Showing 66001 words to 69000 words out of 124261 words

Chapter 23 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

Yarima ne? Naga yanda yake fushi yana ta gudu dama kaman zai tashi sama, sai yasa Nayi mishi karya ya saukeni Kar yaje ya jefamu kan trailer mu mutu, ban ajiye Mai min addu'a ba, ko d'an auren da mata keyi koda shiga ki fito ne ace kadai taba koshi Nayi ai babu laifi......


Bariki tace Hmmm Allah ya kyauta, tare da fad'ama habib abunda ya faru.......


Habib yace amma da iskanci kike akan wani dalili zaki bama wani dama, ai gashi yanzu kinja ma kanki sai ki nemi mafita, ni naga kaman ma nafi son ki auri Yarima domin in Ina wajan da yake Mai kamun kai nake zama, amma ke in banda tsaban iskanci har kice zaki ga wani kuma kin San da wanda kika je wajan.....


Bariki tace ai ka tsaya ka.......


Habib dakatar da ita yayi tare da fad'in Wlh bariki ban son bura uba, akan wani dalili zaki dinga kaini jinsin da ba nawa?... Gskya banso


Bariki tace kwantar da jijiyoyin cillarka.....


Tashi yayi tsaye tare da kama kugu yana fad'in bariki sanin kanki kin San wacece habiba, wlh banki inyi tsirara ba ni dake mu daku......


Bariki tace ah zauna kawata Ina ni Ina fad'a da babbar kawata Allah ya baki hakuri Hjy habiba ikon god....


Zama habib yayi yana fad'in ah toh in banda iskanci taya zaki dinga had'ani da maza har ki dinga cewa in kwantar da jijiyon cilla ta, ni Ina naga jijiya ni da nake da Fata, ai jijiya sai y'an maza ya karasa maganan yana dariya


Itama bariki dariyan ta saki tare da fad'in nidai Wlh na k'osa Yarima ya turo ayi bikin mu Ina gama istabra'i.....


Habib yace yauwa Ina jinki kina ban labari.....


Bariki tace Hmmm nifa Wlh nace ina son ganin mutumin ne saboda muje tare da Yarima amma Yarima yayi min mummunan tunani, yana ganin inda bai dawo ba a tunaninshi zanje wajan mutumin ne.....


Habib yace Kema maiya kaiki?? Ni Wlh ba tun yau na Lura da wannan Yarima dinba akwai shegen kishi Wlh bariki naga kaman kina wasa, samun Yarima Aliyu ba karamin Sa'a bane, inko kika bari ya kubce miki Wlh kinyi Asara, Kut Aina sha fad'a miki inda ni yace yana So Wlh da yaga yanda ake soyayya amma keda yace yana So kina iskanci, namiji har namiji wlh Yarima ya had'u so handsome.......


Bariki tace uhm, waya ce ina wasa da Yarima?? Ni kam duniyar nan banga Wanda nake jin tsoro ba tare dajin tsoran yasan koni wacece ba sai Yarima Aliyu, Kinga kawata inda bana son Yarima yaushe zan damu yasan koni wacece?


Tabe baki habib yayi tare da fad'in ai gashi yanzu kina kokarin ki nuna mishi halin naki ke gindi babu control daka Kinji ance ana son ganinki kin yarda, Allah yasa ba fushi yayi ba sai yasa ya kashe wayoyin nashi ba.


Bariki tace uhm....


Habib yace kyace uhm mana tunda kin shuka tsiya...... Ni tashi muje muyi rawa ko naji sanyi kwana biyu ban girgiza duwaiya ba.....


Bariki tace wa? Rufamin asiri Aini inka ganni a lahira kaini akayi haka kawai tsautsayi ya kaini Yarima yazo a'a Wlh bada niba wai ance da tsohuwa tayi zina......


