Showing 30001 words to 33000 words out of 48594 words
Chapter 11 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt
tareda turo baki tana sake yima *TAUFIQ* din kallon kasan ido, wanda tuni yabud'e idon yana kallonta kafin yamaida kallon akan *Momman* wacce cikin fad'a tace to ina amfanin hakan ace mutum bazayai hakuri akan d'an abu kad'an ba saboda Allah fa eye?...dai-dai lokacin da tasake cewa ga wayar kayi hakuri. "Tace to kaji sai kayi hakurin ka karbi wayarka da sauri yamaida kallonsa kan *TASLEEM* din, inda yai mata wani irin kallo wanda taga kamar nakeda Allah ne akan kazafin dakikai mun, aiko take taji gabanta yai wani irin mugun bugawa wanda hakan yasata saurin du'kar dakai cike da wani bala'in tsoro d'arsu ranta, gawani bala'in kwarjini da *TAUFIQ* din yaimata lokaci d'aya batareda yakarbi wayar daga hannunta ba yawuce rai bace,yanajin zuciyarsa tamkar zata faso tafito waje dan bakin cikin abinda wannan yarinyar tayi masa wanda hakan yasake ba *TASLEEM* din wani irin mugun tsoro, dan hakan ne tayi sauri kallon *Momma* wacce tabi bayansa da kallo cike da mamaki, tace wai nikam me hakane "d'anlele yakeyi daga jiya zuwa yau da anyi magana sai yawuce ya kyale mutane eye?...sai kuma taja tsaki mtsw! tareda cewa to Allah yasawake, sannan takalli *TASLEEM* din wacce take amugun tsoroce tace bani wayar nan kinji, idan yagama fushin yazo kar'bi abinshi tunda dani dake babu abinda zamuyi da wayarsa. Cikin sanyi jiki tamika mata murya asanyaye tace gashi hajiya dan Allah kisake bashi hakuri, murmushi tayi tareda cewa *TASLEEM* 'yata nace karki damu abinda nakeso dai dake shine dan Allah kiyi taka tsan-tsan dashi saboda zuciyarsa akusa take, sannan kiringa bashi girmanshin amatsayinsa na babba agareki kinji ko?...cikin sanyin jiki tace to hajiya insha'allah zan kiyaye, yauwa Allah yaimaki albarka saidai daga yau kidaina kirana hajiyar nan banaso, kiringa kirana *Momma* kamar yanda kikaji yanayi kinji ko?...cikin jin dad'i tace to, yauwa *TASLEEM* to muje ki cigaba da aikinki kinji ko?.., tace tareda shiga gaba Ita kuma *Momma* tabita abaya tanajin kaunar yarinyar har cikin ranta.
******
*TAUFIQ* kam koda yashiga babban falon tuni *T J* da bakin harsun fara cin abinci, saidai ko Kallon inda suke baiyi ba saboda bala'in bacin rai dayake ciki yanufi hanyar shiga karamin falon, da sauri *T J* yace a ah! *TRT* _kasan cewar haka yakan kirasa wani lokaci_ abincin fa?...batareda yatsayaba yace bana bukata, cike da mamaki yace baka bukata kamar yafa?...bai samu amsaba domin tuni har yashige karamin falon. Hakan yasa *T J* ajiye spoon tareda ture flat din abinci da sauri yamike yabishi, saidai ko kafin ya'isa tuni har yashige bedroom dinsa yasa key yakulle hakan yasa *T J* yin tsaye turus, tunda yaga hakan aransa yasan akwai matsala babba kuma yasan ahalin dayake cikin yanzu ko yace yabud'e masa kofar nan bazaya bud'e ba. Cike da mamakin hade da damuwar gani halin da aminin nasa yashiga yanzu nan yafurta to lafiya meke faruwa?...,wata zuciyace tace kaje ka tambayi *Momma* man tunda cikin gida yafito, har yajuya zaya fita sai kuma wata zuciyar tace a ah! kasani ko tsakaninsa da *Momman* ne kila kuma bai kamata kasani ba, kawai kabarshi har sai yahuce tukunna dan haka yakoma ya cigaba da cikin abincin inda har bakin ke tambaryarsa ina Sir *TAFIDA*?..yace masu zayai wani abune kadan amma yana nan zuwa sukace ok sannan suka cigaba da cin abincinsu.
