Showing 51001 words to 52375 words out of 52375 words
nemesaba,da yammaci aka sallame,tsaye suke abakin asibitin suna Neman adedeta,wata motace tazo gabansu ta tsaya,da kallo sukabi motar ganin ya tsaya asetinsu Ahankali mamallakin motar ya bude glass din,da sauri Sukainat takawar da kai ganin Hema dawani da alama itace tasaci tsayawa.Cike da Iya barikanci tace"sannu Sukainat kushigo inrage muku hanya mana?,akuma lokacin ne adedeta yakaraso wajen Malam Ahmadu ya tsayar dashi,cike da kulawa Ummi tace"mungode yata anma gashi munsamu abin hawa,Sukainat kuwa dauke kai tayi kamar bata gan taba suka shiga napep din yaja sukatafi"Ahankali Wanda ke tukin yace"ina kika santa yafada fuskarsa babu walwala"Murmushin yaki hema tayi tace sweetheart kishiyar Nadiya ce baka ganeta bane?tabe baki yayi batare dayace komai ba yaja motar,...
Nadiya dake kwance kan kushin tafashe da dariya tace"kai kawata talauci beyi ba Wallahi!!,ita hema dariyar tayi tace"kede bar matsiyata suna tsaye se rana sukesha anma dayake ta Iya girman ka shine taki shiga inrage mata hanya,Anma suna fama da talauci kingansu kuwa tafada asanda take sake fashewa da dariyar keta,ahaka suka gama wayar Wanda duk hiran aibanta Sukainat da iyayenta suke kafin daga bisani suyi sallama.
Ahmad nadawo wa Nadiya tasanar dashi cewa hema taga Sukainat a asibiti,kana cikin duniyanci da kissa tace"Honey yakamata muje mudubasu"hannu yadaga mata da alamun bacin rai afuskarsa yace"babu inda zanje tunda bani nadaura mata rashin lafiyan ba sannan basu kira sun sanar dani ba mekikeso inje in musu?...zata sake magana yadaga mata hannu alamun besan jin komai hakan yasa taja bakinta tayi shiru....
Abangaren Sukainat kuwa bakaramin kulawa take samu daga wajen iyayenta da yan uwanta ba taciko tafara maida kibarta,baki daya tacanza acikin sati biyu abinda ranta keso shi take ci kowa burinsa yaga ya faran ta mata rai Sofia nazuwa tadebe mata kewa"batada matsala ta kowanne fanni se kewar mijinta dake damunta....Ganin har yau kimanin sati biyu da zuwanta Gida babu Wanda yazo bikonta yasanya Malam Ahmadu kiran layin Alh Ali domin yaji ta bakinsu, lokacin da kiran yashiga wayar Alh Ali suna tare da matar sa Hajiya Bilki,mika masa wayar tayi,Picking din call din yayi aransa yana addu'ar Allah yasa bawani rashin mutunci Ahmad yasake yimusuba.sallaman da Malam Ahmadu yaimasa ne yakatse masa tunani cike da dattako suka gaisa,shiru ne yadan biyo baya kafin Malam Ahmadu ya numfasawa kana yalabar tawa Alh Ali abinda ke faruwa dakuma da lilin ki ransa da yayi.Cike da matsanancin kunyar sa Alh Ali yace"Dan girman Allah Malam kayi hakuri abisa abubuwan dasuke faruwa Insha Allah ganin zuwa gidan yanzu, yana gama fadin haka yakashe wayar tare da maida Kallon sa ga Hjy Bilki data tsaresa da idanu,da alama taji komai... Cikin jimami tace ooh Alh nikam yaushe yarinyar zataji dadi ne yaushe Ahmad ze nutsu yagane mai kaunar sa dan Allah?..Alh Ali bece komai ba yamike yana cewa inna dawo mayi maganar yafada asanda yake ficewa daga falon.
Direct gidan su Sukainat yanufa yana parking yakira wayar Malam Ahmadu tare da sanar masa da yakaraso.Ba dadewa Malam Ahmadu yafito yaimasa iso zuwa dakin dake zaure,zama Alh Ali yayi suka sake gaisawa cike da mutunta juna,shiru ne yabiyo baya nawasu mintuna kafin Alh Ali yace"Dan Allah Malam kayi hakuri abisa abubuwan dasuke faruwa Wallahi bani da masaniya komai dan yaune kahaifeshi baka haifi halinsa ba.murmushin karfi hali Malam Ahmadu yayi kafin yace"haba de Alh halin dan yau aise addu'a dan haka karka damu fatan mude Allah ya dedeta tsakanin su yafada Cike da kulawa.
Ameen thumma ameen "Alh Ali ya'amsa asanda yake sanya hannunsa a aljihu wayarsa yaciro number Ahmad yafito dashi yadanna kira.
"Lokacin dakiran yashiga Har Ahmad yafita coumpound zeshiga mota seya tuna daya mannata wayarsa a falo shine yasanya Nadiya datayi masa rakiya da takoma tadauka masa akuma Dede lokacin ne Alh Ali yakira...Picking call din tayi tare dayin sallama amsawa Alh Ali yayi tare dacewa ina me wayar??Tsaki taja cike da rashin kunya tace"Yana cikin idona,mutum se shegen cusa kansa acikin abinda beda mesaba ina ruwan ka da rayuwar mu kabi kasa min miji agaba da munafurci sekace dama Kai kasa shin yin aure,! dangin danga rere anma se shegen iyayin jaraba da naci kamar wani Uban sa...Shiru Alh Ali yayi yana sauraron rashin kunyar datake tsula masa yama godewa Allah da wayar ba ahandsfree takeba daya shiga kunya,muryan tane yakatse masa tunani asanda take cewa Honey ga Baffa nason magana dakai.Sallama Ahmad yayi tare dayiwa motar ke yana ficewa daga gidan.batare da Alh Ali ya amsa gaisuwar dayake masa ba yace"kazo kasameni agidan su matarka yanzu Wallahi idan bakazoba koda ranka dubune sena bata, yana gama fadin haka yakashe wayar...
