Showing 60001 words to 63000 words out of 124261 words

Chapter 21 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

duk jikinshi yayi weak amma haka Ya daure yayi toilet yayi wanka, bayan yayi wanka yaji karfi a jikinshi, agogon dake manne a bangon d'akin ya kalla yaga 5:06 da sauri ya koma toilet yayi alwala tare da fad'in wani irin bacci nayi haka?


Sallah Yarima yayi azahar da la'asar Bayan ya sallame yasa wata farar shadda tare dasa ba'kin hula yayi kyau Sosai sai gashi ya fito falo gimbiyar na kwance akan kujera tana danna waya....


Jin motsin mutum tare da kamshin Yarima yasa ta tashi da sauri ganinshi tayi cikin shiri.....


Kallonta yayi tare da fad'in where is my phone?


Ganin jikin nashi ya watsake yasa tace Bari in d'auko maka, sama ta haura Jim kad'an sai gata da wayoyin Yarima, bashi tayi ya amsa .....


Tare dayin gaba ya fara tafiya...


Da sauri tace Yarima Ina zaka? Ga abinci a dinning...


Yace Nop am not hungry yana fad'in haka yayi gaba abunshi domin babu inda yake son zuwa sai kaduna wajan Zainab domin yasan yanzu tana can tana tunanin ko lfya may be ma tayi fushi dashi koda ya fita fadawa suka zube suna Mai gaisuwa tare dayi mishi kirari, ganin yayi gaba yasa suka tashi suka bishi direct wajan motocinshi ya nufa tare da shiga wacce ake fita dashi in zasu fita amsan key din yayi tare da fad'a ma fadawanshi bana bukatar ku biyoni yana fad'in haka ya tada motar yayi gaba abunshi


Gimbiya kam ita a halin yanzu bata damu da fitan Yarima ba tunda bai gane ita ba virgin bace farin ciki ne fal cikinta kiran gimbiya Amina tayi tare da fad'a mata ta shigo dan Allah Yarima ya fita










*******
Bariki na zaune ita da habib wajan cin abinci, bariki dai ci kawai take amma ba dad'in abincin take jiba, dan gaba d'aya bata jin dad'in komai a bakinta, burinta kawai taji yarima ya kirata.......


Shi kam habib ci yake cikin jin dad'i da kwanciyan hankali, ganin bariki bata ci yasa ya tabe baki tare da fad'in iska na wahalar damai kayan kara, ni Wlh yanda nake dinnan banga saurayin da zaisa in dinga shiga wannan halin ba , haba bariki dan Allah kici abinci mu tashi mu tafi kin San yau akwai wasa zamu gwaggwaje duwai


Bariki tace Kai gskya ba tare zamu koma ba, dan Yarima yace min zaizo kuma na tabbata zaizo...


Habib yace kince wayarshi a kashe? Taya zaizo Kinga in zaki tashi ki tashi muje yanzu karfe nawa da har kike tunanin zai zo dan Allah tashi muje yau y'an nishad'i aka kira Wasan zaiyi dad'i yau.


Bariki tace uhm nifa yanzu kasan ban cika.......


Habib yace miye wani ka? Waye ka Ina mace akan wani dalili zaki dinga kaini jinsin da ba nawa ba ? Gskya banso yana maganan yana bata fuska.....


Zatai magana karan da wayarta ya farayi yasa hankalinta yayi wajan wayar tare da d'auka da sauri dan taga Sunan Yarima ne akan screen din wayar.... Tasa a kunnanta tare dayin sallama


Amsawa yayi har tana jiyo ajiyan zuciyarshi alaman yaji dad'i data d'auka yace my princess Ina gab da gidanku plz ki zauna da Phne dinki dan bazan gane ba ko kisa wani yazo bakin titi ya tawo dani


Tace ok bari habib yazo muna tare shima yazo tayani murna mumma fita amso Abu ne yanzu zamu dawo saiya tsaya ya jiraka


Yace OK tare da fad'in saina karaso


Bariki kallon habib tayi tace Yarima na hanya muyi sauri zaka tsaya a titi ku karaso gidan tare


Habib yace oh ni habiba yanzu Ina gansamemiyar budurwa in tsaya a bakin titi sai kace na fito good evening, tabe baki yayi tare da fad'in hakanan zanyi hakuri in tsaya tunda Yarima ne zai zo, zadai kisa y'an Maza suyi ta kallo na


Bariki dai bata ce komai ba tayi gaba ganin haka shima ya bita kud'in abincin ta biya sannan suka fita suka hau keke napep direct u/kanawa sukayi inda aka sauke habib a bakin titi ita kuma aka karasa da ita


Koda suka isa ta biya kud'in Keken tayi cikin gidan inda taci Sa'a duka iyayen bariki din data samo suna nan harda namijin yana zaune yana kallo zama tayi ta musu bayanin Yarima yana nan tafe, ta kalli mahaifin nata na Bariki Mlm musa tace dan Allah kayi komai yanda na fad'a ma ban son a sami matsala


Mlm musa yace baki da damuwa zainabu daka yanzu Ina son ki dinga cemin Abba ita kuma ya nuna Uwar bariki ta Karya yace ita kuma ki dinga ce mata Umma dan Kar mutane su gane kin San Gidan akwai mutane, sannan Idan Yarima din yazo ya tafi akwai wasu shawarwari da zan baki


Bariki tace hakane Abba ngd..... Suna cikin haka saiga habib ya shigo yana fad'in tashi kije yana waje yana jiranki


Tashi bariki tayi ta feshe jikinta da turare sannan ta kalli habib tace karka manta kayi komai yanda muka tsara


Habib yace babu damuwa komai zai tafi dai dai amma ki daina cemin kai kice min ki


Bariki dai fita tayi tunda ta fito idon Yarima Aliyu yake kanta ya rasa wani irin so yake mata da baya ji baya gani, tabbas yana son zainab wanda Abunda yasa yake kara Sonta harda irin shigar mutuncin da takeyi komai nata a rufe, ba irin y'an matan yanzu ba da suke nuna tsiraici a waje ba a gniñsu hakan shine Wayewa koyin haKan shi zaisa su sami mazajan aure,Wanda duk wani namiji mai kishi bazai auri macen dake fito da tsiraici waje ba sai dai yayi lalata da ita inma kikai shigan mutunci mutumin banza shakkar yi miki magana zaiyi dan baiga fuska ba domin yana yin shigarki zai bashi tsoro, duk namiji mai kishi bazai auri mace Mai fidda tsiraici waje ba, mace Mai tallan kanta waje ba..... Zuwan bariki ne ya Katse mishi tunani


Da sallama ta shigo cikin motar tare da rufe kofar motar,


Amsawa Yarima yayi tare da fad'in my princess Barka da yamma? Ya taro?


A hankali tace Alhmdlh tare da fad'in ya amarya?


Murmushi yayi tare da fad'in amarya tana lafiya.


Bariki ta d'anji haushi amma saita dake dan karya gane tana kishi


Yace nasan my princess ta gaji yau Sosai


Cikin ranta tace uhm maza kenan, Allah kadai yasan irin abunda yayi da matarshi Kafin yazo nan amma yazo yana mata dad'in baki yanzu.....


Karan wayanta ne ya Katseta kallon wayar tayi taga Alh madu ne da sauri ta kashe karan, tare da tunawa yace Mata yau zai zo,


idon Yarima na kanta yace pick your call


Kafin tayi magana wani kiran ya shigo kallon Yarima tayi taga shima ita yake kallo, kara kashe wayan tayi karan ya d'auke..... Hannu ya bata alaman ta bashi Phne din


Gabanta taji ya fad'i, sai tayi kaman bata ga hannun ba


Duk abunda takeyi idon Yarima na kanta murmushi yayi tare da fad'in Zainab mai kike boyewa bani phone dinki......










