Showing 93001 words to 96000 words out of 124261 words

Chapter 32 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

Mai jin zafin abunda ya gani.... Dr ne ya mishi y'an dube dube sannan yace haba Aliyu, kana son sama kanka damuwa plz ka kwantar da hankalinka an fad'amin you r a doctor so nasan Idan na fad'a maka ka sami bugawan zuciya zaka San abunda ya kamata kayi wajan cire ma ranka abunda ya razana ka...... Yarima baiko Kalli Dr ba balle ya kulashi sarautar ta motsa..... Dr yaci gaba da fad'in Yarima ka gode ma Allah, amma kana son Zainab dinnan da yawa, Allah y.......


Yarima Aliyu ya Katse Dr da fad'in ina son a sallameni......


Dr yace sallama?


Yarima Aliyu yace yes yanzu


Dr yace a'ah ka Bari ka K'ara samun sauki, domin har yanzu baka dawo Normal ba.....


Yarima Aliyu tashi yayi dakyar ya zauna tare da fad'in Dr i am a Dr too I knw how to handle myself, and kace na samu buguwar zuciya?? So zamana a nan baida amfani dole inje gida a nan zan samu nutsuwa...


Dr shuru yayi yana nazari, maganan Yarima Aliyu gaskiya ne, Idan mutum ya sami buguwar zuciya irin haka, iz either an fad'a Mai wani abu ko ya gani, so inya duba yaga abun iz not true a hankali zai Fara samun lfya domin ya samu nutsuwa.......


Yarima Aliyu tashi yayi jiki babu kwari, kaman zai fad'i yayi sauri ya ri'ke hannun Dr din.......


Doctor din yace kayi a hankali, ka zauna let me call your parent su ri'ke ka, taimaka ma Yarima yayi ya zauna yana cije baki alaman yana jin jiki.....


Yarima Aliyu ba komai bane yasa yace a sallameshi sai dan yayi magana da Zainab bariki, akan yaudaran da ta mishi and baya jin zaiyi accepting d'inta a matsayin mata, matar data gama watsewa a duniya ko wani namiji ya santa t.........


Bud'e kofar da akayi yasa ya d'aga ido da yake zubar da hawaye, ganin mum da fadawa yayi, nan Dr yace su taimaka sukai Yarima Mota, kamashi sukayi suka fita, mum kallon d'an nata take cikin tausayawa.. Bayan an fitar da Yarima mum ta kalli Dr tace nidai banso ka yarda ya koma Gida ba, ina jin tsoran Kar wani abu ya sake samunshi.......


Dr yace karki damu, a gidan zaifi samun nutsuwa, Idan mutum yayi irin haka kika ga yace yana son tafiya akwai abunda yake son tabbatar wane, wanda shine yasa ya fad'a irin wannan matsalan, sannan komai ya faru call me.....


Mum godiya tama Dr sannan ta fita.


Bariki bayan sun karasa gida gefenta da aka kaita nan ta shiga, bedroom tayi Kai tsaye, ta zauna a k'asa tana kuka kaman ranta zai fita, wayan Yarima dake hannunta tayi k'ara alaman an turo Mai sa'ko, ajiye wayar tayi a gefe...... Tabbas tasan wannan ba komai bane, tunda tun Farko ta zabi sabama Allah, dole taga bacin rai, dama duk Wanda ya kauce hanyar Allah kuma yasan yabar hanya Mai Kyau dole ya had'u da ukuba tun a duniya, ita Allah na Sonta da rahma tunda harta gane ta kuma yi nadama, sai dai irin hanyar da tasa kanta koda kayi nadama sai an samu masu goranta maka, in bakayi wasa ba harta jikokinka sai anyi musu gori da fad'in ai kakarsu tsohuwar karuwa ce da, ko kuma ayi ma y'ay'anki ace ai uwarsu karuwa ce, in tayi aure tama miji laifi yace ta biyo halin uwa, tasha a nono, kai Wlh rayuwan bariki batayi ba ko kad'an... Kuka ta K'ara saki cikin jin zafin bata rayuwarta da tayi duk da kaddara ne ya sameta..... Wacce bata san yanda akayi Abun ya sameta ba.....


Gimbiya zinatu kam tana shiga gefenta wa'ka ta kunna Tana ta rawa cikin jin dad'i, tare da fad'in first night ya zama ranan ba'kin ciki dariya ta saki cikin jin dad'i...


Koda su Yarima Aliyu suka Iso gida, cewa yayi zai nufi gefen Zainab, duk da mum taso ya bita amma ya'ki, mum bata sa komai a ranta ba, ita a tunaninta da taji yace zashi wajan Zainab, sai tayi tunani ko abunda yayi mata d'azu yake son bata hakuri, sannan a mota ta fad'a mishi abunda Dr sukace inda badan Zainab dinba toh da zai iya mutuwa..... Fadawa na k'okarin rikeshi yace Nop ku barni, zan iya, tafiya yake dakyar harya shiga cikin falon bai ganta ba


Mum ganin ya shiga yasa itama ta wuce


Yarima bedroom dinshi yayi inda tun Kafin ya k'arasa yake jin sautin kukanta, bud'e kofar bedroom din yayi ya ganta a k'asa tana rasgan kuka a hankali cikin murya irin na marasa lafiya wanda yake jin jiki yace wannan ba kuka kike yiba..


Jin muryan Yarima yasa tayi sauri ta tashi, tare da kallonshi tana mamakin ya akayi ya dawo......


Yarima Aliyu idonshi na kanta yana mata wani irin kallo Mai Kama da I hate you, yace Zainab oh sorry Bariki......


Jin ya kirata da Bariki yasa zuciyarta ta tsinke gaba d'aya, abunda take zargi shine ya faru an fad'ama Yarima.......


Katse mata tunani yayi da fad'in how dare you....... Shuru yayi cikin kunan rai hawaye na zuba a idonshi...... Yace kin cuce ni, kin yaudareni, and ina asibiti kin kuma bina har ana fad'in da badan keba dana mutu, Mai yasa kika zo?? Mai yasa ban mutu ba, I wish da mutuwa nayi da Nasan zanga irin wannan ranan, you play with my feelings you all lies to me, you cheat me, kin maida iyayena yara kinyi wasa dasu......


Da sauri tace dan Allah Yarima ka saur......


Yace keep quiet, don't try to say anything, let me speak you cheater......


Bariki kuka take Sosai


Yarima Aliyu yaci gaba da fad'in do you think I will trust you again?? You break my trust, dan shuru yayi sannan yaci gaba da fad'in Zainab I love you from d bottom of my hrt, why are hidden your secret with me??.......


Tana kokarin yin magana yace I said don't try to speak keep your mouth shut, I don't want to listen to ol your lies again,


Bariki kuka take na farko ga Tashin hankalin halinda mijinta ke ciki, gashi ya hanata yin magana


Yarima Aliyu yace but you don't cheat me, you cheat your self, Zainab I was shock to see your pictures with different men's, ido ya rufe yana hawaye domin takaicin abunda yake fad'a ji yake kaman zuciyarshi zata buga, I never expect dat from you, Zainab mai yasa kika bata rayuwanki nawa kike samu? mai kike ji,? mai yasa kika yaudareni,? mai yasa kika boyemin gaskiyan ko ke wacece,? Zainab how old are you kwata kwata da zaki bata rayuwanki just for money?? Mai kika samu Mai kika tara ??


Da sauri tace Yarima plz ka saurareni dan Allah tana maganan tana kuka....


Yace I don't want to listen to ol your lies, komai naki karya ne your love your affection is ol a lies......


Shuru yayi hawaye na zuba daka idonshi Abun gwanin tausayi💔 sanna yaci gaba da fad'in you break d trust dat I have for you, Zainab kwata kwata shekaranki nawa?? Har kin San ki samu iyayen Karya, ki aurar da kanki da kanki, you fool us, mai kika d'auki aure??? Do you think dat marriage is a joke?? Zainab I truly love but I won't accept you d way you are.....


Ihun data saki Tana bashi hakuri akan ya tsaya ya saurareta tayi mishi bayani akan duk wanda ya fad'a yayi ne danya had'asu......


Yace Yimin shuru, Habib zai miki karya ne?


Cikin razana tace habib.....


Yarima yace eh habib call me and tell me everything ol your plan...... Zainab I feel so sad when I hear d truth about you..... Nayi takaici you never love me habib told me you marry me only for money...... Shuru yayi yana hawaye can yaci gaba da fad'in kin aureni dan ki sami kud'i bakya sona Wanda kike so yayi rejecting d'inki sai yasa kika aureni danki nuna mishi kina da Wanda suka fishi..... After dat he send me your pictures matsawa yayi kusa da ita ya d'auki wayarshi ya fara dannawa nuna mata yayi yace Waye wannan hotunan tane da Alh madu, gashi tsirara ya ri'keta, sai kuma wanda tayi da Hon salis...... Yarima yace have you seen it?? Ok shima wannan it ol a lies ko shima wannan so ake a had'amu?? Jefa wayan yayi a K'asa ta fashe...... Idonshi ya rine yayi ja, ga zuciyarshi dake faman tafarfasa kirjinshi na mishi zafi........ Yace you betrayed me, who did I harm to deserve ol this punishment...... Ban kasance mazina ciba, ban taba sanadin lalacewan wata ba, why matar dana aura kowa ya Santa.......


Bariki kuka take Sosai tare da tunanin irin cin amanan da habib yayi mata, lallai don't trust anyone in life,...... Bakinta na rawa ta Fara fad'in Yarima Nasan ni Mai laifi ce a gareka dan Allah kaban dama just once I need to exp......


Yace I won't give you any chance to tell me another lies, karyan da kikayi min baya ya isa...... My heart only beat for you..... Tun a mafarki na Fara sonki, but you never love me, you hurt me alot...... You marry me for money not for love...... Ok even I, I won't accept you as my wife..... You will live here as my servant har karshen rayuwarki zaki zama mai min bauta, and I will make sure to hurt you d same as you did to me, nd I promise to hurt you, keda duk Wanda kukai wannan abun sai Nayi punishing naku, I will make sure to make you regret knowing me in ur lyf........


Da sauri ta matsa kusa dashi tare da kokarin tabashi ya daka mata tsawa tare da fad'in don't you dare try to touch me.... Karki k'ara yunkurin tabani da wannan kazamin jikin naki......


K'asa tayi da giwowinta Tana kuka tare da fad'in Yarima call me wit wat ever name you like, I deserve it, Yarima just once plz ka saurareni plz.....


Yarima yace do you think zan kara sauraran wannan karyan naki?? Harda cemin kin sauke Al'qur'ani, Wat a funny, kin dai yi hadda a bin maza.....


Tace Yarima iz true na sauke al'qur'ani tun I was 11yrs plz Yarima allow me to speak......... Hmmmmmm bari dai muga ko zai bata daman fad'a mishi ko ita wacece 🙆








*Plz kuyi manage I have a headache na gaji da typing din, comments dinku yasa nace bari in takura kaina inyi muku posting, ina matukar yinku Sosai da Sosai*
















~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 19*














D'an shuru yayi kanshi na k'asa yana zubar da hawaye, yana son Zainab yana mata tsantsar so, but da yasan haka take daya ro'ki mutuwa, daya ro'ki Allah ya d'auki rayuwarshi da yasan zaiga irin wannan mummunan ranan........


Jin yayi shuru yasa ta Fara fad'in Yarim......


Yace I said keep quiet, I don't want to listen to you.... Zainab even at once kin taba tunanin irin yanda zanji in nasan gaskiya a kanki???...... Kin taba tunanin ya iyayena zasu d'auki abun in suka San koke wacece??..... Zainab mai kika d'auki rayuwa?? Mai yasa kikai wasa da feelings dina?? You don't love me...... Wani hawaye mai zafi ya zubo Mai sannan yaci gaba da fad'in, tunda bakya sona Mai yasa kika aureni, Zainab inda kin fad'amin bakya sona tun Farko kud'i kike so, I will give you d money dat you want..... Basai kin yaudareni ba kin aure ni b.....


Kafin ya k'arasa abunda yake son fad'a ta Fara matsawa kusa dashi, daka mata tsawa yayi tare da fad'in karki zo inda nake..... Tari ya farayi Sosai......


Da sauri ta nufeshi tare da rik'eshi Tana buga mishi baya a hankali, tana kuka ta Fara fad'in Yarima I knw dat I have lies to you, na boye maka koni wacece Nasan wannan gaskiya ne, but Yarima abunda aka fad'a maka Akan son da nake maka karya ne..... Yarima you are my life, Yarima I love you, I can't live without you...... Tsagaitawa yayi da tarin da yakeyi tare da kallon idonta itama idonta nakan nashi...... Taci gaba da fad'in Yarima sonda nake maka shine yasa na boye maka koni wacece, saboda ban son in rasaka....... Yarima in zaka tuna nasha kuka ina son fad'ama wani abu, sometimes wani abu ya shigo koka katseni.... Yarima I try to tell you who I am but whenever I try to tell you wani abu saiya shigo, and habib yana fad'amin Indai na gaya maka gaskiyan who I am you will hate me and leave me..... Yarima sonda nake maka bazan iya juran rashinka ba..... Yarima Wlh Ina Sonka Ina Sonka, how I wish in bud'e maka zuciyata Kaga irin sonda nake maka..... Yarima plz ka amshi kaddara ta karka juya min baya kaman yanda mahaifina yayi min, Wlh Yarima Idan ka juya min baya zan iya mutuwa...... Jin haka Yarima Aliyu yayi sauri ya rungumeta dukansu kuka Yarima hawaye ita kuma kuka mai sauti....... Bariki tana rungume a jikin Yarima Aliyu ta Fara fad'in Yarima........


Ni d'aya mahaifina ya haifa......


Nice y'ar mahaifina ta Farko kuma tun daka kaina bai k'ara samun haiyuwa ba, tun ina y'ar shekara Goma mum dina ta rasu, lokacin na shiga gararin rayuwa, gaba d'aya na tsani komai dake duniya .


