Showing 24001 words to 27000 words out of 48594 words
Chapter 9 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt
kuka *TASLEEM* takeyi wanda tun *lnna* tana hanata kukan hardai itama tafara inda sai suhadu sutasa *Abban*, agaba sunayi wanda yake kwance rijib.
*TASLEEM* kam gani yanda ciwo yake kokarin kashe mata *Abbanta* yasa suka fara shiga wani hali, musamman *TASLEEM* datake mugun kaunar iyayanta wayanda batada kamarsu duniya, dan haka tafara neman aikatau saidai bata samu ba, dan haka tayima wata mata makociyarsu magana cewa dan Allah tayima wata dillaliya magana tasamo mata aikatau.
"Inda cikin yardan Allah akasamo mata dillaliyarce dakanta takaita har gidan wanda bako ina bane face gidansu *TAUFIQ*, bayan *Momma* sun gaisa da dillaliya dai itama *TASLEEM* ta gaida Ita cikin girmamawa, sannan dillaliya tace hajiya yaudai ga me aiki nasamo maki, cikin murmushi tace to madallah saidai kuma dillaliya matar aure kika samo mun?...
da sauri tace a ah! hajiya budurwace sai ita din dai ma'abociyar saka nikaq dince kasan cewarta natsatsiyar yarinyace, *TASLEEM* bude fuskarki taganki wanda ahankali tad'aga nikaq dinta, wanda saida *gaban *Momman* yafadi saboda tunda take bata ta'ba ganin kyakkawar yarin irintaba, ga fuskarta cikeda kamala hakan yasa take *Momma* taji *TASLEEM* din taji tashiga ranta.
Cikin murmushi tace tubarakallah masha'allah! ga yartawa kuwa kyakkawa, dillaliya tace akuwa dai wlh hajiya yana daga cikin abinda yasa take saka nikaq din saboda tsaro, *Momman* tace "eh hakan yanada kyau dan haka badamu ko nan dinma idan tana bukata zata iya cigaba dasawa babu damuwa, ko bakomai kusan kullum gidan nan cike yakeda jama'a kuma maza.
Nan dai *Momma* tasallami dillaliya ta hanyar bata kudi masu yawa sannan tawuce, sannan takalli *TASLEEM* wacce ke d'ari-dari kasan cewar Ita tunda take bata ta'ba ganin gida me girma da kyau irin hakan ba, dan hakane cikin ranta tafara tunani kaddai dillaliyae nan siyar da'ita tayi domin taga hajiyarnan tabata kudi meyawa.
Ganin hakan ne yasa tace "yata *TASLEEM* kisaki jikinki kidaukeni tamkar ni nahaifeki kinji?...kai ta gyad'a ahankali, tace yauwa to tashi nagwada maki part din dazaki ringa gyarawa tace to tareda sauke nikaq din.
Bayan *Momma* takaita sannan tafito dai-dai lokacin da *TAUFIQ* yashiga falon bakinsa daukeda sallama kallonshi, amsawa tayi cikin saki fuska zama yayi akan kushi tareda cewa wash! my *Momma* nagaji, cikin sakin murmushi tace sannu aidole kagaji tunda kazo baka hutaba kullum sai kafita, neman wannan yaron Allah dai yasa kaganshi yace ammen *Mommana*.
To yaudai ansamu wacce zata ringa gyara maka part yace yauwa *Momma* ai tunda twins dinki suka koma school d'akina yazama wani iri,
tace to sai kaje ka gwada mata yanda zata ringa gyarawa yace ok tareda tashi yanufi part dinsa,
saidai kuma yana cikin taka benen yaji zuciyarsa tana wani irin bugawa ahaka dai yahaye yana tura kofa sukai karo da *TASLEEM*, wacce itama tunda tashiga d'akin take jin bugawar zuciya cike da tsananin tsoro shiyasa zata fito, shine sukai karo kai *TAUFIQ* yad'ogo da sauri inda yaga mutum cikin bakakan kaya ido yazaro cike da mugun tsoro yace.....