Sunkai kusan awa daya dagama waya anma haryanzu shiru babu shu babu alamarsa ran Alh Ali bakaramin baci yasakeba da Wannan rainin wayon da Ahmad keyi musu yasan suna zaman jiransa anma shine yayi banza dasu,Sallamar Ahmad dinne yakatse masa tunani kusa dashi yaje ya zauna kansa akasa semace mutumin kirki.Cike da takaici Alh Ali ke Kallon sa bece dashi komai ba yasa aka kira Sukainat da mahaifiyar ta su zo ayi komai gaban su...
Sanye take cikin wani dogon hijab mai hula Navy blue Wanda yahaska mata fuskarta,bakinta dauke da sallama tashiga kana tanemi waje daga gefen mahaifiyar ta tazauna kanta akasa,bayan tagaishesu.Kallon ta Alh Ali yayi cike da kaunarta aransa kasancewar ta nitsatstsiya uw uba tarbiya da kamun kai,Ahankali yace" yata maimaita abinda kikafadawa iyayenki sannan banaso kiboye komai.Kai Sukainat tagyada tiryan tiryan tashiga zayyane musu duk abinda sukayi mata kamar yanda tafadawa iyayenta.Bayan yagama sauraran jawabin tane yajuya ga Ahmad dakan sa ke kasa kamar ruwa yacinyesa cikin kakkausan murya yace"ina fatan kaji abinda Matar ka tace"agaban idanun ka shin kana da Abin fada??Shiru Ahmad yayi bedago kai ba bare Susa ran ze amsa musu... Kai Alh Ali ya girgiza cike da takaici yace Ahmad kaji tsoron Allah a rayuwar ka shin wai yaushe kazama hakane?yaushe ka zama makaryaci kuma azzalumi!??!.
Rai abace Ahmad tadago kai yana kallon su daya bayan daya sedaya gama karewa fuskarsu kallo kafin yamike tsaye yace "daman tun ba yau ba Ku kecewa in saki Sukainat,bazan Iya riketa ba kowa da irin bakaken maganganun dayake yaba min akanta,abin Har yawuce kaina yakoma kan matata dabata ji ba bata ganiba dan haka zanbaku abinda kuke nema sekufita acikin rayuwa t dana matana.Ya numfasa tare dacewa ni Ahmad nasaki matata Sukainat saki daya....
```Tirkashi🤔🤔🤔yaufa ake yinta.Shin mekuke zaton zefaru anan gaba!??
Shin ya Sukainat zataji da sakin da Ahmad yayi mata duk dakuwa irin dumbin kaunar datake nuna masa tare da jure duk wulakan cin dayake mata anma karshe yasaketa.
Shin Sukainat zata Iya yafewa Ahmad kuwa, shin zata yadda takom gidan sa amatsayin matarsa shin idan takoma wani irin zama zasuyi???
Shin ya Ahmad zeyi asanda yadawo hayyacinsa yaga irin katobaran da yayi!??Anya kuna ganin Sukainat zata yadda takoma gidan sa akaro na uku bayan duk abubuwan daya mata??,to idan ita ta yadda iyayenta fa anya kuwa su zasu yadda??,kodan sakin yar su dayayi agaban idanunsu
Hmmmm nasan zakuso jin yakarshen Nadiya ze kasance anan gaba!.dakuma sanin menene makomarta anan gaba.
se munhadu acikin KI YADDA DANI Wanda zezama shine cigaban KISHIYA KO BAIWA ma'ana RETURN hmm kudaga jin sunan kunsan akwai chakwakiya anan gaba domin dukkan amsoshin dakuke bukata dakuma sanin yazata kasance zaku sameshi Acikin _KI YADDA DA NI_ salon da kuma tsarin labarin da banyake zaku nishsndantu fiye dayanda kuke zato.```
*NASIYYA*👇🏻
' Yan mata kuyi hakuri da duk zabin da iyayen Ku zasu yi muku akan mazajen dazuku aura,domin iyayen mu bazasu taba zabar mana abinda ze cutar damuba. ko wasu iyaye burinsu ace ya'yan su sune akan gaba akomai,wlh babu uwa ko kuma uban dazece ba yaso yaga cigaban dan sa ko kuma ganinsa acikin farin ciki..
So dayawa mukanyi kuskure abisa zabin da iyayen mu suke mana semu bujire mununa tamkar su basusan menene soyayya ba mu adole sede abi zabinmu idan kuwa basuyi mana haka ba semubin San zuciyar mu karshe mudawo muna nadama abisa bijire musu damukayi..Dan Allah yan mata ina kira da babban murya damuyiwa iyayen mu biyayya abisa zabin dazasuyi mana muddin muntabbatar dabaze cutar damu dakuma addinin muba.
Domin yau da za'acewa iyayen mu suzabo gwamna,shugaban kasa, sarauniya ko kuma wani matsayi mai girma,wlh basu da wa anda zasu zaba sama damu ya'yan su dan Allah mudaure muyiwa iyayen mu biyayya....
Tamat bihamdilillah
_VOTE COMMENTS AND SHARE_
*ESHAA CE~*🤙🏻