Shewa habib ya saki tare da fad'in kunji salo nidai Kinga tunda banda tsayayye balle in takura kaina nayi gaba dan yau sai na karkad'a kayan alatu


Bariki tace nan akafi auki....... Lah mota ta na barta a u/kanawa Wlh Yarima ne ya caza min Kai sai yanzu na tuna,


Habib yace tsiyar y'an mazan nan kenan ai sai yasa ni naki yarda Nayi aure, suna auranka suna kaika ciki ka zama nama, sai yasa nake tatsan su a waje... Ke gaki ko ciki baki shiga ba har an fara miki duk da Kece da laifi


Bariki tace uhm bari in kira ubana na Bariki ince a kulan min da motar ni saida ta zanyi ma gobe inna fita


Habib dariya Ya saki tare da fad'in ni sai naga kaman ma kina kama da mutumin Wlh.....


Bariki dariya tayi tare da fad'in amma Allah ya isa......


Habib fita yayi yana fad'in sai da safe zani wajan wasa


Yana fita bariki tasa ma kofarta key ta kwanta tare da kiran babanta na Bariki ta fad'a Mai ya kula da motar, sannan ta kara da fad'a Mai Yarima zai zo jibi dan neman izinin zance..... Tace Bari koma dai miye gobe mayi magana in nazo Abba.










******
Driver din alh madu koda ya koma abunda bariki ta fad'a haka Ya fad'ama Mai gidan nasa,.


Alh madu dariya yayi tare da fad'in yaro man kaza, yaro yaro ne yaro bai San wuta ba saiya taka, lallai Bariki har yau baki San Waye alh madu ba, amma naga kina son in fito in nuna miki Waye ni dan naga kanki yana rawa very soon zanyi maganin ki, sannan Indai bani zaki aura ba sai dai mu zauna muci gaba da mu'amala yanda mukeyi, dan bazaki aura kowa ba inba niba.


D'aukan wayanshi yayi ya doka ma Hjy babba kira, duk da yasan ba lallai bane ya d'auka domin tun dazu yake ta kira bai d'auka ba, harya kusa tsinkewa aka d'auka......


Hjy babba ya d'auka tare da fad'in Allah ya taimaki Sanata alh madu daka majalisan dattawa sai Villa insha Allah


Alh madu yace kana ina duk inda kake kazo yanzu sannan ina son kazo min da bariki kota wani hali kafarka kafarta yau nake bukatar ganinta cikin daren nan a guest house dina ......


Hjy babba yace an gama ranka ya dad'e yanzu zaka gammu


Bayan alh madu ya kashe wayan, hjy babba yace Toh fah hala bariki ta kara Karta Mai rashin mutunci ne Bari inje d'akinta inji y'ar bura ubar itama har mota ya bata ita da bata iya cin arziki ba inda Tana mishi yanda yake so Aida tafi karfin abunda yafi wannan motar duk da tace baida kayan aiki abu kaman ayabar yara kona jarirai ne tace ma oho ni na manta..... Gaba yayi tare da nufa d'akin bariki data fara bacci nocking yaita mata da karfi.......


Tashi tayi tare da sakin tsaki tana fad'in Waye ne??


Muryan hjy babba taji yana fad'in nice bud'e kofar


Bariki tashi tayi ta nufi kofar tana murza ido, bud'e kofar tayi taga hjy babba dinne tace lafiya cikin wannan daren???


Hjy babba yace lafiya mana, ko 12 bai karasa ba kike cewa cikin wannan daren sai kace nazo miki da karfe biyun dare, Kinga ni bama wannan ya kawo niba, nazo ne muje wajan alh madu dake yanzu ya kirani yace yana son ganinki dan Allah shirya muje......


Bariki tace hjyta babu inda zani domin wlh ni aure zanyi kuma istabra'i nakeyi dan so nake inyi tsarkakken aure.....


Hjy babba yace au me????!


Tace aure.......


