Showing 48001 words to 51000 words out of 52375 words
ke adurkushe hannun tasanya tasakalo wuyan Ahmad tare da hade bakinsu waje daya...
Idanu Suky ta runtse dan bazata Iya juran ganin su ahaka ba jitake kamar zuciyar ta ze fashe ga azaban ciwo gakuma takaicin dasuke sake kunsa mata.
Seda Nadiya tayi kissing dinsa san ranta kafin tajanye bakinta daga nasa suka nufi hanyar fita,juyawa Ahmad yayi yace"sekifito inkingama zaman yana gama fadin haka ya karasa ficewa.Hannu tasanya tashare Zafafan hawayen dasuka zubo mata akaro Na barkatai seda tashiga motar yaja suka tafi...
Suna zuwa asibitin aka karbeta tare dabata temakon gaggawa,kana suka tsaida zubar jinin Cikin ikon Allah cikin na nan sede yana cikin hatsari dole sekun kula dashi yanda yakamata dan inde bahaka zaku Iya rasashi ako yaushe cewar Dr yana kallon Ahmad...Kai Ahmad ya girgiza cike da takaici yace"Dr wannan daka ke gani bakaramar munafukace domin ita dakanta tayi kunyurin zubar da cikin.
Kallon mamaki Dr yamasa kafin yace"anma mu abinciken da mukayi bamuga wata alamar magani tasha domin tazubar da cikin Hasalima hakan yafaru ne ta dalilin,faduwa ko duka,kokuma tabugu dawani abin.
Cike da takaici Sukainat tadago kai tace"Wallahi kazafi yayimin anma banyi yunkurin zubar da cikina ba hasilama inason sa fiye da kaina,cikin rawan murya takarasa cewa matarsa ce tayi min duka acewarta seta zubar da cikin!.wani Kallon tsana Ahmad yawatsa mata kafin yace"Wato annamimancin naki haryakai haka ko??
Rai abace Dr yadaga masa hannu Wanda akalla shekarun sa zasukai sittin yace"Bawan Allah kaji tsoron Allah kada kazalunci baiwarsa saboda kaga tana karkashin ka taya matarka za tayi mata haka anma bazaka dauki mataki ba sede ma kabita da sharri??.shiru Ahmad yayi batare dayace komai ba, hakan dayayi yasake tabbatarwa da Dr cewar bashida gaskiya.Fada Dr yaimasa sosai kafin yace" kuma in suka sake yimata haka zehadasu da hukumar hakkin kare mata.Cike da farin ciki Sukainat tayi masa godiya shi kuwa Ahmad ficewa yayi batare dayace"komai ba bayan sa suky tabi ajikin mota tahango yajingina yana jifanta da mugun kallo" seda hanjin Cikin ta yakada anma tadaure ta karasa cikin hargagi da fada yace"...
Not editing kuyi hakuri da typing error sabgogi sunyi min yawa
_VOTE COMMENTS AND SHARE_
*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???.*
_(True life story)_
_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_👇🏻
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah ka jikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 57&58* 🖊️
______________________📖Shiru yayi yarasa abin cewa,hakika bazeso yayi mata kazafi agaban idanunta ba,Kasancewar shi ba makarya ci bane haka zalika basa shiri da makaryaci ko waye.
Kana bazeso ran Nadiya yabaci ba domin yasan muddin be fadi abinda tasanya shi ba ya boni,Uwa uba kuma Alh Ali shin dawani ido ze kalli Baffansa yakarya ta kansa!!.Kasa da kansa yayi yayin da da zufa yashiga karyo masa tako ina asassan jikinsa tamkar babu AC adakin. hakika yana cikin tsaka mai wuya...Murmushin manya Alh Ali yayi yana nazartan yanayin 'dan nasa hakika babu tantama acikin abinda yake zargi wato Ahmad bashi da gaskiya koda yanda yayi shiru ya yaki cewa komai ze tabbatar maka babu gaskiya acikin kalaman sa,anma dan yasake tabbatarwa da kansa zargin dayake seyayi gyaran murya tare dacewa"Ahmad kaina ke sauraro ko baka da abin fada ne intafi dan kana batamin lokaci...