Shikam *TAUFIQ* safa da marwa yakamayi atsakiyar d'akin cike da mugun bacin rai, yake naushi hannu d'aya cikin d'ayan hannun abayyane yafurta Oh! my God me zanyima yarinyar nan narama abinda tayimun ne?....,wata zuciya tace dashi ah! bacewa tayi kamaretaba?...yesss yaba kanshi amsa yauwa to kabari idan tazo gyara maka d'aki ka zazzabga mata kyawawan marukan, afuskan nan nata mekama data aljanu harsai yatsunka sun fito, da sauri yace a ah! ran *Momma* zaya sake 'baci fiyeda da kawai kasa adauke maka "ita akai maka gidanka na fadara lokus tayi tsawon sati biyu kana bata wahala, da sauri nanma yace a ah! *Momma* zata tuhume ni cike da mugun takaici yatura hannu cikin lallausan suman kanshi, tareda furzar da huci me zafi sannan yasake cewa to wai me zanyi mata nahuce abinda tayi mun eye?....shuru yayi tareda lumshe ido tsawon lokaci can kuma sai yasaki wani shu'umin murmushin tareda furta yesss nasamu abinda zanyi maki lallai yarinya zaki gane bakida wayo sannan yamike yafita tamkar bashiba yaje suka cigaba da cikin abincin dashi suna fira har suka gama suka fita.
*******
*TASLEEM* kam cikin sanyi jiki tashiga kicin dan gyarawa, saidai kuma takasayin hakan asalima tsaye tayi shuru tana tunanin abinda yafaru, wanda sosai taji ba dad'i abinda ta aikatawa *TAUFIQ* din musamman yanda taga ko kad'an *Momma* bata bashi gaskiya ba, gashi dai ita ce tayi masa laifi amma kuma shi *Momma* taima fad'a saboda yarda da'ita datayi. Take wata zuciya tace da'ita shin *TASLEEM* kenan yanzu wannan hanyar dakika dauka me bullewace?....karki manta ramin makaryaci kurarre ne, idan har kikacigaba dayin hakan watarana gaskiya zatayi halinta kinga daga ranan dukkan wata yarda da tabaki yazube, kafin hakanma shikan shi *TAUFIQ* idan har zaki cigaba dayi masa irin abubuwan, zaya kara tsanar dukkan wani talaka ne sannan ringa daukar 'ya'yan talakawa basuda tarbiyya, wanda kuma ba hala bane tunda ke karan kanki ba irin tarbiyya da iyayanki sukai maki ba kenan ko?...kai ta gyad'a alamar bakan amsa, dan haka tin wuri kibari idan baso kike yafara yimaki kallon marar kunya da tarbiya ba, take tafurta aitunima yafara tunda abinda nayi masa daga jiya zuwa yau aiko wanene dole yaimata kallon marar kunya da tarbiyya, dai-dai lokacin da wasu hawayen nadamar abinda tayi suka zubo mata, cikin sanyin murya tace insha'allahu bazan sakeyin abinda zayasa yaimun Kallon marar tarbiyya ba saidai ko cikin kuskure, ko dan yardan da mahaifinsa tayi mun dan haka daga yau bani "bashi sai idan yashiga sabgata tabbas zan shiga tasa, tunda yatsani talaka nima natsane shi eye takarasa fadi tareda murgud'a baki cike da tsiwa sannan tawanke idonta tareda fara gyaran kichin din.