Mahaifina babban malami ne a k'asa nan wanda kowa ya sanshi bama kasar nan ba harta kasashen duniya, mahaifina malami ne mai sani Sosai sannan d'an kasuwa ne wanda yayi fice Sunan mahaifina sheik musa monguno...... Dan maiduguri ne, sunyi auren soyayya da mahaifiyata tun a k'asar misra suka had'u lokacin sunje karatu mum dita y'ar Sokoto ce soyayya Mai karfi ya shiga har takai da aure..... Tunda mum dina ta rasu mahaifina bai kara tunanin yin aure ba, shi yaci gaba da kula dani har Nayi hadda na sauke al'qur'ani da sauran littafai lokacin ina shekara shad'aya a duniya..... Ina karatun boko komai nawa dad dina yake min tare da taimakon Mai aikin mum dina wata tsohuwa Wanda na dauketa kaman kakata nake kiranta da Ummaa,


Dangin mahaifina sun dameshi akan ya k'ara aure, domin zamanshi haka bamai yihuwa bane, ya nuna musu babu tsarin k'ara aure a ranshi, domin bai yarda yayi aure ya bada ri'kona wajan matar daya aura ba, domin yana matukar jin tausayi na, ya nuna musu Ummaa na kula dani baya bukatar ya auri wata mata, koda zaiyi aure yace saiya aurar dani shine zai samu nutsuwa......


Haka dai suka barshi Ina shekara shabiyar a duniya Ummaa ta rasu 😭😭, naji mutuwar Ummaa Ina tunanin Nafi jin Nata akan sanda naji mutuwar mum dina, har saida na kwanta a asibiti, a lokacin na k'ara yarda ba mutuwa akema kuka ba, shakuwa ce da Sabo akema kuka, haka na k'ara fad'awa cikin gararin rayuwa tare da kadaici, mahaifina yana matukar jin tausayina Sosai.....


Bayan rasuwan Ummaa family din dad dina suka k'ara taso mishi da maganan aure, wannan karan basu mishi da wasa ba, kusan duka y'an uwanshi suka had'u harda mamanshi wato kakata tunda mahaifinshi ya dad'e da rasuwa, dole yasa ya amince ganin yanda suka nuna fishinsu akan ya k'ara aure........ Wata y'ar uwarshi aka aura Mai Mai suna Falmata wacce mijinta ya rasu ya bar mata yara biyu Mata, ganin abbana yana da kud'i yasa akace zai iya ri'ke yaran dan haka tare aka kawota da yaran, gidan dad dina dake Abuja.


Falmata Tana nuna min so Sosai, bata Bari koda kud'a ya tabani, mahaifina yana jin dad'in hakan, sannan komai zai mana tare yake mana da Kananan yaranta, haka dai rayuwa taci gaba dad dina wata rana ya d'aukeni mukaje bank aka bud'emin account, gaba d'aya kud'in da mum dina ta bari aka samin kud'i masu uban yawa a lokacin kusan 20mil banda kadarori data bari tare da gidan gona Wanda kullum cikin samun kud'i ake, komai na mum dina dad dina yace cikin account dina za'a dinga sawa.... Na nuna ma dad dina daya Bari a wajanshi amma yace a'a in ri'ke hakki nane........ Mahaifina yana nuna min tsantsar so Sosai har baya iya boye son da yakemin gaban kowa kullum magananshi ni tare da fad'in irin tausayi na da yake ji......... Dad dina yana yawan zuwa gari gari wa'azi da kasashe, ganin matarshi Tana kula dani yasa ya yarda yake tafiya yabar mata ni....




Lokacin da nake shekara Goma sha bakwai komai nawa Ya fito, kyau diri Kirjina komai nawa dai tubarkallah, Falmata duk kawayenta kana kallonsu zaka gane y'an duniya ne, sannan basa zuwa gidan sai dad dina baya k'asar........


Wata rana Ina d'aki na fito daka wanka daka ni sai towel, ina zaune ina shafa mai saiga Falmata ta shigo, da sauri na tashi Ina kokarin in d'auko abu in rufe jikina A Kai rashin Sa'a towel din ya fad'i, gaba d'aya idon Falmata na kaina, da sauri na shige towel na rufe Ina kuka domin naji kunya Sosai ranan


Ranan dai a d'aki na wuni banko le'ko ba


Washegari na fito da yake lokacin ina zana waec kuma ranan shine paper na karshe na fito zani skul cikin jin kunya, saiga Falmata tazo ta ri'ke min hannu tare da fad'in haba zainab, mai yasa tun jiya kika k'i fitowa nifa mamanki ce kiyi hakuri dana shigo ba tare dayi miki nocking ba, tunda ta ri'ke min hannu sai wani murmurzawa take kaman filo ta ri'ke, ganin zanyi lati gashi tana ta wani shafa min hannu yasa nace ummi zanyi lati.


Murmushi tayi tare da fad'in muje in rakaki mota,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login