Showing 3001 words to 6000 words out of 48594 words

Chapter 2 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin *TALAUCI* kaimana *ARZIKI* me albaraka, wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.


✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


""""""""""A a aaaaaaaaaha! Malama Allah yabaku hakuri "kuwuce sai "muwuce shikenan aiko?....cikin fad'a hade da jin mugun haushinsu" tace Oho! kuma Allah yabaku hakuri tunda mu *TALAKAWA* mun takura maku arayuwa, shidai sajan labaran bai sake cewa uffan ba sai ido da yaketa zarewa kamar an tsurashi yai karya, kasan cewar sosai lamarin yabashi tsoro.


Yayinda iyan ke bata hakuri domin taga ranta yabaci sosai, cikin sanyi murya tace iya bakomai yawuce ai, yauwa yar nan dan Allah kiringa daukar komai da sauki kinji?....tace to iya muje, tace to yar nan Allah yaimaki albarka ameen ta amsa suka fara takawa ahankali.


"Hakan yasa sajan labaran yakoma yashiga mota da sauri *TAUFIQ* din ya kalleshi cikin cold voice dinsa me cike da izza yace ya akai?....yana kokarin tayar da motar yace yallabai "gasu chan zasu wuce, tsaki yaja mtsw! tareda cewa dakarsu" wuce sugani idan bamubi takansu "mun wuce ba. dai lokacin da suka tsallaka titin sukuma suka wuce da gudu tamkar zasu tashi sama.


*******
Tace to iya Allah yakaddara mun tsallako lafiya "ina zakibi?...cike da jin dad'i iyar ta nuna mata hanya tareda cewa kinga hanyata nan yar nan", nagode Allah yaimaki albarka saidai kuma gashi har zamu rabu ban ga fuskarki ba, sannan bansan sunanki ba kuma yakamata nasani kodan saboda watara idan Allah yasake had'amu ko?...


kai ta gyad'a alamar "eh sannan tad'aga niqaf dinta, aikam take kyakkawar fara fuskarta ta bayyana wanda har saida iyan ta tsorata saboda itakam a iya tsawon rayuwarta, bata ta'ba ganin kyakkawar halitta irin wannan yarinyar ba.


"Kuri iyar tayima kyakkawar fuskarta ta, wacce ke dauke da dogon hanci tareda d'an karamin pink din bakinta me kyau da daukar hankali, cike da yabawa, takai hannunta akan kyakkawar fuskar yarinyar tashafa tareda sakin murmushi tace masha'allah'tabarakallah! 'yata ke kyakkawace.


"Tabbas wannan shigar dakikai tayi matukar dacewa dake domin kyawunki yashahara sosai 'yata tayanda zaya iya haifar maki da matsala, to amma idan har kinayin addu'o'e neman tsari tareda wannan shigar to da izinin Allah babu wani abinda zaya same "ki.


"Dan haka iname umartarki" daki cigaba dayin addu'o'en tareda irin wannan shigar, domin sosai zaya kareki daga fad'awa hannun azzaluman mazan dake kaima yammata farmaki, har kiga sunyi yinkurin yimasu fyad'e idan suka samu sa'a sai kiga sunyi masun fyad'en wanda hakan kad'an ne da aikinsu", dan haka ki kula kinji ko?...'yata" cikin sanyi jiki tace to iya insha'allah zan cigaba dayi.


"Yauwa 'yata karki damu babu abinda zaya same ki" insha'allah, shin yasunanki ne?....kayataccan murmushi tasaki har saida fararan hakoranta da ushiryarta sama da kasa suka bayyana, wanda hakan yasake fito zallar tsantsan kyanta da Allah yaimata gawata yar lutsawa da ha'barta yayi hakan yasake kawata fuskarta sosai gwanin sha'awa.


