadafe yace nifa bahaka nake nufi ba dan haka kibar maganan kawai.
Yana gama fadin haka ya dauki cup ya ha'da tea mai kauri yafice batare daya sake cewa da ita komai ba.
Da kallo tabisa haryafice 'kwafa tayi tace lokacin kane Ahmad.Gas din takunna tacigaba da soya arish da kwai bayan tagama tahade komai a dining area dake sashenta sannan tashiga toilet ta watsa ruwa kasancewar 'ya'yan ta basunan suna gidan mahaifiyar ta.
Yana shiga yaga batanan zaman sa badadewa tafito daure da towel wanda tsawonsa yakai gwiwarta sekuma Wanda tarike a hannunta tana goge kanta"Ido yakura ma santala santalan cinyoyinta"Hannu yasanya yashafi sajen fuskarsa, ita kuwa tsayawa tayi takasa karasawa sakamakon kafeta dayayi da sexy eyes dinsa "bata ankaraba taji yajanyota kansa, dasauri tasanya hannunta tarike towel dinta jin yana kokarin sincewa.Jitayi yafara yimata cakulkuli batasan time datafara 'kyal'kyala masa dariya ba tana kokarin 'kwatar kanta"Fararen hakoranta yazubawa idanu ganin yanda suke haske" Jisukayi anturo kofar bedroom din, dasauri duk sukajuya Nadiya sukagani tsaye takafesu da idanu tamkar zasu zazzago.....










_VOTE_ βœ…
_COMMENTS_
*_AND_*
_SHARE_












*_ESHAA CE~*_πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_


*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*




*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*PAGE 13&14*πŸ–ŒοΈ


________________________πŸ“–Kawar da kai Ahmad yayi tare da janyo Sukainat tafado kansa, ha'de bakinsu waje 'daya yayi yana bata wasu hot kisses masu wuyar mantawa, yayinda yatura 'daya hannun cikin sumar kanta dake da damshi yana yamutsa gashinta"Cikin karfin hali Sukainat tajanye bakinta daga nasa tayi kasa da kanta cike da matsanancin kunya.
Hannu Ahmad yasanya yashafi sajen sa yana sakarmata dawani killer smile,cike da zumudi yasake mika hannu zejanyota taja baya dasauri,tana girgiza masa kai alamar yabari,Cike da begenta yace pls me da'dina kibarni insha wannan sweet mouth din, shiru tayi taki cewa komai kuma taki matsowa kusa dashi"Kamar Wanda akace ya'daga kai yahango Nadiya tsaye kamar wacce aka dasata awajen idanunta sunka'da sunyi jawurr dasu fiye dana farko.
Mutsits-tsika ido yayi domin tabbatar wa shin itace ko idanunsa ke masa gizo"innalillahi wa'inna ilahi raji'un yake maimaitawa aransa, zahiri Nadiya ce atsaye kenan in haka da farko ita yagani be gezau idanunsa kemasa ba,?ya tambayi kansa"wani matsanancin kunyarta da shakku ne suka diran masa a zuciya"Anma dake namijin duniya ne se yada go kansa Cikin basarwa yace My Queen karaso mana kikatsaya a can, shiru tayi takasa cemasa komai sema sake kafesa datayi da kananun idanunta,sake cewa yayi pls come in"Da 'kyar ta Iya cewa no basena shigoba nazo ne in sanar daku breakfast is ready tanagama fadin haka tajuya afusace tabude kofar tamkar zata tashi sama.Dasauri Ahmad yamike zebi bayanta"hannunsa Sukainat tarike tana kallon yanda fuskarsa ke bayyanar da tashin hankali karara,cikin dakewa tace ina zakaje ya Ahmad?, Bakiga yanda Nadiya tafita bane ranta a'bace yafada yana kokarin mikewa janyosa tayi yafada kan bed din,cike da mamaki yake kallonta"Kau da Kai tayi tace agaskiya bazaka bitaba domin ita tashigo dakin batare datanemi iziniba,aganina ita yakamata tabamu hakuri bamu ba saboda haka bawani hakurin dazaka bata.
Har yabude baki daniyyan magana tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login