*Bayan kwana*
********
Komai yana tafiya dai-dai inda *TASLEEM* ta cigaba da zuwa aikatau dinta hankali kwance, domin sosai *Momma* tajata ajiki tamkar yar cikinta haka takejin kaunarta aranta inda take koya mata abubuwan data kula bata iyaba, musamman kalolin abincin turawa da larabawa harma dana gargajiya irin wanda bata iyaba, hakan yasa cikin lokaci kankanin suka shakuda *Momma* saidai kuma tun ranan da abun nan yafaru tsakaninta da *TAUFIQ* bata
sake ganinsa ba, sai yazamana da'ita dashi kadaran kadahan batama ganinsa sosai saboda harkokinsa, da basu barinsa zama gida sai kullum za tashiga ta gyara mashi d'aki tsaf tafito.
Kamar yauma taje ta gyara mashi tafito tana kokarin har fitata gada part din, zata shiga part din *Momma* taji ta tayi wani irin mugun yin baya sakamakon taka wani abu wanda bazata iyacewa ko menene ba, tadaiji ta tafi suuuu sannan tafadi rifffff! inda kafarta murgud'e tabayan sannan kanta yabugi kan tayis, jikake 'kummm! aikam take tasaki wani irin mugun kara dai-dai lokacin da *TAUFIQ* yafito daga bayan labule, yana sakin wani irin murmushi wanda sautinsa yasa *TASLEEM* d'ago dakai ahankali takallesa da idanuwanta suke ganinsa dishi-dishi sai kuma takoma ragwaf. To adai-dai kuma sannan *Momma* tayi saurin karasowa gurinta, kasan cewar fitowatar kenan daga d'aki taji wannan karan wanda ta tabbatar muryar *TASLEEM* din ne, aikam taganta zube kasa magashiya da sauri ta d'agota saidai ko motsi batayi hakan yasata cikin tashin hankali tace.....
Muje zuwa
*MEENAL or LUFHAT*
_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu kayyu mu_
[8/10, 8:42 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page 2️⃣4️⃣-2️⃣5️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.
_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.
*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,
Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
""""""""Subhallahi! *TASLEEM!* garin yaya kika fad'i haka eye?....tana me sake d'agota sosai, *TASLEEM!!* tasake kiran sunanta akaro na biyu saidai bata amsa mata ba, hakan yasata rungumota zuwa jitanta cikin tsananin tashin hankalin irin wanda rabon data shiga irinsa harta manta rana, hakan yasata furta innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'u! *TASLEEM!* *TASLEEM!!* *TASLEEM!!!* tasake kiran sunanta akaro na babu adadi tareda karashe fadin daki amsani mana *TASLEEM!*.
"Shuru *TASLEEM!!* bata amsata ba domin kuma gaba d'aya jikinta yasaki sosai, hakan yasa *Momman* sake shiga mugun tashin hankalin inda da sauri takai kunnanta saitin zuciyarta dan taji yana bugawa kuwa, saidai komai batajiba hakan yasa cikin tsoro tace nashiga uku ni Saudatu kardai yar mutane tamutum,
sai kuma tace a ah! insha'allah hakan bazata faruba ya Allah karufa mun asiri, sai kuma cikin sauri tasake d'agota sosai sannan ta d'auketa, kasan cewar *Momma* irin matan nance dirarru masu karfi wayanda hutu da jin dad'i baisa sun bar jikinsu yalalaceba, kuma da alama *TASLEEM* din jikin ne kawai batada wani nauyi, domin kuwa tamkar yar jaririya hakan *Momman* ta sunkuceta inda kai tsaye tanufi part dinta da'ita cikin sauri.
*******
"Hakan yaba *TAUFIQ* damar yafito da sauri daga bayan labulen da yaboye, saidai ranshi a'bace saboda ganin mugun tashin hankali akan fuskar *Mommansa*, hakan yasa yajin tsanar *TASLEEM* din yasake shiga ransa akaro na babu adadi tsaki yaja mtsw!, tareda furta mayyar "yarinya kawai duk tabi talashewa *Mommana* kurwa nidai kurwata yafi karfinta", sai kuma yaishuru domin jiyai zuciyarsa tad'an bugawa saboda tunowa da ganin halin da *TASLEEM* din take cikin.