*plz kuyi min hakuri ba kullum zan dinga muku posting ba saboda wani dalili amma inna sami lokaci zan dinga kokari Inayi kullum din*








~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 4*








*MAZA KUJI TSORAN ALLAH LOKACIN DA KAKE NEMAN MACE KOMAI TACE TANA SO SAIKA MATA, WANI ABUN MA BATA TAMBAYA KAKE MATA, IN ANYI AURE DUK HIDIMAR DA KAKE MATA SAIKA DAINA, KUMA BAWAI DAN BAKA DA HALIN YI DIN BANE, IN BAKA KYAUTATA MA IYALINKA BA WA ZAKA KYAUTATAMA, SAI KAJE KANA FAD'A AI BATA KWALLIYA BATA MAKA ABU KAMAN DA KAFIN KA AURETA, HMMM TAYA ZATA MAKA KWALLIYA TAYU KUD'IN POWDER DINMA BAKA BATA, KO KUD'IN KITSO A INA KAKE SON TA SAMI KUD'I TAYI??? DA LOKACIN DA TAKE GIDANSU TANA DA KYAU KOMAI NATA ABUN SHA'AWA AMMA KA AURETA KA MAIDATA TSOHUWAR KARFI DA YAJI, BABU KUD'IN LALLE, BALLE NA TURARE😫 HABA MAZA MAI YASA KUKE HAKA?? IN KAJE GIDAN ABOKIN KA YA BAKA ABINCI MAI DAD'I SAI KAZO KANA ZAGIN MATARKA BATA IYA GIRKI BA, BAYAN KAINE BAKA BATA KUD'IN CEFANE WANDA ZAI IYA HAR AYI MAI DAD'IN BA, WLH KUJI TSORAN ALLAH MAZA MASU IRIN WANNAN HALIN DAKA RANAN DA AKA BAKA ITA A MATSAYIN MATARKA KOMAI NATA YA RATAYA AKAN KA, ABUNDA MUTUM YAKE GANIN BA KOMAI BANE ZAI IYA KAISHI GA HALAKA, IN KANA DA HALI KA FARANTA MA MATARKA YANDA INTA FITO ZA'A CE MATAR WANCAN NE SABODA AN GANTA FES, AMMA IN AKA GANTA SABANIN HAKA ZAGINKA ZA'AYI TUNDA ANSAN KANA DASHI PLZ MAZA KU GYARA DOMIN ALLAH ZAI TAMBAYEKU TUNDA KANA DA HALI DAMA BABU NE SAI AYI HAKURI*












Kallonshi tayi cikin tsoro tare da fad'in Yarima plz ka barshi Kawu nane yake kira, so yake Inba ma Abba, wayan Abba ne ya sami matsala in an kira yana ji amma ba'a jinshi, inna d'auka nace bana gida zai iya zuwa har gidan ya sami Abba da Umma yayi musu fad'a akan Mai yasa zasu dinga bari Ina fita da yamma, kuma yanzu inna shiga Gida Umma bazata Bari in fita ba, dan yanzu tana tunanin ina d'akin makwabciyan mune.....


Yarima Aliyu ajiyan zuciya ya sauke, lallai Zainab gidansu gidan tarbiya ne, sabanin yanzu da iyaye suke sakin y'ay'ansu suna abunda suka ga dama, har ma wasu zaku ga kaman su suke juya nasu iyayen sai abunda sukace iyayen nasu keyi..... Amma a fili sai yace Mata my princess na fad'a miki tun Farko ai ki bani dama inga Abba kinki, yanzu Idan yazo ya gammu ya kike so inyi???


Cikin sanyin murya tace bazanji dad'i ba, domin na tabbata Abba zaiyi fushi Sosai, amma Yarima tunda harna yarda yau kazo gidanmu hakan ya kamata ya nuna cewa Ina son Kaga Abba din.....


Wani irin murmushi Yarima ya saki cikin jin dad'i tare da furta Kalman Alhamdullilah cikin ranshi, domin wannan maganan da Zainab tayi mishi yasa shi cikin farin ciki Sosai..... Kallonta yayi cikin ido tare da fad'in my princess kin tabbata kina son inga Abba.???


