Showing 45001 words to 48000 words out of 124261 words
Chapter 16 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt
tana d'an jin kunya kaman dagaske, mum ita da Yarima suka fita
Mum d'akin yarima sukayi tace Yarima Wai mai yake damunka ne? A haka kake son in bari ka kara aure jiba yanda kakema wannan ma Anya zakai adalci kuwa?..
Da sauri yace mum kiyi hakuri, yau raina a bace yake amma ai kin San your son zaiyi adalci mum
Murmushi mum tayi tace waya batama Yarima rai?
Dan shuru yayi Kafin yace mum Zainab taki picking calls dina, wai sai Bayan biki na, gashi babu inda zani Har sai an d'aura aure
Murmushi mum tayi danta gane itace wacce d'an nata yake so, tace bani number dinta in kira maka ita..
Kaman yana jira da sauri ya karanto ma mum number din, dialing mum tayi ringing biyu bariki ta d'auka tare dayin sallama dan tunda taga number din take tunani dan taga special number ne sai yasa tayi sallama
Amsawa mum tayi tare da fad'in my daughter, Yarima ya kawo karanki kinki d'aukan waya.
Jin haka yasa ta gane mum dinshi ce, da sauri ta gaida mum cikin girmamawa.
Amsawa mum tayi tare da bama Yarima wayan sannan ta fita
Yarima yace my princess do you know how worry I am right now? Wannan wani irin punishment ne haka? Kin San zan shiga damuwa Sosai na rashin jin muryanki
Bariki tace shine kasa mum ta kirani koh?
Murmushi yayi tare da fad'in Aida Nasan hakane dama tun dazu na fad'a mata, Zainab am so worried about you, harna fito Zanzo aka kirani....
Tace Yarima amma kace bazaka fita ba sai Bayan aure koka manta kace haka al'adan yake?
Yace ban manta ba, dama Nasan saboda kina tunanin bazan zoba yasa kika 'ki d'aukan wayana, ai inda Banyi magana dake ba yau Toh da komin dare sai nazo na ganki
Murmushi tayi
Yace I miss you my princess, ya shirye shiryen Walima?
Tace Alhamdullilah muna tayi, ga Kai yayi zafi, sai naga anyi an gama Kafin in huta.
Yarima yace Allah ya taimaka, gaskiya Kina bukatar hutu
Tace hakane idan muka gama zanyi tayin bacci har na sati d'aya in kashe waya na in huta
Yarima Aliyu yace joking, ban yarda da kashe waya ba
Murmushi tayi tare da fad'in ina amaryan mu?
Yace Tana nan yanzu ma zani in ganta.
Bariki tace uhm toh sai ka dawo Tana kokarin kashe wayan....
Yace karki kashe min waya ban gama magana dake ba..
Tace Yarima amarya na jiranka fah
Yace I know ita da zamu kwana gida d'aya
Bariki wani abu taji ya tokare mata a rai, amma saita dake tace uhm
Yarima jin tayi shuru yasa ya canza maganan da fad'in my princess very soon za'a turo gidanku so plz next ganin da zan miki a gidanku nake son in ganki, tunda har kin amince min inaga dan nazo babu wani laifi, sannan a ranan da Zanzo Zan nemi izini wajan baba
Tace Allah ya kaimu lokacin da zaka zo
Ya amsa da Ameen tare da fad'in my wife to be insha Allah
Murmushi tayi cikin jin dad'i
Sun dad'e suna fira cikin so da k'auna Kafin sukai sallama, tare da fad'in inya kirata ta d'auka ko ya fad'ama mum, dariya tayi tare da fad'in zan d'auka
********
Hjy habiba ce zaune daka ita sai rigan bacci haulat kuma na kwance akan cinyarta tana danna waya
Wayan hjy habiba dake ajiye kusa da ita ya fara kara, d'auka tayi taga son da sauri ta d'auka tare da fad'in ya naga number dinka na Nigeria?
Dariya yayi tare da fad'in mum Ina airport plz turo a d'auko ni.