Aha! za'afara
Muje zuwa
[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page 1️⃣8️⃣-1️⃣9️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.
_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.
*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,
Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
""""""""Cikin sanyayya muryasa yace wayyo *Momma* meye nan haka kuma ad'akina bakikirin tundaga kasa har sama eye?....
"duk da bugawar da zuciyarta yakeyi hakan bai hanata jan tsaki ba cike da takaici, najin wani maganar rainin hankali dayai mata yana ganin mutum sarai amma wai yana tambaya menene haka, sai kace makaho ko dayake damasu masu kudin nan hakan suke da rainma talaka wayo, jima wani tsabar walakaci har da wani cewa wai menene nan haka ba'ki'kirin a ah! ba ba'ki'kirin bane gawani 'kirine.
"Duk acikin ranta take yin wannan maganar nan tareda kokarin fitowa daga d'akin cike da haushi, yayinda shikuma *TAUFIQ* yasake cewa shin wai mutum ne ko aljan?...tareda matsawa baya, shuru tayi batareda tabashi amsa ba domin gaba d'aya ya'bata mata rai, inda yahad'e da matsananci bugawar da zuciyarta yakeyi wanda tunda tashigo gidan taki jishi,
musamman yanzu da tashigo wannan d'akin me bala'in sanyi kamar kashiga cikin firiza, sannan shikuma wannan yazo ya'kurawa mutane idanuwansa masukama dana mage dan hakan yasa duk take jinta wani iri.
"Yayinda shi kuma ganin hakan yasashi sauri sake matsawa gefe, yanasake kura mata brown eyes dinsa masu saka marajin magana natsuwa, saidai cike da d'an alamar tsoro atareda shi, yace to wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahirramanirrahim!,
sannan yai kokarin juyawa cikin mugun sauri inda yafara taka benan cike da kwarewa.
Yayinda itakuma cike da bacin rai tayi saurin tad'aga niqaf dinta tana me watsama bayanshi harara, tareda cewa kaima wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahirramanirrahim akanka, "kai aljani amma nidin ba aljana bace" balle kayi mun addu'ar aljanu eheee! ta karashe tareda murgud'a masa baki cikin tsiwa.
Da sauri yatsaya chak! "saboda jin wata zazzakar murya wacce duk da cewa cikin 'bacin rai had'eda tsiwa akai magana da'ita", hakan be hana zakinta fitowaba sai kuma yajuyo da sauri tareda sauke kwayar idonshi akan kyakkawar farar fuskarta, wacce shi tunda yake bai ta'ba ganin kyau irin nataba arayuwarsa, hakan yasa yaji kirjinsa yatsananta bugawa da sauri yarintse ido
itama *TASLEEM* jitayi kirjinta yasake bugawa musamman kwayar idonsa data sake kallo sosai kafin yarintse, hakan yasa taji wani irin tsoro yakamata.
"Amma sai tabasar tareda kauda fuska gefe tana turo baki cike da jin haushisa wanda taji lokaci d'aya yakamata, yayinda yabud'e idon da sauri tareda yasake zubasu akanta cikin tsananin sanyi jiki da kasalar da tarufesa lokaci d'aya, yafurta yah! robbi yau nayi gamo tareda sake rintse idon akaro na biyu.
Hakan yasa da sauri tajuyo da fuskarta cike da mamaki take kallonsa, aranta kuma tana fad'in kujimun "mutumin nan fa, ni da naga idanuwa nan nashi irin na mage bance nayi gamoba, sai shine zayace yayi gamo to dame?...
yayinda shi kuma yabud'e idon da sauri tareda juyawa yafara taka benen bibbiyu cikin tsananin zafin nama, wanda kance kwabo har yakai falon *Momman* yana kwala mata kira ba 'kau'kautawa, itakam tsaki taja mtsw! cike da takaici ta furta Allah dai yasa ba part din mahaukaci zan ringa gyarwa ba, sannan tanufi part din batareda ta sauke niqaf dinta ba saidai tanajin kirjinta yana sake tsananta bugawa.
