Showing 39001 words to 42000 words out of 124261 words
Chapter 14 - BARIKI NA FITO BOOK 1 AND 2 BY MARYAM OBAM.txt
wacce fuska take a kumbure ga ido yayi ja, yace Mai zan gani dambe kikayi da wani?
Tace Ya'ki Nayi ba dambe ba.
Habib yace ah daka tambaya? Ke kika sani ina Fata dai kin San yau kina da ba'ko saiki tashi ki shirya muje inda zamu tun Kafin lokaci ya kure, ni Mai kika dafa ne yunwa nake ji wlh.
Tace ban dafa komai ba, nima saida kayi m.....
Yace dakata Mlm ban son iskanci miye wani kayi? Mai ya had'ani da wannan Kalman ina mace
Bariki tace Kai Allah ya kyauta
Habib da hjy babba suka amsa da Ameen
Habib yace dan Allah tashi kisa kaya mu fita daka nan maci abinci dan y'ay'an hanjina har kugi suke
Kaya ta d'auka tayi toilet tasa sannan ta d'auki Wanda zata canza anjima tasa a akwati karami suka fita
Bayan sun fita Hjy babba yaga mota sabuwa fil tana walkiya yace oh ji wannan motar Mai Kyau
Bariki kallon motar tayi ita harga Allah ma ta manta da ita.... Tace Alh madu ya bani ita jiya.....
Hjy babba yace shine baki fad'a mana ba amma dai baki da hali
Tace ni nama manta da ita Wlh sai yanzu dana ganta na tuna
Habib yace bariki Anya Kema baki Fara d'an taba shaye shayen nan ba? Taya zaki ce kin manta da motar da aka baki?
Tabe baki tayi tare da fad'in saboda ban d'auki kyautar da wani muhimmanci ba S.......
Hjy babba ne ya Katseta da fad'in amma dai gaskiya bariki baki da mutunci, wannan motar Mai Kyau matrix cefa, gata Sabuwa fil da ita, mutumin nan yana sonki amma kina mishi tsiya....
Tace hjyta yanzu saboda yaban mota kike wannan abun? Bayan kin San matsalan.
Tabe baki hjy babba yayi tare da fad'in Indai da kud'i ai sai Ayi hakuri haka....
Bariki tace bashi bane damuwa ta, hjyta inna dawo za muyi magana...... Gaba sukayi ita da habib
Habib yace bariki Wai wani tsohon ne ya baki mota kike kushewa?
Tace wani Sanata ne, mai karamin ayaba kaman na jarirai yaban.
Habib yace na shiga uku Nayi gamo karamin ayaba? Kuma kaman na jarirai Toh ya yake cinki da ita?oh ni habiba
Bariki tace ci kodai gogawa dan banjinta ako ina
Habib yace tunda ya baki mota ai Kinji dad'i yanzu dai kin San yakamata kiyi taka tsan tsan dan Kar Yarima ya gane wani abu, in kuma sanatan zaki aura Toh yana kaiwa nan ya sake shewa tare da fad'in sai kuje kuyi ta goge juna, tunda baida abun kwarai
Bariki duka takai ma habib tare da fad'in Rufamin asiri, in aureshi ince ma mutane Nayi me? Wai dana bani miji babu kayan harka
Habib ya saki shewa tare da fad'in shi Yarima yana dashi?
Duka takai ma habib tare da fad'in ban son iskanci
Habib yace karki kassarani, ai gaskiya ne shi yana dashi Mai girma ko ya Kar sai Kinje kiga wacce bata Kai ta jarirai ba
D'aure fuska tayi tare da fad'in habib Wlh ka daina dan ban son ana kushe min Yarima I.......
Habib yace ke zance ma ki daina miye kuma wani habib Toh Waye habib din? Taya zaki dinga kirana da Sunan maza Ina mace karki kuma in ba zaki cemin habiba Toh ki bari ban son iskanci yana maganan ne yana bud'e hanci alaman yayi fushi
Bariki gaba tayi tana fad'in ni Nayi gaba in Kaga dama ka zauna a nan
Binta yayi yana fad'in Wai bariki Mai kike nufi dani ne wai? Kalleni sama da k'asa miye a jikin ki wanda babu a nawa?