Yace gaskiya banji dad'in wannan maganan ba Wlh Ina ke ina wani aure yanda kike da kyau da lafiya ga kuruciya, gskya banji dad'in jikina ba wai mahaukaciya taji duka...... Gaskiya bariki ki canza shawara ai yanzu ne kike da dama kuma shi komai na duniyar nan lokaci ne gwara kici naki lokacin daka baya kyayi auren in kin daina tashe amma haka kawai tsigai fiyau kina tashe ki wani cuta kanki Muma ki cucemu dan abunda muke samu saboda ke mu daina samu, ki makale waje d'aya da Sunan kinyi aure gskya raina ya baci


Bariki tace hjyta nidai bacci nakeji yanzu wlh kuma shi nakeyi kika tasheni dan Allah hjyta ki bari in koma bacci


Hjy babba yace oh yau naga ikon Allah, amma dai wlh bariki kin canza kuma Nasan yanzu bakya d'aukan maganan kowa saina Shegiyar habiba Dan naga yanda take shige miki, karki manta Nina Fara saninki Kafin habiba kuma saboda ni kike nan gidan.....


Bariki tace hakane hjyta kena Fara sani Kafin habiba, and kuma kinmin hallaci Wanda bazan manta dake ba, sai yasa har gobe nake mutuntaki hjyta


Hjy babba yace bariki Indai kina ganin mutuncina kizo muje wajan alh madu ni koda bazaki yarda dashi ba, dan Allah kizo muje Yadai ga na kawo mishi ke domin yana ganin mutuncina ko so kike ya daina, sannan inma Kinje shida kika ce ayabar tashi kaman ta yara Aiko yayi ba komai za kiji ba....


Bariki tace nifa hjyta gskya babu inda zani domin na riga na yanke hukunci kuma na fad'a ma driver dinshi sa'ko ya bashi, wato shine daya fad'a Mai shine ya Aiko ki, Toh wannan karan zaisha mamaki domin babu inda zani kuma na fad'a


Hjy babba yace oh na shiga uku an fasa aurena haka gasau kike fad'a babu inda zaki??.... Amma kam in kikai haka baki hallaci ba bariki ki duba fah har kyautar mota yayi miki......


Bariki tace Aiba ro'kansa nayi ba shiya d'auka ya bani Dan haka kuma ta bayu,.


Hjy babba yace dan Allah bariki Kar kisa nidai ya daina ganin mutuncina ki daure kizo muje koda zaginshi za kiyi nidai yasan na kawo ki, sannan in Kinje kya fad'a mishi abunda ke ranki Kinga tayu ya barki ya nemi wata......


Jin haka yasa bariki tace muje, inji uban Mai yasa ga mata Nan a gari wanda suka fini iya zuba bariki bai nema ba sai ni, muje inji dalili Danni Wlh na gaji da wannan iskancin nashi.... D'akin ta koma tasa hijab dogo har k'asa akan rigan baccinta tare da rufe d'akin tace ma Hjy babba muje.......


Bakin titi suka nufa da yake garin yau ake wasa akwai mutane birjit, samun Abun hawa bai musu wuya ba, inda suka sami Mai keke napep suka shiga, direct gidan alh madu ya kaisu hjy babba ya biya kud'in sukai nocking Mai gadi ya bud'e dan yasan hjy babba da bariki, kofar falon alh madu a bud'e yake dan haka suka shiga baya falo bariki bedroom dinshi tayi taganshi tsirara yana video call daka gani da wata mace yake, alh madu waya yake bai Masan bariki ta shigo ba saida yaga hasken wayarta alaman an d'aukeshi hoto...... Da sauri ya tashi yaga bariki ce murmushi ya saki tare da fad'in Kaga manyan mata maganin kanana, nufanta yayi tare da janyota jikinshi Wanda babu kaya yace Bari in d'auke mu kit kit ya fara d'aukansu a wayarshi bariki kokarin Jan jikinta ta farayi tare da fad'in miye haka ne Dallah sakeni, andai ji kunya wlh kaje can ka karata da sauran y'an iskan y'an matanka badai bariki ba womanizer kawai fuuuuuu ta fita ta barshi yana kiranta ganin ta fita yasa ya fara saka kaya da sauri dan ya cin mata dan yasan Indai ta zille Mai shida ya kuma ganinta sai anji jiki tunda yanzu tazo yau yake son sanin Mai take nufi domin ya shirya Mata kota yarda ta aureshi kota fasa maganan auren da take fad'in za tayi suci gaba da cin juna babu aure, kuma yayi alwashin cikin biyu dole ta zabi d'aya.......










*Ina masoya novel's dina ina muku albishir da novels din da nayi baya wanda babu su a Wattpad zan fara sa muku su wanda na fara sa muku AMINIYA TA CE ,inna Gama sashi zan d'aura muku wani shima insha Allah*












~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 7*


















Alh madu riga kawai ya iya samu yasa ya fito.....


Bariki fuuuu ta fita Hjy babba ya bita yana fad'in bariki Yadai Anya lafiya kuwa?


Bariki bata kulashi ba taci gaba da tafiya cikin sauri


Yace bariki Wai Mai ya faru koya mutu ne Alh madun ???


Bariki tace Aidama mutuwar yayi da nafi kowa murna dan iskan tsoho tsinanne.....


Hjy babba yace oh ni amma gaskiya bariki baki da hali.....


Hango Alh madu tayi yana nufosu da sauri ta fita daka gidan....


Hjy babba ya bita yana fad'in ta tsaya mana ga Alh madu dinnan ya fito yana kiranta....


Ko kallon hjy babba batayi ba ta wuce abunta tako yi Sa'a taga wani mai mashin da sauri ta tsayar dashi tahau, tana fad'a Mai inda zai kaita, mai mashin yace dubu d'aya bata musa ba dan itama tasan dare yayi ba kowa bane zai kaita maraban jos yanzu a mashin ba......


Hjy babba wajan Alh madu ya koma wanda shima alh madu ya koma yasa wando ya fito......


Alh madu bayan ya fito ya kalli hjy babba yace tana Ina??


Hjy babba yace aita wuce ta sami Mai mashin tahau.


Kai Alh madu ya d'aga alaman yaji tare da cema hjy babba ina zuwa, bedroom ya shiga sai gashi ya fito da bandir din dubu d'aya dubu d'ari kenan yaba ma Hjy babba tare da fad'in kaje zan nemeka.....


Hjy babba amsa yayi yana ma alh madu godiya tare da fita........










**********
Bariki ce kwance a d'aki tana ta kiran number din Yarima ya'ki d'auka Dan tsaki taja tare da fad'in bazan kara kira ba, in kaga dama ka kirani, sa wayar tayi a silent ta fad'a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata jallabiya yayi mata kyau ta yafa gyalen jallabiyan ta d'auki jakarta da wayanta ta danna ko zataga miss call din Yarima amma shuru babu ma wanda ya kirata, tsaki taja sannan ta fita cikin damuwa, had'uwa sukayi da hjy babba......


Ja yayi da baya ya kama kugu kaman wanda zaiyi dambe, yace amma ke kam bariki ko ri'kakkiyar y'ar iska, in banda iskanci da wulakanci ki k'ekashe ido kici min mutunci, Nina rasa mai yasa kika tsani wannan mutumin yana sonki kina gudunshi kaman Kinga kashi......


Bariki tace haba hjyta wannan jaraban fah da tujara da sassafe?


Hjy babba yace aike kika so wlh bariki baki da hali, gwara ki canza wannan ba'kin halin naki tun wuri..... Yana fad'in haka yayi gaba yana ta surfa bala'i shi'a dole bariki ta bata mishi rai gwara yayi gaba karma ya tsaya bata ma kanshi lokaci wajan magana da ita.....


Bariki ganin haka ta girgiza kai tare dayin gaba tana fad'in kaji dashi wai anyi ma mai dami sata..... Bama Alh madu ba babu wani namiji da zai kara sanin ko ita wacece domin ta tuba abunda ta aikata baya shima tana ro'kan gafaran uban giji akan ya yafe mata duk da itama inta zauna wani zubin takanyi mamakin irin abunda ta zuba a matsayinta na y'a mace Mai shegen kunya a da, amma lokaci d'aya ta sauya Wanda har yanzu ta kasa gane dalili, sai dai wani zubin takan kalli abun a matsayin Tana son musguna ma iyayenta ne sai yasa take hakan, duk da shima hakan bawai ya tabbatar mata a rai bane kawai inta fad'i hakan ne take ganin hakan shine silan fad'awanta wannan mummunan harkan.....


Bariki u/kanawa tayi inda ta d'auki motar da Alh madu ya bata ta siyar wajan y'an motocin dake u/kanawa ta wajan NDA, bata amshi kud'in cash ba transfer tasa suka mata, sannan ta wuce gidan iyayenta na bariki,


inda abbanta na Bariki ya bata shawara akan ta dawo nan da zama domin d'an gidan sarauta zata aura Karta sami matsala dan inta sami matsala suma suna ciki tunda har dasu a cikin aikin.....


Bariki tace hakane nima nayi wannan tunanin amma tashi na daka can zaiba wasu dama su Fara bincike akan abunda nake shiryawa amma zan dinga kwana a nan camma ina kwana zan dinga diban kayana da kad'an Ina kawo su nan har lokacin bikin yayi a wuce wajan,


Ranan bariki a gidan ta wuni tana ta jiran kiran yarima amma shuru babu kira babu sa'ko, gaba d'aya jikinta yayi sanyi ta kasa sukuni dan tsaki taja tare da kiran Layin Yarima taji line busy alaman yana waya..... Ajiyan zuciya ta sauke tare da fad'in kenan da nice bazaiyi waya ba Hmmmm, babu damuwa ai gobe kace zaka zo wajan Abba zan gani in zaka zo, dan nasan baka karya alkawari saida wani dalili...... Bariki wajan 6 tabar gidan ta koma maraban jos akan cewa gobe zata zo da sassafe insha Allah dan Yarima tana tunanin zai zo......


Bariki koda ta koma ta kasa sukuni gaba d'aya, domin rashin jin muryan Yarima ya sata cikin wani hali, sai yanzu ta kara tabbatar ma kanta tana son Yarima Sosai, kuma zata iya aikata komai akan sonshi Indai Abun bai sabama Shari'a ba duk da tasan wannan auran da zatayi da Yarima bai dace tayi ta wannan hanyar ba, toh amma yata iya tunda haka tata kaddaran tazo Mata, yanzu inta koma Gida AI Yarima zai gane karya ta shirya mishi tun Farko, wani hawaye ne mai zafi ya silalo mata tabbas duk Wanda yabar Allah...... Allah shima ya barshi...... Ta fad'a wannan halin ne duk saboda aikata sabon Allah, gashi Allah ya jarabceta da son Yarima wanda bata son ta rasashi, saboda son da take mishi yasa tana kokarin kara jefa kanta cikin wani bala'in ta tabbata koda Yarima Aliyu ta bashi Labarin ta ya hakura ya amsheta a matsayin mata, toh iyayenshi fah? Ya zasu d'auketa da sauri ta tashi tsaye domin bata taba tunanin iyayenshi a duk cikin wannan abunda take shiryawa ba, ya iyayen Yarima zasu d'auki abun, gidan sarauta gidan Kima da daraja, gidan da babu wasa a cikinsa, kuka ta fashe dashi Mai sauti lallai ina kara jefa rayuwata cikin halaka....... Kuka take Sosai tana surutai ya iyayen Yarima zasu d'auki wannan abun, na tabbata bazasu hakura ba su, sai Sun hukunta ni akan wannan laifin da nake shirin aikatawa, bariki gidan sarauta ne gidan su Yarima ba gidan wasa bane, irin wannan auren bai kamata kiyi shi a gidan sarauta ba, lallai sarauta ba wasa bace, sarauta ba karya bane, ido ta lumshe tunawa da yanda Yarima yakeyi kana kallonshi kasan akwai jinin sarauta a tare dashi Sosai yanda yake abu...... Lallai Indai Ina son Yarima ya kamata in fad'a mishi koni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login