Showing 75001 words to 78000 words out of 124261 words

Chapter 26 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

harna tausaya ma al'umar da kake wakilta basu San tsohon banza suka tura...... Tas ya wanke fuskanta da Mari tare da Jefata kan kujeran falon


Bariki tace u slap me?? Kara mata wani Marin yayi.... Yazo zai kara mata wani tayi wuf ta ri'ke hannun amma karfin mace dana miji ba d'aya ba ya kwace hannunshi tare daja mata hannu yayi bedroom dinshi da ita, yana shiga ya Jefata kan gadon d'akin..... Sannan ya kalleta yana wani huci kaman wanda yayi aikin karfi..... Yace zan nuna miki ni tsohon banza ne, zan ajiyeki a nan har karshen rayuwarki inyi ta cinki sai dai ki mutu y'ar iska kawai.....


Dariyan da bariki ta saki ne, shine yasa ya kura mata ido, tace amma kayi hauka koh?? Ina tunanin Bayan tsufa da toshewan basira ka Fara tabuwa, Bari kaji Kafin inzo inda kake saida na shirya ma, ka d'auka haka kawai Zanzo ba tare da wani shiri ba???? Toh inma haka kake tunani Toh ka daina...... Karka manta dazu ka kirani duk abunda ka fad'a nayi recording, sannan ka turamin ainiyin hotan da ka d'aukemu nida kai, Kaga in kasa an canza wancan zan karyata ta hanyar tura Wanda ka turamin wanda fuskanka ne akai tare da tura recording din da nayi kake ta surutai akan kasa a canza fuska...... D'an shuru tayi tare da kallonshi ganin yanda ya d'an tsorata yasa taci gaba da fad'in Kaga in nasa nawa Nima k'imarka da siyasan ka ya zube...... Madu ina son ka sani bana son bata maka suna amma kana ingizani, are you not are shame, nace na daina harka da maza aure zanyi amma kana son dole saina ci gaba dayi, inaso ka sani daka yau shine rana ta karshe da zaka sake yunkurin shiga al'amari na, zan iya fasa auran da zanyi kaifa zaka iya yarda ka rasa kujeranka???..... Ganin Alh madu ya kasa cewa komai yasa ta Fara kokarin fita har takai bakin kofa ta tsaya tare da waigowa tace ina maka fatan shiriya domin mutuwa ci take kaman rana, a shekarunka yanzu babu abunda ya dace dakai sai istigfari domin neman gafaran Allah dan an bata y'ay'an mutane da dama, kaima ka jira Kaga abunda za'ayi ma naka da yardan Allah...... Fuuuuu ta fita tabar gidan, tafiya take tana kuka a kafa tare da takaicin tsintar kanta da tayi cikin wannan kazamar harkan, amma ta d'anji dad'i tunda yanzu ta tabbata Alh madu bazai K'ara Mata barazana ba akan rayuwarta dama shine matsalanta..... Yanzu Abu d'aya zan fuskanta shine Idan Yarima yasan gaskiya shima zanyi komai yanda ya dace ta hanyar fad'amai da fahimtar dashi komai...


Bayan fitan bariki Alh madu murmushi yayi wanda nidai ban gane na miye ba, na mamaki ne? kona nadama ne? kona shirin wani tuggu ne? oho ...... Koma dai miye zamu gani in yaji gargadin bariki ko kuma zai sake bibiyarta


Bariki tana zuwa kofar gidansu na u/kanawa ta hango motar Yarima a fake, wanda shi d'aya yazo..... Mamaki abun ya bata Toh Mai yasa bai kirata ba, kuma wayarta na hannunta, tace may be yanzu yazo...... Gaba tayi tazo zata wuce cikin gidan tayi kaman bata ganshi ba, shima yana kallonta baice mata komai ba harta shige cikin gidan..... Murmushi Yarima yayi tare da d'aukan wayarshi ya tura mata message kamar haka......


Ko in tafi ne???


Bariki ganin message dinshi yasa tayi dariya tare da fitowa waje ta sameshi inda yake bud'e motar tayi ta shiga


Kallonta yayi tare da fad'in kina ganina kika wuce


Tace Yarima yaushe na ganka??


Murmushi yayi tare da fad'in my princess inafa kallonki, harda wani kawar dakai Kalan baki ganni ba


Tace Yarima nidai naga mota amma ban San Waye a ciki ba, ko kana son inyita kallon maza ne ??


Bai san lokacin da yayi dariya ba, tare da fad'in koda yaushe kin San hanyar da zaki Kare kanki...