Ahasale Nadiya tace"Dan Allah inbaka da abin fadi intafi kaje katasoni ina kwance sannan yanzu kawani yi kasa da kai kamar me daukan darasi.Kai Alh Ali ya girgiza yana jinjina rashin tarbiyanta Sam bata ganin kowa da mutunci, shiyasa tun farko suki auren sa da yarinyar anma yanace dase anyi.A lokacin dayasanar musu daze kara aure bakaramin farin ciki sukayi ba,sede kash!!auren ma be amfaneshi da komai ba se halaka dasake tabewa.Zazzafar ajiyan zuciya yasauke asanda yasauke idanunsa akan Sukainat da kanta ke kasa,aransa kuwa yana mai rokon Allah daya kawo musu karshen Wannan kuncin dasuke ciki...
Sukainat kuwa cike da mamaki take binsu da Kallon dan haryanzu takasa fahimtar ainihin abinda yasa aka tarasu..Muryan Ahmad ne yakatse mata tunanin datake asanda ya shiga maimaitawa Alh Ali abinda yafada awaya,kallo daya zakamai kagane bashida cikakkiyar nutsuwa sakamakon zufar da jikinsa ke fitarwa dakuma yanda jikinsa ke rawa..Boyayyar ajiyan zuciya Nadiya tayi asanda yagama maimata maganan.Shi kuwa Alh Ali haryanzu idanunsa nakan Ahmad baya ko kyaftawa,bayan yagama jin jawabin Ahmad dinne yamaida Kallon sa ga Sukainat da idanunta suka cika da kwalla jin kazafin daya mata...
Cikin taushin lafazi Alh Ali yace" 'yata kinji abinda mijinki yace kina aikata masa shin hakane??,Nadiya jitayi zuciyar ta naneman tarwatse wa saboda takaici lalle ma wannan mutumin akwai dan rainin wayo,taga alamar seta,saita masa hankali zasu dedeta tafada aranta.
"Hawayem da take kokarin hana kanta ne sukazubo akan innocent face dinta, shin wai wani irin kiyayya Ahmad da Nadiya suke gwada matane shin meta tsare musu arayuwar duniya dasuke son saka kiyayyar ta a zuciyar kowa!?,tatambayi kanta bata da mebata amsa dole sesu,hakan yasa tadago kanta ahankali domin tambayar su menene dalilinsu na son tozarta ta a idanun Duniya.Anma se muryan Alh Ali ya katse ta sakamakon sake maimaita mata tambayar dayai mata akaro nabiyu.
Kanta akasa batare data dago ba tasanya hannu tashare hawayen dake ambaliya afuskarta Wanda batasan ranan daza sudena kwaranya daga idanunta ta ba.Zazzafar ajiyan zuciya tasauke kafin tace" Wallahi Baffa narantse da Wanda raina ke hannunsa ban yi abinda yace na aikata ba kazafi suka min hasalima su sukayi min laifi...Nantashiga zayyane masa komai tundaga ranan daya zo yayi musu nasiyya harzuwa yau da Nadiya tayi yunkurin zubar mata da ciki takarashe hawaye masu zafin gaske nabin kyakkyawar fuskarta...Kai kawai Alh Ali kai girgizawa cike da matsanancin bacin rai,shiru falon yadauka nawasa mintuna ba abinda ke tashi aciki banda kukan Sukainat dakuma AC da ke aiki...Cikin taushin lafazi Alh Ali yakira sunan sa yaname kafesa da idanunsa masu cike da haiba da kwarjini.
