Showing 33001 words to 36000 words out of 52375 words

Chapter 12 - KISHIYA KO BAIWA BY REAL ESHAA.txt

06 Mar 2025

3320

aciki komai kankan tarsa muddin kukasamu Matsala babu ruwana sannan duk abinda yasameku kuka jawa kanku"Cikin sauri Nadiya tace"mun a mince, boka inde bukatar mu zata biya,sannan inaso kabani Wanda zan mallakesa yazamto baya jin maganar kowa seni baya tsoron kowa seni"Karki damu bukatarki zata biya muddin kin kiyaye sharudan dazan gindaya miki yafada yana mefashewa da dariyar keta.Wani abin tsafi yadauko kamar tulu yafara tsatsube-tsatube, yadauki lokaci me tsayi kafin yagama,wasu kullin yadauko yamikata maganin tare da fada mata sharadin kowanne dakuma yanda zatayi amfani dasu,Iya tsawon kwana ki gwama zata dauka tana amfani da magungunan muddin takauce ko da rana daya ne batayi ba,aikin yabaci koda kuwa tayi na tsawon kwana ki tarane"Inkuma ta kammala Dede to aranan data gama aranan aikin zekama"godiya suka maisa tare da ajiye masa makudan kudi,Wanda Hema ce tabiya a aljihunta Cike da farin ciki suka hau hanyar komawa gida...


Bayan Ahmad ya kammala hada musu abinci ne yakai yajere musu acikin parlour,kana yakallesu cike da so yace"kuzo kuci,jiki narawa suka taso dan bakaramin yunwa suke jiba.
kallo Hjy kultum tabi dan nata dashi cike da tausayin sa,tasan idan ba asiri Suky tamasa ba babu dalilin dazesa yakasa daukan mataki akanta na azabtar masa 'Ya'ya da yunwa da tayi,amaimakon yadauki mataki akai seya bige dayi musu girki,dan kar ranta yabaci" anma taci alwashin seta kubutar dashi daga kaidin su itada iyayenta...
Tunda ga parlour yake jiyo sheshhekan Ku kanta jiki asanyaye yashiga bedroom din can karshen gado yahangota ta takure tana kuka me ban tausayi,karasawa yayi yarungume ta cike da so yashiga lallashinta tare da fada mata kalamai masu sanyaya zuciya"Shiru tayi se ajiyar zuciya take saukewa akai akai,Harshensa yasanya yana lasar hawayen dake kan innocent face dinta kafin,yasauke harshensa asaman pink lips dinta"hade bakinsu yayi yashiga kissing dinta cikin salon soyayyarsa daga nan labarin yacanza salo...


Gani lokaci yana taja Nadiya bata dawo ba yasanya Hjy kultum tattara su Rufy tatafi dasu,acewarta bazata barsu suky ta kashe su da yunwa ba"batare datayiwa Ahmad sallama ba tayi tafiyar ta."Se misalin karfe takwas Na dare Nadiya tadawo gidan direct sashenta tawuce cike da matsanancin farin cikin burinta yakusa cika,bata damu da rashin ganin su Rufy ba,dan tasan bazewuce suna gidan kakarsuba, direct toilet tashiga tawatsa ruwa,sannan tabi lafiyar gado takwanta,batare da tunanin rama sallolin dake kanta ba.
Cikin baccin ta taji muryansa nacewa daga ina kike!??mikewa tayi tana mummutsika idanu,jitayi kamar ta kwada masa mari kan tashin ta dayayi abacci anma,se tadanne zuciyar ta " tayi rau rau da idanu"cikin wata raunanniyar murya tace"kayi hakuri Hajiya tace batada lafiya kuma banason tashinka alokacin shiyasa natafi, anma in ranka yabaci dan Allah kayi hakuri bazan sakeba takarashe hawaye nabin fuskarta.jikinsa ne yayi sanyi yace "Ayyah aiban saniba Allah yabata lafiya"ameen ta'amsa, kokarin kwanciya yake agefenta,Tayi saurin cewa kaje yau nabarwa kanwata kwanan dan bana cikin nutsuwa,harya bude baki zeyi magana tayi saurin daura hannunta abakinsa tana girgiza masa kai alamar batason jim komai"Hannu ta yajanye tare da bata peck a lips dinta,cike da kulawa yace kikula min da kanki yana gama fadin yafice daga dakin cike da farin cikin ze sake kasancewa da Sukainat...
Dakallo tabi bayan sa Har yafice"wani killer smile tasaki tace ka kusa fadawa tarkona Ahmad,kwanciya tayi dahaka bacci me dadin gaske ya dauketa...




_VOTE, COMMENTS, & SHARE._


*ESHAA CE~*πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_


*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_


*WATTPAD*
_Realeshaa_


_Like my page on Facebook_ πŸ‘‡πŸ»


https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/


*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*Dedicated to*
_NAZIFI YARIMA Alherin Allah ya tabbata agareka aduk inda kake_




*PAGE 43&44*πŸ–ŒοΈ


_______________________________πŸ“–Wani irin zama Sukainat da Ahmad suke me cike da tsantsar so da kauna"kula na musamman Ahmad ke bata koda motsi tayi,Jiki narawa ze matso ya tambaye ta metake bukata?,inko yaga tazauna tayi shiru!,seya matso kusa da ita tare da tambayar ta ko wani abin na damunta?ko kuma akwai abinda take bukata,ganin yanda yadamu da ita,dakuma nuna damuwar sa akanta yasa tarage damuwar datake ciki Na kiyayyar da Hjy kultum ke nuna mata domin karya ga kamar yagaza wajen bata kulawa.Acikin kwanaki Bakwai dasuka yi atare dashi tayi fresh, jin dadi da kwanciyar hankali sun wa daceta."Kulawar da tasamu daga bangaren mijinta shiyafi komai kwantar mata da hankali, akullum addu'ar ta Allah ya tabbatar musu da zaman lafiya yakuma tsaresu daga sharrin abin ki acikin zaman takewar auren su!!.Kasancewar su Rufaida basanan tun ranan da Hjy kultum tatafi dasu basu dawo ba,yasan Sukainat sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa"Cike da farin ciki takira mahaifiyarta dakuma aminiyar ta tasanar dasu halin datake ciki"Sosai Ummi da Sofia' suka taya ta farin ciki tare dayima ta addu'ar kasancewa da mijinta Har abada....
Nadiya kuwa tadauke idanunta akansu domin burinta bewuce tasamu damar kammala aikinta ba,duk dakuwa tanajin takaicin ganin yanda Ahmad ke manne wa Suky anma ta danne zuciyar ta,tace dashi yayi sati adakin Suky,Duk dan tasamu damar aiwatar da kudirinta batare daya gane ba ko kuma ya zargeta"Acewarta na karamin lokaci ne hakurin da zatayi dasu.Sukainat na cikin kwanciyar hankali da farin ciki domin amarcin ta,takeci,wanda ko asatin farkon ta agidan ba tasamu irin wannan kwanciyar hankali da nutsuwar datake ciki ayanzu ba...Abangaren Nadiya komai Na tafiya yanda take so domin duk yanda boka drogoni yace"tayi haka takeyi,babu kuskure akan,yanda yatsara mata"Inda yanzu ya kasance tana cikin kwana ki na takwas da fara aikin,yarage saura kwana ki biyu ta kammala aikin ta wanda take fatan dacewa...
Wayewar garin yau da wani irin matsanancin ciwon mara ta tashi tun safe takeji anma ta daure batasanar wa Ahmad ba domin tayi zaton zedena zuwa wani dan lokaci"Gani lokaci yaja be dena ba,sema sake murda mata dayake ga lokaci yaja sosai.Ahankali tamike tasanya hijabi akan kayan baccin dake jikinta,cikin nutsuwa tanufi sashen Nadiya.Da sallama dauke abakin ta tashiga parlour,ba kowa aciki se AC dake aiki"Ahankali tadaga kai ta kalli hadedden Agogon dake manne a parlour takwas da Rabi tagani nadare.Ganin dare beyi sosai ba yasa tanufi bedroom din,knocking tayi tare da jingina bayan ta da jikin bangon.Lokacin datayi knocking Nadiya na toilet, hakan yasa Ahmad dake kan bed yana danna system,yamike yanufi kofar tare da budewa."Ganin ta ajingine talumshe idanunta,yasanya shi dafa kafadarta yana karantar yanayin fuskarta.Ahankali tabude idanunta tana kallonsa.Cike da kulawa yace"ya akayi ne My Kainat,?koki na bukatar wani abune?,yajero mata tambayar alokaci daya "Batare da tace dashi komai ba tanuna masa Cikin ta da hannu hawaye na taruwa a idanunta"bece komai ba ya dauketa kamar baby direct sashenta yanufa da ita.a parlour ya ajiyeta tare da kwantar da ita adaya daga cikin kujerun parlour, hannu yasanya yacire hijab din tare da daura hannun sa akan mararta yana shafawa"batare dayace da ita komai ba,lumshe idanunta tayi tanaji kamar ciwon ake cire mata."Da karfi aka banko kofar parlour tamkar za aballa,Dasauri suka daga kansu suna kallon kofar dan gani ko wanene!."Cikin fusata Nadiya tace wannan wani irin zalincine Ahmad??, meyesa baka da imani ne!?duk irin wannan halarcin danayi maka kadawo dakinta natsawon sati be meka ba har sekasake satar kwana acikin rana ta,ka kawo mata saboda gata matat so Wallahi in de bakadena zalun tanaba se Allah yatasheka da gefe daya ashanye ranan gobe kiyama.Ahankali Suky tamike daga kwancen da take tace"Dan Allah momyn Rufy kiyi hakuri Wlh banajin dadin jiki...hannu ta daga mata afusace tace rufemin baki munafukar banza,Annamimiya kawai ko kina nufin duk abinda kike yi ban saniba bane?,saboda tsaban jaraba da munafurci irin naki se lokaci da kikaga yana dakina zaki zo kice baki da lafiya!,kokina zaton ban fahimci inda kika dosa bane?.Rai abace Sukainat tadaga mata hannu tace"Ya isheki haka malama bazaki shigo Har dakina kice zaki cimin mutunci akan gaskiya taba dan haka kifice min daga daki inyaso kiyi awaje"baki daya na fahimceki kin tsani ki bude ido kiganmu Inuwa daya da, ya Ahmad kuma insha Allah munriga da munzama daya sede duk abinda zakiyi yi.Tsaki mai karfi Nadiya taja tana binta dawani kas kantaccen kallo tace"Lalle hausawa sunyi gaskiya dasu kecewa 'ya'yam matsiyata basu Iya samun wajeba,ke Har ina kikaga dakin dazakiyi min gori kokin manta yanda gidan tsohon ki yake ne?Idan ana ruwa sede akoma kofar daki ayi girki,saboda kinsamu waje shine zakiyi wa mutane feleke.Dariyar rainin hankali Sukainat tayi,Duk dakuwa kalaman Nadiya sun yimata zafi azuciya,Cikin kunsa takaici"tace"Kinyi gaskiya,kan cewa yayan matsiyata basu Iya samun wajeba,Wannan haka yake domin koni zan iya bada sheda akanki,Saboda ke naki uban Aliko dan gotane,ko kuma ince karuna, tunda yagina miki gida,da komfononi,yakuma saimiki motoci yarako ki dasu gidan miji base kin bukata awajen saba"taci gaba dacewa ko kina zaton bansan komai bane,dan gane da gidan Ku ba,toh bari kiji ina sane da cewa abinci ma se mijinki yatemakawa iyayenki da Wanda zasu ci!Anma Kinzo kina yiwa mutane karyan banza, takarashe tana maka mata harara dan baki daya tagaji da Cin mutunci da zagin iyayenta datake gwanda itama tanuna mata cewa tasan sirrin gidan su...Cikin wani irin kunan zuciya da bakin ciki!!Nadiya tadaga hannu tana huci da niyyan wanke Sukainat da mari.Cikin sauri Sukainat tarike hannun ta,tare da kife ta da wasu tagwayen mari hagu da dama.Dafe kuncin Nadiya tayi tana bin Sukainat da kallo cike da matsanancin mamakin yanda tayi nasaran marin ta.Cikin bacin rai Sukainat tace"Wlh wannan yazama karo Na farko kuma nakarse dazaki sake zagar min iyaye ko kuma kice zakiyi gangancin saka hannun ki ajikina da sunan duka,Wlh zan baki mamaki aduk sanda kika sake gangancin hakan.Wani irin kuna zuciyar Nadiya keyi dan haka tasake kaiwa Sukainat duka akaro Na biyu azafafe,rike hannunta Sukainat tayi,tare da sake zuba mata marukan dasukafi na farko,atake gefen baki Nadiya yafashe yana fitar da jini!.Hannu tasanya tashafa wajen ganin, jini abakinta yasata juyawa tafita afusace."Ganin fitar ta yasa Ahmad yamike dasauri yace"Zo in boyeki karta dawo tayi miki illah ya fada yana rike hannunta da niyyan janta daki.takaici ne ya tokarewa Sukainat makoshi jin abinda yace wai tazo yaboyeta saboda tsaban lusaran ci,"Hannun ta tafincike daga nasa tace"babu Inda zanje in buya aidama duk abinda take yimin kyaleta nike bawai karfi na tafiba dan haka tazo ashirye nake da taranta.Har ya bude baki zeyi magana sukaga Nadiya ta banko kofa hannunta rike da muciya,tayo kan Suky gadan gadan...Tana karasowa batayi wata wata ba tadaga tare da bugawa Sukainat agoshi, runtse idanu Sukainat tayi sakamakon wani radadi daya ziyarci kanta,sake dagawa Nadiya tayi da niyyan bugawa Sukainat,cikin sauri Sukainat ta kauce tare da nufar bedroom dinta,tana shiga tadauko kujeran tsugunno datake tafito,karo sukaci da Nadiya tabiyota domin azatonta gudu tayi"batare da bata lokaci ba Sukainat tadaga kujeran ta kwada mata agoshi.Ihun azaba Nadiya takurma tana yowa kan Sukainat gadan gadan..cikin Dakewar zuciya Sukainat tasheke wuyanta tare da sanya kanta atsakanin hammatar ta tadunga dukanta tamkar wacce Allah ya aikota..Ganin abin bana karewa bane,kuma Sukainat zata Iya yiwa Nadiya illah" yasanya Ahmad dake zaune yana kallon su kamar TV mikewa,Janye Sukainat yayi daga jikin Nadiya,fisgewa Suky tayi tana kokarin komawa,sake janyota yayi ya rungumeta yana bubbuga bayanta alamar tayi hakuri"Kin hakura tayi se fisge fisge take adole seta komai ta cigaba da dukan Nadiya.Kukan takaici Nadiya tafashe dashi ganin irin cin mutunci da Ahmad yayi mata,agabant wata tayimata dukan tsiya, yana gani be tanka ba sannan yasake rungumeta soboda cin fuska da wulakanci"dan haka ta dauko muciyar ta dedeci keyarsa ta buga masa da karfin gaske"dasauri yasake Sukainat yana dafe wajen cikin azaba,Cikin sa'a tana dagawa tasamu Sukainat agadon baya ta buga mata da duk karfin ta...
Ahaukace Sukainat ta dauki kujeran tabuga mata akai, atake wajen yafashe yana zubar da jini!!Ihun azaba ta kwalla tare da yi wowa kan Sukainat"taran ta Sukainat tayi suka fara fada cikin sa'a Allah yabaiwa Sukainat nasara ta kwantar da ita akasa tadunga dukanta tamkar tasamu yar ta sede ta kumbura mata fuska da jiki baki daya tasauya mata hallitar fuska.Cike da bacin rai Ahmad yabuga musu wata razananniyan tsawa cikin bada Umarni yace".ko wacce ta tattara kayanta tabarmin gida na nasake ku saki daya-daya..Yana gama fadin haka yafice daga dakin."Dagudu Nadiya tabisa tarike kafafunsa tana kuka tace"dan Allah Honey kayi hakuri kamayar dani dakina,Wallahi natuba bazan sakeba kayi...mari ya kwada mata amatukar fusace yace"Wallahi in baki tashi kin tafiba sena karasa sauran dake tsakanin mu.Dasauri tamike har tana tuntube tanufi dakinta dan tasan tunda yafada ze Iya aikatawa dan in ransa yabaci babu abinda baze Iya aikatawa ba"Ita ba sakin da yayi mata bane yake daga mata hankali, kamar aikinta data kusan kammalawa tasan muddin tabar gidan aikin ya lalace ga sharadin da boka drogoni ya gindaya mata hannu tadaura akai tace"nashiga uku"Dasauri tasanya hannu tadauki wayarta dake kan beside drower ta danna kiran layin Hema,anma abin takaici akashe,zama tayi tana sake gwadawa akashe, takira yafi sau akirga anma duk be shiga...Cikin tsawa da hargagi taji muryan Ahmad nacewa Wallahi idan baki fitoba na shigo sena balballaki,dasauri tafito tana gunjin kuka,ko kallonta beyiba"yakawar da kansa"gate tanufa tana waiwayan sa ko ze tausasaya mata seta ga ko kallon Inda take ma beyi,bare yaji tausayinta.haka tafice daga gidan zuciyar ta cike da tashin hankalin abinda zefaru muddin akasamu matsala acikin aikinta...
Abangaren Sukainat kuwa yana cewa"yasake su tadauki hijab da wayar ta,tafice ko ka'dan bataji takaicin sakin dayayi mataba,bawai dan batason shiba a'a"sedan yanda tasamu Allah yabata nasara akan Nadiya zuciyar ta wasai tafice daga gidan...Bayan fitarsu Ahmad ya umarci Baba mai gadi da karyabar kodaya daga Cikin su tashigo idan tadawo"domin yasan nacin Nadiya seta Iya dawowa da baya...Aikuwa hakan ce takasance domin tana fita kamar da minti goma tadawo tafara buga gate din.Waye? Baba mai gadi ya tambaya,yana sake matsawo jikin gate din kasancewar harzuwa lokacin ba adena knocking, batare daya bude yace yasake cewa,Waye!?Ashar Nadiya ta kunduma masa tare dacewa zakazo kabude min ne kokuma zaka tsaya yimin tambayar banza matsiyaci kawai!..Cike da takaicin zagin da tayi masa yace"kiyi hakuri Hjy anma Alh yace"kada in bar kowa yashigo acikin Ku"Yana gama fadin haka yashiga dakin dake mallakinsa ya kwanta.Durkushe wa Nadiya tayi awajen tanajin tamkar tasa hannu aka tatai zabga ihu tarasa mafita ashar tadunga kunduma wa Baba maigadi tare da la'antarsu"Baba mai gadi najinta yayi mata banza.Tagumi tayi tana tunanin mafita yanzu tasan inhar bata kwana agidan ba shikenan aikinta ya ruguje abanza duk tsawon kwana kin data dauka tanayi sun wargaje kenan!? Burinta baze cika akansu ba,sunyi galaba akanta.Ihu tasanya tare dacewa karyane,karyane Wallahi Baku Isa Ku mayarmin da aiki baya ba Baku Isa kuruguza min shiri ba...Cikin sauri tamike tafara tafiya, batayi wani tafiya menisa acikin unguwar ba tatsaya akofar wani gida tafara buga musu kofa"ba dadewa wata dattijiwa tafito tana tambayar waye?Dasauri Nadiya ta amsa dacewa nice mama.Kece wa?Dattijiwar tasake tambaya!?Nadiya ce tafada tana gunjin kuka. Cike da mamaki matar tabude mata kofa kasancewar tagane muryanta...


*****
Sosai Ummi kemata fada ta Inda takeshiga batanan take fitaba"bayan tagama jin abinda tayiwa Nadiya,Sam bataji dadin dukan datayi wa Nadiya ba" itade hakuri kawai take bata anma kokadan batayi dana sanin akan abinda ta aikataba...Koda Malam Ahmadu yashigo Ummi tasanar dashi abinda yafaru seyashiga yimata nasiyya da fada kan bata kyauta ba kuma ta kiyaye gaba kada yasake jin tayi irin haka"Sannan tayi masa alkawarin baza tasake fada da Nadiya ba.Cike da ladabi ta'amsa tare dayimasa alkawarin Insha Allah hakan bazesake faruwa ba"Albarka yasanya mata kafin yafice...
Koda Malam Ahmadu yafita daga dakin, number Alh Ali yakira bayan sungai sane,Ya sanar dashi abinda yafaru tsakanin Sukainat da Nadiya..Hakuri Alh Ali yabashi tare dacewa Insha Allah yana zuwa yanzu ze mai da ita dakinta"Godiya malam Ahmadu yaimasa kafin yakashe wayar,yakoma dakin.Koda Alh Ali yakashe wayar seya kira number Ahmad anma,akashe"kwafa yayi dan yasan halin Ahmad da gangan ze kashe wayar dan kar aneme sa,fitowa yayi yadauki key motarsa direct gidan Malam Ahmadu yanufa... Abangaren Ahmad kuwa bayan fitarsu yakashe wayoyin sa duka dan kar atakura masa dakira"Kana yamike ya fita coumpound din tare dasake bawa Baba mai gadi umarnin karya bar kowa yashiga masa gida....




Am backπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


Alhamdulillah nagama exam insha Allah zakuna jina akai akai.Nagode da addu'o'inku Allahu yabar zumunci😘😘




_VOTE, COMMENTS & SHARE_




*_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_


*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_


*WATTPAD*
_Realeshaa_


_Like my page on Facebook_ πŸ‘‡πŸ»


https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/


*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*




_Wannan page din kyauta ne agareki hazika kuma fasihiyar marubuciya *AUNTY BINTA UMAR ABBALE* Ubangiji Allah yakara daukaka ki fiye da yanda baki zato Alherin Allah ya kaimiki aduk Inda kike Inai miki fatan alkhairi._ 😍😍😍😍




*PAGE 45&46*πŸ–ŒοΈ


_______________________________πŸ“–Madede cin parlour dattijuwar suka shiga;Wanda akalla shekarunta zasu Iya kaiwa hamsin da biyar, ko sittin.Cike da dattako tanunawa Nadiya wajen zama,tana mebin fuskarta da kallon tausayi ganin yanda fuskar ta tuttuje kamar wacce sukayi kokawa da zakan ya".Zama Nadiya tayi tana matsar kwallar takaici da bakin ciki"Cike da tausayi dattijuwar takalle ta tace"Nadiya barayine suka shiga gidan ku sukayi muku irin wannan danyen aikin haka!?ina mijin naki shi kuma yashiga? ina fatan de basuyu masa illah irin taki ba!?ta karashe cike da jimamin ganin yanda halittar fuskarta tasauya baki daya!.Kuka Nadiya tafashe dashi tace"Wlh Mama hansi ba barayi bane sukayi min wannan abin face kishiya ta,dubi irin wannan abin da tayi min kuma abin bakin ciki agaban mijinmu tayi min, anma sam be dauki mataki akai ba kokuma ya dakatar da ita"karshe ma sakina yayi yakuma Koreni acikin wannan Daren yace inbar masa gidan sa!"Ga mahaifiya ta batada cikakkiyar lafiya,Hawan jini ke damunta,nasan kuma muddin naje mata da wannan bakin labarin, ciwon ta ze Iya tashi karshema yajanyo sanadiyyan ta,shiyasa nazo kitemaka min kamar yanda Allah yatemake ki takarashe cikin wata raunanniyan murya.Cike da jimami,gamida tausayin ta Mama hansi tace taya zantemake ki Nadiya?"Bayan bawata alaka me karfi bace atsakanina da mijinku banda alakar musulunci.Hawaye tashare tace inde mukaje ki kabashi hakuri ze hakura yamayar dani dakina,dan yana ganin kimarki da mutunci ki,amatsayin ki na Dattijuwar arziki wacce duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login