Showing 111001 words to 114000 words out of 124261 words

Chapter 38 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt




Yarima Aliyu da tunda yaji ance ciki Zainab take dashi ya bud'e ido, lokaci d'aya wani karfi yazo mishi, jinshi sukayi yana fad'in Dr kana nufin Zainab Tana da ciki??


Su duka suka bishi da ido alaman mamaki, tashi Yarima Aliyu yayi zaune, yace Dr she is my wife plz tell me is she pregnant??..


Dr yace yes she is pregnant, but where is she??


Yarima Aliyu cire oxygen din dake hanncinshi yayi tare da tsige Abun drive din dake hannunshi, da sauri Dr yace Aliyu ka tsaya, da sauri Dr din ya nufeshi tare da ri'ke Mai hannun dake zubar da jini, Yarima Aliyu yace Dr leave me I will handle it, am a Dr too..


Dr yace I know but plz ka tsaya kasan yanayin da kake ciki, bai kamata ka fita haka ba, u need to rest


Yarima Aliyu yace how will I sit hare and rest matata da unborn child d'ina suna cikin had'ari bayan kace cikin zai iya fita, I have to go and find her.


Babu yanda Dr ya iya dole yabar Yarima ya fita, inda yana fita yaga mai martaba da mum da fadawa.


Mum ganin d'an nata ya fito yasa ta saki wani murmushi Tare da furta Alhmdlh, nufanshi tayi tare da rungumeshi tana kuka, mai martaba shima tashi yayi yana fad'in Aliyu ya jikin naka, amsawa yayi da Alhmdlh Abba, mum sakinshi tayi tana fad'in ya jikin naka ya amsa da Alhmdlh mum, tare dayin gaba da sauri.


Mum damai martaba binshi sukayi da ido, ganin Dr yasa suka nufeshi suna fad'in ina zashi, nan Dr Ya fara basu Labarin Yarinyar da aka shigar da ita d'azu matarshi ce, and tana da ciki Yadai basu Labarin komai, tare da fad'in abunda na Lura is lyk kaman itace wacce lokacin da yayi irin wannan tayi mishi magana ya tashi koh??


Mai martaba yace eh Dr itace, nan Dr yace gskiya yana mata son so, dukansu bazasu iya rayuwa babu dayansu ba, dan haka ku tabbata Yarima duk inda zashi ko ince kar'ayi abunda zasu rabu da juna, ban taba ganin irin wannan son ba sai a Fina finai ko a littafai, ashe yana faruwa da gaske, duk da Muma a karatun mu anyi mana wajan, but ban taba d'aukan abun serious ba dan Banyi tunanin zai faru ba, sai gashi na gani yanzu, and shawaran da zan k'ara baku shine ku tayashi dubata, domin Indai bai ganta ba gaskiya I don't know wat will happen, nan Mai martaba yace mun gode Dr, Dr yace babu komai ganin matar tashi shine lafiyanshi.


Mum kam gaba d'aya duk abunda Dr yake fad'a babu wanda ya shiga kunnenta, ita tunda d'anta ya tashi Alhmdlh, sannan maganan a nemo matarshi bai taso ba, tunda ya Mata saki uku, and kuma cikin dake gareta ta tabbata bana d'anta bane, sai dai in wani ya Mata ciki y'an iskan samarint.... Mai martaba ya Katseta da fad'in Kinga ikon Allah koh? Kina tunanin kin rabasu amma Akwai ajiyar jikanki a jikinta, Kinga har yanzu ala'ka bai 'kareba tsakaninsu, Idan babu ala'kan aure Akwai na abunda zata haifa, lallai ki godema Allah da yasa sai da akayi auren kika san ko wacece, domin na tabbata inda kin San ko wacece b4 suyi auren Nasan bazaki amince ba, not even you Nima da kaina bazan amince ba, Kinga Ashe Akwai rabon wannan cikin, kuma rabo na kisa, and inma baiyi kisa ba za'a kawo mana jika babu aure shi kuma wannan sai muce me??


Duk abunda kikaga Allah yayi, karkiyi jayayya akan abun, yanzu kina murna kin raba d'anki da matar da kike kira karuwa, gashi a karo na biyu ta k'ara taimaka mishi, lallai Khadija keda kanki kike son kashe d'anki, yanda d'anki yake Sonta itama take sonshi in bakiyi wasa ba za kiji suna zaman dadiro ko kiji yasa tayi auren kissan wuta, daka k'in gaskiya sai bata yana fad'in haka ya tafi ya barta domin yaga wani hali d'an nashi ke ciki


Hmmm Tashin hankali mum duk maganan da mijinta ya fad'a mata, babu wanda ta d'auka domin idonta ya rufe, lallai Asirin bariki yayi tasiri har akan mijinta, domin gaba d'aya taga baya ganin laifin kowa sai Nata, wacce take ganin abunda tayi shine dai dai, lallai dole ta nemi maganin karya sihiri taba d'anta da mijinta, itama binsu tayi domin taja d'anta suyi gida, dan tasa a Fara mishi addu'a,


Yarima Aliyu tafiya yake cikin haraban asibitin jiki babu kwari sai waige waige yake, kallo d'aya zaka mishi kasan yana cikin Tashin hankali tare dajin zafin ciwo, gaba d'aya cikin asibitin baiga mai kama da Zainab ba, dan haka ya fita waje, nan mutane suka fara tareshi ana fad'in Yarima Aliyu, mai jiran gado, gaba d'aya mutane sun hanashi yin gaba suna k'okarin gaisawa dashi, ganin haka fadawan dake binshi a baya suka zo suka fitar dashi suka sashi a mota, koda Mai martaba ya fito ganin abunda ke faruwa shima motar ya shiga yace su nufi Gida, Yarima idonshi nakan titi ko zaiga Zainab amma baiga koda Mai kama da ita ba, haka har suka k'arasa gida, Yarima Aliyu hannunshi ri'ke dana Mai martaba suka shiga gefen mahaifin nashi, suna shiga Yarima ya fad'a kan kujeran falon ya fara hawaye tare da ri'ke kirjinshi dake faman mishi zugi da rad'adi, ganin haka Mai martaba ya fita tare da kiran waziri akan suje su duba gidan iyayen yarinyar na k'arya may be tana can, nan su waziri suka amsa da angama ranka ya dad'e suka tafi.


Bariki kam tunda ta fita daka asibitin cikinta na Mata ciwo Sosai, samun wani waje tayi akwai rumfa ta kwanta, domin babu komai a hannunta, harta wayarta bata hannunta, gashi yanzu babu bank sun tashi da taje ta cira kud'i ta check book, haka ta kwanta a wajan domin ciwon cikin yana damunta Sosai, ita bata ma San tana da ciki ba, Hmmm Bariki babu riba, lallai rayuwar mace kalilan ce, zakiyi iskanci lokaci kad'an kiyi sanyi a daina yi dake, in kinso shiriya mutane su dinga nuna miki kyama da hantara, tare da goranta miki, inma kin samu mijin aure kin haiyu aita miki gori ana ma y'ay'anki gori, daka fad'a ya had'asu da wani aita musu gori, y'ar uwa Mai yafi wannan ciwo da zafi? Gashi kullum in kika fita miji yaita zargin ki, kai Wlh Mata iskanci da fitsari bashi bane wayewa, babu abunda yakai kame Kai da tsare mutunci dad'i, Idan ke ta'kamarki bin maza kina bud'e musu k'afa suyi lalata dake, daka ranan da kikace d'aya daka cikinsu ya fito ya aureki, zaki ga yace shi dan iska ne da zai aureki? Bayan kin gama bin maza ai inada kishin kaina, daka ranan ma in bakiyi wasa ba yabar kulaki, mai wayau kuma zaiyi ta miki Karya tare da alkawarin zai aureki, inya gama cin moriyarki ya gudu, ke koda shine ya fara saninki kuma shi d'aya kike bi, wlh bazai iya auranki ba, domin shifa a kullum tunani yake kina bin wasu mazan, zaki ce ai maza nawa sukayi lalata da Mata suka auresu Toh Bari kiji Wlh Mata da yawa y'an duniya wanda suka amsa sunansu y'an Bariki, akwai namijin da suke nunamawa su ustazai ne basu taba sanin namiji ba, daka anyi aure yaji kofar a bud'e take sai kuji ya saketa, aure kuga ko sati baiyi ba Ya mutu, wasu kuma asiri suke ma mazan su auresu, Hmmm kuma duk abunda aka had'a da asiri baya 'karko domin asiri dai yana karyewa daka ranan daya karye ranan zaki gane shayi ruwa ne, y'ar uwa komai zakiyi ki yishi akan gaskiya, da yawa zaki ga y'an duniya suna hulda da malamai, amma daka karshe ya rayuwarsu take k'arewa? Idan har kin San miye rayuwa kuma kina nazari kina kallon abunda ke faruwa, wlh zaki ji tsoran duniya da rayuwa kiga ba komai bace, yanzu maza yawancin su babu abunda suka iya sai soyayyar shan minti, daka sunje wajan Yarinya zasu Fara mata maganan banza da rashin kunya, daka nan sai a fara tabe tabe, wani ma so yake ya aureki, amma yana gwadaki daka ya taba yaga kin biye mishi, sai yace y'ar hannu ce shida yazo da niyan aure sai ya nemi kwanciya dake daka kin bashi ya gudu, ke kina ganin hakan shine wayewa, lol


Wlh mata ku kiyaye, sai yasa yanzu y'an mata sukai yawa, babu mazajan aure, domin mazan suna mana kallo a d'age, suna ganin kaman duka d'aya muke, yau Idan namiji yazo Wajanki yayi k'okarin tabaki kika rufe ido kika ci mishi mutunci kika tafi kika barshi, wlh Indai aurenki zaiyi gobe zai dawo, domin zaice kinci jarabawan shi, amma daka ya tabaki saiki bada Kai bori yahau, kai Wlh Mata masu irin wannan halin aji tsoran Allah, domin duk iskancin namiji so yake ya auri nitsatsa ba ballagaza ba, wacce kowa ya Santa, Allah ya kyauta.


Koda su waziri suka isa gidan iyayen Bariki na k'arya, mamanta tace ai tunda tayi aure bata zoba.


Koda su waziri suka koma suka fad'ama sarki, Yarima babu abunda yake sai kukan zuci, domin yanzu hawayen dake fuskanshi Ya'ki fita, saboda yana cikin Tashin hankali da damuwa, fiye da tunanin mai karatu, Yarima Aliyu yasan rashin matarshi kaman barazana ne ga rayuwanshi, gashi ba ita d'aya ba, tana d'auke da cikin shi, lallai Mum ta gama dashi da tasa ya saki matarshi, inda tasan irin son da yake mata da bata ce ya saketa ba, mai yasa mutane basa d'aukan kaddara Indai ba'a kansu ya fad'a ba?? Mai yasa mutane basa ma wasu uzuri Indai basu bane suka aikata?? Mai yasa duk abunda ba damuwarka bane mutane basa d'auka da muhimmanci?? Shin Mum tasan zan iya rasa raina akan Zainab tayi k'okarin rabani da ita? Shin tasan Sonta a jini na yake? Lallai Indai banga Zainab ba komai zai iya faruwa domin yanzu dauriya kawai nake, Yarima Aliyu lokaci d'aya ya fara girgiza kai domin tunawa da yayi Karta koma irin rayuwarta ta da, tashi yayi da sauri.


Mai martaba yace Aliyu Ina zaka?


Yace Abba neman Zainab, zani in dubata, Abba Ina tsoran ta nanata irin rayuwar da tayi baya, Abba ban son ta k'ara bata rayuwarta S....


Mai martaba yace Aliyu zoka zauna, nasa a nemota, Aliyu zama yyi tare da fad'in Abba Kirjina tare da ri'ke wajan ya kasa magana, da sauri mai martaba yayi kansa....










******
Habib ne zaune gaban hjy Umaima yana fad'in, na samu Labarin Yarima ya saki bariki, dama sai yasa na fad'a miki iyayenshi basu sani ba, gwara da kika turama uwarshi, Kinga yanzu aiya saketa,


Hjy Umaima dariya tayi cikin jin dad'i tare da fad'in yanzu sai a nemo min ita


Habib yace hjy aiki kwantar da hankalinki ita da kanta zata kawo kanta, tunda Yarima ya saketa ai dole ta dawo gidan jiya, dama saboda shi ta shiryu, yanzu Kinga tunda ya korota ai dole a dawo gidan jiya, ko dan a sami na rufin asiri.


Hjy Umaima tace hakane yanzu abunda ya kamata shine, ka koma kaduna nasan for sure zata koma gidan barikin da take tana zuwa call me, Zanzo kaduna din.


Habib yace an gama, ai hjy Wlh bariki komai kika ce mata yanzu zata yarda domin bata da wani zabi, saina abunda kikace, tunda komai ya cabe Mata, yace hjy inada y'ar tambaya?


Hjy Umaima tace inaji


Yace hjy Idan kuna wannan lesbians din dad'i kukeji?


Hjy Umaima tace Kai Idan ana cinka ta baya dad'i kake ji?


Habib yace na shiga uku, Nayi gamo amma gaskiya banji dad'in wannan zancen ba, wlh har kinsa naji kunya, wai anyi da mutum yaji


Hjy Umaima tace Aiba k'arya Nayi ba, ni kaga ko Kinga zance dan Allah kama hanya zan maka transfer yanzu dan banda cash, koya ake ciki call me, inma bata zo ba make sure ka nemo min ita zuwa gobe, Yarinya sai shegen kafiya, Nayi Asirin amma shuru, aiki ya'ki kamata, ni Allah yasa tana da ruwa ma,koda yake ko bata dashi yanda na kwallafa rai sai naci ko ana ha maza ha mata saina d'ana, tunda na Kwadaita


Habib yace ah wannan zance yafi karfina, Kinga Nayi gaba, inji alert , domin komai danshi nakeyi.


Hjy habiba iya tashin hankali ta shiga, farhan tunda yabar gidan sai cikin dare ya dawo, a falo yaga mum din tashi, wani irin kallon tsana ya Mata tare da d'auke idonshi daka kanta, dan baya bukatar yana ganinta ko kallonta, domin abunda ya gani shine yake dawo mishi.


Ganin yana k'okarin wucewa yasa ta tashi ta nufeshi tare da fad'in farhan plz ina bukatar magana dakai, dan Allah ka saurareni.


Yace plz matsa min a hanya, I hate to see ur face, bana bukatar koda muryanki inji, sai kuma ya saki kuka.


Hjy habiba tace farhan Nasan dole zaka tsaneni amma Kafin nan ina son kaji dalili na, kayi min uzuri kuma tare da adalci n....


Yace babu abunda zan saurara daka gareki Wlh inda kin San hukuncin abunda kika aikata da bakiyi ba, lallai mum shaidan ya gama dake, kiyi gaggawan tuba tare da ro'kan gafaran Allah, karki bari mutuwa ta riskeki kina Mai aikata wannan mummunan aikin zunubin, wlh mum da kin San irin bala'in dake cikin wannan abun da baki aikata ba, mad'igo wai Uwar data haifeni ita take aikata wannan mummunan abun, amma babu damuwa Allah zai hukunta ki, sannan tun a duniya zaki gani, ko ince kin Fara gani, domin Allah ya jarabci d'anki da son wacce kuke aikata wannan mummunan aikin, kuma Wlh Indai Kinga ban auri haulat ba Allah yasa ba matata bace, ko kuma ni na mutu ko ita ta mutu, saiki shirya amsan abokiyar lalatanki a matsayin surukar ki matar tilon d'anki yana fad'in haka yayi gaba, Tashin hankali ........






*NOT EDITED*


















~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 26*














Yarima Aliyu sai nishi yake sama sama, mai martaba ya cire mishi rigan jikinshi ya rage daka shi sai singlet, sai zufa yake ta keto ma Aliyu, duk da kuwa akwai AC a d'akin, mum shigowa tayi cikin tashi hankali ganin halin da Aliyu ke ciki,


Kuka ta Fara tana fad'in Aliyu sannu, tare da kallon mijin Nata tace mu maidashi asibiti.


Mai martaba yace ai kinfi kowa sanin maganinshi, dan haka ki barshi kawai, babu abunda asibiti zasu iya mishi.


Mum fita tayi Jim kad'an sai gata da limam, tana fad'in dan Allah kayi mishi addu'a, nasan wannan Asirin Nata *BA'KIN AJANI* Ta tura mai, dan Allah mlm dubashi Karta kashe min yaro, tana maganan tana kuka


Mai martaba yace Khadija ina tunanin Kece kike bukatar ruki'a bashi ba, kallon limam Mai martaba yayi tare da fad'in limam kaje abunka.


Limam fita yayi


Mum tace na shiga uku, haba Kai baka ga halinda yake ciki ba, yanzu Inba asiri ba taya danya saki matarshi zai shiga irin wannan halin, wannan wani irin sone haka? Wannan aikin sihiri ne ba komai ba, ban tunanin koni na mutu Yarima zai shiga wannan halin, amma akan y'ar iskan karuwar yarinyar can duk ya d'aga hankalinsa W....


Mai martaba ya daka mata tsawa tare da fad'in Yimin shuru, Khadija zan saba miki, naga alaman kina son wuce gona da iri, ki barshi yaji da abunda yake ji, kinsa ya rabu da matarshi ki barshi haka karki k'arasa shi, komai ya sami Aliyu Kece sila.


Mai martaba kallon Aliyu yayi da yake faman jin jiki tare da fad'in Aliyu Ina son kayi hakuri ka d'auki komai ya faru da bawa kaddara ne, sannan zansa a nemo maka matarka duk da kun rabu zata zauna a nan har sai ta haiyu.


Mum dai fita tayi tana kuka ita an gama da d'anta da mijinta


Koda labari ya iske gimbiya zinatu da gimbiya Amina, zo kuga murna, inda sukai ta fad'in Ashe y'ar iska ce amaryan daya aura, nan suka tashi suna cashewa, inda daka nan magana ta canza ana cikin rawa gimbiya Amina ta kamo kugun gimbiya zinatu tare da fad'in yau zaki cika min Burina tare da alkawarin da kikamin in Kinyi aure zamu fara soyayy.....


Gimbiya zinatu tace dole In cika miki wannan burin naki my love domin Ina cikin nishad'i, sannan bani da wata fargaba K..... Kafin ta k'arasa magana gimbiya Amina takai bakinta cikin na gimbiya zinatu ta Fara kissing dinta.....


Washe gari da safe Bariki ta tashi,kuma Alhmdlh ciwon cikinta ya warke bata jin komai, direct bank ta nufa inda ta tsaya tana jira 8 tayi, lokaci nayi ta shiga ta amsa check book ta rubuta adadin kud'in da take bukata, sannan ta bu'kaci a bata ATM, nan dai ta gama komai cikin awa d'aya, tun tana bank din take jin kaman hanjin cikinta zai fita, dan haka tana barin bank din taga inda ake siyar da waina Aiko nan taji ranta ya biya, zuwa tayi ta siya gashi ba'a cikin shago bane, akan benci kowa yake ci, babu yanda ta iya haka ta zauna tana ci, ita dai burinta taji wainar cikin bakinta, tana ci tana mamaki Wai itace take cin abinci a irin wajannan ga maza, gashi akan titi, Yarima ya fad'o mata a rai tare da tunanin ko wani hali yake ciki yanzu oho, wani hawaye taji ya zubo mata Mai zafi Sosai, lokaci d'aya taji wainar ya fitan Mata a rai, gashi tana jin tashin zuciya, da sauri ta tashi taje gefe ta Fara kwarara amai kaman zata fitar da hanjin cikinta, wani irin jiri taji tana ji, Wanda yasa dole ta zauna a wajan tare da lumshe ido, tana sauke numfashi dakyar, duk wannan abunda take ledan kud'in data ciro yana hannunta, mutanan dake wajan wasu sun tausaya mata, yayin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login