Jiki amace Ahmad ya amsa batare daya dago kansa ba"Murmushin takaici Alh Ali yayi kana yace"Dan girman Allah Ahmad idan kasan baza ka iya adalci a tsakanin matan kaba to ka sauwakewa Sukainat domin kar yazamto kana zaluntar ta inhar Kasan baza ka iya zama da mata biyu ba,saboda ni bazance ka saki Nadiya saboda Sukainat domin Nadiya uwar ya'yan kace, haka zalika bazance kasaki Sukainat saboda Nadiya ba anma zanso ka ka kwatanta adalci atsakaninsu,domin kana da 'Ya'ya mata komujima ki mudade abinda kayi wa yar wani shi za'ayiwa taka.Yana gama fadin haka yamike tare da Kallon Sukainat da harzuwa lokacin batabar kuka ba yace"yata kici gaba da hakuri mai hakuri shike dafa dutse harya sha romonta Insha Allah kece danasara. yanagama fadin haka yafice daga falo batare daya amsa seda safen da Ahmad ke masa ba...
Afusace Nadiya tace"Wannan ai renin wayo ne Wallahi idan bakajawa Wannan kawun naka kunne ba sena yimasa abinda baya zato,tana gama fadin haka tamike tabar falon tana mai jin tsanar mutumin har cikin ranta..Wani irin kallo Sukainat tawatsa Ahmad kafin tamike tabar falon.Rasa wani irin kallo take binsa dashi,kwafa yayi kafin yamike jiki asabule yabi bayantan ta.Tana shiga daki tacire hijab din yarage daga ita se dan figigin rigan baccin dake jikinta,wutan dakin takashe tana kokarin kwanciya taji anrungumeta tabaya,Amatukar tsorace tabude bakinta zatayi ihu yayi saurin sanya tattausan tafin hannunsa yatoshe mata baki,kana yakunna hasken dakin yana jifanta dawani irin kallo mecike da nuni da zallan feeling. Rai amatukar bace tashiga kokarin turesa daga jikinta anma takasa kasancewar karfin ba daya ba,murmushin mugunta yasake tare da wurgata kan gadon yabita ya danneta.Kuka tafashe dashi tace"kadagani Ahmad,bana son abinda kakeyimin natsaneka mugu azzalumi mayaudari maha'inci Wallahi Allah baze barka ba abisa zaluncin da kayi min....bata karasa abinda zata fada ba yakifeta da mari rai abace yace"Duk abinda zaki fada sede ki fada kazama kawai,ke harkin kai matsayin dazaki dinga hada jikin ki dani banza kucaka,yana gama fadin haka yahade bakinsu waje daya,kukan bakin ciki tafashe dashi tana turesa daga jikinta!,ganin zata bata masa lokaci ne yasanya shi danneta da karfin sa tare da yaga figigin rigan baccin dake jikinta atake manya manya breast dinta suka fiti suna tsole masa idanu,cike da shauki yasanya bakinsa yafara yimata wani irin tsotso cikin ficewan hayyaci yashiga murzata cike da mugunta.Sukainat kuwa sandare masa tayi kamar gunki taki temaka masa shikadai yayi kidinsa yayi rawansa,Wani irin tsanarsa ne yamamaye mata zuciya cike da danasanin auren sa.
"Ahmad kuwa cike da mugunta yadinga murzanta San ransa duk da yasamu nutsuwa hakan besa yasarara mata ba seda yagama galabaitar da ita..kafin yamike yafita zuciyar sa wasai,dan rabon dayasamu irin Wannan nutsuwar ya mance...
Dakyar ta Iya mikewa tashiga toilet tana share hawaye,ruwan zafi tahada tashiga seda tagasa kanta sosai kafin tayi wankan tsarki me hade da alwala tafito gefen gadon taratse ta kwanta tana jin wani irin tsanar Ahmad aranta da haka bacci yadauke ta cike da mafarkai marasa dadi...
Ahmad kuwa nafita direct sashen Nadiya yashiga cikin sa'a tayi bacci hakan yasa shi wucewa toilet yayi wanka yana fitowa yasanya kayan baccinsa metaushi ya kwanta kusa da Nadiya tare da janyota jikinsa dahaka bacci yadaukesa zuciyar sa wasai....
Washe gari:Bayan ta idar da sallah agajiye tafito tanufi kitchen duk dacewa batajin karfin jikinta hakan be hanata hada musu breakfast mai rai da lafiya bayan tagama tajere a dining kana,tafice compound din tayi duk wani aiki da tasan itakeyi seda ta kammala kafin tade bo kayanta da sukayi datti tawanke.falon takoma batasamu kowa aciki ba se wani guntun arish plate wanda befi akirgaba da ruwan tea empty akofi Wanda ta tabbata nata ne,Ahankali tasanya hannu tadauka tanufi bedroom dinta zama tayi tanaci tana hawaye na zuba daga idanunta tana mai addu'ar Allah yakawo mata karshen Wannan halin datake ciki ahaka tagama ci takai plate din kicin tahada da Wanda sukayi amfani dashi tawanke.Bakiyat tanufa kayanta da tawanke takwaso agajiye tazubasu akan gadon tafara ninkewa....Tana cikin ninkewa ne taga mutum tsaye akanta fuskar sa amurtuke kamar ko yaushe,Jitayi zuciyar ta yatsinke anma seta daure tace"Wani abun kake bukata ya Ahmad??, tafada adake.
Murmushi yasakar mata Wanda yayi matukar bata mamaki da al'ajabi domin rabon dataga irin Wannan murmushin afuskarsa har ta mance lokacin, Muryan sa ne yakatse mata tunani a lokacin daya kecewa Wannan kayan tafiya Gida kike shiryawa?,Cike da rashin fahimtar tambayar tasa tace bangane me kake nufi!,Fara'ar fuskarsa yarage yana maka mata harara yace me abin rashin fahimta acikin maganata yakarashe adan fusace.Kanta ta sunkuyar kasa batare da tace"komai ba tana nazartan kalaman sa"Tunda baki fahimta ba barina fahimtar dake ina nufin gidan ku zaki tafi kike shirya kaya!?.
Kai ta girgiza hawaye nataruwa a idanunta aranta tace wannan wace irin tambaya yake mata"Cikin sanyin murya tace"A'a wankesu nayi shine yanzu nake ninkewa takarashe cikin raunin murya!!, tsaki yaja tare da maka mata harara,kafin yazagayo gabanta yatsaya suna fuskantar juna,Ahankali tajanye idanunta daga nasa dan babu abinda take hangowa acikin kwayar idanunsa banda tsantsar-tsananta.
So nake kitambaye ni abinda ko wace mace ke tambaya awajen mijinta idan tanaso takoma gidan su,yafada babu alamar wasa atare dashi.Cike da mamakin furucinsa take Kallon sa cikin dakewa tace"ni babu abinda nake bukata,In kincika yar halak dan Allah kitam bayeni Sukainat,banza tayi masa tacigaba da ninke kayanta.
Har tagama yana tsaye yana jifanta da kallon datakasa fassara na menene,tsaki mai karfi yaja yace"jarababbiya kawai da kitam baya mana idan ba tsoro ba yafada asanda yake fita daga bedroom din...
Inmalillahi wa'innah ilahi raji'un tafada asanda kuka yaci karfin ta shin Wannan wani irin jaraba ne shin wai wani kalar kiyayya Ahmad kenuna mata!?azatonta kowani irin laifi tayi masa beci ace yana nuna mata irin Wannan kiyayyar ba koda kuwa ace auren dole akayi musu bare ace auren soyayya sukayi anma bashida makiyiyar data wuceta,kan gado tafada tana Jan zuciya,hakika da ace hawaye Na karewa to da tuni nata sunkare,dahaka baccin wahala yadauke ta batare data shirya ba...
Bata fuska tayi asanda yagama labarta yanda sukayi da Sukainat cikin daure fuska tace" kana nufin ka fada mata haka!?Cikin rawan jiki yagyada mata kai alamar eh"tsaki Nadiya tayi tace"tunda nake bantaba ganin mace mai naci irin Wannan matar takaba,koda yake banga lafinta ba domin daka koreta Aida tuni tatafi anma dake kaima nason zama da ita shine kakasa tabuka komai. Cikin sauri yace"Wallahi my Queen bayanda zanyi ne anma nima nagaji dazama da ita!.hmm nifa banga amfanin zama da macen dabata da ibada ba,dan ko a musulunci idan mace bata sallah be hallata kazauna da ita!!..