*********
Yana shiga falon yazube akan kushin me zaman mutum biyu yana sakin numfashi tareda dafe kai cike da bugawar zuciya, dai-dai lokacin *Momma* tashiga falon da d'an saurinta, kasan cewar taji kiranda *TAUFIQ* din yake mata da karfi, tamkar wani makaho sabon kamu. Kallonshi tayi cike da mamaki tace 'danlele lafiya kake kwalamun irin wannan kira haka kamar makaho,
da sauri yad'ago kai yakalleta cikin fad'uwar gaba yace *Momma* aidole nakiraki haka domin yau nayi gamo, banma sanko mutum bace ko aljana ko dayake kai! *Momma* da aljana nayi gamo. Dai-dai lokacin da *TASLEEM* tashigo yace yauwa gatanan *Momma* wannan din dai bamutum bace aljanace, cike da haushi *TASLEEM* tace kaine dai aljani bani ba eheeeee!.
aikam me *Momma* zatayi ba dariya ba, tareda tafa hannu tace kai! d'anlele wani lokaci da wauta kake kamar d'an fari ashekai, *TASLEEM* ce fa sabuwar yar aikin danake fad'a maka nasamo maka zata ringa tayani aiki tana kuma gyarmaka part dinka, tunda su "Hussy masu gyara maka sun koma school kuma ai daka shigo nafa'a maka har nace kaje kaganta" ko har ka manta ne?...,
Fuska had'e yace a ah! ban manta ba amma saboda Allah *Momma* sai arasa wacce za'asamo mun, sai wannan me kama da aljanun sannan tawani saka bakaken kaya tundaga kasa har sama sai kace wata ojuju, *Momma* kuma kinsan banason bakin abu ko?...
da sauri *TASLEEM* tace kada Allah yasa kaso bakin abu din ina ruwan wani, dad'inta dai bakin kalace me daraja ato kuma malam kar kasake kirana aljana domin ni din ba aljana bace saidai idan kaine aljani,
kuma kaima ojuju eheee! takarashe tareda murgud'a masa baki cike da tsiwa.
"Aikam baki yasaki tareda kura mata ido yana kallonta cike da mamaki, yayinda aransa yana fad'in wannan wacce marar kunyar yarinyace haka yau *Momma* takwaso eh?....,
yayinda *Momma* take ta dariya domin sosai wannan dramar tayi mata kyau had'eda dad'in kallo, fuska yasake had'ewa tareda cewa *Momma* idan har "yarinyar nan tacigaba da gayamun maganar banza zan tatttakata agurin nan wlh. Da sauri *TASLEEM* tace katakani lallaima wlh baka isa kata kaniba malam, saidai kataka takalmin kafarka eheee...
"Mikewa yai da sauri tareda d'aga hannu cikin zafin nama yanufita da nufin marinta, aikam da sauri *Momma* tashiga tsakaninsu tana me 'kumshe dariyarta, tace a ah! d'anlelena abin baikai haka ba, cikin karfin hali me had'eda bugawar zuciya tace kutttt! lallaima wannan mutum, hajiya aida kin barshi yamareni dayasan waya ahamara, rai amatukar bace yad'aga murya cikin turanci yace ke din wacece?...
da sauri tabashi amsa dafin, kaima wanene?...cike da takaici yace kanama bakisan koni wanene ba kikazo aiki gidanmu?....tace ina ruwana dasani kokai wanene, nidai *MUTUMCE* me kima sannan fuskata me matukar darajace dan haka bazata ta'ba maruwa ba agareka eheee.
Tsaki yaja mtsw! cike da takaici yace sai ko namareki kuma namari banza babu abinda za'ai, itama cikin takaici tace wlh baka isa kamare niba kace babu abinda za'ai, da sauri *Momma* tace yanzu dai ya'isa haka kaga zauna zama yai yanajan tsaki cike da mugun takaicin.
