Showing 18001 words to 21000 words out of 48594 words

Chapter 7 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

zakai mamaki akananun shekarunsa dayake gudanar da wayan nan harkoki, alokaci daya tunda alokacin duk bai wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba, amma idan kaga yanda yake tafiyar da al'amuransa sai karantse d'an shekara talatin ne.


"Sannan ahakan kuma yake d'an kulawa da kamfaninsu na minna, saidai ba sosai ba saboda wanda yake manager kamfani, amintattace daddysa ne kuma yanada kirki da rikon amana sosai, dan haka yana kulada komai cikin amanar da aka damkamasa amma ahakan yabukaci *TAUFIQ* din daringa zuwa yana ganin abunbuwan dake gudana acikin kamfani shiyasama yake zuwa.


Hakan kamfanin kwantagora shima akwai wayanda ke kuladasu, suma amintattun daddysa kasan cewa lokacin da daddysa yakeda rai mutum ne shi me matukar kyautatawa ga mutane, hakan yasa yakeda mutane kirki.


"Ahaka *TAUFIQ* yacigaba karatunsa da gudanar da kasuwancinsa, batareda neman *Mommasa* ba kasan cewa tun lokacin data rabu dashi da daddysa yake fushi da'ita, kasan cewar yana matukar kaunar daddysa tareda tayasa kishin mijin da *Momman*,wanda bai ta'ba ganinsa ba amma yanajin haushinsa tareda mugun kishinsa.


Yayinda fushinsa da kishinsa yakaru lokacin da *Momman* tazo gaisuwar rasuwar *daddysa, ta goyon su twins wayanda tunda yakallesu bai sake bita kansuba saboda mugun haushin ubansu, dayakeji har *Momman* tagama jinyarsa ta wuce saidai kuma duk da haushinta dayakeji babu abinda yarage,


daga kaunar dayake mata acikin zuciyarsa wacce take tsakanin d'a da uwa domin kuwa tun ranan data Barsu babu ranan dazaya wayi gari baiyi tunanin taba da tunanin wani halin take ciki, har bayan zuwanta da komawarta saidai kawai yana basarwa ne amma *Mommasa* tanan kwance acikin ransa.


*******
"Aban garanta *Momma* kuwa lokacin bayan komawanta kano da wata biyu mijinta dayaita fama da matsananciyar jinya yarasu,wanda hakan bakaramin tayarmata da hankali yaiba nayanda yabarta da kananan marayu, hakan tafara takaba wanda watan d'aya da farawa sai ga mummunan labari ya isketa cewa *TAUFIQ* dinta yamutu.


Aiko tayanke jiki tafadi wanda tundaga ranan take fama da matsanaciyar rashin lafiya ga gowonsu twins, wanda alokacin basufi wata biyar ba da haihuwa ba haka nan abokiyar zamanta taketa kulawa "da'ita da yaran, kasan cewar suna zaman lafiya harsuka gama takabar.


"To kuma ance arai dangin gorone yana bukatar hutu" dan haka tuni tafara gajiyawa, da jinyar *Momman*, inda bayan anraba masu d'an gadon da mijinsu yabari wanda bai wani taka kara yakaryaba, sai tafara tunani fad'awa yan'uwanta kasan cewar *Momman* tace kar afad'ama su gudun tashin hankalikasu, musamman mahaifiyarta wacce takasace itakad'ai tarage mata sannan alokakin tasufa sosai.


to amma dataga ciwan babu sauki wanda harda rashin isassa magani ne yasa tayanke shawar fad'a masu.


"Wanda ana cikin hakan ne sai *TAUFIQ* yai mummunan mafarki da *Momm* tana cikin wani hali, hakan ne yasa yaje gidan kakaninsa dake unguwar yamma wanda rabonsa dazuwa tun bayanda *Momma* tawuce, kasan cewar ko daya dawo bai jeba kasan cewar harda su yanajin haushinsu, tunda alokacin gani yake sune suka sata tabarsu shida daddysa taje tayi aure kanon.


"Dan hakan ko da yadawo basuji labari ba balle suji ashe yanada rai bai mutuba kamar yanda akafad'a, shiyasa lokacin dayaje suka ganshin sunsha mamaki bayan yasanar dasu komai da yafaru dashi, inda suka jajanta masa tareda fad'amasa cewa mijin *Mommasa* yarasu, duk da yanajin haushin mutumin hakan bai hanasa jin mutuwarsa ba.