Hjy habiba tace what a surprise, Bari in turo yanzu tashi tayi tana fad'in haulat tashi kisa kayan mutunci d'ana ya dawo yanzu za'a dauko shi a airport.
Haulat tace wow mum kice bros dina, tashi tayi itama ta nufi toilet dan tayi wanka dan basu dad'e da gama she'ke ayarsu ba suka zauna a nan
Hjy habiba tasa aje a d'auko mata gudan d'an nata daka airport inda itama tayi wanka tasa riga da zani na atamfa ya Mata kyau dan dama tana da kyan jiki, zama tayi a parlour tana jiran zuwan d'an nata...
Haulat ce ta fito itama cikin wata doguwar rigan less dinkin yayi mata d'as a jiki tayi kyau Sosai nufan hjy habiba tayi tare da manna mata kiss a baki
Hjy habiba taja baya tare da fad'in a'ah dakata mubar wannan abun sai a cikin d'aki any moment d'ana zai iya fad'owa so ya kamata mu dinga taka tsan tsan
Haulat tace Kai mum naga kin min kyau ne dana ganki harna Fara sha'awanki so nake miyi love plz mum
Hjy habiba tace sorry my daughter Bari farhan yazo inya shiga d'akinsa sai muje muyi abunda za muyi
Haulat tace ok mum
Suna cikin fira saiga wani saurayi ya shigo falon
Da sauri hjy habiba ta tashi ta nufeshi tare da rungume shi tana fad'in welcome son
Yace mum I really miss you tare da kara rungumeta
Idonshi ya sauka akan haulat dake tsaye tana ta murmushi, ido ya kura mata na wani lokaci sannan ya d'an saki mum dinshi tare da fad'in mum Bakuwa kikayi?
Hjy habiba tace eh sun tare da fad'in haulat ga farhan
Haulat tace sannu da zuwa
Murmushi ya sakan mata tare da fad'in yauwa nagode
Hjy habiba janshi tayi sukai sama direct d'akinshi suka nufa, suna shiga yace Kai mum wannan yarinyar tana da kyau Sosai
Hjy habiba bata fuska tayi tare da fad'in toh inma kana tunanin wani abu ka Bari domin bikinta ya kusa
Dariya kawai yayi sannan ya shiga toilet dan yayi wanka
Ganin ya shiga toilet yasa Hjy habiba fita danta jirashi a dinning yazo yaci abinci,
A falo taga Haulat tana waya tana murmushi tun Kafin ta karasa ta d'aure fuska domin ganin yanda take wani murmushi, kusa da haulat taje tana fad'in ke dawa kike waya?
Kashe wayan tayi tare da fad'in mum nida wani guy dina ne
Hjy habiba tace OK dan a zaton ta haulat na waya da wata mace ne sai yasa take wani kanne murya
Farhan ne ya fito cikin Kananan kaya yayi kyau Sosai dan dama babu laifi yana da kyau dogo ne bashi da jiki Sosai ga idonshi manya......
Kallon haulat yayi wacce take danna waya yace Mata haulat come let eat together
Tashi tayi suka nufi dinning din Wanda hjy habiba ke zaune na jiran fitowan nashi
Hjy habiba ce ta zuba mai abinci, Fara ci yayi yana yi yana kallon haulat duk hjy habiba na Lura da hakan wanda take ganin ya kamata ta d'auki mataki tun da wuri.... Hmmm muje zuwa dai
*******
Yau ake shirya mothers day Wanda mum din Yarima ce ta had'a, a cikin masarautar za'ayi, karfe biyu na rana aka saka mutane har Sun Fara hallara
Amarya ce cikin wani shegen less Wanda kallo d'aya zaka masa kasan Mai shegen tsada ne, anyi mata kwalliya na Kece raini babu laifi tayi kyau Sosai, bayan an gama shiryata da zata fita aka saka mata wata alkyabba akan kayanta nan kawayenta suka jeru gaba kuyangi baya ma kuyangi har wajan da aka tanada dan zaman amarya.
Yarima Aliyu kam yana gefenshi cikin bedroom dinshi shida usman falon abokananshi ne, Usman dake zaune a gefe yace plz Yarima ka tashi ka shirya mana kasan zamu je muyi mata koda 5mnt ne sai mubar wajan plz ka tashi ka shirya K...... Kiran mum din Yarima cikin wayar usman shine ya Katse Mai magana tare da fad'in Kaga mum ce ka tashi muje
D'auka usman yayi ban San mai mum tace ba naji yana fad'in ga munan ranki ya dad'e
Usman kallon Yarima yayi yace mum tace maza maza muzo yanzu
Tashi yayi rai a jagule ganin ya tashi yasa usman fita danya bashi waje ya shirya
Yayi wajan 30mnt sannan ya fito cikin wata Shegiyar shadda tare da malin malin ba karamin kyau Yarima Aliyu yayi ba kamshi kawai ke tashi ganin fitowanshi yasa abokananshi suka tashi dan tafiya wajan mothers day din tun a nan wasu suka fara d'aukanshi hoto, suna fita fadawa suka fara kirari har wajan mothers day din suka je, inda Yarima ya zauna kusa da amarya wato gimbiya zinatu, sunyi matukar kyau Sosai ana ta d'aukansu hoto
Nan aka saka wa'ka inda aka bu'kaci amarya da ango su fito, Yarima tashi yayi inda suka jero tare gimbiya ta sa'kale hannunta cikin na Yarima har filin inda za suyi ranan inda suka fara rawa tana manne a jikinsa, duk da Yarima yana dan basarwa baya son yi, nan abokananshi suka fito suna musu spraying, kawayenta ma Suma suka fito suna musu liki, abun dai gwanin sha'awa ana ta d'auka a hoto har y'an gidan tv Suma sun zo suna d'auka, Anata watsi da naira kaman ba gobe
Yarima ko 1hr baiyi ba yabar wajan ya samu ya silale ango ya gudu sai a bokanan ango kawai, ganin Yarima baya wajan yasa Suma suka bar wajan
Yarima d'akinshi ya shiga inda ya kira bariki har sau uku batai picking ba, yace where did she keep her phone ?
K'ara kira yayi amma still batai picking ba jin karan bud'e kofarshi yasa bai kara kira ba friends dinshi ne suka shigo suna fad'in saika tafi babu wanda ya Sani
Shuru yayi ba tare daya tanka musu ba danshi rashin d'aukan wayan zainab yana sashi cikin wani hali
Bariki kam tana kallon kiranshi taki d'auka domin wani irin azabban kishi take ji, danya fad'a mata yau za suyi mothers day tasan muddin ta d'auka sai taji wani abun ta rasa mai yasa ta kasa controlling kanta tana matukar kishin Yarima, wani hawaye ne ya zubo mata tare da fargaban duk ranan da Yarima yasan tana bin maza ta shiga uku, kirgawa ta farayi rabonta dana miji tace dole ina gama istabra 'I muyi aure karya ja wani lokaci Kafin a sami masu bakin jaba su fad'a ma Yarima ya fasa auranta, tunawa tayi sanda yake fad'a mata zina kawai zaki aikata in fasa auranki.... Lallai Yarima in yasan nabi maza bazai aureni ba, dole insa Ayi bikin da wuri in yaso Bayan bikin zan fad'a mishi komai da baki na tabbas dole auran ya zama na sirri ba kowa zai san da auran ba sai an d'aura a hankali ta furta karuwanci baiyi ba yaune rana ta farko da tayi data Sani tare da biye ma zuciyarta data ingizata tace mai yasa na yanke hukunci cikin fushi kuka ta saki mai taba zuciya .....