Yayinda takalli *TASLEEM* wacce sosai taji tasake shiga ranta saboda hango tsananin karfin halinta, murmushi tayi tareda dafa kafad'arta tace yi hakuri kinji 'yata *TASLEEM*, zumbur yamike da sauri tamkar wanda akasokama allura yace haba *Momma* nifa tagayama maganar rashin kunya amma kuma kike bata hakuri?....,
kafad'arsa tadafa ciki murmushi tace to aikai babbane shikuma babba da hakuri akasanshi, cikin haushi yace shikenan kuma sai ariga gaya mashi maganar banza?....tace a ah! to yanzu dai kaima yi hakuri shikenan ko?...yace hum! kuma karta sake shigarmun part danwanna bakin kayan eheee! sannan yazauna tareda jan kuta.
Cikin dariya tasake kallo *TASLEEM* wacce itama take kallo tareda sanjin hukuncin dazata yanke, akan abinda yafad'a sai kawai tace mata jekiyi aikin dake gabanki kinji?...cikin sanyi murya tace to, domin ko kad'an batayi tsammani hakan daga hajiyar ba saboda yanda tafad'ama d'anta maganganu, agabanta ko shayinta batayiba wata zuciyarce tace mata to aishine yafara dan haka aiba wani abun bane dan kin rama.
Har tajuya zata koma d'akin sai *Momma* tace au! 'yata *TASLEEM* jimana hakan yasa tajuyo. Tace muje d'akina kicire wannan hijab din da niqaf idan kingama aikin sai kisaka abinki dafatan bantakura makiba?.....
cikin sanyi jiki ta girgiza kai tace yauwa to nagode sosai da girmamani, sannan suka shiga d'akin *Momman* yayinda *TAUFIQ* yabi bayan *TASLEEM* din da harara, tareda jan tsaki mtsw! sannan yakishingid'a tareda rufe ido inda sosai aransa yakejin wani irin mugun haushin wannan yarinyar wacce da alama yar talakawace.
*********
Bayan sunje tacire hijab da niqaf din harda safar kafan data hannu, inda kayan jikinta suka bayyana wato riga da siket ne na atamfar roba wanda yad'an fara shanjiki, saidai kuma kasan cewar yana hannun me tsafta sannan yasamu d'inki me kyau wanda yafito da ainihin surar jikinta me d'aukan hankali, dan haka ba lallaine kagane tsufan shiba.
Sannan wanda motsin fitowarta ne yasashi bud'e ido tareda d'orasu akan kayan jikinta zuwa surarta, wacce tasa saida yaji zuciyarsa tai wani irin mugun bugawa amma sai yabasar tareda jan tsaki mtsw! har tawacesa, yace aikin banza aini nasan duk wannan bazaki wuce yarta takawaba.
"Da sauri tajuyo tareda fadin tabbasa ni yar talakawace bakai karyaba, saidai kuma kasani bawai dan nakasance yar talakawa bace shine zayabaka damar cimun mutunci na kyaleka ba, dan kaga zan kasance akarkashinku kagane ko?...
banza yai da'ita hakan yasa tawuce tana tafiyarta me d'aukan hankali, tareda wasada tsintsiyar laushin hannunta, hakan yasashi bin bayanta da kallo dai-dai lokacin data juyo, da sauri yad'auke kai yana daga barin kallonta yana jan tsaki mtsw.
Yayinda ita kuma cikin tsokana tace da mutum yatanka mana idan ba tsoro ba, Hakan yasa yamike zumbur cike da bacin rai kinsan Allah idan banyi ball dake ba agurin nan kice menake, cike da tsiwa tace to dama me kake bayan d'an adam matas tabbas eye?...kwalama *Momma* kira yayi aikam sai gashi tasake fitowa da sauri, tana fad'in haba d'anlelena har yanzu bakayi hakari bane?...cikin kunar rai yace *Momma* ki kori yarinyar nan bana bukatar aikinta,
tace haba d'anlelena hakuri zakai tunda kaga nariga na dauketa kaji?...cikin hassala yace to kigaya mata ni ba sa'anta bane dan haka idan har zata cigaba da gayamun maganar banza, zan karyata wlh, ido *Momma* ta zaro tareda cewa haba d'anlelena duk me yai zafi hakan eye?... batareda yace komai ba yakwashi wayoyinsa yafita cike da bacin rai, *Momman* tana kiransa amma bai amsaba balle yajuyo yadawo.
Murmushi tayi tareda kallon *TASLEEM* wacce kanta ke kallon kasa cike da jin kunyar *Momman*, tace dan Allah 'yata kiringa sanin maganar dazaki fad'a masa kinji?...saboda zuciyarnan tashi akusa take d'a abu kad'an sai ya'bata masa rai, cikin sanyin murya tace to hajiya kiyi hakuri insha'allah zan kiyaye tace bakomai nagode, jekiyi aikinki tace to tareda wucewa tana murmushi ita kuma *Momma* ta girgiza kai tareda shigewa daki tana dariyar wannan dirama.
********
Bayan *TASLEEM* tagama gyarma *TAUFIQ* d'aki tsaf tafeshesa da turaran d'aki, sannan tafito takoma part din *Momma* da sallama tashiga falon ta amsa tareda zama kusa dakafarta tace hajiya nagama, tace to madallah sannu da aiki.
Gashi yau duk masu aikin nawa sunje ganin gida kauyansu, dan haka tashimu shiga kichin kitayai mud'ora girkin rana kinji?..tace to hajiya, Nan suka shiga kichin din wanda kad'an yarage *TASLEEM* tayi kauyanci, saboda tsabara had'uwarsa cikin kankani lokaci suka gama girkin ranan,
bayan sun jera akan dinning table tace tasaka hijab tadauki na masu aikin mata takai masu, bayan tadawo sai *Momma* tace tazuba masu suci cikin girmamawa *TASLEEM* tace hajiya ina azumi yau, tace eyya to Allah yabada lada kinga nimafa inayi kwana biyu ne dai kawai banyiba saboda nad'anji ulser ta nakokarin tashi, cikin murmushi tace Allah sarki Allah yakara sauki tace amin nan *Momma* taci abincin, sun gama d'aya daba cikinsu yakawo kwanonin ta wanke ta gyara kichin.
Kasan cewar yau alhamisce babu islamiya dan haka sai gurin karfe biyar *TASLEEM* tabar gidansu *TAUFIQ*, cike da kaunar *Momma* wacce ta cikata dakayan bud'e baki cikeda leda tareda had'a mata dabata kudin mashi naira dubu da d'ari biyar, koda tasauka akan mashin bata shiga gidaba tukun gidan makociyarsu tashiga wacce tasamo mata aiki dan tayi mata godiya.
Da sallama tashiga inda matar me suna iya Habi ta amsa tareda cewa a ah! su *TASLEEM*
har andawo aikin?..., cikin dariyarta me kayatarwa tace "eh wlh iya Habi dawowata kenan banmako shiga gidaba nace bari na shigo nasake yimaki godiya sannan nabaki abinda nasamo kema kisa abakin salati takarashe cikin dariya tareda tsugunnawa tana kokarin ciro abu cikin leda
Yayinda iya habin tace Allah sarki *TASLEEM* aiba komai wlh ni ina nan ina tayaki murna ashe gidan Alh *TAUFIQ RASHIN TAFIDA* shahararran matashin me kudin nan akasamo maki aiki da sauri *TASLEEM* tad'ago kai ta kalleta cikin bugawar zuciya tace......
Aha!wasan yafara dan haka muje zuwa.
*MEENAL* or LUFHAT*
_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page 2️⃣0️⃣-2️⃣1️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.
_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.
*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,
Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin