Showing 69001 words to 72000 words out of 124261 words

Chapter 24 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

wacece...... Da sauri kuma ta Fara girgiza kai tunawa da tayi yana fushi da ita akan ance ana son ganinta, jiba yanda ya nuna kishin shi akai inaga yaji tana bin maza kuka ta kuma saki na tabba bazaka aureni ba Yarima inma ka yarda Wlh iyayenka bazasu Bari ba, dan gidan sarauta baza'a Bari ya auri karuwa ba k'asa tayi tana kuka lokaci d'aya kanta ya fara mata wani irin azababban ciwon kai ga idonta daya kad'e yayi ja, Kun San farar mace ba wuya, in tayi kuka a gane, kwanciya tayi a k'asa tana kuka, wayarta keta kara amma ta kasa tashi ta d'auka dan bata jin zata iya tashi domin yanda take jin kanta.......... Lallai rayuwar bariki ba komai bace face kaskanci da wulakanci Wanda ta tabbata bata ga komai ba sai ranan da Yarima yasan ko ita wacece.... Bugun kofar da ake mata ne yasa kanta yake ta kara mata ciwo dakyar taja jiki ta tashi ta bud'e.....


Habib yaja baya yana fad'in ya ilahi Mai zan gani haka?? Bariki baki da lafiya ne? Maiya sameki?


Bariki kanta ta nuna mishi da hannunta alaman kanta na ciwo


Habib cikin tausayin bariki yace sannu Allah ya baki lfya, Yarima yazo yana jiranki har yaje ya nemi izini wajan mahaifinki na Bariki,......


Da sauri bariki tace dagaske? amma gobe yace zai zo


Habib yace Toh gashi yazo yau, shima Nasan yayi kewarki sai yasa yazo dan haka maza kizo muje yana Bayan layi yana jiranki, yace ya kira baki d'auka ba shine ya kirani, shima abbanki na Bariki yaita kira baki d'auka ba yana son fad'a miki wai baki dad'e da tafiya ba Yarima yazo yasa akai sallama dashi.....


Bariki da sauri tayi toilet ta wanke fuska sannan ta kara feshe jikinta da turare ta yafa gyalen jallabiyan data cire sannan ta fita, suka jera Ita da habib.


Har wajan da motocin Yarima suke suka nufa, yau yazo da fadawa motoci har biyar kaman yanda Ya saba zuwa da, tun daka nesa Yarima ya gane Zainab ce ke tawo wa, amma ganin kayan jikinta jallabiya sai yasa shi jin kishi domin a ganinshi bai kamata tasa jallabiya ba duk da komai nata a rufe yake, ido ya lumshe tare da fad'in yanzu Nasan haka aketa kallon mun ita,


Usman dake zaune kusa da Yarima yace Yadai naga kana ta Jan tsaki??


Yarima yace plz bamu waje zan kiraka ku gaisa inna Gama magana da ita.....


Usman dariya yayi sannan ya fita


Koda bariki ta karaso habib ya bud'e Mata motar sannan ya juya.....


Bariki shiga tayi idonta nakan Yarima shima idonshi na kanta, bayan ta shiga ta rufe motar......


A hankali Yarima ya furta my princess maiya sameki?? Mai yasa kikai kuka tell me plz mai yake damunki? Duk a tare ya jefo mata wannan tambayoyin..... Idonshi na kanta yana jiran amsa daka gareta......


Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fashe da kuka Sosai....


Yarima cikin tashin hankali ya janyota jikinshi tare da rungume ta, yana sauke ajiyan zuciya tare da shafa mata baya, a hankali ya fara magana my princess plz stop it kin San bana son kukanki, plz tell me Mai yake damunki????