~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*
*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad @maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 25*
*INA MIKA SA'KON TA'AZIYA GA UMMU ABDALLAH TARE DA SAURAN MEMBERS DIN GROUP DIN BARIKI NA FITO FAN'S 1 WANDA TAYI RASHIN D'ANTA GUDA D'AYA TILO ABDALLAH😭😭😭😭ALLAH UBAN GIJI YAJI QANSHI YASA MAI CETO NE ALLAH YA BAKI HAKURIN RASHI🙏🙏🙏🙏*
Babu abunda take a halin yanzu saida na sani, duk da abunda aka mata yasa ta aikata hakan ido ta lumshe tana kokarin tuna baya, da sauri ta bud'e idon dan bata son tuna abun ba'kin cikin daya faru da ita, lallai mutane basa ansan kaddara Idan ya faru akan wani sai dai in akansu ne mai yasa ba'a amshi abunda ya faru da ita a matsayin kaddara ba kuka ta saki mai sauti, ina gatan da aka nuna mata ina kulawan da aka nuna mata Mai yasa da kaddara ya fad'a mata ba'a amsheta ba n....... D'an tsagaita wa tayi da kukan da takeyi tare da fad'in lallai shima Yarima ban tunanin zai amshi kaddara tunda iyayena sun kasa amsa lallai Yarima shida ya ganni daka sama bazai amshi kaddara ba Mai yasa na rayu Mai yasa ban mutu ba tun ranan dana had'u da wannan mummunan abun Mai yasa naci gaba da rayuwa kuka ta kuma saki mai sauti...
Kuka take Sosai lokaci d'aya idonta ya kumbura tare dayin ja, duk duniya babu wanda yakai mahaifinta Sonta inta cire mum dinta, haka shima mahaifinta duk duniya yafi Sonta cikin yaranshi amma shine mutum na farko daya Fara kyamarta da mummunan kaddara ta sameta Wanda bata san Ya akai ya sameta ba, mahaifinta shine mutum na farko daya Fara nuna mata kyama saboda gudun kunyar duniya duk da mutum ne mai sani amma baiyi amfani da sanin shiba la.... Jin karan wayanta yasa hankalinta yayi kan wayar Sunan Yarima ta gani harya tsinke bata d'auka ba kara kira yayi shima bata d'auka ba
Ido ta lumshe son Yarima Aliyu yayi mata yawa tana matukar sonshi sai dai bata tunanin shima zai amsheta a yanda take Dan yanda yake ta nanata mata bazai auri mace mazinaciya ba ido ta lumshe mai yasa son Yarima yayi saurin shigana? Mai yasa so yayi min shigan sauri tana maganan tana kuka Jin karan wayanta alaman sa'ko yasa ta d'auka ta bud'e ganin Yarima ne yasa ta bud'e dan taga Mai yace....
Zainab maina miki? Yau true out kinki d'aukan phone dina, kin San yanda nakeji kuwa? And I know kina ganin kirana in baki d'auki phone dina ba zaki ganni cikin daren nan.
Tana karantawa ta Fara kokarin kashe wayanta saiga kiranshi nan ya kuma shigowa k'in d'auka tayi dan a halin da take jinta yanzu bata tunanin zata iya magana gashi inta d'auka yaji muryanta saiya tambaye ta Mai yasa take kuka, wata zuciyar tace in yazo fah? Da sauri ta doka Mai kira k'in d'auka yayi sannan bai kirata ba ganin haka ta kara kiranshi amma ya'ki d'auka hankalinta ne ya tashi cikin sauri tasa dogon hijab tare da d'aukan wayanta tayi waje tana fita koh tayi Sa'a taga habib shida jamil suna zaune da sauri ta nufesu taja hannun habib sukai gaba
Habib yace lafiya kuwa? Kike jana kaman wata kububuwa?
Bariki cikin dashewan murya tace yarima, yarima
Habib yace maiya sami Yariman?
Tace yana hanya zai iya fad'owa koda yaushe
Habib yace na shiga uku cikin wannan tsohon daren karfe Goma saura fah yanzu Mai zai zo yayi miki kodai shima kin bashi zumar ne yasha?
Bariki tace a'ah saboda ya kira naki d'auka S..... Karan wayan habib ne yasa bariki yin shuru
Ciro wayan habib yayi cikin wata karaman jaka daya rataya yace lah Kinga d'an halak Wlh shine ke kira na, d'auka habib yayi ban San mai Yarima yace Mai ba naji yace eh Tana nan maraban jos, tare da kashe wayan. Habib kallon bariki yayi yace toh Yarima dai yana hanya dan haka saimu karasa gidan da yake ganinki
Bariki tace dare yayi bari in kara kiranshi banso yazo yanzu Kar wani abu ya sameshi..... Kiran Yarima tayi harya tsinke bai d'auka ba message ta mishi tare da fad'in
Plz Yarima pick my call, plz am begging you pick my calls
Kara kira tayi baiyi picking ba, gaba d'aya ta shiga damuwa message ta kara mai
Plz Yarima karka zo dare yayi karka biyo hanya plz
Shima shuru babu reply
Kallon habib tayi tace ina tsoran ya taso yanzu dare yayi karfe nawa zai zo Ya koma dan Allah kirashi kace karya zo.....
Habib yace nifa bariki ban son rashin mutunci na fad'a miki ki daina kaini jinsin da banawa ba
Bariki tace yakuri dan Allah ki kira min shi
Tabe baki yayi tare da fad'in yanzu kikai zance tare da Doka ma Yarima kira harya tsinke bai d'auka ba, habib yace Kinga Ya'ki d'auka nasan yana hanya dan haka sai kizo mu karasa
Babu yanda ta iya dole gidan suka karasa inda suka shiga ciki dan gidan na wata tsohuwa ne da y'arta guda d'aya itama y'ar duniya ce amma tana da aure basu yi koda 20mnt ba saiga Yarima yana kiranta da sauri ta d'auka....
Kafin tayi magana ya rigata da fad'in come out Ina waje yana fad'in haka ya kashe wayan
Kallon habib tayi da yake ta fira shida masu gidan tace ina zuwa yazo yana waje
Habib yace ok bari in jiraki a nan
Fita tayi amma abun mamaki bata ga motocin Yarima ba sai wata mota data gani kiran jeep tana shek'i gashi motar gaba d'aya baka ganin wanda ke ciki, har zata koma taji ana mata horn ganin haka yasa ta gane Yarima ne a ciki motar ta nufa tare da bud'e baya taga ya'ki buduwa gaban motar taga an bud'e gaban ta shiga tare da mamaki ganin shi yayi tukin yazo ba tare da kowa ba...
Kallonta yai tayi idonta duk ya kumbura yayi wajan 3mnt yana kallonta ba tare da yace komai ba, haka itama tunda ta shigo bata ce mishi komai ba
Hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi yayi hugging dinta, baka jin karan komai saina motar dan a kunne yake saboda AC yana kunne, sai kuma sautin numfashin su....
A hankali yace my princess Mai yasa kika k'i d'aukan wayana? Kin San yanda na damu kuwa? Mai yasa kike son d'agamin hankali? Kin San yanda nakeji Idan na kiraki baki picking ba? Dame kike son inji da auran da ake kokarin...... Shuru yayi tare da d'agota daka jikinshi yace my princess tell me maiya faru yasa kika k'i d'aukan wayana? Tell me
Kokarin magana takeyi amma ta kasa domin muryanta a dashe yake ganin haka yasa ta fashe da kuka....
Yarima Aliyu gaba d'aya ya shiga damuwa, yace Zainab plz stop it, mai yake faruwa?
Ganin taki magana kuma taki daina kukan yasa ya d'aura hannunshi akai cikin damuwa kanshi yaji yana juya Mai ga sautin kukanta da baya son ji..... Matsawa yayi kusa da ita ya rungumota tare da fad'in plz stop it bana son jin kukanki tell me maike damunki plz my princess...
A hankali tace Yarima Ina tsoran abunda zai faru gaba Ina Sonka ban son in rasaka, ina tsoran kaki amsan kaddara Nasan ban dace dakai ba m.....
Dakatar da ita yayi tare