Rai abace yakalleta yana hura hanci yace"kina nufin bata ibada shine baki fada min ba!?Dan marairace wa tayi tace ai tsoron fada maka nake,tafada tana kunshe dariyar ta.Daga yau karki sake bata abinci har natsawon kwana biyu seta fara sallah kafin tafaraci.
Haba Honey anya hukuncin be yimata tsauri ba kuwa??,hade fuska yayi cikin bada umarni yace"nagama magana yafada asande yake ficewa daga dakin...
Se misalin karfe biyu ta tashi toilet tashiga tawatsa ruwa kana tadaura alwala tazo ta tayar da sallah bayan ta idarne tanufi kitchen tahada musu jollof din taliya dayaji kayan hadi se kamshi ketashi kana tajere komai a dining kafin tanufi bedroom din ta.Ga mamakinta data fito bataga abincin taba,bedroom din Nadiya tanufa tayi knocking daga ciki taji anbata izinin shiga.Da sallama dauke abakinta tashiga,daga kofar dakin tatsaya tace"Aunty ina abinci na!?Murmushi Nadiya tayi tace "Au Dadyn rufy bece miki komai ba ne?kai tagyada alamar eh.Ayyah ainayi zaton yasanar dake domin yace kar asake baki abinci senan da kwana biyu!,Rai abace Sukainat tajuya tafice batare datace komai ba...
Yau kimanin kwana biyu Sukainat bataci abinci ba kamar yanda yafada Iya galabaita ta galabaita,gashi babu abinda suka ragemata na bautar datake musu...Kwance take atsakiyar dakin tana fitar da numfashi da kyar, da sallama abakinsa yashiga dakin tsayawa yayi akanta yace" kin shirya yin sallah yau abaki abinci??.Cikin karfin hali tamike hijab din ta dake kan kofa tadauka tasanya tare da daukar wayarta trolley tajanyo tashiga sanya kayanta duk yana tsaye yana Kallon ta seda tagama shiryawa tadago rinannun idanunta dasuka dafe dakuka tace"ya Ahmad zan barmaka gidanka ayau din nan insha Allah idan har ina cutar dakai azaman takewar auren mu zakagani idan ma bana cutar dakai zakagani bayan bana nan, badan komai zanbar gidan kaba sedan kazafin dakayimin kancewa bana sallah kaje Na barka da mai kowa mai komai shize yimana sakayya tana gama fadin haka tafice daga gidan tana hawaye....Da kallo yabita har tafice,cikin daga murya yace"kifi ruwa gudu...
Tafiya sosai tayi kafin ta Isa bakin titi lokacin tagalabaita cikin ikon Allah tana karasawa tasamu adaidaita hawa tayi tare dasanar dashi inda ze kaita bamusu yace"tashiga,da bismillah dauke abakinta tashiga jin gina Bayan ta tayi tana jin jiri nadi barta addu'ar ta daya Allah yakaita gida lafiya koda mutuwa ne ta mutu agaban iyayenta,kunna adedetar yayi suka tafi.
Suna Isa tasauka tabiyasa hakkin sa kafin tashiga gida da kyar take Iya daga kafanta,azaure sukaci karo da Malam Ahmadu dake shirin fita sallan la'asar amatukar galabaice tatsugunna tagaishesa yayin da muryan ta ke sarkewa saboda tsananin yunwar dake damunta gatarin gajiya da tashin hankali datake ciki.Dasauri Malam Ahmadu yatareta izuwa jikinsa ganin zata fadi.Dagota yayi yariketa ajikinsa suka shiga gidan, direct dakin Ummi yanufa da ita ya ajiyeta yana mata sannu cike da damuwa,Da kyar take Iya Jan numfashi yayin da idanunta ke Neman kafewa asama,cikin sauri Ummi tashafa addu'ar tajuyo garesu cikin tashin hankali,da dimuwa,fita waje tayi ta debo ruwa akofi tashiga Shafa mata afuska tare da tofa mata addu'o'i,Ahankali idanunta suka fara dawowa dai-dai sejan ajiyar zuciyar datake akai-akai.Malam Ahmadu kuwa yakasa tabuka komai banda kafe yar tasa dayayi da idanu cike da matsanancin tausayin ta, ganin duk yanda tawani jeme tamkar wacce ta warke daga cutar amai da gudawa...
Cikin shakakkiyar Muryan ta da befita sosai tace"Ummi yunwa nakeji tafada jikinta na rawa tamkar mazari tsaban yunwar dake addabar ta.Dasauri Ummi tamike ta dauko flaks din dake cike da ruwan zafi tazuba mata tea kana tadauko peak sachet da Milo na sachet,tazuba mata,sesetawa tayi sedataga zafin yayi dai-dai kafin,takarasa inda take takafa mata kofin abakinta cikin sauri tafara sha,seda tashanye tass kafin tajanye bakinta ajikin kofin tana maida numfashin wahala yayinda taji zuciyar ta natashi tamkar zatayi amai...
Ahankali Ummi tamaida Kallon ta ga Malam Ahmadu daya zubawa Sukainat ido ko kyaftawa bayayi cikin sanyin murya tace"Malam kayi sallan kuwa?, Cikin yanayin damuwa yace"Yanzu zanje inyi yafada yana asanda yake mikewa,ficewa yayi yanufi masallaci lokacin dayaje Har an idar hakan yasa yayi shi ka'dai bayan ya idarne yashiga addu'o'i kan Allah ya dedeta tsakanin Sukainat da mijinta.
Sukainat kuwa idanunta talumshe ajikin mahaifiyar ta yayinda taji nutsuwa naratsa kowani lungu da sakon dake jikinta hakika iyaye rahama ne duk Wanda yarasa su toh yayi kuka musamman Uwa domin wata garkuwa ce acikin rayuwar yayanta Wanda in babu ita rayuwar su bakomai bane.daga ta Ummi tayi daga jikinta tanufi kitchen tuwon masara miyan danyen kubewa tazuba mata,Hannu baka hannu kwarya Suky tafara ci.Sosai Ummi tayi mamakin yanda takecin abincin tamkar mayunwa ciya tass tacinye,tace akara mata,Karo mata Ummi tayi sannan tabata ruwa tasha,baki daya tacinye abincin da ruwan kana tashiga sauke ajiyan zuciya...
Kai kawai Malam Ahmadu da Ummi ke jinjinawa a lokacin da Sukainat tagama sanar musu da halin datake ciki dakuma irin kuncin datake fuskanta bata boye musu komai ba domin batada kamansu kaf duniya yazama dole tasanar musu da sirrinta...Cike da dattako Malam Ahmadu yace"Allah yarufa asiri yakuma kiyaye gaba,sannan kidage da addu'a kan Allah yazabar miki abinda yafi zama alkhairi,Iya abinda yafada kenan yafice daga dakin duk Iya abinka bazaka gane yanayin da fuskarsa keciki ba"Ameen Ummi ta'amsa tana maijin tausayin yar tata....
Cikin dare Sukainat tafarka dawani matsanancin ciwon ciki Wanda dole yasanya su nufar asibiti, suna zuwa aka karbeta tare da bata temakon gaggawa kana akayi mata alluran bacci.se asannan Malam Ahmadu da Ummi suka samu sukaje sukayi sallan asbah kasancewar lokaci yayi...lokacin dagari yawaye Dr yakira Malam Ahmadu yaita masa fada kan yunwar da akabarta dashi natsawon kwanaki.hakuri Malam Ahmadu yabasa,rubuta masa magunguna yayi yace"yaje yasayo karba Malam Ahmadu yayi tare da ficewa...
Yau kimanin satin Sukainat daya a asibiti alhamdulillah jikinta yayi sauki kuma Har yau Ahmad bene mesuba haka zalika iyayenta ma basu