Showing 39001 words to 42000 words out of 48594 words

Chapter 14 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

mata alamar "eh cikin faduwar gaba tace meyafaru to da kakeyin kuka haka eye?...cikin shasshekan kuka yace *TASLEEM!* *TASLEEM!!* *TASLEEM!!!* saida yafadi sunan har sau ukku, sannan yace tun bayan batanta nakanji matukar tsoro narashin sanin halin datake ciki shin tana cikin yanayi me dadine?...ko kuma akasin hakan?...Allah masani,




Cikin sanyin jiki tace hakane *Abban* *TASLEEM* kayi hakuri kadaina kukan hakan kasan ba lafiya gareka sosai ba,wallahi nima ina matukar jin tsoron halinda take ciki,wanda tabbas Allah shine masani dan haka addu'a zamu cigaba dayi mata Allah yakareta daga dukkan tsanani
datake ciki.




Kai ya gyada tareda da share hawaye sannan yadaga hannuwansa sama tareda kallon sararin samaniya, yace yaAllah ubangijin sammai bakwai da kassai bakwai yawanda yasan abinda ke fili da boye Allah ga "baiwar kanan wacce ita kadai tarege mana tilo,




sai gashi kuma tabace mana yautsawon wata daya kenan batareda munsan inda takeba dakuma halinda take ciki, amma kai kasani saboda buwayarka da isaka ya Allah muna rokonka idan har tana cikin halin tsanani ya Allah ka kubutar da'ita kadawo mana da'ita garemu, sannan yashafa addu'ar wacce tareda *Inna* suka shafa cikin sanyin murya tace muje kayi wanka kaci abinci sai kahuta, jiki asanyaye yace to.






*******
Aban garansu *TAUFIQ* kuma koda yashiga dakin kamar yanda likita yace hakane ya'iske *TASLEEM* tana sharan barci abinda, yayinda numfashinta yake yasauki ahankali cikin nitsuwa hakan yasashi sauke ajiyar zuciya yayinda yaji hankalisa yakwanta sosai, ko bakomai *Mammansa* bazata shiga tashin hankalin rashin wannan aljanar yarinyar ba yakarasa da zuba mata harara.




"Sannan ahankali yaja kujera yazauna tareda sake ciro wayarsa dayasaka cikin aljihu tin lokacin dazaya ci kwalar likita, danta yafarayi tsawon lokaci yana danna waya still yana jan tsaki mtswww! dakuma hararanta, wanda da alama har yafara zama mashi jiki yayi nisa chat batareda yasake kallon inda takeba, kasan cewar tuni yajuya mata baya can sai yaji kamar motsi tabayanshi hakan yasa yajuya da sauri ga mamakinsa zaune ya'iske *TASLEEM* atsakiyar gadon ta lankwashe kafafunta,


tanata faman gyaran gashinta da yarufe mata fuska tana tabe baki da sauri yaja kujeran zuwa gurinta gabansa nafaduwa yazauna agabanta, dai-dai lokacin datayi nasaran maida gashin nata abaya but amma still wani yasauko tagefen fuskarta sai yakara mata kyau duk dacewa fuskar tayi fau irin tamarasa lafiya, kallonsa tayi fuska kwabe shidinma kallonta yake fuskarsa hade yace sannu yajiki?...




shuru tayi kamar me nazarin wani abun still tana kallonsa, kara hade fuska yayi fiyeda farko yace ke dalla gafar can danma kinsamu angaida ke shine zakiyima mutane iskanci kiwani tsuramun ido sai kace mayya, to koma kedin mayyace saidai kici kanki nidai kam bazan ciwuba domin nafi karfinki dan haka kurwata kur! kinji ko?....




itadai batace komai ba sai kallonsa take musamman bakisa dayake motsi, tsaki yaja mtswww! yaname sake kafeta da ido yace malam sai wani kallona kikeyi ko bakiji bane nace sannu yajiki?....ahankali cikin cool voice dinta me dadi wacce takara laushi saboda yanayin datake ciki na rashin lafiya, tace sannu yajiki?...ido *TAUFIQ* yazaro cikin tsanani tsoro da bugawar zuciya yace.....






Aha muje zuwa






_Ya ALLAH kasa mucika da imani ameen yahayyu yakayyumu_
[8/10, 8:45 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️


🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page 3️⃣3️⃣-3️⃣4️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,


sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.


_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.


✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


"""""""" _What?_....ke! malama nikam lafiyata lau kece dai bakida lafiya dan haka nema kikaji nace maki yajiki wanda albarkacin *Mammana* kikaci har nace maki yajikin, amma kuma saboda kedin dakikiyace sai kikasake maimaita abinda nace wai sannu yajiki,




yafadi tareda kwaikwayon yanda tayi maganar yaname hararanta ita dai "shuru tayi tana kallonsa da alama tana nazarin abinda yake fada ne. Can kuma tamkar maganar ta kufto mata tace wai sannu yajiki, ido yazaro tareda fadin innalillahi! ke lafiyarki kalau kuwa?....




still abinda yafada tasake maimaitawa shuru yai tareda tsura mata ido zuciyarsa tana wani irin halbawa, saboda yatuna abinda likita yafada kai ya girgiza cikin sanyin murya yace ya salam! shekenan abinda ake gudu ya afku tayi losing memory ta, cike da takaici yace ohhhh! God is another problem.






Still sake maimaita abinda yafada nakarshe tayi, cikin tsawan da har saida yasata tarazana tareda kame jikinta tana kallonsa cike da tsoronsa yayinda shikuma yawatsa mata harara yace ke! idan kikasake maimaita abinda nace saina fasa maki wannan d'an mitsitsin bakin naki mekama da gidan tsotsa kinaji ko?....




cikin turo baki tace gidan tsotsa kinaji ko?...kai yadafe tareda furta oh! my God if nabi tawannan yarinyar zararre zata maidani irinta.




"Sannan yaja tsaki mtsww! tareda sake hararanta yace to dalla gafara malama daina kallona haka nan da wannan idon naki me kama dana mujiya, batareda tabar kallon nasaba ya maida hankalinsa akan wayarsa dayake dannawa dai-dai lokacin aka kira sallar magrib, daina dannan wayar yayi yafara bin kiran sallar har aka gama yai addu'a yashafa, itama *TASLEEM* tashafa hannuwanta akan fuskarta tayi kamar yanda taga yayi, kasan cewar duk tana kallon abinda yakeyi especially bakinsa dataga yanata motsawa.




"Bayan yagama ne sannan yamike yana kallonta yace ga abinci can acikin kula idan kinga dama ki dauka kici kafin *Mamma* tazo, bin inda yanuna mata tayida kallo batareda ta fahimci abinda yafada ba sannnan tadawo da kallonta kanshi, shima din ita yake kallo kafin yace af aina manta da mai mantau nake magana kilama kinmanta da wani abu wai shi abinci ko?...




Tsaki yaja mitwss! sannan yace oho! maki ke kika sani dan haka sai kijira *Mamma* tazo ta tunatar dake domin nikam banida wannan lokacin, yanajin tasake tamaimaita abinda yafada nakarshe yatabe baki tareda cewa tabdijam lallai! aiki yakamaki dan haka sai kiyi tayi nikam kinga tafiyata yafadi tareda nufar hanyar fita.




"Aiko *TASLEEM* tamike zumbur tabi bayansa cikin tafiyarta me cike da natsuwa, kasan cewar kafarta babu takalmi dan haka kokad'an baiji motsinta ba yayinda shima cikin nitsuwa yake tafiya me cike da izzada isa irin ta cikakkun lafiyyayun maza, yayinda take cigaba da biye dashi abaya ba tareda yasaniba ahankali take tafiya tamkar zata fad'i kasa, da alamar jirine yake dibarta narashin karfin jikin da batadashi amma ahakanan take binshi abaya tamkar mahaukaciya.




Kasan cewar gashin kanta duk yazubo abayanta da kafadarta gashi dayawa da tsawo gata sanye da rigar marasa lafiya wacce ta tsaya iya guiwanta, tabbas idan wani yaganta Kallon daya zayai mata amma sai yarantse da Allah mahaukaciyace sabon kama, shikam *TAUFIQ* tafiyarta kawai yake baima sanan tana binshiba asalima sauri yafarayi dan yaji har anfara fadi adai-daita sahu.




Dai-dai lokacin dazaya fito daga cikin wani koridon dazaya sada shi da masallacin, yaji wani nurse yace a ah! yallabai ina kuma zakaje da mara lafiyan naku alhalin ba'a sallameta ba eye?...da sauri *TAUFIQ* yajuya yakalleta fuska hade cikin tsawa yace ke! lafiya bakida hankaline dazaki biyoni zuwa masallaci eye?....,




kuka tafashe dashi taname bata fusta tareda yarfe hannunta daya yayinda take yamutsa cikinta da dayan hannunta, da alama yinwa takeji baki yatabe tareda cewa oh! lallai wai kukama zakiyi?...sai kuma yakalli wannan nurse din yace kai! dan Allah maida ita room dinta ni sallah zanyi kaji?...




yace ok tareda kokarin kama hannunta, amma sai taki yarda juyin duniya nurse yakamata takiyarda ita dai adole sai tabi *TAUFIQ*, wanda gaba daya takaicinta yacika masa ciki musamman dayaji har antayar da sallah, cikin masifa yace ke! wai ni dan gidanku ne dazaki nace sai kin bini har masallaci halan haka kikaga anayin agarinku eye?...ita dai kam sai kuka takeyi tana mika masa hannunta alamar yakamata sutafi tare yayinda yaketa aikin masifa da hararanta.




"Ana cikin wannan takaddamar da'ita saiga direba yakawo *Mamma* amota bayan yai fakin sannan yabude mata tafito, *TAUFIQ* naganin fitowarta da sauri yakarasa gurinta yace yauwa thank God *Mamma* kin iso dan Allah kirike wannan "yarinyar taki zanje nayi sallah ne amma taki barina wai sai tabini saboda ita din mahaukaciyace,




ita kam *Mamma* tsabar farin cikin ganin *TASLEEM* tafarfado har gata tsaye akan kafafunta yasa ko bin takan *TAUFIQ* din batayiba balle taji abinda yafada, asalima tagefen shi tabi tanufi gurin *TASLEEM* din wacce ke biyeda shi abaya, da sauri tariketa cike da matsananciyar mamaki tace ikon ALLAH *TASLEEM* kece nake gani tsaye da kafafunki?....,




yayinda ita ko Kallon *Mamman* batayi sai kallon *TAUFIQ* takeyi tana sharan kwalla tareda tamika mashi hannu take, shiko baki da hanci yasaki yana kallon *Mammansa* wacce yaga ko kallonsa batayi gaba daya hankalinta yana kan *TASLEEM*, sai taba jikinta takeyi cikin tsananin farin cikin dayakasa boyuwa akan fuskarta, nata fadin alhamdulillahi!.




*TAUFIQ* kam ganin hakan da *Mamma* tayi masa yasashi sake jin mugun bacin rai sosai, domin kuwa wannan ne karo nafarko arayuwarsa da *Mammansa* tanuna halin ko'in kula akansa, kuma duk saboda wannan banzan yarinyar?...aiko take yaji tsanar *TASLEEM* din yakara d'arsuwa aransa, hakan ne yasa batareda yasake cewa komai ba yajuya zuwa masallacin da sauri *Mamman* tace danlele shine *TASLEEM* tafarka amma baka kirani kasanar dani ba.




"Batareda yajuya yakelleta ba rai bace yace kiyi hakuri, bata" dade da farkawa ba dama nabari sai nadawo daga sallah ne zan kira nafada maki ta farfado, tace Allah sarki to badamuwa katafi sallan gashi canma har anfara sai kadawo hakanan yasakai yawuce yanajin ransa ba dadi.




Yayinda *Mamman* cike da matsananciyar farin ciki tamaida kallonta kan *TASLEEM* tace sannun *TASLEEMA* yajikin?...batace komai ba saidai bin bayan *TAUFIQ* datayi dakallo still tana sake mika masa hannunta alamar dai yatafi da'ita masallacin, dariya *Mamma* tayi batareda tagane manufar *TASLEEM* dinba tadai ja hannunta suka nufi room din datake.




_Bayan wasu awanni_


********


Saida *TAUFIQ* yai sallar isha'i sannan yadauki hanyar koma dakin danufin ya sallami *Mamma* yatafi gida, fuska hade yashiga tareda sallama inda ya'iske likita tsaye agaban gadon *TASLEEM*, yana dora wasu magunguna da yashigo dasu akan table din dake gefen gadon yayinda ita kuma take zaune atsakiyar gadon, saidai ta dunkule jikinta guri daya inda ta tura kanta tsakanin cinyoyinta akan gado tana shasshekan kuka. yayinda *Mamma* take can zaune gefe akan kujera sai aikin kuka take me cike da damuwa.



Da matukar sauri yakarasa gurinta jikinsa har yana rawa yace *Mamma* meye kuma yafaru kike kuka haka eye?....cikin kuka tace danlele meyema be farubama eye?...kalli *TASLEEM*, fuska hade yace *Mamma* naganta ai tun dazu tafarfado dama aishine matsalar ko?....tace "eh, yace to *Mamma* bashikenan ba amma *Mamma* saiki zauna kinata kuka alhalin kinsan banasan kukanki ko?..




tace humm! danlele nasani amma to yazanyi?...yanzu fa kaduba kagani tunda muka shigo sai kuka *TASLEEM* takeyi nakira likita gashinan yadubata inda yake tambayarta yanzu meyake yimata ciwo sai itama tafadin abinda yafada, saida yai mata tambaye har uku kuma duk irin abinda yafada take sake fada shine na tambayesa meyasa "take haka?...




sai yace mun aidama yafada mana cewa dakyar idan bata manta komaiba to sai kuma gashi tamanta din yanzu fa har dakanta duk tamanta, shin danlele wannan wani irin masifa ne ace mutum kanshima yamant to badole hankalina yatashi nayi kuka ba?...cikin rashin jin dadin damuwar datake ciki yace *Mamma* "to kiyi hakuri kiyita" mata addu'a kamar yanda kikai tayi har Allah yasa tafarfado yanzuma hakan zakiyi in sha Allah zata samu sauki kinji?...




cikin sanyi murya tace to shikenan ni babu abinda yafi damuna yakesa kake ganin ina yawanyin kuka wallahi sai irin rashin sanin unguwarsu da gidansu, balle naje nafadawa iyayanta" halin datake ciki wanda nasan yanzu haka suna chan cikin tashin hankalin rashin "yarsu", cikin kwantar da hankali yace ki kwantar da hankalinki in sha Allah zataji sauki nan bada dadewa ba takoma gidan iyayanta kinji?...tace to Allah yasa hakan yace ameen.




"Murmshi likit lamir yayi tareda da tafawa yace kai! madallah yallabai ka kyauta dakai nasaran lallashi hajiya, domin nikam tund'azu naketa faman lallashinta amma bata sauraran ba sai dakazo yanzu tayi shuru, lallai masha'allah alhamdulillahi da karfin soyayyar dake tsakanin 'DA da UWA, murmushi *Mamma* tayi cike da jin nauyin likitan domin kuwa babu wai abinda yafada, yayinda shima *TAUFIQ* murmshin yai.




Sannan likitan yace yauwa to yanzu kuma sai aba mara lafiya abinci taci domin dai wannan rigimar datakeyi har da yinwa takeji, da sauri *Mamma* tace to tareda mikewa tanufi gurin kulolin abinci har tabude wata kula me dauke da farfesun kaji, sai likita yace afara bata ruwan tia me zafiyi yai kauri sosai sannan abata abinci tace to.






Bayan ta hada mata sai taje kusa da'ita cikin kwantar da murya tafara kiran sunanta saidai, bata amsaba sannan bata dago daga dunkulan datake ba cikin murmshin likita yace hajiya aiki nefa sabo domin kuwa hatta da sunanta tamanta,




kinsan yanzu takoma tamkar jaririya sabuwar haihuwa, dan haka komai yanzu bazata iyayi dakanta ba domin duk tamanta sai dole ankoya mata cike da mamaki me hadeda tashin hankalin *Mamma* tace subhanallahi! mun boni, likita komai fa kace sai ankoya mata?...kenan harda cin abincin yace tabbsa hajiya karki manta wanda yamanta kanshi to meye bazaya manta ba?...




kai *Mamma* ta gyada cikin sanyin jiki ta tabata
tareda fadin sunanta da sauri ta dago kai! takalli *Mamman* wacce takema kallon rashin sani
tana ganin *TAUFIQ* tsaye, tayi saurin saukowa daga kan gadon jikinta har yana rawa sauran kad'an tafadi likita yai sauri riketa amma sai ta fisge,




tanufi gurin *TAUFIQ* wanda yahade giran sama Dana kasa yadaure fuska sosai wanda har saida tasha jinin jikinta, amma dai hakan ta tsaya tana kallonsa yayinda shikuma yadauke kainsa likita yai murmshin tareda karban tia din dake *Mamma*, wacce jikinta yai sanyi sosai tayi shuru tana kallon *TASLEEM* cike da tausayin halinda ta tsinci kanta.




"Cikin nutsuwa likita yakarasa gurinsu" cikin kwantar da murya yace yallabai gashi kabata abaki tasha, cikin mugun sauri yajuyo yaima likita wani irin mugun kallo me cike da bacin rai da tsantsar masifa yace.....








~Pls Kuyi hakuri da jina shuru wlh cikina yaketa ciwo shiyasa, har nafara typing sai na ajiye~






Muje dai zuwa






_Ya ALLAH yasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu_
[8/10, 8:45 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️

🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login