Ganin bazata iya juran kallon cikin idonshi ba yasa ta kawar dakai gefe tare da fad'in eh Ina so ka ganshi, domin hakan ya kamata Ayi tun Farko


Murmushi yayi tare da fad'in zan iya ganinshi yau?


Tace eh amma sai dai ka tura wani yaje ya maka sallama dashi duk da ban tunanin ya dawo amma kuma hala ya dawo din dan lokacin dawowarsa yayi .....


Dariya Yarima yayi tare da fad'in am joking bazan iya zuwa ni d'aya ba, but zuwa jibi Zanzo da Usman da wasu friends dina sai mu ganshi mu nemi izinin zuwa zance Kafin manya su shiga


Murmushi tayi tare da fad'in Allah ya taimaka


Ya amsa da Ameen, tare da fad'in where is my promise?


Kallonshi tayi taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kanta gefe tare da sakin murmushi sannan tace wani promise??


Yace abunda ya faru wajan Walima.


Dariya tayi wanda ya kara mata kyau sannan tace Yarima ban samu daman d'aukan komai ba saboda jama'a Wlh kunya duk ta hanani gashi mune masu saukan..... Amma munyi hoto a gida da kawaye na Wanda mukai saukan tare


Yace OK Nasan duk kinfi yin kyau


Tace a'a tare da danna wayarta tace na tura maka ta whatsapp


Murmushi yayi ya d'auko wayanshi ya fara dannawa, yace my princess duka sun sa nikaf Kema Aida kinsa ko so kike ayi ta kallemin ke


Dariya tayi tace a cikin gida nefa babu Mai kallo na sai Kai ta karasa maganan tare da rufe fuska


Murmushi yayi tare da fad'in my princess yunwa nake ji banci komai ba tunda safe.....


Da sauri ta kalleshi tare da fad'in mai zakaci in kawo ma? Yarima taya zaka zauna har yanzu bakaci komai ba ulcer zai kamaka plz mai zaka ci??


Murmushi yayi cikin jin dad'i domin ganin yanda ta nuna kulawanta akanshi, ya tabbatar mishi da cewa tana sonshi Sosai......


Katse mishi tunani tayi da fad'in Yarima ko in kawo maka tea kasha Kafin in dafa maka wani abu??


Yace a'ah ki barshi zanje Inci abinci yanzu


Shuru tayi tana d'an nazari can tace ko in kira habib yaje ya kawo ma wani abu kaci?


Hannunta ya koma tare da ri'ke mata su duka biyun yace my princess karki damu zanje wani waje Inci, ko zaki raka ni?


Da sauri tace eh muje Kafin Abba yasa Umma ta kirani a d'akin da take tunanin ina ciki inya dawo Kar yasa a kirani yaga bana nan koda yake Nasan ma ya dawo ganin habib Nasan bazai damu daya ganni ba.


Murmushi yayi yace Nop Bari inje alone banso Ayi miki fad'a my princess


Tace Yarima plz muje kaci abinci habib na nan bari in kirashi sai muje tare zance ma Abba zani maraban jos In kwana bazai hana ba sai muje kaci


Yarima yace ok my princess


Fita tayi ta shiga cikin gidan Jim kad'an sai gata ita da habib da abbanta na Bariki Sun fito daka gani ya fito raka habib dinne a yanda Yarima ya fahimta kenan🤣 har bakin titi ya rakasu sannan ya dawo ya shiga gidan yarima yana kallonshi cikin ranshi yace wannan daka gani Dattijo ne yana yin kamalan shi ya nuna ma Yarima hakan🤣🤣🤣 kai ana abu a duniya sai yasa akace sometimes abunda ka gani bashi bane gaskiya......


Yarima tada motar yayi shima ya nufa titi bai gansu ba kiran Zainab dinne yasa ya dauki waya tare da fad'in my princess where are you?


Tace muna gaba wajan NDA Abba saida muka shiga mota ya koma shine muka sauka a nda


Yarima yace ok ga ninan zuwa, Yarima juyawa yayi ya nufi nda din ya d'aukesu ta shiga gaba habib kuma baya, Yarima ya kalleta yace Ina zaki kaini Inci abinci??


Ido ta d'an zaro tare da fad'in ni Ina na sani tunda ba zuwa nake ba


Habib dake Bayan motar yana jinsu cikin ranshi yace bariki ko y'ar iska ke inane baki Sani ba cikin garin kaduna yanda kuka san map din garin ne a kanta amma yanzu tana wani nuna ita ta Allah ce..... 🤣


Yarima wani babban restaurant ya faka motarshi wajan yayi mugun had'uwa gashi babu irin tarkacen mutane a wajan, daka ganin alama wajan ba kowa ke zuwa ba sai y'an gayu na gaske, private waje suka zauna, shidai habib cewa yayi cikin mutane zai zauna danya dinga ganin masu shiga da fita


Bariki tace muje tare mana


Yace ke barni in zauna nan ko zanyi kasuwa


Bariki dai dariya tayi sannan ta nufi ciki inda Yarima yake domin yace baya son su zauna inda akwai mutum ko d'aya dan baya son ana kallon mishi ita.......


Yarima ya fad'a abunda za'a bashi bariki kam tace ta koshi Yarima yace dole taci wani abu, babu yanda ta iya tasa a kawo mata snack dan a koshe take shima takeaway tace tana so, yarima yace abar snack din in Sun tashi fita zata zaba abunda take so.


Wajan 15 mnt aka kawo ma Yarima abinci lokacin ana ta kiran sallah magrib tashi yayi ya Kalli bariki tare da fad'in bari inyi sallah.


Tace OK tare da kallon Wanda ya kawo abincin tace maida kayan inya dawo sai kayi warming din abincin ka kawo.


Mutumin yace ok ma, Yarima bai tafi ba saida yaga mutumin ya fita dan ya Lura dashi yanda yake kallon zainab kaman yana son yi mata magana.....


Yarima Aliyu na fita kam saiga mutumin ya dawo da sauri yana fad'in ma plz I need to talk to you.


Bariki tace lafiya maiya faru?


Yace ma ance in amso phone number d'inki ne


Tace what? Are you mad da aurena inzo da mijina kazo kace min in baka phone number dina get lost frm hare Kafin mijina ya dawo ya ganka


Mutumin yace sorry ma Nima na fad'a mishi kina da aure saboda irin shigarki amma yace babu damuwa koda kina da aure in amso mishi number d'inki


Bariki tace Waye zan iya ganinshi??


Yace let me go and ask him in yace in kawo ki sai kizo


Bariki tace ok yana tafiya saiga Yarima ya dawo Allah yasa bai ganshi ba


Bariki tashi tayi tare da fad'in har an idar kiran mutumin tayi da baiyi nisa ba yazo tace Kawo Mai abincin


Yace OK ma


Bai dad'e ba saiga abincin ya kawo, Yarima coffee ya fara sha sannan ya kalli bariki yace my princess feed me plz


Dariya tayi tare da fad'in feed ur self u r not a baby


Yarima kallonta yayi tare da fad'in oh really? Ni baby dinki ne


Ido ta rufe alaman jin kunya


Hannunshi yasa yana kokarin cire mata hannunta da tasa ta rufe fuskanta ..... Muryan Wanda ya kawo abincin ne yazo yana fad'in ma he said that you can come he is waiting for you......








*Plz kuyi ma my hrt addu'a Allah ya bata lfya my princess my queen phareejay, Allah yasa kaffara ne🙏🙏😫😫*






*kuyi manage plz Nima ba wani lfya gareni ba Nayi muku ne dan kusa my hrt a addu'a plz 🙏🙏*










*plz ku dinga hakuri da typing error banda tym din editing*








~MARYAM OBAM~




*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 5*








*Y'AR UWA KOMAI MUJINKI YAYI MIKI AMSA KIYI GODIYA TARE DA NUNA FARIN CIKIN KI DUK KANKANTAR ABUN KARKI RAINA, DOMIN YAU IDAN MIJINKI YA KAWO MIKI PURE WATER YAGA KINA TA MURNA TOH GOBE SWAN WATER ZAI KAWO MIKI YAGA WANI IRIN MURNA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login