"Ahankali tad'an d'aga giranta wanda ke barazanar had'ewa, sannan tajuya blue eyes dinta masu dauke da zara-zaran gashi masu matukar kyau da birgewa, sannan cikin rad'a danuna alamar kamar batason wani yaji tad'an du'ka dai-dai kunnan iyar sannan tace iyata sunana *TASLEEMA*, amma zaki iya cewa *TASLEEM* kawai.


murmushi iyan tayi tace masha'allah suna me dad'i to *Tasleem* nagode Allah ya albarkaci rayuwarki, yabaki miji nagari wanda zayasoki tamkar yanda uwa takeson *'DANTA* ya azurtaki da 'ya'yanda zasuyi maki biyya yasa kigama da duniya lafiya, cikin jin dad'i tace ameen iya nagode yauwa sannan idan "iyayanki suna raye Allah yakara masu" lafiya danisan kwana me albarka yasa kigama dasu lafiya, idan kuma sun rigamu gidan gaskiya to Allah yajikansu" da rahamasa yasasu" aljannar firdausi madauwamiya.


"Rungume iyan tayi cike da matsananci jin dad'in wayan nan kyawawan addu'o'en, tace ameen! ameen!! ameeeeeeen!!! Iyata nagode! nagode!!! sosai kema Allah yajika iyayanki ya albarkaci zuri'arki yasa kigama da duniya lafiya ameen yar albarka.


To iya sai anjima takarashe fad'i tareda sakin iyar sannan ta sauke niqaf dinta cike da farinciki, tabi ta gefenta tawuce zuciyarta cike da kaunar tsohuwar itama iyar tawuce taname jin kaunar *TASLEEM* din aranta.


*********
G R A first 2 sabuwar unguwace, wacce takasance dauke da "kayatattun gine-ginen zamani masu kyau da daukar hankali, a kofar wani tsararran gida me farin fenti da ruwan toka, wanda yake dauke da tabkeken get shima me ruwan toka da ratsin fari, anan ne motar farko ta tsaya inda sauran suma duk suka tsaya.


"Yayinda suka fara sakin wasu mahaukatan horn ajere cike da 'kaguwar azo abud'e masu get dinsu shiga, to amma shuru ba'azo anbud'en ba kamar yanda suka bukata, da alama megadin baya kusane dan haka sun kai wasu yan mintuna suna sakin horn.


"Kafin daga chan megadin cikin matukar hanzari yazo yabud'e masu", inda sukai tashiga cikin tafkeken harabar gidan wanda tun daga bakin get har zuwa guri fakin mota titine shin fid'e, yayinda sauran harabar gidan yake jere da intalos gefe-gefe kuma shukokin fulawoyi masu kyau da tsari.


Gidan yana dauke ne da kyawawan part guda biyu wanda yake ginin bene ne, sai wani d'an madaidaicin masallaci me matukar kyau achan gefe, yanda fanti waje yake haka na cikin gidan yake wato fari da ruwan toka harda masallanci shima irin fantin ne.


"Kai tsaye gurin fakin suka nufa sukai fakin, cikin sauri wani escos yafito daga cikin motar farko sanye da ash din suit da bakin glass fuskan tamkar baisan wani abu waishi dariya ba arayuwarsa, cikin sauri yaje yabud'ewa *TAUFIQ* kofa wanda saida yadauki yan second ni sannan yafito hannunsa dauke da wayoyinsa,


sai wata jaka daganin na laptop domin ga tambarita nan ajikinta, da sauri escos din yakarbi jakar harda wayoyinsa yayinda shikuma, cike da izza da takama yai tsaye yana shan kamshi chan yashaki iska yafurzar sannan fuska ba annuri gadan-gadan yanufi gurin megadi.


"Dai-dai lokacin da sauran escos din duk suka fito daga motoci" wayanda suma duk sanye suke da ash color suit, inda sukaje da sauri suka bud'ema wayanda suke cikin motocin nan uku kofofi, duk "suka firfito suma sanye" suke da suit saidai baki, kallo daya zakai masu kagane ba hausawa bane, dukkansu tsaye sukai suna kallon.


*TAUFIQ* wanda tuni ya isa gurin megadi sai faman masifa yake da "shi akan yaki zuwa yabude masu" get akan lokaci, yayinda me gadin yake tsugunne akasa sai aikin bashi hakuri yakeyi cike da girmamawa, yana sake fad'an dalilin dayasa shi zuwa da sauri wato yakewa bayine shiyasa be bud'e get din dawuri ba, "tsaki yaja mtsw! tareda furta matsalar talaka kenan duk yanda ka had'a aiki dashi" sai ranka ya'baci", sannan yawuce cike da izza inda escos dinda yake rike da tarkacesa tareda bakinsa dayazo dasu sukarufa masa baya su takwas ne cif mutanan.