Dariyan da bariki batai niya ba ta saki tare da fad'in taya zan sani tunda kaya Sun boye muje kowa yayi tsirara sai a gani
Habib yace Aini ba y'ar iska bace in zaki zo muje kizo muje dan zaki iya ganin yarima ya fad'o koda yaushe
Gaba sukayi Dan zuwa gidan y'an uwan bariki na karya😹
********
Karfe hudu da wasu mintinoni motocin Yarima suka tsaya a kofar gidan su zainab wato bariki, message ya Mata tare da fad'in ina kofar gida
Bariki dake kwance akan tabarma taji wayanta yayi kara, d'auka tayi ta duba ganin sa'kon Wanda tun dazu take jira yasa ta tashi da sauri ta kara feshe jikinta da turare tare da shafa powder, fita tayi
Tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso matsowa yayi ya bud'e Mata kofar ta ciki
Tana kokarin bud'ewa taga an bud'e murmushi tayi sannan ta shiga da sallama tare da rufo kofar dan AC a kunne yake
Amsawa Yarima yayi tare da fad'in maiya sameki? Kina ciwon ido ne?
Kai ta girgiza alaman a'a
Yace Toh maiya sami idonki naga kaman sun kumbura? Ko kuma kikayi?
Tace Yarima wani mafarki nayi Wanda Yaban tsoro cikin mafarkin Wai nida kai muna fad'a har kace bazaka aureni ba saboda an fad'a maka mugayen Abu a Kai na kum........
Hannunta ya ri'ke Wanda yasa tayi shuru daka abunda tayi niyan fad'a, yace my princess bana tunanin akwai abunda wani zaice a kanki in fasa auranki Abu d'aya za kiyi wanda ko a masarautar mu babban laifi ne kuma yana d'aya daka cikin laifin Wanda Idan ka aikata dole kabar masarautar shine zina, wannan abun ne kad'ai zaki aikata na fasa auranki domin ni namiji ne mai kishi Sosai ina da kishin abunda nake so, wanda na tabbata ke bakya d'aya daka cikin masu aikata alfasha sai yasa a kullum nake kara sonki, ban kasance mazina ciba sai yasa a kullum nake ro'kan Allah ya bani mace tagari wacce ta tsare kanta daka rudin zamani
Wani hawaye ne ya silalo daka fuskan bariki wanda bata san sun zubo ba .....
Jin hannun Yarima tayi akan fuskanta yana share mata hawayen tare da fad'in baby maiya faru?? Ki daina wani tunani ina tare dake nazo jin amsa kona karbu Ashe an dad'e dayin accepting dina.
Murmushi tayi cikin sanyin jiki ba tare da tace komai ba, domin gaba d'aya maganan Yarima yasa ta fita hayyacinta tare da neman hanyan mafita, tabbas Idan Yarima yasan ita wacece bazai taba auranta ba, kenan mafarkinta gaskiya ne?.....
Katse mata tunani yayi da fad'in my princess tell me Mai kike ji a kaina?
Murmushi tayi tare da fad'in ai kace ka sami amsa
Yace eh but Ina son in kara tabbatarwa
Tace Yarima tabbatarwa ya wuce yardan da nayi za muyi aure Tana maganan ne tana rufe fuska alaman kunya take ji
Matsawa yayi kusa da kunnenta ya fara mata magana cikin rad 'a tare da fad'in I need my kiss...
Tana jin haka tayi saurin matsar da kunnenta Tana fad'in zan koma Gida
Murmushi yayi tare da fad'in yau babu inda zani har sai anyi min abunda nake so, sannan kema kina nan babu inda zaki
Tace Yarima ko gaisawa ba muyi ba.
Murmushi yayi dan yasan Tana son su canza zancen ne sai yasa tace basu gaisa ba , yace oh hakane fah bamu gaisa ba
Tace eh Ina wuni? Da fatan kazo lafiya
Murmushi yayi tare da fad'in lafiya qalau, toh mun gaisa yanzu koh?
Tace eh cikin murmushi
Yace Toh am waiting for it
Tace what???
Yace kiss
Ido ta lumshe ba tare da tace komai ba, wani irin son Yarima yake fusganta sai yau ta kara tabbatarwa da tana sonshi tunda ta ganshi taji wani irin sonshi na fusganta
Shima haka ta gefenshi wani irin sonta yake ji har cikin ranshi ji yake kaman ya tafi da ita ace yau mallakinshi ce da yafi kowa murna, daya nuna mata so Wanda bazata taba samun wanda zai Mata shiba, amma dai a kwana a tashi burinshi insha Allah zai ciki, ya tsara musu abubuwa da dama shida ita ya tanadar mata soyayya tsantsa Wanda zai nuna mata inya mallaketa
Bariki ido ta bud'e ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo, da sauri ta kara lumshe ido, tare da tunanin abubuwa da dama, lallai Idan Yarima yasan wacece ni Toh daka ranan na rasa shi, maiya kamata inyi? Hawaye ne ya silalo mata a fuska......
Janyota yayi jikinsa tare da share mata hawayen yace mai yake damunki ne yau my princess?
Tunda ya janyota jikinshi ya saka mata kanta a kirjinshi ta lumshe ido domin gaba d'aya jikinta ya mutu ga kamshin turarenshi dake dad'a tayar mata da hankali, yau ce rana ta farko da namiji ya Mata haka taji har tana sha'awa da sauri ta Fara kokarin Jan jikinta daka nashi amma saiya kara manneta dakyau
Ta gefen Yarima kam shima jinshi yake wani iri, ya rasa wani irin so yake mata, kwata kwata baya son ganinta cikin damuwa ko kad'an baya son yin nesa da ita akan dole yake tafiya ya barta, yau ne rana na farko daya kosa ayi bakinshi da gimbiya zinatu dan Ayi maganan auranshi da zainab dinshi....
Bariki ce ta katse shi da fad'in Yarima wayanka na wuta kaman ana kira.
D'aukan wayan yayi yaga gimbiya zinatu ce, murmushi yayi tare da d'auka har yanzu bariki na manne dashi yaki sakinta. Yace gimbiya Barka da yamma... Yana maganan ne yana Satan kallon bariki dake manne a jikinsa ban San mai gimbiya tace mishi ba naji yana fad'in saura kwana nawa a kawo ki kaman jibi ne koh? Tunda anan za'ayi komai.....
Bariki dake kwance a kirjinshi taja jikinta da karfi har wayan tayi kasa ta silale daka hannunshi, kallonta yake tayi yanda yaga ta murtuke fuska abun yaso ya bashi dariya amma saiya dake dama da biyu yayi hakan, wayan yake kokarin d'auka bariki kuma tana kokarin bud'e kofar, hannunta ya ri'ke Bayan ya d'auko wayan kashe wayan yayi gaba d'aya, ya kalli zainab dinshi yace Ina zaki?
Tace zani gida in d'auko Abu ne tunda naga kana waya
Yace Toh yanzu na gama
Tace ina zuwa yanzu zan dawo
Yace OK tare da sakar mata hannu,
Fita tayi tana shiga cikin gidan ta fashe da kuka, yanzu dan wacce zai aura ta kirashi nake wannan kishin shifa Idan yaji na bayar da mutunci na ga wasu mazan ya zaiyi? Kuka ta kuma saki Sosai tare da fargaban abunda zai faru in Yarima yaji wannan zancen.......
~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*
*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad @maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 22*
Kuka tayi Mai isarta, sannan ta wanke fuskanta tare da shafa powder dan Kar Yarima ya gane, saida ta tsaya ta seta kanta sannan ta fita.....
Tunda ta fito yake kallon fuskanta wanda dama tunda ta shiga idonshi nakan kofar gidan, tun Kafin ta karaso ya gane tayi kuka domin idonta yayi ja, dan farar mace Indai tayi kuka sai an gane dan fuskanta zata canza tayi ja ja......
