Showing 36001 words to 39000 words out of 48594 words

Chapter 13 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

a asibitiba dan haka ita zata zauna tayi jinyarta har tadawo hayyacinta, saidai duk yanda sukai da'ita dan takoma gida takiya dole suka barta inda tace saidai shi *TAUFIQ* yatafi gida yadauko mata wasu kayanta yakuma daukoma *TASLEEM* cikin nasu Hussaina ko za'a bukata, haka sai yatafi badan yasoba.


*******
Aban garansu inna kuma, sunga *TASLEEM* yanzu sun ganta anjima shuru har dare yayi bata dawoba kamar yanda tasaba, dan hakan sai hankalinsu saidai kuma hankalinsu bai sake tashiba saida sukaga har gari yawaye dare yasakeyi, amma *TASLEEM* dinsu bata dawoba dan haka hankalinsu yai mugun tashi. Wasa wasa yau har kwana ukku babu *TASLEEM* babu labarinta sosai hankalinsu yai mugun tashi, haka inna taketa shiga makota tana tambayansu ko sun san gidan da *TASLEEM* dinta take aiki?...


saidai kuma babu wanda yasani, yayinda wasu suke tajin haushinta wai akan wani dalili zata tura "yarta tana aikatau sannan kuma tace bata sannan gidan datake aikin ba, wannanma zance take taje can tanemi yarta wanda kwad'ayi yasasu katura ta aikatau, Allah dai yasama ba gidan yankan kaine suka turataba kilama sun yankata shikenan sun huta, haka dai mutanan dasuke makiyansu keta fada mata maganganu marasa dadi masu konarai dasake sakata cikin tashin hankalin rashin sanin takamaimai inda *TASLEEM* dintake.


Sosai inna tayi kuka har tagaji domin duk yanda tayi dan tagano unguwa da gidan da *TASLEEM* din ke aiki takasa, kasan cewar tuni dillaliyar datakai *TASLEEM* din gidan aikatau din tun washegari data kaita tabar gari, inda tabar dillancin takoma garinsu kwatakwata dazama ita kuma inna Halira datasan dillaliyar taje ganin gida, dan haka babu wanda *inna* zatace aigashi yasan gidan dole sukai hakuri suka zubawa sarautar Allah ido.


Tunda sunyi cigiyar har sun gaji dan haka suka dukufa rokon Allah, akan yadawo masu dayar tilon yarsu kwaya d'aya data ragemasu aduniya wacce takasance sanyi idaniyarsu saidai kuma shuru kakaji wai malam yaci shirwa, ganin hakan yasa inna ta cigaba da neman maganin gargajiya na ciwon kodar da *Abba* yake fama dashi, wanda dama tanayi ahakan har tahadu da nawani bawon Allah dayabar sadaka (zanyi bayaninsa a page nagaba in sha Allah) cikin hukunci Allah sai gashi *Abba* yaji sauki har yafara zuwa gurin aiki saida yarame sosai saboda damuwar yarshin yarsa, hakan itama *inna* wannan kenan.




*Bayan sati ukku*


**********
Sannu ahankali lokaci yake tafiya yau gashi har kimanin satin *TASLEEM* ukku cur, amma har zuwa wannan lokacin ko dan yatsatar bata motsaba, duk da irin kokarin da likitoci sukeyi akanta amma har zuwa wannan lokacin shuru kakaji wai malam yaci shirwa, dan haka ne duk inda hankalin*Mamma* yake yatashi duk tabi tarame sosai domin kuwa tasa damuwar rashin farfadowar *TASLEEM din aranta, wanda yaimata yawa bata da aikin dayawuce kuka da addu'ar Allah yadawo da *TASLEEM* din cikin hayyacinta,


tsabar ganin damuwarta datake ciki yasa *TAUFIQ* cikin matukar tashin hankalin kasan cewar idan har akwai abinda yatsana aduniya to ganin tashin hankali akan fuskar *Mammansa*, dan haka sosai tsanar *TASLEEM* yasake samun gurin zama acikin ransa domin kuwa duk ita ce silar fadawar mahaifiyarsa cikin tsananin damuwa haka, kuwa ganin tsabar damuwan hakan yasa yadukufa addu'ar Allah yadawo da ita cikin hayyacinta ko *Mammansa* tasamu nutsuwa.