"Inda suka nufi daya daga cikin part din nan biyu, kai tsaye suka shiga wani tabkeken kayataccan falo dayaji kayan zamani, wanda tsayawa fad'in abinda ke ciki bata lokacine infact dai falon yahad'u kwarai da gaske, musamman da'aka kawatashi da irin fantin nan me shaining shima fari ne da ash color, hakan labulaiyan da manya-manyan lumtsuma-lumtsuman kushins din duk ash colors ne, sai kamshin airfreshnan dana sanyin ac ne ke tashi acikin falon wanda sosai yaji komai na more rayuwar duniya.


"Bayan escot din ya ajiye kayan yafita yace" masu Pls have a site duk suka zauna tareda cemasa thanks! "kai ya gyad'a sannan shima ya zauna, nan suka fara tattaunawa cikin turanci inda na kula duk akan kasuwanci ne tsawon kamar minti shabiyar, sannan yatashi suma duk suka tashi hannun yabasu sukai musabiha, sannan cikin harshen turanci "yace nagode insha'allah gobe da safe" misalin karfe 9am zan iskeku ahotal din sai mukarasa tattaunawa ko?..


sukace "ok badamuwa suma sun gode sai Allah yakaimu, nan yarakosu" harabar gidan inda ya umarci escos dinsa guda hudu dasu rakasu escos din suka shiga motarsa daya, yayinda sukuma suka shiga motocin nan nasu guda uku suka tafi kaisu otal din wanda shine yakama masu, sannan shikuma yanufi d'an part din.


*******
"Aban garenan *TASLEEM* cikin natsuwarta take tafiya batareda tunanin ruwan yana iya saukowa ba akowani lokaci, zuciyarta babu sauran 'bacin rai akan abinda *TAUFIQ* da direbansa sukai masu, asalima jin ranta take fari kal saboda sosai taji dad'in addu'o'en da "iyarnan tayi mata".


Dan haka cike da farinciki take tasakin murmushi, dai-dai lokacin dazata shiga layin gidansu dake unguwar nasarawa alokacin ne kuma akasaki ruwa kamar da bakin kwarya, hakan yasa kowa yake gudun yakarasa gida amma banda *TASLEEM* wacce bata chanja ba daga tafiyar datake ahankali.


"Asalima cewa tayi alhamdulillahi! sun sauko Allah kasa agama lafiya, inasonku mutane na, ahaka dai take tafiya tana magana ita kad'an, wanda kafin kace me duk tajike sharkaf da ruwan ahaka har tashiga d'an madai-daicin gidansu, wanda yake ginin bulon amma kasan cewar anshefesa da suminti bazaka ta'ba cewa ginin bulon kasa bane.


"Bakinta dauke da sallama tashiga zauran inda hayaki yafara amsa mata sallamar ta", kafin mahaifiyarta dake tsugunne bakin murhu tana hura wutan ta amsa mata cike da kulawa, "tace sannu dawowa" yanzu saboda Allah *TASLEEMA* maimakon ki tsaya har ruwan nan yatsagaita sannan kitaho, amma sai kika 'kiya saboda "ke shiga ruwa bai da meki" ba shine kika shigo cikinsa face-face ko?...,


"Ahankali ta d'aga niqaf din wanda yaketa tsiyayar ruwa" murmushi dauke akan kyakkawar fuskarta, tace yauwa sannu *Innata* da aiki wutar taki kamawa ne ko?...
murmushi *Innan* tayi wacce suke mugun kamada *TASLEEM* din, sannan tace humm! *TASLEEMA* kenan yar *Innata* ainasan bazaki bani amsar tambayata ba, saboda indai za'ai magana akan shiga ruwa ne to sai ki kauce.


"Shin nikam dai wai menene had'inki" da shiga ruwa ne eyeee?.. yarinya sai kace yar ruwa, cikin dariya me had'eda da shagwa'ba tace kai! *Innata* sai kiyi tace mun wai kamar yar ruwa, kuma *Innata* kin fasan Aljanune ake kirada yan ruwa ta karashe cike da shagwa'ba.


Dariya tayi tace "eh nasani su" ake kirada yan ruwa, to amma ai dole nakirki hakanan tunda ko banza sud'in mutananki ne.