Nan yace masu yanaso yaje kano dan haka yabukacisu bashi adireshin, bayan sun bashi aranan yashirya sai kano wanda ajirgi yaje kasan cewa tun daddysa yanada rai yakware gurin hawa jirgi, kod'aya isa kano baisha wahala gurin gane unguwarba tadalilin adireshin da aka bashi, alokacin dayaga halin da *Mommasa* da kannasa suke ciki kuka yakamayi sosai cikin tsanani tausayinsu, inda washegari yakwasosu suka dawo kwantagora.




********
Alokacin da suka iso yakira direbansa yadaukesu kai tsaye asibiti yace yaisu, inda aka karbisu cikin lokaci kankanin akafara basu kulawa, musamman *Mommasa* datake cikin matsananci hali.


Aiko sai gashi cikin sati biyu *Momman* tafara samun sauki sosai, saboda kyakkwan kulawa datake samu daga gurin likitoci tareda taimakon d'anta *TAUFIQ*, wanda dakanshi yai jinyarta inda gaba daya ya'ajiye komai na tsawon wani lokaci yake kulada da'ita, ta hanyar yimata duk wani abin da marar lafiya yake bukata haka nan twins dinta duk shiyake kuladasu, yayinda suka walwale daga yamushewar dasukai wanda rashin isassa abinci ne yasasu yin haka, kasan cewar tunda *Momman* batada lafiya suka daina shan nono.


"Dan haka ne yake basu madara sukai bulbul abinsu, ahaka dai yai tajinyar *Momman* tareda kulawa da twins din kannansa, wayan da tin lokacin da yaga halinda suke ciki na rashin uba yaji so da kaunarsu me tsanani tashiga zuciyarsa, hakan yasa ke basu kulawa ta musamman har dai *Momman* taji sauki aka sallameta suka koma gidansa, inda suma twins suka murje abinsu inda sukai mugun sabo dashi.


Tuni yakoma harkokisa ahaka rayuwa tamika cikin kwanciya hankali suke rayuwarsu gwanin sha'awa, gashi ga *Mommansa* da twins din kannansa dayake matukar kauna had'eda tausayinsu, shekaru sukaja yafara zama cikakkan mutum alokacin yafarajin wani mugun feeling yanada damunsa, wanda hakan yasa yagane cewa shid'in mutum ne me matukar sha'awa ne, saidai kuma Allah yayisa damugun tsamar ZINA.


Wanda ko bayan hakan idan yatuna cewa ZINA fa bashice duk wanda yaci bashinta sai yabiya, tahanyar idan ka aikata da yar "wani ko matar wani" ko "kanwar wani" to babu makawa, sai an aikata hakan danasa dan haka ko sai d'aya bai ta'ba aikatawa ba, domin yasan idan har yayita to ba makawa sai anyi da kannansa, su Hussy wayanda alokacin tuni sun girma har ansasu makaranta.


"Shikuma ayanda yake masifar kaunarsu" da tausayinsu baya fatan aketa masu mutuncisu, dan haka saidai kawai yana rage zafi ta hanyar neman yammata yayi romance dasu yabiyasu, yayinda kosu" yammatan sai wacce ta amsa sunanta sannan yake romance din dasu, wanda kuma duk abokinsa *T J* ne yake samo mashisu kasan cewar dama shine yabashi shawar yaringa romance din dasu, tunda yace" bazaya ta'ba shiga daga ciki ba. Saidai shikam *T J* sosai yake shiga cikin yai sha'aninsa dasu, domin shikam yace bazaya iya wannan d'and'ani haukaciba gara yashiga honey pot din nan, yasha dad'in marar musaltuwa.


Yayinda *TAUFIQ* yakance masa hum aiko watarana zakayi nadama marar musaltuwa, saidai yayi dariya kawai domin bayada wani cikakken sani akan addinisa, sabanin *TAUFIQ* wanda shikam sosai yakeda sani akan addinisa yana kuma aiki dashi hakan ne yasa yake nunama *T J* illar sake cikin ZINA amma baya dauka, achan gurin nemo mashi yammatan me yasamo masa Line wacce dukkan cikin Yammatan dayake hulda dasu babu kamarta, domin tanada tsafta sosai tana kumayi mashi yanda yakeso gashi tana d'aura jigida wanda yana d'aya daga cikin abinda yake daukar hankalisa, kasan cewar yana masifar kaunar yaga jigida a'kugun mace.


"Sun fara samun matsala ne da'ita" tin lokacin da tanuna tanason sai yayi sex da'ita, shikuma yace mata a ah bayada ra'ayin hakan ga kowace mace saidai matarsa ta sunna.


Ahakan dai yacigaba da harkokinsa wayanda suke ta tafiya yanda yakamata, har yakammala karatunsa cike da nasara, inda yafiko cikakken *DSS* wato dan sandan ciki kamar yanda yaci buri wanda batareda 'bata lokaci ba yasamu aiki, yayinda cikin lokaci kankanin yaifice yai suna sosai kwarewa akan aikinsa, saboda yanada wani irin kwarjini da haiba wanda hakan ajininsa yake,domin kuwa duk wani me laifin da yagagara kamawa musamman wayanda suka zamo tantiran criminals, tuni *TAUFIQ* yake kamosu cikin sauki aimasu hukunci dai-dai da laifinsu dasu aikata.


Hakan yasa yaketa samun nasarori had'eda cigaba arayuwa tako'ina, saboda tsananin addu'o'en dayake shadaga *Mommansa* da twins din kannansa, wayanda yawadatasu da dukkan abubuwan jin dad'in duniya, yayinda suma mutane keyi masa addu'a kasan cewar suna matukar kaunarsa, saboda tsananin tausayinsu dayake had'eda tai makonsu musamman marayu, wayan da suka kasance "mutanansa domin sosai yake tausayin marayu wanda hakan ne yahaifar masa da matsananci kaunarsu" azucin zuciyarsa, har da fundition yaimasu na zallar tai makonsu.


"Saidai zuciyarsa tanan cike da tsanar talakawa da alama abinda matar daddysa da yan'uwansa sukai masa bai fita daga ransa ba, alokacin tuni yazama shahararran matashin me kudi,wanda sunansa yafantsama aduniya bayan dukiyar da daddysa yabar masashima yamallaki tasa, yanada gidaje da kamfanoni agaruruwa da dama,


musamman kasarsa kwantagora kasan cewar tuni wannan kamfanin dake nan kwantagora yashara sosai, saidai yafizama agarin abuja kasan cewar acan aikinsa yake yayinda yafi maida hankalinsa akan, hukunta 'ya'yan "wasu masu hannun da shunin dasuke kama 'ya'yan mutane sunayi masu fyad'en.


"Amma ba'a d'aukan mataki me karfi akansu wasuma sai kaga idan ankai maganar kotu sai aikutun kutun amaida laifin akan yaran da'akai masu fyad'en, daga karshema sai kaga anshare da shari'ar aki bi masu hakkinsu musamman wayanda suka kasance marayu basuda me tsaya masu sai Allah.


Dan haka shike yatsaya masu da taimakon Allah da addu'o'en *Mommansa* data bayin Allah, yake kwato masu hakkkinsu cikin ruwan sanyi, yanzu haka daga Bauchi yafito watansa uku acan kasan cewa yaje kama wani tantirin yaro inda kuma yakamoshi, yanzu haka anyanke masa hukunci dai-dai da laifin da ya'aikata.


Yayinda yanzu kuma yazo aikin ne akan wani tantirin yaro dayaima wata marainiyar Allah fyad'e, kasan cewar aikinsa kenan yima yaran muta ne fyad'e musamman yake zuwa gari-gari yake yaudarian yammata, ta hanyar yin soyayya dasu daga baya sai yanuna yanason yin sex dasu idan suka ki amincewa sai yimasu fyad'e,


takarfi wasu har mutuwa sukeyi amma ankasa hukunta shi akan hakan kasan cewar "babansa me kudine sosai anajeriya, yayinda shikuma *TAUFIQ* yad'auki alwashin sai yane moshi anhukunta shi, inda yaji labari yana nan agarin kwantagora, dan hakan nema yazo caf karsa aha wannan kenan.




*Cigaban labari.........*




Muje zuwa yanzu za'a fara wasan


*MEENAL OR LUFHAT*


_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️


🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page 1️⃣4️⃣-1️⃣5️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,


sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.


_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.


✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


"""""""" *TAUFIQ* yana kokarin hawa bene sai ga *T J* yafito da sauri daure da towel a'kugunsa, cikin d'aga murya yace haba mutumina yanzu saboda Allah "koran Linan kayi akan d'an sex din dazakai da'ita" wanda bai wuce mintin shabiyar ba kunyi gama, amma shi zaka kiya yanzu kayi mata adalci kenan?...yakarasa fadi dai-dai lokacin da yakarasa gurinsa.


"Yayinda *TAUFIQ* din yajuyo da sauri fuska had'e yawatsa masa harara, kafin cikin masifa yace "eh banyi mata" adalcin ba kuma bazanyi sex din ba, tunda ba dole bane sannan dakake cewa abinda bai wuce mintin shabiyar ba angama, to kasani acikin minti shabiyar din nan zaka iya had'uwa da masifa da bala'in natsawon shekara shabiyar.


Yace hum! haka nan kusan kullum kake fadi, amma nidai banga alamar hakan ba yace ina zaka gani tunda kwakwalwarka tariga tatoshe gurin aikata kazanta, dariya yai cikin basar da maganar yace nidai banji dadin hakan dakai mun ba kasan mutane masu yawane fa "na'iske suna layin jiranta dan suyi sex din nan da'ita, amma takiya tazo gurinka shine kakoreta saboda Allah ka kyauta kenan?...


fuska daure yasake watsa masa harara sannan yace kaico! harda layi ake "mata saboda itad'in karyace ko?...., kace ma koranta danayi yayi dai-dai domin nibazan iya cigaba da hulda da karyaba.


"Fuska had'e yace karya kuma kamar yafa?...hassale yace kamar yanda ita ce mazan karnuka sukeyima layi suna sex da ita, kaga tunda "itama anai mata layi ayi sex da'ita to kenan itama karyace ko?.., yace hum! gaskiya *TAFIDA* kai! mugun d'an walakaci wlh, da sauri yace masa gidanku nasa akasu d'an raini hankali kawai.


"Dariyace ta kufce *T J* inda yashiga yi sosai harda rike ciki, yayinda *TAUFIQ* yaketa hararansa saida yai me isarsa sannan yatsaya, yace wato karewar walakaci kenan shine kasa gidan mu akasuwa ko?... fuska daure yace Oho!, yace hum! to ai shikenan idan kasiyar sai nadawo gidan ka na tare nayita cin karena babu babbaka, yakarasa fad'i tareda kashe masa ido d'aya cike dai da zolaya.


Yayinda shikuma sai aikin banka masa hararar yake tareda yajan tsaki sannan yace kaidai kasani d'an iska kawai, cikin zolaya yasake cewa abokin d'an guguwa ba, da sauri yakai masa wani uban naushi cike da bacin rai yace *T J* bafanason iskanci kaji ko?...da sauri yakwauce yana dariyar shakiyanci yace ah! yallabai karka 'batamun fuska kasuwata yarage gurin yammata, sannan kai kama isa kace bakason iskanci alhakin kana abokin d'an iska, ko ba haka kirani yanzu ba?...Cike da takaicinsa yace banza kawai bunsuru, domin tuni yasaba da iskancin *T J*.


"Yayinda shikuma cikin dariyar zolaya yace na daiji, ni mamaki kake bani wai yanzu Linance ka kirada karya har kana koranta saboda kagama cin moriyar ganga ko?...yace "eh din nima basai akoreni ba, yace ah! a ah wanene ya'isa yakoreka kaida gidanka,


tsakin yaja mtsw! ba tareda yasake cewa komai ba hakan yasa yajuya yashige d'akin yana dariya da fadin mu kwana lafiya tazuru, da karfi yace masa banza tazurai dai bakin yace sannan yahaye sama yana me jin mugun haushin *T J* aransa.


**********
Ko daya ahau saman kai tsaye bedroom dinshi yashige, bai kwanta ba kamar yanda yacema *Mommansa* zayai.


"Jakar laptop dinsa yad'auko tareda jawo d'an karamin kujeran dake gaban mirron, ya'jiye agaban gadon sannan yazauna gefen gadon tareda fito da laptop din yad'ora ta akan kujeran, sannan yakunna inda wani kyakkawan hotonsu yabayyana shida *Mommansa* da su Hussy suna dariya sunyi matukar kyau.


"Cikin natsuwa ya fara gudanar da'aikin dayazayai",wanda yad'auki tsawon awa uku yanayi kafin yagama yarufe laptop din tareda "mikewa da'ita rike ahannu yaje yajonata ajikin chaji".


Sannan yai wata irin mi'ka, wacce kallon d'aya zakai mashi kagane bayan gajiyar dake tareda shi akwai wani abinda yake matukar bukata, bayan yagama salatin mikar dayai sannan yakoma yazauna agefen gadon tareda yin baya yakwanta akan gadon, kenan yai rigingine.


sannan ahankali yakalli agogon dayake manne jikin bangon d'akin, inda yanuna mashi karfe d'aya nadare da minti goma "Kyakkawan idoshi yalumshe masu cike da tsanani gajiya had'eda mugun feeling din da yakeji, ahankali yakai hannunsa kan joystick sa wanda take nuna masa tana matukar bukatar abincita, message dinta yafarayi ahankali ahankali da alama yanajin dad'in abinda yakeyi still idonsa lumshe.


"Chan kuma sai yabud'e idonsa da sauri wayan da tuni har sun fara rikid'ewa daga fari zuwa ja, tareda cire hannun nashi daga kan joystick dinsa cikin masifar sauri ya yarfe hannunsa taukar yata'ba wuta yayinda jikinsa da basinsa suka yad'auki rawa.


Inda da sauri yashiga furta astagafullah! astagafullah!! astagafullah!!!.Oh! Allah natuba kayafe mun, sai kuma yatura hannusa duk biyu cikin lallausan suman kanshi yana yamutsawa, sosai yaji wani irin bacin rai yana ziyartar zuciyar har zuwa gaggar jikinsa.


sai kuma ya lumshe ido tsawon lokaci yana sauke ajiyar zuciya, tamkar wanda yaci kuka yakoshi sai kuma yabud'e idonsa ahankali sannan cikin tsananin sanyin muryar, yafurta yah! robbi kasan har cikin zuciyata bazan iya aikata ZINA ba, hakan ne yasa nake aikata wasu abubuwan wanda nasan basuda kyau shiyasa nake rokonka kayafe mun, sannan ka taimake ni narage jin wannan muguwar sha'awar.


"Wacce kullum me makon taragu amma sai karuwa takeyi, shin yah! Allah me zanyi ne dan sha'awar nan tawa tarage ne eye?....take yaji zuciyarsa tabashi amsa da cewa kayi aure idan har kayi aure komai zaya rage sosai, kai ya gyad'a alamar gamsuwa da amsar da zuciyarsa tabashi, sai kuma wata zuciyarsa tace" humm to kai wazaka aura tunda ko budurwa baka dashi eye?... jikinsa ne yai sanyin.


Ahankali yamike tareda shiga to toilet ya dan dade kad'an da alama wanka yai, saboda karan zuban ruwa sannan yafito still sanye da wannan rigar barcin jikinsa da laimar ruwa da alama yadauro alwa ne, wedrof yabude ya dauko watafarar jallabiya me dogon hannu yaje gaban mirron yad'auki turare yafesa, sannan yashinfid'a abun sallah yafara cikin nutsuwa yatada kabbara inda yafara gabatar da lafilfili.


*******
*TAUFIQ* kenan zuciyarsa me kyauce kwarai da gaske wacce ke cike da tausayin "marayu sosai, wanda da alama hakan ajininsa yake domin kuwa saboda tsabar tausayinsu" dayake, yasa ko karya akai "masa dasunansu yakanyi alkhairi me yawa zuwa garesu".


"Yayinda yakasance mutum me matukar riko da ibada tareda aikata ta aduk inda yake, ma'abocin raya dare kwarai da gaske musamman, idan yakasance cikin irin wannn yanayi sosai yake kaima ubangijinmu kukansa akan yayaye masa abinda yake damunsa,wanda sau dayawan lokacin yakanji yarage tahanyar yin kokarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login