Isowarta ne yasa tunanin da yake ya kawar
Bayan ta bud'e motar ta shiga da sallama muryanta a dashe....
Amsawa yayi tare da fad'in my princess yau kwata kwata na rasa gane maike damunki? Mai yasa kikai kuka da kika shiga ciki?
Gabanta taji ya fad'i ya akai yasan nayi kuka toh kodai ya biyoni ciki ne kai Anya a'a Toh y......
Katse mata tunani yayi tare da kiran sunanta da zainab
Da sauri ta d'ago ta kalleshi dan tasan magana zai Mata Wanda yake bukatan hankalinta tunda ya kirata da sunanta....
Yace I don't know why yau kaman you are not happy, plz Idan kina da wani matsala ko damuwa let me know, ban son kiji shakkan fad'amin wani abu da kike bukata ko kunya, plz tell me maike damunki?
Muryanta na rawa tace Yarima Ina son inyi maka wata tambaya, ina son Kuma ka bani amsa...
Murmushi yayi tare da fad'in go ahead....
Tace kasan al'amarin aure yana da abubuwa da dama, yau Idan akace mutum zaiyi aure sai ayita kushe shi, ko kuma azo ana ya'da Labarin karya akan mutum yan.....
Dakatar da ita yayi da fad'in enough my princess it seem like wannan mafarkin da kikayi yasa kike wannan maganan, na fad'a miki zina ne kawai zaki aikata in fasa aurenki..... Bayan haka banga abunda zaki aikata ba ince na fasa auranki ba, sannan ina so ki sani sonda nake miki ba Wanda wani zaizo ya fad'a magana akanki bane in yarda I trust you nasan bazaki taba bani kunya ba
A hankali tace in fah wani yazo yace maka ni karuwa ce ya Z........
Yace ya isa haka ya isa yana maganan ne cikin jin haushin abunda tace, yace karki kara danganta kanki da wannan Kalman infact ma ban son ki karamin wannan maganan plz..... Let change the topic
Shuru tayi ba tare da tace komai ba, Satan kallon Yarima tayi wanda taga gaba d'aya yana yinshi ya canza alaman ranshi a jagule yake.....
Katse mata tunani yayi tare da fad'in Zainab kinsa naji babu dad'i, mai yasa zaki damu da mafarkin da kikayi haka har kike zargin wani abu? Har kike dan ganta kanki da wannan mummunan Kalman, Zainab duk Wanda ya kiraki da wannan Kalman sai Nayi karanshi dan ba haka kike ba, I trust you more than my self, ina jin kaman na sanki tun tuni karki manta tun a mafarki na Fara ganinki ban taba ganin Fuskanki ba a mafarki ba sai a zahiri na ganki sannan na gane Kece..... Hannunta duka biyun ya ri'ke yace Zainab nasan had'uwa na dake had'in Allah ne, babu wani abu da wani zaice a kanki yayi tasiri a wajena Indai ba gani nayi da ido naba, so inaso ki daina duk wani tunani akan sonda nake miki
Wani hawaye mai zafi ne ya fito mata daka ido, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, tana son Yarima kuma tana son fad'a mishi ko ita wacece gashi ta d'auko hanyar fad'amai ya dakatar da ita, lallai in Yarima yasan wacece ita bazai aureta ba, zan Bari saiya aureni in fad'a mishi koni wacece na tabbata zai fahimce ni S........
Katse mata tunani yayi tare dasa hannunshi yana goge mata hawayen idonta, yace Zainab bana son ganin wannan hawayen naki, kina min asaransu.....
Murmushi tayi tare da fad'in na daina Yarima na daina bazan kara ba.
Hancinta yaja tare da fad'in yauwa my princess
Murmushi ta saki
Yace ya maganan Walima dinki? Mai zamu shirya?
Tace banda wani Abun cewa sai yanda kace.
Yace Nop ina son in San mai kike so..... Yauwa you never tell me what you like nd dislike
Tace Yarima komai kake so shi nake so
Murmushi yayi tare da fad'in toni ke nake so....
Dariya tayi tare da fad'in ni kuma?
Yace eh ke nake so,duk wannan abunda suke hannunshi na ri'ke da nata
Sakin hannunta yayi tare da matsawa ya d'auko wani karamin akwati ya bata yace gashi sai kiyi abunda ya dace, sannan akwai check a ciki nasa iya kudin da za'a cira amma ban sa suna ba Wanda zai cira sai yasa sunanshi, kiba ma islamiyya din, gudun mawarki....
Tace Yarima nagode Allah ya saka maka da gidan Aljanna ban San wani....
Ya dakatar da ita tare da fad'in ya isa haka my princess
Tace Yarima amma kaman hidiman yayi yawa Sosai
Yace komai na miki baiyi yawa ba, u deserve it
Tace ngd
Ido ya kura mata yana kallonta ko kyaftawa bayayi
Ganin irin kallon da yake mata yasa tayi saurin yin k'asa dakai
Hannunshi yasa ya d'ago Mata fuskanta yace my princess d'ago ki kalleni....
Ido ta rufe domin bazata iya kallon idonshi ba, dan yana mata wani irin mugun kwarjini Sosai
Ganin ta rufe ido yasa yayi murmushi tare dakai bakinshi kusa da kunnenta yace I want my kiss now, Bayan ya fad'a mata hakan yayi baya tare da kallon fuskanta yaga har yanzu idonta a rufe, iska ya hura mata a fuska tayi saurin bud'e ido, murmushi ya sakan mata idonsu duka yana kallon na juna, fuskanshi ya fara matsawa kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta ganin haka tayi saurin rufe ido, murmushi yayi yakai mata peck a goshi jin a goshi yayi mata yasa ta sauke ajiyan zuciya har yana ji, baya yayi tare da fad'in I don't want the kiss now
Kallonshi tayi suka had'a ido da sauri tai k'asa dakai
Murmushi yayi yace wannan kunyan yayi yawa but very soon zan rage miki shi
Murmushi tayi ba tare da tace komai ba
Yace Zainab very soon you will be mine
Ganin taki magana yasa yace bari inzo mu wuce tunda my princess ta k'osa in tafi
Da sauri tace nifa bance haka ba...
Murmushi yayi yace kina son in zauna?
Murmushi tayi tare da fad'in wannan tambayar..
Sai kuma tayi shuru
Yace Ina ji fad'a min?
Tace Mai zance?
Murmushi yayi yace say you love me
Itama murmushin tayi tare da fad'in yaushe zaka tafi?..
Dariya yayi yace oh saboda karki fad'a kike korana koh?
Tace a'a nifa ba haka nake nufi ba
Yace anyway ya kamata inzo in gudu naga yamma yayi Sosai gashi an kusa kiran sallah magrib...
Tace toh ka Bari in kukai sallah saiku tafi.
Yace OK my princess, yace banga mutumina ba yau?
Tace habib?
Yace eh
Tace baya nan amma zaka iya ganinshi ya fad'o yanzu
Yace OK.... Dan shuru yayi Kafin yace naso inzo saukan ku but I will try in samu inzo
Tace a'a Yarima basai kazo ba, ka Bari kawai duk abunda akayi zan turo maka, ranan fah shine Washe garin auranka kaga karka shiga hakkin amarya
Idonshi na kanta yace Kema ai tawa ce, sannan Idan abun murna ya sameki dole inzo in tayaki
Tace Yarima plz basai kazo ba Wlh na yafe maka, abunda bazan so ya faru akaina ba banso Ayi ma wata akai na
Yace really?
Tace eh
Yace Sai yasa nake sonki, but amma duk da haka Zanzo
Tace shikenan tunda haka kace, but Ina son Yarima na ya zama mai adalci, tunda ni nace na yafe
Murmushi yayi tare da fad'in shikenan Yarima dinki zaiyi adalci insha Allah tare da ja mata hanci
Tace akwai