Cikin turo baki tace *Innata* mutane na kuma?...tace "eh idan ba haka ba to me had'inki da shiga ruwa ko dayaushe eye?.., tace *Innata* Allah nima dai ban saniba kawai dai nasan inason shiga ruwan sama arayuwata, tace to ai shikenan mun godema Allah madai da ruwan bayai maki komai, badan haka ba aida tamu tasame mu.


Cikin dariya tace kai *Innata* tace, to yanzu dai bara nacire kayan nazo na hura maki wutar, yanzu zakiga takama insha'allah takarashe fad'i tareda shiga cikin gidan.


"Wanda yake dauke da d'akuna biyu da yar karamar baranda", yayinda dan matsakaicin tsakar gidan yake shafe da siminti, "kwance niqaf din tayi" tareda cire hijab din inda take suranta yabayyana kai! masha'allah! agaskiya *TASLEEM* tanada tsari me kyau sosai.


Ta kasance kirar coca cola wacce malam bahaushe yake kira dame kirar kalangu, samanta cike yake da dukiyar fulani daga tsakiyarta atsuke yayinda kasanta yake abud'e, tanada manyan mazauna da hips sosai wanda katon hijab din data kesawa yake rufe wannan kayan alatun nata, masu daukar hankali me kallonta musamman cikakken lafiyayyan namiji.


*TASLEEM* kenan kyakkawace ta gaske kamar yanda iyarnan tafad'a haka ne, zataki shekarunta goma sha biyar zuwa sha shidda aduniya hankali taciro jakarta wanda Ita kad'aice bata jike ba ajikinta, kasan cewarta taleda irin wacce ake kira da wankan gefe wato swaga bag, ta ajiye gefe sannan ta cire kayan jikinta wanda doguwar riga ne na atamfar roba-roba ja, harda zuwa safar hannu da takafa, inda tarage daga Ita sai dogon shimi wanda yatsaya dai-dai guiwarta.


Bayan tagama cirewa saije tashanya akan igiyar dake daure atsakar gidan, sannan tad'anyi juyi acikin ruwa hakan yaba jelar bakin gashin kanta shima juyawa yame siyayar da ruwa, cike da farinciki ta d'aga kanta sama idonta rufe tareda bud'e hannunta, ruwan yana saukowa kan fuskarta zuwa kan kirjinta dayake cike da nashanu wanda suka sakeyi tantsan tantsan, saboda ruwan da sukasha har suwa kan shafaffan cikinta wanda yake kamar bata saka masa abinci, zuwa kan manya manyan hips dinta dasuma suka sha ruwa sukai luta-luta gwanin sha'awa lol.


"Takai kamar minti uku ahakan tana juyi sannan da sauri tace wayyo *Innata*, tana chan tana jirana na hura mata wuta tafad'i tareda shiga d'aki da gudu tana dariya, ga dukkan alama dakin yakasance natane, wanda kallo daya zakai mashi kagane hakan d'akin bawani tarkace yana shinfid'e da leda atsakar dakin,


sai yar karamar katifa dake yashe kasa wacce ke shinfid'e da zanin kago me kyau gefe wani d'an table ne, dake dauke da littafai nakaratu da rubutu sai chan gefen kuma abin sallah ne shinfid'e da yake dauke da qur'ani me girma, da wasu takardun sai wani d'an akwati da saman shi kuma wani bakko ne da alama dai kayan sawanta ne aciki.


tabakin kofar d'akin kuma takalmanta ne agere duk flat kala uku, da sauri taja zani dake rataye akofa ta daura tacire shimin da pant taje suma tashanya sannan tadawo, tabude bakkon nan taciro wata t-shirt ja da hula baka tareda wani pant tasa cikin sauri-sauri sannan tafita tanufi gurin *Innanta*.


********


"Aban garan *TAUFIQ* kuma dai-dai lokacin dayake kokarin shiga part din ne ruwa yasauko, hakan yasa shiyin gudu fuska dauke da annuri cikin turanci yace yin hakuri ruwa karka bigeni a gidan mu mana Oh!, sannan cike da shagwa'ba yafara kwala kiran my sweet *Momma* and darling twins am back tareda shiga kayataccan falon, wanda yaji komai na more rayuwa tamkar wance falon.