Shuru tayi tana tunanin I wish Yarima yasan gaskiya ya fara sona, hawaye ne ya gangaro mata a ido da sauri tasa hannu ta goge dan karya gani tare da d'ago kanta taga koya gani.... Kur taga yana kallonta...... Da sauri tayi k'asa da kanta


Yarima Aliyu yace Zainab a kullum nazo Wajanki kina Sani fargaba, Wai Mai kike boyemin ne?? Kina sani tunani Kala Kala plz tell me Mai yake damunki banso ki barni cikin duhu.....


Kuka ta farayi tare da fad'in Yarima tunda nake ban taba jin son kowa ba sai Kai, ina jin tsoran abunda zai faru in kasan gaskiyan al'amarin da nake boye maka....... Karan wayan Yarima ne ya Katseta


D'aukan wayan Yarima yayi ganin Sunan waziri ne, ji nayi Yarima yana fad'in ok gani nan zuwa, har kun karaso?.... Kashe wayan yayi tare da kallon zainab yace Bari inje in dawo yanzu.


Bariki tace ok tare da fad'in saika dawo sannan ta fara kokarin fita daka motar.....


Hannunta ya ri'ke tare da fad'in haka zaki fita Fuskanki yana hawaye??..... Janyota yayi jikinsa tare da goge mata hawayen fuskanta yace plz my princess kibar wannan kukan yanzu zan dawo sai muyi magana Kinji?


Kaita d'aga Mai alaman eh.


Murmushi yayi tare da fad'in dat my girl, inna dawo zan fad'a miki albishir


Murmushi tayi tare da fad'in saika dawo sannan ta fita.


Yarima direct u/sarki ya nufa inda Zai had'u dasu waziri a nuna mishi filin da Mai martaba ya bashi sannan suje asibitin shi y'an jarida su d'auka domin a tallata asibitin duk da Yarima baiso hakan ba, amma waziri yace ayi tunda yace zai Fara aiki na wata uku kyauta akan matsalolin mata tunda shi likitan mata ne, ta gidan tv da radio mutane za suji marasa karfi su zo..... Asibitin ba Yarima kadai bane zaiyi aiki a cikinsa ba harda wasu likitoci na fanni daban daban......


Bariki bayan ta shiga cikin gida, ummanta tace Zainab Yadai har Yarima din ya tafi?


Tace eh amma zai dawo.... Wai har yanzu habib bai zoba? Tun dazu yake cemin yana hanya.....


Sallaman habib dinne yasa tayi shuru ya shigo yana gafaran ku dai masu gida


Shiga d'akin dasu bariki suke yayi yana fad'in in shigo ko in jira a kimtsa....


Bariki tsaki taja Tana fad'in Asara, bayan ka shigo din kake tambaya koka shig......


Waige ya farayi yana duba dawa bariki take magana, yaga babu wani namiji a wajan yace ke dawa kuma?? Naga banga ko wani namiji a nan ba


Bariki tace dakai nake mana...


Yace Wlh bariki zan miki rashin mutunci miye wani ka? Mai yakai mace jinsin maza, gskya banso yana maganan yana hura hanci Kalan ranshi ya baci.....


Umman bariki ta Karya babu abunda take sai dariya, tace Zainab gskya bakya kyautawa taya zaki dinga kiranta dana miji Bayan kin San macece y'ar uwarmu....


Habib yace fad'a mata dai


Bariki dariya tayi tare da fad'in ni bama wannan ba kawata kina ji??


Habib yace kunne aike ji


Bariki bashi Labarin yanda sukayi da Yarima tayi Kafin yace zaije ya dawo, taci gaba da fad'in Wlh Ina son fad'a mishi gaskiya Kinga sai muyi aurenmu lafiya ba tare da matsala ba.....


Habib gyara zama yayi yace lallai Bariki, ban taba sanin baki da wayau ba sai yau. Ke kina tunanin in kika fad'ama Yarima gaskiya zai aureki?? Kin bashi iyayen karya tare da Labarin karya ke kina tunanin duk son da yake miki zai yarda ya aureki? Karki manta kina fad'amin yanda yake kyaman mace mazinaciya, sannan kike gigin son fad'a Mai gskya? Toh inma shi Yariman ya yarda ya aureki kina tunanin iyayenshi zasu yarda??? Bariki kin San Gidan sarauta kuwa?? Shawaran da zan baki shine kiyi shuru da bakinki kiyi yanda kika tsara in an d'aura aure kya fad'a mishi gaskiya tunda naga kina mishi son tsakani da Allah kuma naga kina son zaman auren, kuma nasan bazai sakeki ba tunda ya aureki kuma basa saki..... Yau inda bakya sonshi Kinje gidan da wani manufa ne sai kice mai fyad'e aka miki, amma tunda son gaskiya kike Mai saiki fad'a mishi gaskiyan koke wacece.