"Dan haka da sauri yafita daga part din nasa yanufi hanyar shiga part din *Momman* ta kofar waje, saida yanutsu sannan yashiga falon da sallama tamkar baisan abinda yafaruba, inda ya'ise *Momman* cikin tsananin tashin hankali tuni har ta kwantar da *TASLEEM* din akan kujera me saman mutun uku, tad'auko ruwa tazuba mata amma ko motsi batayi ba dan hakan ne taketa faman girgiza *TASLEEM* din cikin tashin hankali da tsoro tareda kiran sunanta saidai shuru.
Saiga sallamar shi hakan yasata d'ago dakai cike da tashin hankali da firgici, tace yauwa na nagodema Allah dayakawo munkai taima kaduba mun "ita Allah yasadai ba mutuwa tayi ba. Cikin d'an basarwa yace me yasa meta?...nan taf'ada mashi abinda yafaru, cikin rashin damuwa da halin da *TASLEEM* din take ciki yaja tsaki mtsw! tareda cewa *Momma* "yarinyar nan batada hankali, shiyasa batayin komai cikin nutsuwa to ai gashinan gurin haukanta da rashin nutsuwa taje tafad'i.
"Fuska had'e tace nikam dai d'anlele meye had'inka da *TASLEEM* ne?.., aransa yace tsana wlh na tsaneta afili kuma yace me kuwa tareda hade fuska cike da tsanar *TASLEEM* aransa, rai a'bace tace humm! kadai tsani yar mutane haka kurum shine kake "binta da mugun kalamai *TASLEEM* dince marar hankali da natsuwa?..
"Yace "eh mana idan ba haka ba itaba makauniyace ba yaza'ai tafad'i haka kawai tana ciki tafiya eye?...tace kana nufin kace mun bakasan tsautsayi bakome eye?...yarinyar da tunda nake ban ta'ba ganin me natsuwa irin ta'ba, dan tsautsayi yafad'a mata shine zakace mata mahaukaciya, haba d'anlele meyasa kake hakane eye?...
Kallonta yake aransa kuma mamaki yake, yanda wannan mayyar yarinya tashiga zuciyarta cikin lokaci kankanin. Katseshi tayida fadin shin yanzu zaka dubamun Ita ko bazaka duba mun itaba?...cikin kwantar da murya yace kiyi hakuri *Momma* nidaba Dr ba
yaza'a nasan meyasa meta eye?...da sauri tace "eh kuma fa hakane to kira dr Lamir yazo maza yaduba mun Ita.
"Nan yad'aga waya yakirashi kasan cewar shine family Dr dinsu nan yace masa gashin nan zuwa yace ok sai yazo din tareda kashe wayar, yafad'awa *Momman* cike da tsananin fargaba tace to, kallonta yai cike da tausayi yace *Momma* ki kwantar da hankalinki maybe dogon suma tayi dazaran yazo yai mata irin dabarunsu na likitoci zata farfad'do kinji?..cikin sanyin jiki tace to.
Sannan yace yauwa to ki zauna yafad'i tareda kamata ya zaunar da'ita akan kujera me zaman mutum biyu, tana me kallon kyakkawar *TASLEEM* din datayi fayau lokaci d'aya sosai takejin tsoro kar wani abu yasamu yar mutane.
Sai kuma tafashe dakuka hakan yasashi saurin cewa a ah! *Momma* meye kuma abin kuka?...,cikin kukan tace ba dole nayi kukaba ni wlh tsoro nakeji kar wani abun yasame yar mutane nashiga uku, fuska yasake had'ewa yanasake jin tsanar *TASLEEM* din aransa fiyeda tuna me karatu,
kafin da sauri yace *Momma* kidaina kirama kanki shiga ukun saboda wannan banzar yar talakawan, cikin kuka had'eda fad'a tace d'anlele wai meye hakane?...cikin turo baki yace to me kuma nayi?...Hararansa tayi tareda cewa wai tambayata kake me kayi ko?....to *Momma* aidai gaskiya nafad'a kidaina zubar da hawayanki akan wannan yar mahaukaciyar yar talakawan me kamada aljanu.
