Showing 114001 words to 117000 words out of 124261 words

Chapter 39 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

wasu suke fad'in hala tayi cikin shege ne aka korota har suke fad'in tir da ita, Bariki dai ita burinta jiran ya saketa ta tashi ta shiga cikin kaduna.


Tana nan zaune kaman daga sama taji ana mata magana, da sauri ta bud'e ido, wanda ya sauka a kanshi sukai ido biyu, gabanta taji ya fad'i, ba kowa bane sai Mai kid'a , duk da tana jin jiri saida ta tashi tare dayin baya.


Yace Bariki Kece a yashe a nan haka? Murmushi yayi tare da fad'in daka gani kina neman taimako, yanzu abunda za'ayi kizo muje inada d'aki a nan saiki huta.


Bariki ido ta bishi dashi Wanda jikinshi ga kurajen HIV nan duk sun feso mishi a jiki duk Wanda yasan Kalan kurajen yana kallo zai gane yana da cutar, mai karya garkuwan jikin d'an Adam.


Yace taimakon ki zanyi, kin tsaya kin kafeni da ido, naji ance kinyi aure? Ko dama k'arya ne? Muje in baki masauki ki huta, ko ince Mu huta.


Bariki kai ta girgiza tare dayin gaba dan bata tunanin zata iya furta wani kalma a yanda take jin jikinta.


Binta yayi yana fad'in nan ba maraban jos bane, gwara ki bini in taimaka miki, in bani bama Waye zai kalleki, kalli yanda duk kayanki suka baci, m.... Motar data tsaya a gaban Bariki ne yasa Mai kid'a yin shuru


Wata mota ce 'kiran Prado ta tsaya gaban Bariki, da sauri aka bud'e motar hafsat ce ta fito daga cikin motar tare da ri'ke Bariki tana fad'in Zainab Ina zaki haka? Usman shima faka tashi motar yayi Bayan ta hafsat, tare da fitowa, tun sanda bariki take cin waina ya ganta shine ya kira hafsat dama jiya da suke waya da hafsat take fad'a mishi halinda Yarima yake ciki, da Kuma neman da Mai martaba yasa ayi mata.


Hafsat tace Zainab maza kizo muje Gida, Yarima yana bu'katarki.


Bariki tace a'ah hafsat tare dayin gaba lokaci d'aya jiri ya kwasheta ta Fara k'okarin yin k'asa hafsat ta kamata tare da sata a mota, suka wuce.


Usman kallon mai kid'a yayi tare da fad'in mai kake binta kayi Mata?? Mai kake nema wajanta? Bud'e Mai ido usman yayi


Mai kid'a ya fara bashi hakuri tare da fad'in taimako nake nema wajanta yana fad'in haka ya ruga da gudu, dan ya tsorata da usman yana tsoran Kar yasa a kamashi.


Bariki dake kwance cikin mota bata san inda kanta yake ba, hafsat kiran Mai martaba tayi tare da shaida mishi Anga Zainab a halin yanzu ga sunan suna tafe, amma kaman ta suma.


Mai martaba yace ma Hafsat ta kaita asibiti, shima yanzu zaizo shida Aliyu, domin ga shinan kwance bai San inda kanshi yake ba.


Hafsat tace toh Abba.


Asibiti takai Bariki inda akai emergency da ita domin bata ko motsi, nan aka fara bata taimakon gaggawa.


Basu dad'e da zuwa ba saiga Mai martaba da Yarima an kawo an sashi akan Keken d'aukan marasa lafiya, nan shima aka shigar dashi emergency, likitoci dai suna nan tsaye kan masoya biyu, suna iya bakin k'okarin su.


Yarima ne ya fara sauke numfashi sama sama, alaman yana jin jiki Sosai, sannan sanda aka kawo shi ko numfashin baya iyayi da kyau, irin haka inda an k'ara bata lokaci a gida, sai mutum ya rasa ranshi gaba d'aya, Yarima yana kwance yana nishi sama sama, d'aya daka cikin Dr din ya fara mishi magana tunda yana d'aya daka cikin wanda suka duba Yarima lokacin da abun Farko ya faru, a kunne tare da fad'in Yarima wake up ga matarka kusa dakai, kallon abokanan aikinshi yayi tare da fad'in su matso da gadon da bariki take kusa.


Nan aka matso da gadon sauran Dr din suna son suga Mai d'ayan Dr din zaiyi, idan kuka duba in za'a ma mutum operation tiyata, za kuga likitoci fiye da d'aya ne suke aikin, domin ko wanne zai bada nashi gudun mawan, wani yana da experience fiye da wani, so wannan shine dalilin da yasa suke kallon d'ayan Dr din suga Mai zaiyi.


Kamo hannun Yarima yayi dana Bariki ya had'a waje d'aya, tare da k'ara yima Yarima Aliyu magana a kunne ka tashi matarka na bukatar taimakon ka, Plz wake up.


Yarima tun sanda aka sa mishi hannun Zainab a nashi, zuciyarshi ta Fara harbawa da sauri, suda kansu sauran Dr din sunyi mamaki, lallai soyayya ba k'arya bane and basu taba ganin irin wannan son ba, ashe hakan na faruwa, ikon Allah.


Yarima Aliyu a hankali ya fara bud'e ido, wanda suka sauka akan selling d'in d'akin, lokaci d'aya ya waiga ganin Zainab kwance kusa dashi ya fara k'okarin tashi, da sauri Dr ya rik'eshi tare da fad'in plz Aliyu ka kwanta matarka Tana kusa dakai babu inda zata.


Yarima Aliyu hannun Dr yake k'okarin cirewa daka jikinshi amma ya kasa saboda jiki babu 'kwari.


A hankali yace plz leave me, I want to see my wife.


D'aya daka cikin Dr din yace ka d'agashi ya ganta.


D'ago Yarima Aliyu yayi tare da matso dashi gadon da Zainab take, k'ara matse hannunta yayi yana hawaye tare da fad'in my princess I will never ever let you go from me again, I can't live without you, my princess why r you go far away from me?..... Lokaci d'aya kuma yayi shuru komai ya tuna kuma oho, yayi wajan minti biyu yana kallon Zainab, lokaci d'aya kuma ya rungumeta duk da tana kwance, sun dad'e a haka Kafin Bariki ta farka tare da bud'e idonta itama kukan ta Fara, tare da matse mijinta a jikinta tana fadin Yarima zan mutu , mai yasa mum bazata duba irin sonda nake maka ba, Yarima plz kaba mum hakuri ta hakura ta barmu tare, bazan iya rayuwa ba tare dakai ba, plz Yarima kazo mu gudu muyi rayuwa a wani waje wanda babu wanda zai gammu....


Muryan mum sukaji Tana fad'in Sai dai ke ki gudu ba d'ana ba, y'ar iska, har abada d'ana bazai taba barin iyayenshi ba, kaman yanda ke kika bar naki, y'ar iska karuwa hafsat dake Bayan mum tana takaicin abunda mum din ke fad'a tare da tausaya ma d'an uwan nata da matarshi, k'okarin fita tayi domin kiran Mai martaba dake waya a waje Aiko jiri ya d'ibeta lokaci d'aya tayi k'asa, nan mum ta waiga jin kaman mutum ya fad'i, ganin hafsat ce yasa ta saki ihu tare da fad'in na shiga uku, da gudu ta fita ta kira Dr inda aka fara duba hafsat din itama.


Nan mum ta fita ta kira Mai martaba take fad'a mishi hafsat ta fad'i Tana ciki ana dubata, hankalin Mai martaba ya tashi Sosai, yara uku ba lafiya, Yarima da matarshi ga hafsat, mai martaba ko zama ya kasayi saboda tashin hankalin da yake ciki, tare da fargaban maike damun hafsat itama


Sunyi wajan 30mnt suna jira Dr ya fito wanda tun a ciki Dr ya fad'ama Yarima Aliyu abunda ke damun hafsat, ya shiga mugun damuwa wanda ko magana ya kasayi, Bariki ce tayi karfin halin ro'kan Dr akan karya gayama mum da Abba a waje saboda Akwai fadawa, ya shigo dasu nan ne Kafin ya Sanar musu, hakan ko akayi aka kira mum da Mai martaba, inda Mum ta Fara fad'in Dr dan Allah fad'amin abunda ke damunta?


Hafsat na kwance tana bacci abunta, ansa Mata drive.


Dr yace hjy tana d'auke da ciki na wata uku, abunda yasa ta fad'i saboda jikinta yayi weak, is lyk Tana cikin damuwa so..... AI tuni mum tayi k'asa sumamma, shiko Mai martaba kasa magana yayi sai Innalillahi'wa inna ilaihirajiun da yake ta faman furtawa cikin ranshi, ganin mum tayi k'asa yasa ya d'agota da sauri inda Dr ya d'auko ruwa aka yayyafa Mata ta Farko .


Kuka tasa tare da fad'in Hafsat kin cuceni, kin gama dani, yanzu irin tarbiyan dana baki kenan? Kin d'auko mana Abun kunyar da ban taba jiba ko a zamanin baya ba, ace y'ar gidan sarauta tayi cikin shege, kuka Mum take Sosai cikin 'kunan rai, tare da ba'kin cikin abunda y'arta ta d'auko, shiko Mai martaba kukan zuci yake lallai basai kayi abuba Allah yake jarabtanka, koda baka kasance mazinaci ba, Allah yakan jarabceka da samun mata mazinaciya ko kuma cikin y'ay'anka, lallai babu yanda Allah bayayi akan wannan al'amarin, Allah yakan jarabci bayinshi tako Ina, yaga ya za suyi.


Zainab dai itama tana zaune tana hawaye, lallai abunda ciwo, ganin yanda mum take kuka saita tuna da dad d'inta, irin halin daya shiga sanda yace tana da ciki, Wanda ita bata san Wanda yayi mata ba, sai yanzu Bariki take k'ara ganin laifin kanta wanda komai dad d'inta zai Mata bai kamata ta fad'a Bariki ba, danta kuntata ma mahaifinta ba, gashi yanzu abunda tayi shi take girba,tayi aure amma saboda rayuwar da tayi baya ya bata mata rayuwar auranta, kuka ta saki mai sauti wanda hankalin kowa yayi kanta.


Mum kallon Bariki take irin yanda take kuka, jikin mum yayi sanyi, lallai abunda mijinta yake fad'a mata gaskiya ne, kaddara tana kan kowa, gashi yanzu ya fad'a kan y'arta, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun. Hmmmm Allah sarki rayuwa kenan, kowa baya yarda da kaddara saiya fad'a kanshi, sannan zai san kaddara ne, Abu Indai ba'a kanka ya fad'a ba to wajan kowa ba kaddara bane wasu sai su dinga fad'in dagangan mutum yayi ko kuma ace shiya sa kanshi, Hmmm mutane suna bani mamaki, wlh baki shi yake Kai mutum ga halaka, sai kuji mutum yana fad'in Wlh ni ai duk wacce take karuwanci ita taso maganganu dai irin haka, toh Wlh y'an uwa ku iya bakinku, Domin kuwa Allah zai iya jarabtanku ku fad'a cikin harkan karuwancin sai yaga yanda za kuyi, sai yasa a kullum ake son mutum ya dinga fad'in Alheri, kaman dai irin abunda mum ta dinga fad'i akan Bariki ita bata haifi karuwa ba, sai gashi y'arta da cikin shege, lallai dubaranka ko wayanka bashi bane zai sa Allah ya'ki jarabtanka, Allah yana jarabtan bayinshi ta hanyoyi da dama domin ya gwada imaninsu, wasu ta dukiya, wasu ta ciwo, wasu na talauci babu yanda Allah bayayi, sai dai muyi fatan Allah yasa mu cinye ko wace jarabawa da zata zo mana a rayuwa.


Mum tashi tayi tare da nufa inda Yarima da Bariki suke ta Fara bashi hakuri tare da fad'in lallai ni uwa ce, wacce ban kasance mai fahimtar abunda d'ana yake soba, ni uwa ce Mai son kanta, tunda na nuna nafi son y'ay'ana akan na wasu, na kasa amsar kaddaran data fad'a ma matarka, Ina gudun kaci gaba da zama da ita, yau gashi nima Allah ya jarabceni y'ata d'auke da ciki ba tare da aure ba, ciki harna wata uku, lallai Allah ya nunamin ishara, kamo hannun Bariki tayi tana fad'in dan Allah ki yafemin Wlh Ina jin kunyar kaina irin munanan kalaman dana dinga fad'a miki, gashi nasa d'ana ya miki saki har uku, banyi la'akari da cewa Kece rayuwarshi, ba idona ya rufe Ina ganin kaman kin mallake min d'ana kuka yaci karfinta Sosai.


Bariki cikin kuka tace mum kiyi hakuri, nayi imani da kaddara, lallai na yarda sakin da Yarima yayi min yana cikin kaddara na, ban taba ganin laifinki ba, abunda kika aikata ko wace uwa abunda za tayi kenan, babu wata Uwar da zata so d'anta ya zauna da macen da tayi rayuwar Bariki, lallai nima na cuci kaina kuka ta saki mai sauti wanda duk wannan abunda suke idon hafsat biyu tana ji itama hawaye take, lallai tayi kuskuren mallaka ma Umar jikinta gashi yanzu baya Raye.


Mai martaba daya kasa magana sai yanzu ya iya bud'e baki, yace Zainab daka ina kika fito, Ina son ki fad'amin koke wacece dan a nemi iyayenki mu samman yanzu da kike da juna biyu ya kamata musan iyayenki


Bariki taba cikinta tayi tana mamaki dama ciki gareta? Wani hawaye mai zafi ya fito mata nan ta Fara bama Mai martaba Labarin irin abunda ya faru da ita harda irin rayuwar da tayi a bariki, ta k'arasa maganan cikin kuka mai ban tausayi .


Kowa ya tausaya mata,ciki harda hafsat dake kwance tana jinsu, jikin mum ya k'ara sanyi Sosai, tare dayin nadaman abunda ta aikata ma Bariki, lallai tayi kuskure babba, ashe itama babban kaddara ne ya fad'a mata, had'e da Sharrin matar uba, lallai wasu matan bazasu ga annabi ba, tayi sanadin lalacewan yarinya danta k'i yarda da kudirinta na aikata mad'igo, Mum jikinta yayi sanyi Sosai, gashi ta raba d'anta da ita, koya rayuwarshi zata kaya?


Mai martaba yace dama ke yarinyar Sheikh musa monguno ce? Ikon Allah, d'azu dashi muke waya kan cewa yazo Nigeria nace mishi muna asibiti, nasa aje a d'aukoshi daka airport Wanda na tabba sun kusa zuwa nan bada dad'ewa ba, Abokina ne tare mukai karatu a k'asar misra, lallai abun yaban mamaki, Yarima yasa in gayyato shi akan yana son ya gabatar da lacca, Amma Zainab kinyi kuskure babba, iyaye ai iyaye ne, komai suka miki bai kamata ki k'ara bata rayuwarki ba danki kuntata ma mahaifinki, haba zainab ina iliminki? Kin aikata babban kuskure a rayuwa.


Kallon Yarima Mai martaba yayi tare da fad'in ko kasan shine mahaifinta dama??


Yarima yace eh Abba, ranan da aka d'aura mana aure na gane tamin k'arya, inda daka baya ta fadamin gaskiya, shine na bukaci ka gayyatoshi dan nasan inka kirashi zai zo, kayi hakuri Abba Nayi maka k'arya akan ina son yazo yayi lacca, Nayi hakan ne danka kirashi yazo in dai daitashi da y'arshi, ni bamma san abokinka bane, dani dakai na zani wajansa har misra din.


Mai martaba yace lallai Aliyu kayi jahadi, Allah yayi maka albarka, karan wayar Mai martaba ne yasa ya d'auka tare da fita waje, Jim kad'an sai gashi ya shigo da sheik musa monguno da matarsa Falmata wacce tasha hijab har k'asa kamar wata mutuniyar kwarai, idon sheik musa monguno ya sauka akan na gudan y'ar tasa Aiko yana ganinta ya fara nunata da hannu lokaci d'aya kuma ya fad'i k'asa....... Hmmm muje zuwa muji maike faruwa?



























~MARYAM OBAM~




*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*MY DEAR MY LOVELY FRIEND QWEEN PHAREEJAY*








*BOOK 2*




*PAGE 27*
























Bariki ihu ta saki cikin tashin hankali, nan mum ta fita da gudu kiran Dr, yayin da Falmata take ta zunduma ashar kan cewa Bariki zata kashe mata miji, Bariki kam kuka take tana manne jikin Yarima, Falmata k'okarin cafko Bariki take, Yarima kaman ya Lura da hakan yasa ya dawo da Bariki baya tare da shiga gaba.


Dr shigowa yayi inda ya bu'kaci su mum damai martaba da Falmata su fita danya samu ya duba patient din, nan Dr Ya fara duba sheik musa monguno, cikin ikon Allah ya Farfado nan ya fara kuka tare da zufa dake faman keto mishi, tashi yayi tare da nufa wajan da Bariki take inda ya fara kuka yana neman gafaranta akan abunda yayi mata, wanda yace Wlh bai San ya akai har shida kanshi ya koreta ba,


Dr fita yayi domin yaga ba wani serious ciwo bane, suma yayi and kuma ya Farfad'o, ganin Dr Ya fita yasa su mum shigowa.


Falmata ganin mijinta ya tashi yasa ta Fara rusa kuka lokaci d'aya kuma ta Fara dariya tare da fad'in Nina sa akama Zainab ciki saboda ka tsaneta Wlh nice nasa aka mata hahahaha hahahaha sai kuma ta saki kuka lokaci d'aya kuma taci gaba da fad'in


Nice nasa mata kwaya cikin juice tasha, tayi bacci Mai nauyi, Nasa driver ya mata ciki, hahahaha bayan nasashi na koreshi, daka karshe ya faramin barazana nasa aka kasheshi har lahira, wlh nice nasa aka mata ciki, saboda ta'ki yarda dani, ni kuma ina sonta Sosai ina son in lashi zumarta, Wlh Ina Sonta Sosai dan Allah ku bani ita, ko ku aura min ita, sai kuma ta k'ara fashewa da dariya taci gaba da fad'in abunda yasa nasa aka mata ciki saboda ina son Dad d'inta ya tsaneta, yace ta d'auko mishi abun kunya, kuma Nayi wannan tunanin ne saboda Kar wata rana ta tauna min asiri dan yana jin magananta, kuma in ya tabbatar tana da ciki zai daina yarda da ita, bayan nasa anyi mata ciki, nasa akaje min maiduguri wajan wani boka inda na amso mugun sihiri Wanda na rufe mishi ido da baki sai abunda nace, duk da lokacin sihirin baiyi wani tasiri Sosai ba, dan Bayan ya koreta yaita fama da ciwo tare da damuwa yana mamakin Wai shine ya Kori y'arshi da kanshi, ganin irin damuwan da yakeyi gashi ana kawo mishi hotanta da shigar banza, hakan yasa hankalinshi ya tashi Sosai, ganin irin halin daya shiga yasa na tafi maiduguri dakai na wajan boka, gashi ina takaicin ban haiyu dashi ba, yau Idan ya mutu ba wani kud'i zan samu Sosai ba, inda Nayi mishi bayani, tare da cewa Ina son a cire mishi tunanin Zainab harta danginshi kona mamanta karsu nemeta, boka yace wannan aikin akwai hatsari Sosai sannan akwai zunubi Sosai, domin raba y'a da iyayenta babban aiki ne, nan nace ma boka na d'auka, boka yace dad din Zainab yana matukar son y'arshi Sosai koda anyi aikin muddin ya ganta komai zai lalace, Indai kina son aikin yayi tasiri karki bari su had'u, nace ma boka babu damuwa


Yace an gama, za'a tura mishi Aljani, wanda zai dinga juyashi, nan na amince boka ya k'ara min kashedi Idan na Bari suka had'u komai ya faru dani Kar ince bai fad'amin ba? Nace na amince domin a lokacin idona ya rufe.


Bayan na dawo Abuja naga aiki yayi, domin a lokacin tunanin Zainab yasa dad d'inta ya rage ibada, domin yana cikin ciwo, wannan ne yasa nayi nasara akanshi, har Aljani ya shige shi, saboda ina fargaban karsu had'u nasa muka koma misra gaba d'aya inda na bu'kaci Nima Ina son inyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login