Showing 84001 words to 87000 words out of 124261 words

Chapter 29 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt

dake??


Haulat tace bariki Wlh wasa nake miki, AI nasan bazaki taba aikata wannan abun ba... Kinga mubar maganan kiban shawara akan abunda ke damuna....


Bariki tace uhm, gskya Abun naku ne babba, toh amma inaga Indai auran kike son yi dagaske kuma tsakani da Allah, ya kamata ki daina aikata abunda kike yi, Indai kina son Allah ya taimakeki ki daina aikata sabo, and ita hjy habiba Indai zatai adalci ya kamata ta Bari d'an nata ya aureki, tunda harda ita cikin masu kara lalataki, inko ta hana d'anta auranki bata da adalci, sannan ita in Tana da hankali ya kamata ta gane Allah yana Sonta da shiriya ne, tunda har hakan ta faru d'anta na cikinta yake son abokiyar cin mushen ta, Kai Allah ya kyauta.... Uwa taci d'a zaici ta hanyar sunna 🤦‍♀


Haulat tace Kedai bari Wlh Ina cikin tsaka Mai wuya


Bariki tace ai bamu ga komai ba, tunda tun Farko mun zabi sabama Allah, yanzu muka fara gani ta karasa maganan tare da zubar da hawaye, taci gaba da fad'in haulat, sai yanzu na hango abunda ake cewa rayuwar mace kalilan ce, yanzu ki duba ki gani Ina manyan karuwai irin su magajiya jummai yanzu wake son zuwa wajansu tunda Sun tsufa, yanzu kowa mu yake rubibi daka mun Fara girma sai Muma a watsar damu, muna ganin ana rubibin mu duniya na rudar mu, sai muki yin aure, in mun Fara girma sai muji muna son aure lokacin mun daina samun kasuwa , sai a lokacin zamu fara dana sani, domin mun k'asa samun mijin aure, saboda mun bata rayuwar mu, amma namiji saiya Gama she'ke ayarsa ya auru, sannan kiga tsohon namiji yana neman yarinya y'ar shekara Goma sha, amma karya ne kiga matashi yana neman tsohuwar mace, wlh haulat aure shine ya dace da mace ba bariki ba, bariki babu komai sai dana sani fushi bacin rai, wanda bai isa ba ya fad'a maka magana, in bakai wasa ba wata rana wani ya zaneka, babu kuma yanda za kayi, kai rayuwar bariki rayuwar banza ce da shirme, duk da wasu suna fad'awa bariki domin Sun rasa abunda za suyi, wasu kuma kaddaran rayuwarsu ce hakan, wasu kuma ra'ayi ne yasa suka fad'a..... Kuka Bariki ta saki Tana fad'in haulat a duk ranan dana aikata zina Sai nayi kuka tare da takaicin fad'awa ta wannan harkan, sai yasa bana wasa da ibada domin neman gafaran Allah, tare da ro'kan shi ya canza min rayuwata, wanda kuma Alhmdlh Allah ya amsa ibada ta, na daina aikata abunda nakeyi..... Kuka yaci karfinta


Haulat itama idonta yayi ja alaman any moment zata iya zubar da kwalla daka idonta.... Tace bariki Magananki gskya ce, da yawa matan da suke fita Bariki bada son ransu bane, amma mutane basa gane kowa da irin tasa jarabawan sai su dinga aibanta mutum, wasu mutane are selfish Indai mummunan kaddara ba akan mutum ya fad'a ba sai su dinga ganin kaman da gangan mutum yake aikatawa, har Su dinga ikirarin cewa duk wacce ta zama karuwa ita taso, suna mantawa da Allah suma zai iya jarabtansu sai yaga yanda za suyi, yana dakyau in kaga mutum yana sabon Allah, Kayi mishi fatan shiriya ko kayi shuru...... Bariki duk karuwa Tana da burin tayi aure kaman ko wace mace but our destiny take us to where we are now..... Itama hawayen ne ya zubo mata, taci gaba da fad'in ni Nasan komai mutum yayi tashi kaddaran kenan Allah ya riga ya tsara komai, babu yanda za muyi, sai dai muyi fatan shiriya na har abada......


Dukansu kuka suke alaman tsoran Allah ya kamasu su duka biyun, suna cikin kukan wayar bariki ta Fara K'ara ,ganin Yarima Aliyu yasa ta d'auka tare da sawa a kunnenta Tana kokarin goge hawayen fuskanta.....


Yarima yace you are crying??


Ganin ya gane yasa cikin muryan kuka tace how did you know dat am crying??..


Mai makon ya bata amsar tambayan da tayi mishi, sai yace kina ina??


Tace ina maraban jos


Nanata Sunan yayi maraban jos??


Tace eh Yarima


Ok kawai yace tare da fad'in I will come to your house in d next 30mnt so ki dawo yanzu, yana fad'in haka ya kashe wayan.....


Bariki sororo tayi tare da tashi,


haulat tace ashe dagaske ne aure za kiyi,?


Bariki tace hakane zan baki labarin komai in mun had'u ko kuma muyi waya, zan tafi ana jirana.......






















~MARYAM OBAM~




*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 15*
















Bariki direct u/kanawa ta koma, har takai gida Yarima bai zoba, dan haka taita zaman jiranshi, tayi wajan 30mnt din sai gashi ya kirata akan ta fito yana kofar gida.....


Tashi tayi ta fita inda ta sameshi cikin mota....


Gaidashi tayi cikin kulawa tare da fad'in ya aiki??


Mai yakon ya bata amsa saiya kafeta da ido, ba komai yake tunawa ba sai kalaman mahaifin nashi, inda yace karya K'ara mishi maganan auran da yake son k'arawa ..... Ido ya lumshe yana tunanin abubuwa da dama, ya tabbata bazai iya juran rashin Zainab ba, amma ya, ya iya tunda mahaifin nashi haka ya bashi umarni.... Tunda yake abbanshi bai taba cewa Kar yayi abu ba ya ketare, yana ji a jikinshi bazai iya juran a hanashi auran Zainab ba......


Jin yayi banza da ita yasa ta d'ago taga ita yake kallo da sauri tayi k'asa dakai tare da fad'in Yarima lafiya kuwa??


Murmushi yayi tare da fad'in lafiya, kawai I miss you ne...


Murmushi tayi tace kullum fa saika ganni jiya ne kawai baka ganni ba....


Yace hakane, jiyan kawai da ban ganki ba, yasa naji kaman Nayi shekara ban ganki ba


Dariya tayi mara sauti domin taji dad'in maganan da yayi.......


Sun d'an taba fira, sannan ya mata sallama ya wuce.....


Bayan Yarima ya koma Gida direct wajan mum dinshi ya nufa, bayan ya gaidata ya zauna kusa da ita tare da fad'in mum plz ina son magana dake which maganan ya shafi rayuwana.....


Gaba d'aya hankalin mum din yayi kan Yarima wanda magananshi ya bata tsoro, musamman daya ce maganan dazai Mata ya shafi rayuwanshi..... Tace Yarima Mai ya faru?? Maiya sameka? Wani abu ne?


Yace mum akan maganan k'arin auren da nake son yine. Plz mum Ina son yarinyar Sosai, mum Bari kiji tun a mafarki na Fara ganinta........


Mum tace mafarki??


Yace eh, tare da bata labarin abunda yake faruwa... Ya d'aura da fad'in mum had'uwa na da yarinyar had'in Allah ne, ina matukar sonta, mum Idan aka hanani auranta ban iya j......


Da sauri mum tace ya isa haka, jikinta a sanyaye tace Yarima zanyi magana damai martaba, Kaje ka huta dan naga alaman kaman yanzu ka dawo.....


Yace eh mum, tare da tashi ya fita.....


Mum shuru tayi tana nazari, lallai ya kamata abar Yarima yayi wannan auran, tunda har Ya iya cire kunya ya Mata bayani irin haka..... Tashi tayi ta nufi gefen mijin nata , toko ci Sa'a shi d'aya ne, zama tayi tare da fad'in Barka da yamma.


Mai martaba Ya amsa da yauwa, yana ga kaman kina cikin damuwa? Domin Fuskanki ya nuna hakan.


Tace inada magana ne akan Yarima.


Da sauri mai martaba yace maiya sami Yarima din??


Tace babu komai magana ne akan auranshi da yake son karawa....


Mai martaba yace ba jiya nace abar wannan maganan ba, sai nan gaba


Tace hakane, amma ina son fad'a maka Yarima yanzu yabar wajena, akan maganan auran nashi, labarin yanda sukai da Yarima ta fad'a mishi harda mafarkin da Yarima yakeyi, sannan tace ina son in baka shawara ,tunda muke da Yarima bamu taba cewa yabar Abu ba, sannan daka baya ya dawo da maganan......


Mai martaba ya dakatar da ita da fad'in, lallai wannan babban magana ne, Yarima yana mana biyayya a matsayin mu na iyaye..... Tunda har na hanashi maganan ya kara taso da ita bai kamata in hanashi ba, domin hanashi zai iya sawa ya bijire mana, domin shi SO daban yake, sannan muma ya kamata mu masa adalci mu amince da duk wata bukatarshi Indai bai sabama Shari'a ba..... Yau na fahimta abunda ya dad'e yana damuwa, lallai iyaye k'alu bale garemu Idan d'anka ko y'arka suna maka biyayya tare dajin duk wata magana taku, Indai yaron ya Kawo muku abu kuka nuna bakwa so, Indai ya dage Toh ku tayashi son Abun tare da mishi fatan alkhairi..... Sau da yawa wasu iyayen suke saka yaransu suke bijire musu Bayan yaran suke da gskya amma iyayen Suki yarda da kudiran yaran, in ba'a sami Mai hakuri ba saiya bijire musu, yaka mata iyaye su dinga Lura da miye yaransu suke so tare da abunda suke bukata.... Kar matsayinku na iyaye yasa ku manta hakkin yaranku akanku...... Haka zalika Kuma yaran Kar soyayya yasa ku bijire ma iyayenku ,domin Kaf duniya babu mai muku son gskya kaman iyayenku....... Akwai wani labari da naji na wani yaro da yake son auran wata yarinya....... Yarinyar kowa yasan bata ji, Ma'ana dai y'ar iska ce yarinyar, lokacin da yaron Ya fad'ama ma iyayenshi sai suka k'i yarda suka ce ya nemi wata, shiko yaron yace Wlh ita yake so, aka buga aka raya, Baban yaron yace sam bai yarda Yaronshi ya auro yarinyar ba domin y'ar iska ce....... Ganin yanda babanshi ya dage, sai yaron Ya daina musu komai dama iyayen ba masu karfi bane, yaron ke musu komai tunda yana aiki,...... Toh Kunga irin matsalolin dake faruwa, a sanda naji wannan labarin Nayi takaici Sosai, ai iyaye iyaye ne, yaka mata mu dinga hakuri dasu, mu muna ganin mune akan dai dai, haka suma suke gani sune akan dai dai, in kayi hakuri kabi umarnin su, kasan kwana nawa za suyi a duniyar?? Koko saika rasa su zaka Fara kuka dayin dana sani?? Wlh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai basa raye, sai munyi hakuri da iyayenmu sau da yawa kana ganin abunda yake dai dai kuma kowa yasan dai dai ne amma su sai suce sam, in mutum ya duba Aida basa haka, yanzu harda girma daya kamasu sai yasa suke irin haka, Idan mutum yana girma tunaninshi yana kara canzawa...... Idan har yaro yana tuna haka ya kamata ya dinga hakuri da iyayenshi, sannan abunda kama iyayenka kaima haka naka za suyi maka shairi ko khairan, sannan Indai kai burinka kuntata ma iyaye bazaka taba ganin haske ba a rayuwa..


Mum tace hakane, Allah yasa mu dace


Mai martaba ya amsa da Ameen, tare da fad'in zan tura aje a nema masa auran yarinyar cikin satin nan insha Allah, saiku Fara shiri


Mum tayi y'ar murmushi tare da fad'in Allah ya bada Sa'a zamma Yarima albishir


Dariya Mai martaba yayi tare da fad'in dan nema ba, Ashe tun a mafarki yake ganin yarinyar ikon Allah.


Mum tace Wlh nima nayi mamaki, Allah dai yasa abokiyar zama ce.


Mai martaba yace lallai soyayyarsu had'in Allah ne, duk Wanda yace zai shiga tsakani akwai matsala


Mum tace hakane, tayu rabo ne na kusa tsakani sai yasa ya kasa hakuri, kuma rabo na kisa


Mai martaba yace hakane, Allah ya shige mana gaba.....






Mai martaba yasa an tura gidansu bariki, inda su waziri suka je, kuma babu laifi su waziri Sun yaba da irin gidan tarbiyan da bariki ta fito, domin tunda Yarima ya fad'a mata ranan da za suzo bariki ta hayo wasu mutum biyu Sunan sune y'an uwan mahaifinta, sannan duk ta tsara musu yanda za suyi.


Koda waziri yayi maganan sadaki akan nawa zasu yanke


D'aya daka cikin kawun Bariki na karya yace dubu hamsin ya isa, domin karancin sadaki shine albarkan aure,


Waziri yaji dad'i Sosai domin ya gano gidan mutunci Yarima yake neman aure sannan ba masu kwadayin abun duniya bane, duk da ya gansu talakawa kuma ko yanzu a sauron gidan suke zaune, Ma'ana a zaure.


Nan take Waliyan Yarima suka biya sadaki, dubu hamsin tare da K'ara million d'aya suka ce wannan kaman matsayin kyautatawa ne, tunda iya abunda suka yanke shine na sadakin,


Dakyar iyayen bariki suka amshi kud'in, domin cikin mutanan Yarima sunce gidan sarauta in sun bada Abu dole ake amsa, ba'a miyar musu. Sannan an tsaida rana nan da wata biyu


Nan dai akayi addu'a tare da tashi kowa Ya wuce.....


Cikin Wanda sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma'ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi magana Mai Kyau akan gidansu bariki 🤔 ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take?? Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za muji zamu gani....


Koda su waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad'a mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad'amai sai dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan, kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad'in sai dai abunda ya kara burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun duniya


Mai martaba yaji dad'i Sosai, tare da fad'in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su koma, wannan kyauta ce daka gareni


Waziri yace an gama godiya suke .


Bariki bayan magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan, nan suka bata kud'in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu. Tafiya sukayi suna godiya.


Kallon abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau


Yace Sosai kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had'asu, ina tsoran ranan da asiri zai tonu


Bariki tace karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.


Yace dakyau tare da fad'in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure


Bariki tace dagaske kakeyi?


Yace dagaske nake Wlh


Bariki tace Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu ai zan had'a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada


Yace ina godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne


Dariya bariki tayi tare da fad'in wannan haka yake.


Yarima Aliyu yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta sameshi a mota


Yarima kallonta yayi cikin jin dad'i tare da fad'in amaryata


Murmushi tayi cikin jin kunya tare da gaidashi


Amsawa yayi tare daja mata hanci, yace am so happy today


Kallonshi tayi tare da fad'in happy for wht?


Yace soon zaki zama tawa ..... Oh na manta kin ma riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki...


Murmushi kawai tayi


Yarima yace yaushe za muje kiga gininki?


Tace a'a basai Naje ba,


Yace toh ni ina son kije ki gani , ya za'ayi kenan??


Tace zan tambayi Umma inta amince sai muje


Murmushi yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??


Tace kaman me??


Yace event din da za'ayi


Shuru tayi tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su fad'ama Yarima gskya Kafin ita ta fad'amai, kai gskya a'a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi'a.....


Kamo hannunta yayi tare da fad'in, a'a ya kamata muyi koda Abu d'aya ne, muyi dinner, inaga zaifi


Tace toh amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta'ki yarda da maganansa.....


Kallonta yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud'i Kisai irin kayan da kike so, duk da za'a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki K'ara da irin naki choice din .


Bariki ido ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada dama Ayi mishi.


Sunyi fira akan in zai dawo zai Kawo Mata kud'i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata sallama ya tafi ..... Toh andai ce duk abunda akace an yishi had'e da karya komai daren dad'ewa gskya zata bayyana, zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa........




















~MARYAM OBAM~




*BARIKI NA FITO*








*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*WWW.Maryamobamnovels.com*




*Wattpad @maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*








*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*








*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








*BOOK 2*




*PAGE 16*












Bariki gida tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi tace Umma.....


Amsawa tayi da fad'in ya akayi? Yau dai Kedai shar


Bariki tayi dariya, tare da fad'in ina son miki magana Allah yasa zaki amince....


Umma din tace name fah.?


Bariki tace akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga zaifi muku.


Umma tace aure? Dawa Rufamin asiri, barni inyi abunda ya kawo ni.


Bariki tace kin fiso ki zauna babu aure??


Tace a'a ina so inyi mana inna samu dai dai ni


Bariki tace gashi kin samu


Dariya tayi tare da fad'in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had'awa??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login