******
Yau asabar wanda yai dai-dai da kwanan *TASLEEM* ashirin da takwas wato sati hudu kenan cur da shiganta comman, *TAUFIQ* ne zaune agaban gadon da *TASLEEM* ke kwance yana danna waya jefi-jefi yana kallonta yana jan tsaki mtswww!, kasan cewar yau sati ukku kenan duk ranan weekend yace *Mamma* ta ringa zama agida, shi yaringa zuwa ya zauna da'ita tun daga safe har dare sannan *Mamma* tazo takwana da'ita, shikuma yatafi gida saidai daga safe zuwa dare yanajan tsaki fiye da guda dubu saboda takaicin *TASLEEM* din.


Kamar yanzuma cike da jin haushinta yadaga kai yaimata wani irn kallo me cike da harara yaja wani dogon tsaki jikake mtswwwww!, har yakauda kai daga barin kallonta sai kuma yai sauri yasake kallonta domin sai yaga kamar tana motsi da kwayar idonta aiko hakan ne, zumbur yamike tareda matsawa kusada ita yakura mata ido zuciyarsa tana wani irin bugawa, domin kuwa sosai take motsa idonta ahankali na'uran dake manne da yar yatsanta yafara motsawa,


yayinda sannu ahankali numfashinta yafara daga kirjinta ahankali ahankali har yafar dakarfin, yayinda DUKKAN jikinta yadauki wani irin mugun rawa har na'urorin dake jone ajikinta sun fara cirewa, cikin rawar murya hadeda rarraba kalmomi yafara kiran likita da d..o..c..t...o...rrrrr! cikin sa'a saiga likintan yafado dakin kamar anjohoshi,


da sauri yafara bata taimakon gaggawa sannu ahankali sai jikinta yasaki babu alamar motsi sosai likitan yake kokarin ganin numfashinta yadawo amma ina shuru duk yanda yaso abin yacitura, cikin sanyin jiki yafara zare dukkan wata na'uran dake jone ajikinta duk *TAUFIQ* yana kallonsa, wanda zuciyarsa yaketa aikin bugawa wanda yarasa dalilinsa najin hakan, har likitan yagama yakalli *TAUFIQ* wanda shima kallonta yakeyi, girgiza kai yai cikin turanci yace kayi hakuri tacika, da karfi yace me😳?....yace tarasufa nake nufi cikin mugun bala'i tashin hankali *TAUFIQ* yachakumi kwalar rigansa yarike yace.....




Aha!






Muje zuwa


_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyumu_
[8/10, 8:45 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️

🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page3️⃣0️⃣-3️⃣1️⃣-3️⃣2️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,


sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.


_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.



✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_




""""""""Kuttttttt!wlh karyane mutuwafa kace?...yace "eh tamutu, yace ahaba dai dr sai kace mutuwar wasa, yace a ah yallabai wani irin mutuwar wasa kuma, yace ah! to idan na mutuwar wasaba to mutuwar me tayi?....




yace mutuwar gaskiya mana tunda dai kasan cewa wannan din aikina kuma kasan nasaba yinsa aiko?...yace "eh lallai nasani, yauwa to kagani kuma kasan ban tabayi maka wasa ko karya akan aikina ba ko?....




da sauri yace kwarai kuwa nasani saidai yau kam kuma yanzun nan kayimun wasa, sannan kayi mun babban karyama domin dai wallahi wannan "yarinyar naji ajikina bata mutuba,yanzu nan fa "tagama motsi da dukkan sassan jikinta shikenan daga kawai ka d'an tabata shine zakace wai ta mutu" ina wallahi sam bazaya yiwuba, kasan mutuwarta meyake nufi kuwa?.....




kai likita ya girgiza yaname kallon *TAUFIQ* cike da mamakin yanda yacimasa kwalar riga tamkar shine wanda yadauki ran nata.




*TAUFIQ* yace humm! to bari kaji mutuwar wannan stupid "girl din yana nufin mutuwar *Mammana"*, kuma wallahi ni banshirya daukan hakanba, cikin mamaki likita Lamir yace kamar yafa ban gane ba?....yace aibazaka taba ganewa ba, yace to naji tunda bazan ganeba aikai nasan kagane abinda ake nufi da kaddara ko?....


wani irin matsiyacin kallo *TAUFIQ* yawatsa mashi tareda cewa, niko nasan abinda ake nufi da kaddara tunda naganta arayuwa kala-kala, likinta yace good to saika dauki kaddaran cewa tarasu kawai dan haka sakar mun riga.



Murmushi *TAUFIQ* yayi tareda cewa Ok naji nasakar maka riga yafadi tareda gyar masa kwalar rigan yanasake daure mashi igiyar dake rataye a rigan,yaname cigaba da fadin to amma kasani wallahi ban yarda wannan "yarinyar ta mutu ba.




Dan haka duk abinda zakayi sai kayi domin kadawo da numfashin wannan stupid girl din dana tsana tamkar yanda natsani mutuwata, yana kaiwa nan amaganarsa sai yakoma yajin gina da bango tareda hard'e hannuwa akirji yazubawa likitan jajayan idonunsa, masu cike da firgici hadeda bacin rai yasake cewa Oya bismillah start ina jiranka.




*******
Cikin tsananin mamaki likita Lamir yace a ah yallabai nifa yau gaba d'aya narasa gane maka, yace "eh ai nafada maka ba dole ne kagane mun ba, to amma inason kai! kagane wannan wato ina matukar kaunar mahaifiyata fiyeda komai aduniya nan kai! fiyema da kaina,




so dan haka kayi duk abinda zakai domin kadawo da numfashin wannan banzar yarinyar nan dana tsana fiyeda yanda natsani mutuwata, wanda tunda tashigo cikin rayuwarmu komai yakeshirin jagulewa, yakarasa tareda watsama *TASLEEM* mugun harara wacce take kwance magashiya batasan inda takeba balle tasan wainar da ake toyawa akanta.


"Yayinda shikam likita Lamir cikin bacin ran dayafara kama shi yace taya zanyi hakan tunda rayuwata ba ahannuna yakeba eye?...yakarasa fadi cikin fada, shima *TAUFIQ* cikin fada yace nasani tabbas rayuwarta ba ahannuka takeba to amma wallahi sai kayi duk abinda zakai domin numfashinta yadawo jikinta,




cikin fada yace to kai basai kayi duk yanda zakai dinba don kadawo da numfashin nata jikinta ba, cikin masifar fadan dayafi na likita *TAUFIQ* yasake cikin kwalar rigansa da iyakacin karfinsa yashake masa wuya da karfi yace dalla gafar malam ai ba'aiki nabane, so kai kuma aikinka ne don haka oyo ka dubata da kyau kaji ko?....




wasa-wasa rigima takaure tsakanin Likita Lamir da *TAUFIQ* wanda gaba d'aya kansa yakulle yashiga rud'ani matuka najin cewa wai *TASLEEM* tamutu, yayinda ya nace dole sai Likita Lamir yadawo mata da numfashinta.


(Yakuma san cewa babu wanda ya'isa yadawoma dawani bawa numfashinsa, idan ba wanda yakagi numfashin nasaba wato ALLAH Ubangijin halitta,).


Amma tsabar rudewa da kuma tsoron tashin hankalin da mahaifiyarsa zata shiga yasa duk ya manta da hakan, saboda ganin yanda mahaifiyarsa ta kwallafawa *TASLEEM* din rai.




********
Suna cikin wannan rigimar wanda har wasu daga cikin nurses sun fara taruwa suna basu hakuri, sai ga babbar yatsan hannun *TASLEEM* tafara motsawa ahankali, da sauri wani nurse yace dr she still alive gashinan hannunta yana motsi hakan yasa *TAUFIQ* saurin sakin kwalarsa, yana cewa kagani ko?...aina fada mashi cewa bata mutuba, amma saboda rashin ba'aiki mahimmanci yace wai aita mutu.




Dai-dai lokacin da gaba d'aya suka nufi gurinta wanda kafin su karasa tuni gaba d'aya ilahirin jikinta rawayake, cike da jin haushin *TAUFIQ* din likinta Lamir ya kalleshi me hadeda harara yace to yallabai aisai kafita kabamu wuri mudubata ko?...batareda yace komai ba yafita da sauri.




Inda cikin sauri yafara dubata tareda taimakon wasu nurses guda biyu, sai gashi tadaina jijjagar inda cikin hukuncin Allah numfashinta yadai-daita dataimakon alluran barcin dayai mata, wanda cikin lokaci kankani barcin yadauketa inda ahankali take sauke numfashi.




Sannan Likita Lamir yashare gumin goshinsa tareda gyara kwalar rigarsa da igiyan rigar, sannan yakalli nurses din cikin turanci yace oh! Allah nagode maka tanada rai, kai! inda tamutu tabbas nasan mutumin can zayace ne dagayya nakasheta kilama yasa akamani adaure, dayan nurse din yace gaskiya kam sir "zaya iya aikatawa domin naga alamar bayada sauki",




yace humm! ina yaga sauki sai shegen karfi kamar shari'a dubi yanda duk yabi yashake mun wuya, yakarasa fadi dajan dogon tsaki mtswww!sukace sorry sir yace it's okay thanks last go tareda nufar hanyar fita daga dakin inda suka rufa masa baya.




********


"Abakin kofa suka iske *TAUFIQ* yanata safa da marwa yana ganin firowarsu yanufesu da sauri, fuska dauke da annuri yace Dr Lamir "tadawo ko?....kallonshi likita Lamir yai fuska cike da mamaki kamar bashine YANZU yagama cimasa mutunci ba", fuska hade yace yes cikin farin ciki yace good dr yanzu aikinka yai kyau so ina iya shiga?...yace yes saidai munyi mata alluran barci saboda tana bukatar hutu, dan haka barci takeyi yace ok karka damu zan ganta" ne kawai dan natabbatar
da dawowar mata.




"Har zaya shiga sai Dr yace but amma yallabai gaskiya banji dadin abinda kaimun yau ba wallahi ko kadayan kamar yau nafarayi maku aiki, murmushi *TAUFIQ* yai me kayatarwa tareda d'an dukan kafatar likitan yace sorry our special dr bazaka gane bane, saboda my *Mamma* tana mugun kaunar "yarinyar nan ne fiyeda tunaninka so kaga if anything happen to her" humm! wallahi akwai dus sosai, shiyasa kaga gaba daya am very confused so thanks sannan yashiga dakin.




Shikam likita Lamir ajiyar zuciya yasauke tareda girgiza kai batareda yace komai ba domin dai shidin shedane akan abinda *TAUFIQ* yafada cewa "mahaifiyarsa tana mugun kaunar yarinyar, wanda yagani hakan tun ranan dasuka kirasa cewa yazo yarinyar tafadi har zuwa kwanakin dasukai acikin asibitin nan,




duk yana kulada irin tashin hankali da damuwar da mahaifiyar "nasa tashiga naganin halinda yarinyar take cikin, hakan nema yasa tun daga ranan yake tunani tareda da tambayar kanshi shin to ita wannan yarinyar meye alakarsu da'ita" ne haka?...,da hajiyar tayi matukar shiga tashin hankalin tareda matsananciyar damu akan halin da yarinyar take ciki ne?...




to shidai yasan ita din dai ba yar'uwarsuce ta jini ba, domin dai yasan wasu daga cikin yan'uwansu especially su Hussy kyawawa yammata to amma ko kad'an batayi kama dasuba, domin kuwa tafisu kyau nisa bakusa ba asalima ita tafi kamada buzayen asali da alama shi yasama takeda matukar kyau nadaukan hankali,




kuma wani abinda yake daure masa kai shine yakula kwarai babu jittuwa tsakanin yarinyar da yallabai *TAUFIQ* kome yasa hakan Oho!, yana kai nan da zancan zucin dayake yadaga kafada alamar koma dai meye alakarsu da'ita shiba ruwansa, yadai godema Allah dayasa numfashinta yadawo, idanma ta farka zaya sallamesu suje chan gida su cigaba da jinyarta domin bazaya iya tashin hankalin yallabai *TAUFIQ*.




********
Aban garansu *inna* da *Abba* kuwa gaba daya damuwar rashin sani halin da yar tilon yarsu guda daya tayimasu yawa, daurewa kawai "sukeyi bayin Allah cikin karfin hali suke kokarin kwantarma da junansu hankali, yayinda kowani yake kokarin ganin dan'uwansa baya cikin damuwar rashin yartasu",




Musamman *Abba* sosai yake tausayi *inna* saboda ita mace me matukar rauni shiyasa yake kokarin ganin batasa damuwar rashin *TASLEEM* din aranta sosai ba.




Itama anata bangaran hakane tana iya bakin kokarinta naganin baisa damuwar rashin *TASLEEM* aransa sosai ba, musamman dayake kaunarsa da *TASLEEM* din abayyane take sabani nata dayake aboye, gashi yakwallafa ranshi dason cika mata burinta nasonyin karatun aikin asibiti saidai kuma gashi kamar burin nata bazaya cika ba, aduk lokacin da yatuna da hakan yakanji ransa babu dadi narashin yartasa.




Misalin karfe takwas da rabi nadare *Abba* ne yadawo daga gurin aiki kamar kullum kanshi nade da rawani irin dai nasu na buzayen asali, ahankali yake tafiya kamar wanda kwai yafashewa aciki har yashiga harabar matsakancin gidan nasa, saidai tunda yashiga yai faka mashin din yai tsaye rikeda ita yai shuru babu wacce yake tunawa sai *TASLEEM*,




yasan inda tana nan datuni tazo ta tareshi da sannu da dawowa *Abbana* kadawo lafiya ya hanya yakuma aikin *Abbana* ga ruwan wanka can nakai maka kajeyi, idan kafito sai kaci abinci sannan ka kwanta kahuta nasan duk kagaji ko?... *Abbana*.




Yana kai nan yasaki wani irin kuka tambar yaro karamin sosai dattijon yake kuka me cike da ban tausayi, tunaninsa wani irin hali yarsa take ciki shin tafada hannun mutanan kirkine ko kuwa tafada hannun mutanan banza,




Musamman idan yaga dare yayi yakanji wani irin tsoro yakamashi domin tunda tabata yakanji aransa cewa *TASLEEM* dinsa tana cikin wani mawuyacin hali, hakan yakesa shiyi tunanina ko cikin wani yanayi take yanzu ko taci abinci ko bataciba Allah masani,




dan haka aduk lokacin da yai tunanin hakan yakanyi kuka aboye batareda *Inna* tasaniba saidai yaukam yakasa rike kanshi, dan haka ne yaketa kuka sosai.




"Yana cikin wannan halin ne *Innar* tafito kasan cewar dama tunda ta idar da sallar isha'i take zaune tana lazumi, taji motsin shigowarsa amma sai taga shuru
be shiga dakin ba shiyasa tafito dan tagani lafiya be shigoba, sai taganshi tsaye yana kuka harda shassheka cikin tashin hankalin da tsakanin tsoro takarasa gurinsa tareda rikeshi tana fadi subhanallahi! *Abban* *TASLEEM* yau kai ke kuka haka?...




kasan cewar tasan shidin mutun ne me matukar dauriya da juriya akan dukkan abinda yasameshi, kai! ya gyada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login