Showing 39001 words to 42000 words out of 52375 words
tarike plate din,tare dacew aikuwa bazaki ci ba domin baki isa kina zaune inyi miki girki ba,maganar tsiya dakike kiwa Allah ne yaga damar barin mu ahaka"Sannan nagodewa Allah daya bawa mahaifina wadatar zuci,baya zuwa maula.
Takaicine yakama Nadiya hakika yarinyar taga gadon baccinta anma bakomai daf take daseta mata hanya"Kisake min abinci"Kin sakewa Nadiya tayi,Fincike plate din Sukainat tayi da karfi,cikin rashin sa'a ya kwabewa Nadiya akafa!..
Ihu tasanya ta durkur kushe awajen tamkar wacce ake yankar naman jikinta"Rau rau Sukainat tayi da idanu ganin yanda abincin ta yatarwatse akasa,jitake kamar tafashe da kuka.Arazane Ahmad yashigo kitchen din jin ihun Nadiya,Ganinta adurkushe yasanya shi saurin karasowa gabanta,tsugunnawa yayi yana kokarin rike kafar,cike da damuwa?yace"meyasa meki haka my Queen!?,Kukan kissa Nadiya tafashe dashi tajanye kafar ta,duk dakuwa bawani zafi kafar keyi mata ba anma tadauki alwashin musgunawa rayuwar Sukainat"cikin muryan kuka tace"Kawai danna ce tabani indomie inci shine tahau zagina!hadda cemin wai bazata bayar ba tunda ba ubana ne yasaya ba,ta inda take shiga batanan take fita ba,karshe ma dubi abinda tayimin tafada tana nuna kafarta da indomie ke azube...
Cike da matsananin cin bacin rai Ahmad yamike yadun fari Sukainat,yana me binta da wani shegen kallo,.Baya tafara ja,dan ta tsorata daga nin yanayinsa bakaramin razanata yayi ba"ganin yanda lokaci daya idanunsa suka canza kala izuwa tsantsar bala'i,da jaraba datake iya hangowa aciki.Cikin sauri tajuya tafice daga kitchen din,cikin mugun sauri domin tasan idan tatsaya komai zai Iya faruwa a irin yanda take kallon kwayar idanunsa.
Taku biyu yayi yariko hannunta,cikin wani irin murya mecike da karaji dakuma hargagi yace"kije kinemi yafiyarta abisa lefin da kikayi mata!,dasauri takallesa cikin rawan murya tace"kamar ya in nemi yafiyarta?kamata yayi katamba yeni meya hadamu anma bawai kace...Be bari ta karasa fadar abinfa tayi niyya ba, yakife ta da Marin daya sanya taga gilmawar taurari a idanunta.cikin karaji yace"wannan yazama karo nakarshe da zanbaki umarni kiyin musu,in bahaka ba zanyi miki abinda bakyayi zato ba da kikiya kawai.Zafafan hawayen dasuka zubo mata yayi saurin sanya hannunta tashare,Jin diban albarkan daya kemata agaban kishiyarta" kokarin hana kanta kukan dake cinta take kodan Nadiya dake kallon ta tana sakar mata da murmushin mugunta...
Wai bazakiyi abinda nasaki bane sena tattakaki!?"muryansa yakatse mata tunani cikin tsawa.Ahankali ta karasa shiga kitchen din, cikin rawan murya tace"kiyi hakuri.Wani kaskantaccen kallo Nadiya tawatsa mata,kafin tamaida kallonta ga Ahmad dake tsaye yana kallonsu"cikin bada umarni tace"Honey kasa tadafa indomie yanzu inada bukata,tana gama fadin haka tafice daga kitchen din tana murmushin mugunta"Wani shegen kallo ta watsawa Sukainat kafin tafice,ranta fari sol.
Ina fatan kinji abinda tace tana bukata,base nasake maimaita mikiba?shiru tayi kanta akasa takasa furta komai banda sake sake da zuciyarta keyi.Ahasale yace"Ke bamaga na,neke dake ba kinyi min banza, koda yake balefin kibane,Lefin iyayen ki ne da basu baki cikakkiyar tarbiyan dazaki yiwa mijin ki biyayya ba.
Kukan datake kokarin dannewa ne yakufce mata shin wannan wani irin cin mutunci ne Ahmad keyimata.Durkushe wa tayi awajen tashiga rera kuka mecike da ban tausayi da kuma tausayin kanta.Tsaki yaja kana yamaka mata harara kokadan babu digon tausayinta azuciyar sa hasalima yatsani koda ganin fuskar tane"Afusacr yace"Wallahi minti goma nabaki kigama abinda tasanya ki inba haka ba kofa yayi batare daya karasa fadar abinda yayi niyya ba yafice....
Sosai tayi kuka,Wanda yasanya mata matsananncin ciwon kai" dakyar ta Iya mikewa tsaye,tana jin jiri nadibar ta,ahaka tadafa mata indomie,sannan tajuye a plate tanufi dakin,ahankali take tafiya sakamakon jiri dake dibarta.Da sallama tashiga parlour...kasa karasa sallamar tayi,sakamakon ganin Nadiya da Ahmad na kissing junansu tare da wasu abubuwa Wanda idanunta bazasu Iya gani ba.Dasauri ta ajiye plate din tafice hartana tuntube da kofa.
Tanashiga daki tafada akan kujeran tare dafashewa da kuka meratsa zuciyar duk wani mai imani kuka ne irin na Wanda yake cikin tsananin damuwa da tashin hankali"Yunwa takeji anma saboda damuwar datake ciki takasa cin abincin..Da karfin gaske aka banko kofar dakin tamkar za'aballa.Arazane tadaga kai tana kallon kofar tare da furta kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un....
_VOTE COMMENTS &SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_
*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_ππ»
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 49&50*ποΈ
_______________________________πCikin tsawa Nadiya tace"ke dakata shedanu kikagani kome!?dazaki tsaya kina yimana sallami,au na manta ashefa yar malamaice,tafada cike da kaskanci.Shiru Sukainat tayi batace komai ba,cikin ranta tace" aibabu maraba da shedanun,azahuri kuwa setayi kasa da kanta.Kafin tayi wani yunkuri daga inda take zaune,Nadiya tadaga plate din indomie dake tiririn zafi ta watsa mata.Jin saukar Abu mai zafi ajikinta yasanya ta daga kanta,Akidime tana kallon Nadiya dake tsaye da plate din indomie adaya hannunta,yayinda daya hannun ke kugunta tana jijjiga cike da bala'i!.
"Kallonta ta mayar kan Ahmad dake tsaye abayan Nadiya kamar bodyguard ko alamar gezau beyi ba ganin abinda Nadiya taimata hasalima dauke kansa yayi kamar bega abinda kefaruwa ba.Cikin rawan murya tabude bakinta da niyyan magana...Anma kafin tafurta komai Nadiya tarigata da fadin" ke yar talakawa dangin jaraba,saboda rainin hankali irin naki shine zakije kidafamin abinci me uban attaruhu saboda kina bakin ciki dani kinason ganin bayana to bari in sanar dake abinda baki sani ba wallahi ko ubanki ne sarkin malaman duniya baku Isa kuga bayana ba bare ma shi bakowa bane face dan maula,dan haka ina me gargadinki dakifita daga cikin rayuwar mu inba haka bane nuna miki bakin rijiya bawajen wasan makaho bane.
Cikin muryan lallashi Ahmad yace"kiyi hakuri My Queen kidena wahalar da bakinki akan wannan bakauyiyar yarinyar ni nasan matanki da zan dauka akanta Wanda setayi danasa ni akan abinda ta aikata miki,domin babu wani mahalukin daya isa ya wulakanta ki in kyalesa komai matsayinsa aduniya bare kuma kaskantacciya mara mutunci."Hannu tasanya tashare hawayen dake ambaliya afuskart,cikin dauriya da kafewar zuciya tace"Naji ni kaskantacciya ce awajenka,dama bana neman ka daukakani"daukakar Allah nake bukata bana mutum ba,Maganar danasani kuwa na nawa ya Ahmad!?ai danasani tunda ga ranan dana shigo cikin gidanka, amatsayin matarka nakeyi kuma har gobe bazan dena ba harse ranan da kagyara rayuwar ka, kadawo cikekken namiji mai cike da ikon fada agidan sa Wanda yasan hakkin aure yakuma San hakkin Allah akansa kana yasan halak da haram,hmm ya Ahmad ina mai tausaya maka ranan da ubangiji ze tsaidaka agabansa ya tambayeka hakkin daya baka akan matanka shin maizaka fada masa!?...Cikin wani irin matsanancin fushi da tsanarta yakwasheta da mari.wanda yasanya ta faduwa tabuga kanta ahannun kujeran atake wajen yakumbura.Cikin rashin tausayi yasanya hannunsa yadagota tare da shake wuyanta mari yashiga kifa mata hagu da dama yana cewa Wallahi ko duk duniyar nan gatankine yau sena nunamiki ni basa ankibane,Inaso ko mafarki kikayi kinyi musayar yawu dani inkintashi kirazana bare kuma kiyimin rashin kunya.Kafewa idanunta sukayi asama sekakari take,dakyar ta iya kokarin daga hannunta tarike nasa dan kwatar kanta anma ta kasa danko gezau beyiba,zubawa sarautar Allah ido tayi domin tasan yau karshenta yazo.
Ganin yana kokarin kisa yasa Nadiya saurin karasowa tarike hannunsa,Cike da tsoro tace"Honey sake mata wuya karka kasheta kaja mana bala'i!.kinsaketa yayi sema sake matse ta dayayi ajikin bango da duka karfinsa dan wani irin tsanarta yayi acikin rayuwar sa gwanda yakasheta kowa yahuta.Cikin tashin hankali Nadiya tabuga masa tsawa tare dacewa wai bazaka saketa bane seka kasheta!!??tafada tana janye hannunsa ganin ko motsi Sukainat tadena"Saketa yayi yana wani irin huci afusace yajuya yafice daga dakin.Zubewa Suky tayi sumammiya awajen"Cikin sauri Nadiya tabude Frigg tadauko ruwa me sanyi tasheka mata.Numfashi taja,kana tabude idanunta dasuka kada sukayi jawur dasu"Ganin ta farfado yasa Nadiya tajuya tafice...
Kuka Sukainat tafashe dashi Wanda muryanta befita,se hawaye dake ambaliya akan innocent face dinta.Dakyar ta Iya mikewa tashiga toilet ruwan zafi takunna tagasa jikinta da goshinta dake mata zafi,kafin tafito kan gado tafada"tayi rigingine, sotake bacci yadauketa kozata rage damuwar dake ranta anma Hakan yaki domin idanunta bushewa sukayi ba alamar bacci acikinsu.Rufin
P.O.P dake dakin tazuba wa idanu tana tunanin rayuwa,baki daya bata da sa'a acikin rayuwar ta. Ahmad yazame mata karfen kafa tun daga ranan data shigo cikin gidansa take cikin bakin ciki da takaici Wanda batasan ranan karewar saba
.Lumshe idanunta dake cike da hawaye tayi tana, tuna ranan data fara haduwa da Ahmad acikin rayuwar ta ranan da kaddararta tasauya izuwa kunci da bakin ciki,takuma dawo baiwa.Hawayene suka wanke mata fuska lokacin data tuna ahanyar ta nadawo daga islamiyya tahadu dasi.lokacin da aka tashe a islamiyya yamma yayi sosai kasancewar zasuyi musabaka hakan yasa suka dade,se da tafito taga hadari yahadu bakikkirin yana bada iska alamar daf ruwa yake da saukowa,gashi babu masu abin hawa hawa duk da kasamcewar tsakanin dutsen tanshi da federal Sacateria bawani nisa sosai.Hong dataji yayi yawa abayanta yasa tayi saurin matsawa gefe batare data juyaba domin sauri take ta Isa gida,sake danna mata hong akayi da karfi, hakan yasa tajuya akuma dede lokacin ne ruwan sama ya barke kamar da bakin kwarya.Zuge glass din motar yayi cike da nutsuwa yace"Barka da wannan lokacin kanwata,amsawa tayi da yauwa"tana kokarin barin wajen ganin yanda ruwa kedukanta,cikin kasa da murya yace"kishigo in rage miki hanya karmura yakamaki!,kai ta girgiza masa cikin yanayin sanyinta tace"ngd.sake sassauta murya yayi yace"pls kishigo mana inrage miki hanya"kin amincewa tayi.Duk Magiyan da yaitamata kantashiga yarage mata hanya anma fir taki. tayi tafiyar ta acikin ruwan yayinda shikuma yadinga bin bayanta ahanli har ta Isa Gida batare datasan yana biye da ita ba...
Sukainat kitashi kibamu abinci"Muryan Rufaida yakatse mata tunanin datake"Ahankali tabude kumburarrun idanunta takalle ta,Cikin muryan ta dabaya fita sosai tace"banyi girkiba.Dariyan shekiyanci Rufaida tasheke dashi kafin tace"Meyasa meki haka kofaduwa kikayi ko kuma kinyi fada ne amafarki da wacce tafi karfin ki!?hhhh gardiya tafadi akasa, tana gama fadin haka tafice daga dakin tana dariyar mugunta,dan dama ba yunwa takejiba Nadiya ce tasanya ta zuwa tambayi abinci...
Shiga parlour tayi tana dariyar mugunta hadda rike ciki,Hararanta Hjy kultum tayi tace ke lafiya kike irin wannan dariyar kamar wata zararriya.tsagaita dariyar tayi tace"Wlh grany bakiga fuskar Sukainat bane kamar wacce sukayi kokuwa da kada..Fashewa da dariya Nadiya tayi tace ke banson karya fa"Allah Momy bakarya nakeba dagaske nake..
Tsaki Hjy Kultum taja tace taje can takarata da mugun halinta matsalar tace duk bakin halinta kanta zekare ai,Ina aikar da aka miki tafada tana kallon Rufaida!?cewa tayi batai girki ba"anma bari nakira miku ita sekuga yanda fuskarta tayi, tana gama fadin haka tafice batare datajira jin amsar suba,tana shiga dakin babu sallama tace" Sukainat kawar kada kizo Hjy tazo kugaisa...Da kallo Sukainat tabi bayanta,tana mamakin sunan data kirata dashi wai kawar kada,kawar da tunanin tayi aranta kana tamike ahankali tadauki hijab dinta tafita daga dakin...
Kanta akasa tashiga parlour,bakinta dauke da sallama"Ko kallon ta basyi ba bare tasamu arzikin amsa salamarta.Bata damu da hakan ba domin inda sabo yaci ace tasaba da hallayar su.
Cike da ladabi ta tsugunna kusa da kujeran da Hajiya kultum ke kai tace"Sannu da zuwa Hjy fatan kinzo lafiya!?,Azabure Hjy kultum tamike tana watsa mata kallon tsana tace."Bana bukatar gaisuwarki mara tarbiya,se kizo kina wani sissinne kai kamar mutuniyar arziki!"maza fice kibani waje bana kaunar ganin wannan shedaniyar fuskar taki.Batace komai ba tamike tana kokarin hana kanta hawaye domin bataso suga raunin ta.Haba Sukainat kamata yayi kitsaya kibata hakuri dan Hjy kamar uwa take agareki,bekamata kinuna fushin ki kan tayi miki fada ba,anma yanda kika mike din nan yananu ni da kinfusata da fadar datai miki, takarashe tana satan kallon Hjy kultum dake jijjiga kafa cike da bala'i.
Murmushin takaici tayi,tarasa meta tsarewa Nadiya arayuwarta Wanda bata da burin daya wuce taga ta kuntatawa rayuwar ta."Cikin dashash'shiyar muryan ta da befita sosai tace"Wallahi ko daya banji takaicin kalaman Hjy ba dan yanda zan daraja Ummi na haka itama zan darajata amatsayinta na mahaifiyata...Cikin sauri Hjy kultum tadaga mata hannu tana huci tace"Allah yasauwa ke min in haifi mujiya kamar ke,me bakin jini da mugun hali,kije can kinemi uwarki anma ni bana fata in zama uwarki,dan da nahaifi irinki gwanda inda wama bani da 'da aduniya lalacacciya kawai...Cikin sauri Sukainat tafice daga dakin tana matsar kwalla,dan bazata Iya jure zama suna jifanta da munanan kalamai ba gara tafice tabasu waje.
Bayan fitarta Nadiya takalli Hjy kultum tana tabe baki tace"Hjy Wallahi yarinyar nan ta mugun renaki Sam bata ganin girmanki da kimarki sekace ke basurukar taba ce!,tafi karfin baki hakuri kenan akan lefin data miki gaskiya Hjy sekinyi gaggawar daukar mataki a kanta inba haka ba nan gabama se tayi abinda yafi wannan!?.Kwafa Hjy kultum tayi tace"bar matsiyaciyar yarinya ninasan maganinta dan sena dauki tsatstsauran mataki akanta...
Se bayan sallan la'asar Ahmad yashigo gidan agajiye.Lokacin dayashigo Hjy kultum nashirin tafiya ganin sa yasa takoma tazauna.Kusa da ita yazauna yagaishe ta"amsawa tayi da murmushi afuskarta tana tambayar sa kasuwa?"Dan yamutsa fuska yayi yace"Kasuwa babu dadi dan acikin wata daya nayi asara tafi na milliyan uku baki daya, harkan kasuwanci na Neman tabarbare min nakasa gabe meke damuna!? Se asara naketayi komai se lalace min yake."
Wani irin ka kasa gane abinda ke damunka bayan ga Abu afili,akuma kusa dakai"cewar Nadiya tana jifansa da wani shu'umin kallo"Kamar ya akusa dani My Queen ban fahimci mekike nufi ba yafada yana me kura mata idanu alamar yana son jin Karin bayani.Yanzu kuwa zan fahimtar daku,sede bansan yanda zaku amshi maganata ba. Daga shi har Hjy kultum ido suka zuba mata batare da sunce komai ba,sede da ka kalli fuskokinsu zakasan suna Bukatar Karin bayani....Murmushin samun nasara tayi kafin tace"...
_VOTE COMMENTS AND SHARE._β
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???.*
_(True life story)_
_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_ππ»
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 55&56*ποΈ
_________________________π Uban me yakawo ki wajena!?Aida sekije kibisa tun yanzu ku kaini wajen hukumar kare hakkin mata bawai Sena sake yi miki komai ba,idan kukayi hakan se intabbatar dacewa kuncika yan halak kuma dagaske kukeyi"!yakarashe afusace dan har cikin ransa yake jin takaicin cin mutunci da mutumin ya masa hakika badan yaci darajan furfura ba daseya tsula masa rashin mutunci da harya mutu baze manta dashi ba...Banza tayi masa dan wani mugun haushi yake bata,batare da ta tanka masa ba ta jingina bayan ta da jikin motar jin kafafunta sungaji da tsayuwar.Akufulace yace"Ke dan Ubanki ni sa'anki ne da zanyi miki magana kina jina kiyi min banza ya fada yana zazzare mata daradaran idanunsa!?Idan motar dake wajen ya amsa to itama ta amsa.
"Wannan shirun datayi bakaramin kona mai zuciya yayi ba hakika yarinyar nan taga gadon baccina bacin haka yaushe ze mata magana tayi banza dashi,afusace yasanyo hannu acikin aljihun wandansa yaciro dari biyar ya wurgama tare dacewa kidauka kibiya kudin transport kiwuce gidan ku inyaso daganan sekiwuce kuje kukaini kara keda sabon Uban naki!.Yana gama fadin haka yashiga motarsa batare daya jira jin abinda zatace ba kana ya buleta da kuran motarsa yabar wajen...Murmushin takaici tayi a lokacin da motarsa ta bace mata koda amafarki bata taba zotan irin Wannan wulakan cin daga wajen Ahmad ba,Dasauri tasanya hannunta tashare hawayen dake kokarin zubo mata.Jiki amace tafara tafiya har tafita daga cikin haraban asibin yayinda zuciyar ta keta yimata sake-sake kan tawuce gidan su,yayinda wata zuciyar ke cewa takoma gidan sa.Cikin ikon Allah tana fitowa tasamu adedeta, taransa tayi tare dasanar masa dacewa bayan driving school ze kaita,kai dan acaban ya jinjina mata tare da fada maya yanda zata biyashi bamusu ta amince da bismillah tashiga shikuma yatayar suka tafi...
"Tafiyar minti talatin ne yaikusu unguwar har kofar Gida me adedetan yasauketa kafin ta sallameshi,juyawar dazatayi ta hango motar Ahmad yakutso kai cikin Unguwar tayi mamakin ganin tarigasa karasawo da alama yatsaya awani wajen ne.
Cikin sauri takarashe shigewa cikin gidan har tana hadawa da gudu,dan kar ya cimmata"Da kallo Baba mai gadi yabita cike da tausayi yayinda zuciyar ke tunanin ya akayi tadawo ita ka'dai Karan Hong da akayi masa da karfine yasanya shi saurin mikewa.
Direct sashen ta tawuce da gudu tana shiga ta danna wa kofar key tabar sa ajiki kana ta wuce bedroom din ta takwanta tana maida numfashi.
Kogama parking beyiba yafito amatukar fusace yanufi sashenta yana murda handle din yaji arufe,Cikin takaici yadaki kofar da karfi.Seda tatsorata da yanda yake bugun kofar da karfin gaske kamar ze karya hakika ba dan kofofin masu kyau da nagarta bana daya karya su.Duk da tana jin yanda yake kiranta cikin hargagi hakan besa ta motsa ba bare ta amsa masa,afili ta furta inkagaji zaka tafi.Cikin hargagi da tsawa tajiyo muryan sa akaro na barkatai yana cewa Wallahi Sukainat idan baki bude dakin nan ba kika bari na balla kofar na shigo sekin gwammaci kida da karatu.Banza tayi masa sema bedroom din ta data nufa tayi kwanciyar ta tana mecewa inka gaji da tsayuwa ka koma ai jarababbe kawai...
Jin andafa kafadarsa ne yasanya shi juyawa amatukar hasale"Nadiya yagani tsaye takafe sa da kananun idanunta cikin tuhuma take Kallon sa kafin tace"mekake nema anan!?
Kwafa yayi yace"ni Wannan yarinyar zata to zarta acikin mutane My Queen yakarashe kamar zeyi kuka da alama haryanzu yana jin takaicin abinda Dr yafada masa!.Metayi maka tafada tana metsaresa da idanu akaro nabiyu.Zazzafar huci yafesar daga bakinsa kafin yashiga zayyane mata yanda sukayi da Dr dakuma yanda sukayi da Sukainat...Batare da tace dashi komai ba tarike hannunsa suka bar wajen domin tana ganin wani dama tasake samu akanta.Direct sashen ta suka nufa akan 3siter tazaunar dashi kana tazauna akan cinyarsa, hannu tasanya tasakalo wuyansa tare da hade bakinsu waje daya seda tayi kissing dinsa San ranta kafin tajanye bakinta daga nasa,tana kallon yanda yake binta da wani mayataccen kallo kawar da kanta tayi daga kallonsa.Cikin bada umarni tace"banaso kayi mata magana akan abinda yafaru tsakanin ku tasake kai karanka wajen Baffan ka,daze zo yai tamaka ihu batare daya tambaya ke yaji tabakin kaba dan haka kafin tace zataje tashirya masa karya da gaskiya inaso kai karigata.
Numfasawa yayi cike da gamsuwa da kalamanta,Ahankali yace"toh mezance dashi idan