Mahaifiyar bariki ta Karya, tace bariki gaskiyan habiba ne, wlh Indai kika fad'a mishi gaskiya zaki iya rasashi kuma na har abada, gidan sarauta zasu iya yarda su rasa d'ansu akan ace ya auro musu karuwa domin abun kunya ne, ki duba kiga su ko aure kayi a gidan sarauta sai Anga jini shine kin Kai budurci... Bayan bako wace mace ke jini ba kuma budurwa ce


Habib ya tabe baki tare da fad'in nidai Allah yasa ina d'aya daka cikin mata masu zubar da jinin, Kar insha gorin miji .... Dan mazan nan ba mutunci garesu ba.....🤣🤣🤣🤣


Bariki tace toh kuna ganin inna aureshi na fad'a mishi zai hakura dani?


Habib yace insha Allah, dole ma ya zauna dake tunda bada gardi ya kamaki ba, ai yanda kikaji dad'i al'adan gidan basa saki, sai an kamaka da gardi kuma kince kin tuba.....kuma na tabbata koda yayi fushi zai sauko tunda ya aureki zaki san hanyar da zaki janyo hankalinsa ma dole ya sauko, domin ya sami. santaleliyan yarinya son kowa k'in Wanda ya rasa...... Toh Bari dai mu gani bariki zata fad'ama Yarima inya dawo koko ta d'auki shawaran habib au🤭 Anty habiba.....


















~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 11*
















Dariya bariki tayi tare da fad'in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh ban son inga ya shiga wani hali, bazan iya jura ba, ina sonshi da yawa.....


Habib yace Toh fah, yau Ina ganin bariki.... Toh yanzu dai Mai kika yanke....??


Bariki tace abunda kuka fad'amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d'aura aurenmu aka kaini ranan zan fad'ama Yarima gaskiya.....


Habib shewa ya saki tare da fad'in Aiko ki tabbatar kin fad'a mishi tun Kafin ya shiga yaji ya shige zirif kaman bakin gate.....


Bariki duka takai ma habib iya karfinta tare da fad'in rafi ne ba gate ba


Habib ya ri'ke wajan da takai Mai duka yana fad'in na shiga uku zata kassarani..... Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu ki takarkare iya karfinki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba......


Bariki tace andai yi Asara


Habib yace ke kikaga Asara bani ba


Umman bariki tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu sai su kaimu gaba....


Habib yace gaskiyanki domin naga matar can d'akin ta kusa daku Tana min wani kallo wanda ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci in cire kaya mu daku Dan ban son iskanci....


Suna cikin haka Yarima ya kirata tare da fad'in baby come out Ina waje.....


Tashi tayi tana fad'in bari inje inga Yarima na.


Habib yace oh kunga salo a gayas....


Fita tayi tana fad'in kaji dashi.....


Motarshi ta nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud'e motar ta shigo ciki tare dayin sallama....


Amsawa yayi tare da fad'in my princess na gaji, tunanin driving nakeyi in zan koma Gida.....


Kallonshi tayi tare da fad'in ko in tu'ka ka, in kaika gida??


Yace dakin taimaka min kuwa


Dariya tayi tare da fad'in kaman dagaske....


Yace dagaske nake mana Kinga Idan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa....


Hannu tasa tare da rufe fuskanta tana dariya


Yarima kiran sunanta yayi da Zainab.....


Da sauri ta d'ago ta kalleshi domin jin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai muhimmanci.... Wanda yake bukatar natsuwanta


Yace d'azu kina son Yimin magana Ina jinki yanzu....


Murmushi tayi tare da fad'in Yarima a kullum Ina tsoran fad'a maka cewa ni dakai bamu dace ba, saboda kai ka fito gidan girma ni kuma ba y'ar kowa bace ina tsoran auranka domin gudun wulakanci irin na mas......


Da sauri yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad'in enough, dama duk wannan nonsense din kike son fad'amin shine kike d'agamin hankali?..... D'an tsaki yayi alaman jin haushi tare da kawar da kanshi gefe.....


Ganin ranshi ya baci yayi banza da ita, yasa ta d'ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri, ban San zakai fushi ba.....


Katseta yayi da fad'in Zainab ban taba tunanin zaki dinga irin wannan tunanin ba.... And kina ma sona kuwa????.....


Da sauri ta kalleshi tare da fad'in Yarima baki bazai iya fad'in irin sonda nake maka ba, how I wish in bud'e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka..... Yarima Ina Sonka yanda baka zato duk wani jini dake gudana a jikina yana gudana ne da Sonka I..... Da sauri tayi shuru ganin yana kallonta.....


Jin tayi shuru yasa ya ru'ko mata hannu tare da fad'in Zainab are you sure akan abunda kika fad'a??


Kai ta d'aga Mai alaman eh


Wani irin murmushi ya saki cikin jin dad'i, tare da fad'in nace zan baki albishir d'azu right?


Tace eh


Hannunta ya saki tare da fad'in ina goran albishir din???


Dariya tayi tare da fad'in zan baka in naji albishir din


Dariya yayi tare da fad'in promise?


Tace yes I promise....


Yayi murmushi tare da fad'in mai martaba ya amince da maganan aurena dake.... But at first yace in Bari nan gaba tunda ban dad'e dayin aure ba.... Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra'ayi ba yace za'a turo gidanku ayi magana d'azu waziri yake fad'amin May be cikin week dinnan a turo......


Bariki gaba d'aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba d'aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai....


Ganin tayi shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad'in lafiya kuwa my princess? Kodai you are not happy ne dan za'a turo??


Da sauri tace a'a am so much happy tare da sakin murmushi....


Ganin ta saki jiki yasa Yarima jin dad'i sun dad'e suna fira sannan Yarima yace Zai tafi tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a ciki ba....


Amsa tayi tare da fad'in ngd


Hancinta yaja tare da fad'in sai munyi magana.....


Tace OK tare da fita tayi cikin gida,.... Tana shiga habib ya amsa ledan tare da fad'in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa nakeji tun safe babu abunda naci....


Su turare ne Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud'i a ciki.... Habib d'aukan kud'in yayi dubu d'aya d'aya bandir biyu, dubu d'ari biyu kenan..... Yace Kai Yarima akwai kyautar girma....


Uwar bariki ta Karya tace ai gidan sarauta ya fito dole ya dinga kyautar girma.... Domin da suji kunya gwara dukiyarsu ta k'are....


Bariki kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad'in mai kuke cine Wai??


Ummanta tace abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya...


Bariki tace toh yanzu tunda nazo inyi sati d'aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib tayi tare da fad'in muje muyi cefane mu dawo......










********
Tsakanin haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da kalamai masu dad'i da kwantar da zuciya...... Sai dai abu d'aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar Hjy habiba ta yarda d'anta ya aureta ..... Sai dai haulat din tana ganin in bata yarda ba kaman ta nuna mata rashin adalci, and inma ta yarda ta auri d'an nata ya zasu dinga yima juna kallo........


Farhan ne zaune a falo shida mahaifinshi domin yana kasar.....


Farhan ya kalli dad dinshi yace dad I find someone dat I wanted to marry......


Kallonshi mahaifin nashi yayi tare da fad'in farhan aure Bayan baka kammala karatu ba


Yace dad Ina final year ne, Ina son a fara magana b4 in Gama....


Dad din nashi ya kalleshi cikin son gudan d'an nashi yace why are u so rush to marry??


Yace dad just


Dad din yace ok but wacece yarinyar and Waye mahaifinta??


Farhan yace sunanta haulat mum tasan ta domin at tym Tana kwana gidan na......


Muryan hjy habiba sukaji tana fad'in karyanka Wlh koda zaka mutu bazan bari ka aureta ba, gwara ma kabar wannan maganan.....


Mijin hjy habiba ya kura mata ido tare da fad'in akan wani dalili?? Har kike kiran koda zai mutu bazaki Bari ya aureta ba?? Kin kuwa San abunda kike fad'a kuwa? D'an nawa kike ma fatan mutuwa??..... Toh let me tell you Wlh Indai Inada rai kuma yana Sonta dole In tsaya mai.....


Tace ni kuma ban amince ba domin bai dace da ita ba....


Mijin nata yace habiba akan wani dalili? Miye rashin dacewan? Kallon farhan yayi tare da fad'in naji kaman kace yarinyar tana kwana a nan wani zubin....


Farhan yace eh dad


Kallon hjy habiba yayi tare da fad'in na tabbata inda yarinyar tana da aibu bazaki kawota gidan nan ta kwana ba, harki kasa fad'amin, domin naga Idan kikai ba'ki kina fad'amin but baki fad'amin wannan ba, ina son ki sani kaman farhan ya aureta ya Gama Indai Allah yasa matarshi ce babu yanda za kiyi.....


Hjy habiba tace ni kuma Indai har Ina numfashi kuma ni na haifeshi ban yarda ya aureta ba, kuma bazan taba yarda ya aureta ba....


Dad din farhan yace habiba Ina son ki fad'amin dalilin da yasa bakya son ya aureta??


Tace hakanan kawai ban son ya auri yarinyar


Dad din yace you are not serious.... Tare da kallon farhan yace inka kammala karatunka I promise zan tsaya maka har sai ka aureta.... Yana fad'in haka ya haura sama Fuuuuu tare da fad'in rabo dai yana kisa.....


Kallon farhan hjy habiba tayi cikin bacin rai tace wato

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login