Tana manne a jikinshi ta Fara magana Yarima kasan ina Sonka bazan iya juran rashin kaba koda na awa biyu bane, yau inata kiranka kaki d'auka, jiya na kira baka d'auka ba, na kara kira naji wayarka a kashe yau tunda safe naita kira kaki d'auka... Kuka taci gaba dayi lokaci d'aya kuma taci gaba da fad'in Yarima kasan ko kad'an Ina tare dakai bazan kula wani ba, yakamata ka yarda dani ka yarda da irin son da nake maka, yarima dan Allah karka kara fushin da inna kiraka zaka ki d'aukan min waya, koda zaka d'auka ka zageni dan Allah ka d'auka rashin jinka yana sani cikin wani hali n...... Kuka ne yaci karfinta Sosai wanda yasa dole tayi shuru


Yarima kasa magana yayi sai bayanta da yake shafa mata, jin sautin kukan nata har cikin kanshi yasa ya d'ago ta tare da kallon fuskanta da ya baci da kuka Sosai, murmushi Yarima yayi tare da fad'in Kinga kina ta zubar min da hawayenki, my princess plz ki daina I trust you sai yasa na dawo gareki and naje na sami Abba ya yarda ya bani izinin zuwa zance har mu fahimci juna manya su shiga, ya kuma nunamin yaji dad'i yanda na Fara neman izini sabanin mazan yanzu basa haka, yace ya yaba dani ya yarda da irin tarbiya na, duk da na fito gidan sarauta ban nuna iko ko sarauta ba wajan zuwa wajanshi, my princess Abba mutumin kirki ne, lallai na yarda iyayenki Sun baki tarbiya domin Abba yayi min magana na dattaku....... My princess I really love you, Ina miki son da nida kaina ina mamaki, jiya nayi fushi dake amma gaba d'aya na kasa sukuni, saida nazo na ganki na samu nutsuwa...... Ganin ta lumshe ido yasa ya kura ma fuskanta ido, ji yake kaman ya tafi da ita, yana Mata son da bai taba tunanin Zaima kowa irinshi shiba,


Hura mata iska yayi a fuska wanda yasa ta bud'e ido da sauri idonsu ya had'e suka fara kallon juna, cikin ido gaba d'ayansu wani irin son junansu suke ji, Sun d'auki lokaci suna kallon juna Kafin bariki tayi k'asa da kanta dan bazata iya juran ci gaba da kallonshi cikin ido haka ba, wannan dinma da tayi tana mamaki, ta rasa mai yasa Yarima ya banbanta da sauran maza, yana Mata wani irin kwarjini da bata ji akan sauran mazan da tayi hulda dasu,.....


Katse mata tunani Yarima yayi tare da fad'in daka ina habib ya kiraki Ina kika je?


Cikin sanyin murya tace ina gidan wata kawar innata ce, naje amso maganin ciwon kai na Hausa, Ina can habib yazo, nama bar wayata a gida tana caji.....


Yarima yace ok but yaushe zaki koma Gida? I dnt knw why bana son wannan anguwar domin mutanan da nake gani a cikinta, plz ban son kina yawan zuwa my princess ya karasa maganan cikin damuwa....


Tace Yarima Karka manta y'an uwana suna nan


Yace eh I know, bawai nace ki daina zuwa bane, kawai Ina so ki rage zuwa ne plz, and my princess plz ki daina irin wannan dressing din, sai a gida na, ki dinga sa hijab dinki inso samu nema harda nikaf plz banso kowa yana ganinki .....


Bariki murmushi tayi tare da fad'in Yarima wannan jallabiya ce babu komai ai dan nasa, shima kaman hijab ne.....


Yarima yace, Nop akwai banbanci nidai bana so ana sawa, Kinga yanda yayi miki kyau kuwa? Only god knows maza nawa kika burge da kika fito.... Sai yasa tunda yau naga Abba Yaban izini very soon za'a turo ayi bikin kowa ya huta in kika zama tawa sai inga Wanda zai kara cewa yana son ganinki.......








*jiya saida Nayi typing har 2read more komai nawa ya goge na whatsapp 😭😭😭😭 ol my chats yanzu ma saboda nacin my mum my salmaty yasa dole nayi typing dinnan, plz duk Wanda sukai min magana ban basu amsa ba suyi hakuri Wlh komai nawa Ya goge in important magana ne zaku iya Yimin resending message din pls, nayi bayani ne Kar a kaini gaba ace in anyi min magana bana kulawa, maryam ba haka take ba, kowa nata ne thanks*


















~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 8*
















Bariki dariya tayi, tana mamakin irin kishin Yarima Aliyu, gashi baya iya boye kishin shi, dole saiya fito dashi......


Katse mata tunani yayi da fad'in dariya koh??


Tace a'a Yarima kawai naga kana tunanin daba haka bane.....


Yace miye ba haka bane? Tell me, tunda kika fito zaki cemin maza basu kalleki ba??


Tace Yarima yanzu fah dare ne Waye zai kalleni? Inba Kai ba.


Murmushi yayi tare da girgiza kai yace my princess you r too much kin iya Kare kanki..... Anyway yaushe kike son Ayi bikin mu?? Domin Idan Mai martaba ya turo lokaci kad'an za'a sa.


Bariki rufe fuskanta tayi cikin jin kunya tace Yarima *BANDA ZABI* sai abunda su Abba sukace.....


Yarima Aliyu yace hakane but Nasan Kema kina da lokacin da kike so ayi in muka shirya basai mu fad'a ba!?


Tace hakane


Yarima yace ni ko yanzu aka bani zan tafi dake.....


Ido ta zaro lokaci d'aya kuma ta saki dariya Sosai, tace Yarima ni nafi son yakai Nanda shekara d'aya.....


Da sauri Yarima yace what?? Amma dai you are joking koh? Ni bamma tunanin yakai nan da wata d'aya....


Bariki tace Yarima watsa d'aya yayi wuri, ni Ina tunanin nan da wata uku....


Yarima yace hakan yayi miki???


Kai ta d'aga alaman eh, domin Kafin nan ta Gama istabra'i sannan zata samu lokacin gyara kanta Sosai duk da tasan komai tayi bazata dawo budurwa ba, amma zata gwada duk wani kayan gyaran jiki danta d'an gyara kanta.....


Katse mata tunani yayi da fad'in gobe ki koma Gida Zanzo in ganki a can da rana insha Allah,


Tace Yarima gobe kuma?


Yace yes ko you don't want to see me ne?


Da sauri tace a'a kawai naga kullum sai kazo, baka zama ga amarya a gida, inaga ya kamata ka zauna ka bata hakkinta, da lokacinka


Yarima yace ok hakane, zan zauna bazan zoba har sai kin nemeni, sannan ita amarya Ai tare muke kwana da ita.....


Ganin yanda ta canza fuska yasa yayi murmushi danya Lura taji haushin magananshi ne.....


Kamo hannunta yayi tare da matse su duka biyun, yace my princess I love you so much, plz ki dinga kulan min da kanki Sosai...


Kallonshi tayi ganin shima ita yake kallo yasa tayi k'asa da kanta, cikin sanyin murya tace Yarima....... Shuru kuma tayi tana jin nauyin abunda zata fad'a.....


Yarima Aliyu yace ina jinki my princess.....


Hawaye ne ya zubo mata Mai zafi da sauri tayi k'asa da kanta dan karya gane tunda hannunta na nashi hannun..... Cikin rawan murya tace Yarima Idan ka aureni kaji ba yanda kake expecting ba zaka iya saki na????


Yace ban fahimta ba?? Mai kike nufi?


Tace Yarima Ina nufin Bayan auren mu kaji ba yanda nake ba I mean..... Shuru kuma tayi lokaci d'aya tasa kuka mai sauti........


Yarima ido ya kura mata cikin rud'ani...... Tare da tunanin mai take son fad'a mishi haka???? Ganin kukan nata na k'aruwa yasa ya fara share mata hawaye cikin tausayinta....... Ya fara magana kamar haka Zainab Ina son ki fad'amin abunda yake damunki ko miye I will accept you a yanda kike, ina miki so dani kaina ban taba tunanin zanyi ma d'iya mace irin wannan son ba, tell me maike damunki????


Kasa magana tayi sai kuka da take ta faman saki cikin tashin hankali da damuwa,....


Yarima kam ido ya kura mata ganin taki magana sai kuka,... Yace Zainab kodai kina pretending ne bakya so na.......


Da sauri tace a'ah Yarima Ina Sonka, kaine rayuwa na, Ina maka son da baki bazai iya fad'anshi ba, sonda nake maka sai yasa nake tsoran fad'a maka abunda nake son fad'ama a halin yanzu saboda ban San yanda zaka d'auki abun ba......


Katseta yayi tare da fad'in Zainab tell me?? Fad'amin Mai yake faruwa?? ......plz Zainab tell me abunda yake damunki kin sani cikin damuwa......


Kuka take Sosai lokaci d'aya ta fad'a jikinshi ba komai take son fad'a mishi ba sai rayuwarta wanda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya yasa ta kasa fad'a mishi sai kuka tare da nadama


Yarima tunda ta fad'a jikinshi ya kasa furta koda kalma d'aya ne sai Shafa mata baya da yakeyi tare da tunani Kala Kala akan Mai take son fad'a mishi?? Lallai akwai wani abu mai muhimmanci daya danganci rayuwarta da take fargaban fad'a mishi, to miye abun??? I need to knw, tunanin baya ya farayi tasha son fad'a mishi magana amma saita kasa, lallai akwai wani abu a tare da ita toh miye wannan abun?? I have to find out........


D'agota yayi tare da fad'in Zainab kukan ya isa haka, what I want you to knw is dat Ina sonki I cnt live without you...... Zainab tun a mafarki Allah ya had'ani dake har na had'u dake a zahiri, ina son ki sani had'uwa na dake had'in Allah ne, na Fara sonki tun Kafin inga Fuskanki, ina son ki sani bawai saboda kyanki ko wani abu nake sonki ba a'a kamalanki da mutunci da yanda kike suturta jikinki yasa na kara sonki koda na had'u dake...... So Zainab dnt be afraid to tell me what in ur mind..... Zainab Abu d'aya zaki aikata in barki duk irin sonda nake miki domin bazan iya juraba dan Indai zan ganki Abun zan dinga tunawa shine *ZINA* duk da Nasan rasaki a rayuwa ta kaman baraza na ne a tare da rayuwa na, bana tunanin koda a mafarki Zaki iya aikata hakan, ina matukar kishinki Sosai harta habib da kike mu'amala dashi hakuri nakeyi badan ina so ba, tunda kince kaman dan uwanku ne, ban son inga wani abu yazo inda kike Inba niba........ Ido ya kura mata tare da fad'in tell me wht on ur mind I need to knw......


Bariki jikinta yayi matukar sanyi Sosai lallai Yarima in yasan wacece ita ya barta har abada..... Tsayawa tayi da kukan amma hawaye na zuban Mata a ido Sosai amma yata iya tata kaddaran kenan dole ta fad'a mishi gaskiya domin hakan shine zai sa ta sami salama duk da itama ba zata iya juran rashin Yarima Aliyu a rayuwarta ba, domin so ya mata shigar sauri sonshi ya shigeta Sosai wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba.......


Katse mata tunani yayi tare da fad'in Zainab tell me plz....


Shuru tayi tana kokarin yin magana amma ta kasa domin muryanta ya dashe......


Ganin haka yasa Yarima fad'in kiyi shuru kibar wannan kukan plz Kinji my princess?


Kaita d'aga mishi alaman toh


Yarima Aliyu idonshi na kanta ya tabbata akwai abunda take boye Mai, but koma miye zai sani..... Ganin tasa hannu a kanta alaman yana mata ciwo yasa yace my princess ciwo Kai din yake miki?


Kaita kara d'aga Mai alaman eh , bud'e kofar motar yayi ya shiga wajan driver ya kunna motar,


Da sauri ta d'ago ta kalleshi ganin yaja motar yasa ta kura mishi ido, taga Ina zashi da ita...... Karan wayanshi ne yasa ta dawo daka duniyar tunanin data fad'a


D'auka yayi tare da fad'in USMAN sorry yanzu zamu dawo, zan kaita pharmacy ne a bata magani she has a headache..... Yana fad'in haka ya kashe tare da fad'in Ameen


Yarima cikin gari suka shiga inda aka bama Zainab magani, tare da sai mata kayan fruit sannan suka kamo hanya, bayan sun karaso Bariki suka gaisa da USMAN sannan Yarima yayi mata sallama akan taje tasha magani, ta kwanta ta huta sai sunyi waya......


Bariki gidanta take ta koma ta shiga d'akinta ta kwanta bayan tasha magani bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita


Usman tun a mota yake tsokanan Yarima Aliyu, akan dole ya mutu akanta yarinyar tana da kyau sai dai karama ce ba wata babba bace......


Yarima dai banza da USMAN yayi domin haushin yanda yake ta fad'in Tana da kyau yakeyi, d'an tsaki yayi cikin ranshi yace bazan kara zuwa dashi ba, tunda Kalle min Mata yake tayi...


Yarima bayan sun koma direct gefenshi ya nufa inda yayi bedroom dinshi yayi wanka, yana cikin sa jallabiya danya kwanta


Gimbiya zinatu ta shigo d'akin tare da fad'in Yarima .....


Yace ya akayi....


Tace ina son magana dakai


Baice mata komai ba sai zama da yayi akan gadon d'akin tare da d'aukan wayarshi yana dannawa.....


Kollonshi tayi cikin jin haushin rashin kulata din da baiyi ba, tace haba Yarima wai mai yasa kake haka, yau kwana na uku a gidan nan a matsayin matarka, amma baka da lokaci na, kullum inka fita sai dare, karka manta wannan baya d'aya daka cikin abunda miji ya kamata yayi ma amaryanshi, duk wani ango zama yakeyi a gida in yayi aure ya dinga kula da matarshi, yau koda bazawara ka aura ai kayi d'auki balle ni budurwa....


Yarima Aliyu kallonta yayi tare da d'an sakin murmushi yace d'auki?? Akan me? Bayan har yanzu ban San maina aura ba......


Cikin faduwan gaba tace kaman ya Yarima ban gane ba ...


Idonshi na kanta domin yana son yaga yanda zatai reaction amma ga mamakinshi sai yaga batai yanda yake zato ba, kenan gimbiya budurwa ya sameta dagaske, inko hakane ya kamata ya dinga bata hakkinta duk da bawai yana jin Sonta bane a ranshi, amma tunda ta kawo budurcinta sai yaji tayi girma a idonshi, duk da Abun ya bashi mamaki, dan baiyi zaton haka dinba......


Jin kukan gimbiya zinatu shiya sa yarima ya dawo daka duniyar tunanin da yake...... Ganin yanda take kuka yasa zuciyar Yarima tayi karaya tare da tausayinta , tashi yayi ya ka mota ya kwantar da ita akan jikinshi yana fad'in plz ki daina wannan kukan.....


Cikin kuka take fad'in haba Yarima dole inyi kuka, yanzu Yarima ace Ina amarya amma kullum saika fita, kuma inka fita sai dare, har an fara magana akai na, ana fad'in baka d'auki na , kasan gidan sarauta akwai ya'da magana haba Yarima mai yasa baka sona? Maina rasa......


Hannunshi yasa akan bakinta yace ya isa haka,


Ganin kaman Yarima ya tausaya mata yasa taita Mai juye juye a jiki,


Nan sha'awa ta motso ma Yarima Kafin ace Mai har an fara harka.......










*********
Alh madu ne shida hjy babba kallon hjy babba alh madu yayi yace abunda yasa na kiraka dagaske ne bariki zatai aure ko wasa takeyi??


Hjy babba yace haka tace kuma ina ganin kaman dagaske take, dan naga gskya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login