Saidai wannan yana dauke da manya-manyan hotuna sa dana wasu dattijai wanda ga dukka alama iyayanshi ne, domin kamanninsu danashi sun nuna hakan, sai kuma na wasu twins sisters kyawawa kallo daya zakai masu kagane kannansa ne saboda suma suna kama.


"Masu aiki ne kawai afalon sunata aikin" jera abinci, akan wani tabkeken dinning table me kyau dayake zagaye da kujeru kimanin guda takwas, da sauri suka zube kasa suna gaidashi fuska had'e ya amsa tareda tambayarsu ina *Momma* take?...Har zasu bashi amsa sai ga wata kyakkawar mata tafito wacce ko ba'a fad'a makaba mahaifiyarsace, tanada d'an tsawo dakiba amma ba irin me munun nan ba wanda dai yake tabbatar maka da cewa tsabar hutu da jin dad'i ne suka samu gurin zama ajikinta.


"Sanye takeda wani ratsa-tsan brown din less da ratsin fari me kyau wanda dagani kasan tsadadde, dinkin doguwar rigane irin bud'adan na wuyanta da kunnanta had'eda hannuwanta kuwa gwala-gwalai ne keta walwali, kanta yafeda farin mayafi wanda bata rufe wuyanta dashi ba hakan ne yabani damar ganin sarkan dake shinfid'e cikakken wuyanta, fuskarta dauke da annuri tace ganin nan *'Danlelena* barka da zuwa yace yauwa my sweet *Momma*.


Dai-dai lokacin da kyawawan yamatan nan najikin hoto suka fito,sanye suke cikin wata ratsatsiyar abaya ja wacce tafito da surar suta indomie generation, sai sukai roling mayafin abayan, sunyi kyau sosai duk ba zasu wuce shekaru goma sha biyar aduniya ba kallo d'aya zakai masu kasake tabbatarwa kanka sud'in ajebo girls ne, domin kuwa sosai jikinsu da fuskokinsu yanuna hakan dagudu suka nufeshi suka rungumeshi, cike da farincikin ganinsa sukace Oyoyo *Bros T* barka da dawowa we really miss suna sake rungumeshi tamkar zasu kayar dashi.




Cikin dariya yace wayyo *Momma* me kike ba twins dinki ne sukai karfi haka har zasu kayar dani?...,cike dariya tace hum! "eh fa lallai yan biyu komaima cisuke kamar tsutsotsi saidai fa basu dawani karfi dazasu iya kayar mun dakai, yace ayya *Momma* kallesu fa yanda sukai lukutaye da karfifa naji sun chakumeni liki kamar zasu kayar dani ko?...
cikin dariya sukace a ah *Bros T* bazamu yarda kai ba, kawai murnan ganinka ne because of munyi keyarka sosai Husscy tace "eh mana inji cewar Hasscy.


"Cike da kulawa had'e dajin tsananin kaunar kannan nasa, ya rungumesu" yana me cewa Allah sarki my lovely twins 6ters nima nayi miss naku sosai, to yakuke yakuma students?...sukace lafiya lau yace gud am happy to hear that, dai-dai lokacin da mahaifiyarsu ta karasu gurinsu fuskarta dauke da annuri.


Sakinsu yayi yanufi gurinta cike da kewarta yana kokarin rungumeta tayi saurin dakatar dashi, ta hanyar d'aga masa hannu fuska had'e tace karka kuskura ka matso gurina ido yazaro, cike da tsoro yayinda yaji zuciyarsa yai wani irin mugun bugawa, cikin rawar murya yace......


To yah! muje zuwa ne?


*Idan naji ruwan comments lallai bafashi zan cigaba da yardan me kowa da komai, idan kuma naga akacin hakan to fa kamar yanda nace zan ajiye alkalamina eheeee*


_ALLAH yakasa mu cika da imani ameen yahayyu yakayyu mu_
[8/10, 8:40 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️


🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)


_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page 5️⃣-6️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu, dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku.


Domin kuwa yana dauke ne da wata iriyar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*, sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda "Ita kuma duniya ba wanda ta tsana irin wannan mutumin ahaaaa! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..hmm! Akwai rikici had'eda chakwakiya is a very Romantic love story fa aha! akwai shanawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login