Cikin fad'a tace ah! kamace aljanarce kaji tunda kai talaka bayada daraja agurinka, shiyasa sai kanata kirasa da dukkan sunan dakaga dama kuma kullun ina fad'a maka ba duka aka taru aka zama d'aya ba, sannan kuma kasani asalin kauye dai birni ne sannan asalin me kudin talaka "ehe dan haka idan har baka tausaya mata dan takasace yar talakawan daka tsanaba, aika tausaya mata dalilin kai taje gyarama daki har tsautsayi yafad'a mata tafad'i, saboda Allah fa kaduba kaga halinda take ciki amman kana tafad'in maganganu akanta marasa dad'inji, takarashe fad'i rai a'bace.
Cikin sanyi murya yace to *Momma* kiyi hakuri kidaina kukan hakanan, insha'allah babu abinda zaya sameta shikenan nafadi magana me dad'i akanta ko?...kai ta kawar batareda tace komai bahakan yasashi zama kusa da'ita idonsa akan *TASLEEM* wacce take magashiya, sosai yakejin zuciyarsa tana bugawa saboda farkaban kar sanadinsa tamutu wanda idan har hakan tafaru bazaya ta'ba yafewa kansaba, tunda har yai sanadiyar mutuwar wani adoron kasa sai kuma yaja tsaki mtsw! wanda har yasa *Momma* kallonsa da sauri tana cewa meye kuma?...
Kai ya girgirza mata alamar bakomai, yayinda aransa yace wawuyar yarinya kawai duk abinda yasameta ai ita ce tajama kanta, inda bata shiga gonata ba aida banshiga gonartaba.
Suna zaune dr yashigo da sallama d'auke abakinsa bakine gajere amma kyakkawane, shekarunsa duk bai wuce talatin da bakwai zuwa da takwas yana sanye da wando baki riga t-shirt fara me dogon hannu, yayinda hannunsa rike da babban first aid box, da sauri suka mike tareda amsa masa sallamar cikin girmamawa yagaida *Momma*
tareda mikawa *TAUFIQ* hannun sukai musabiha.
Dai-dai lokacin da *Momma* tace Dr dan Allah dubamun ita Allah yasa dai ba mutuwa tayiba, saboda naga tund'azu ko motsi batayi ba cikin sauri yace ok hajiya me yasa meta ne?...tad'uwa tayi wlh, yace "eyya insha'allah zata farka I tink dogon suma tayi cikin sauri tace to Allah yasa hakan, yace ameen tareda tsugunnawa yabud'e first aid box din yaciro abin nan nasu na likitoci yafara dubata.
Inda nan yaga tana darai dan hakan yafara kokarin ganin numfashinta yadawo tafiya dai-dai, saidai duk yanda yai kokarin hakan abin yagagara gaba d'aya duk yahad'a gumi sosai hakan yasa yakallesu tareda share gumin goshinsa, sud'inma shisuke kallo kowani zuciyarsa cike da mugun fargaba kar wani abun yasameta, gyaran murya yayi sannan cikin faduwar gaba yace hajiya saifa ahankali domin yarinyar nan tayi nisaa cike da tsoro tace ta mutu ko, da saurin yace.....
Anan zan dakata har sai Allah yabani lafiya, dan haka zanyi amfani da wannan damar ina barar addu'o'en ku domin za'aimun operation ina rokon, kusani acikin addu'o'en naku Allah yasa nashiga lafiya nafito lafiya Allah kuma yasa adace, dan haka dukkan wanda na'batawa ya yafe mani insha'allah dazaran naji sauki zan cigaba da izin Allah nagode Allah yabar zumuncin.
_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:42 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page 2️⃣6️⃣_2️⃣7️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA TA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya