Showing 48001 words to 48594 words out of 48594 words
Chapter 17 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt
tayi mutukar yimata kyau, sosai ko dan ita din me kyauce kallo daya zakai mata kagane lafiya da hutu dajin dad'i sun kama jikinta sai babu lafiyar kwakwalwa.
Tsaye yai yana kallonta me had'eda harara aransa yana fadin kalleta dan Allah, mtsww! sai shegen kyau anfadawa *Mamma* cewa aljanace tabarta tayita tafiya can gurin aljannu yan'uwanta, tace a ah ai mutumce zata zauna da'ita to aigata nan sai tayi tazama da'ita din nidai nafi karfin aljannu bama aljana ba, eheee! yakarasa fadi dajan dogon tsaki wanda yafito fili still bata jishi ba domin.
"Ta shagala da kallon katum din sai dariya takeyi dan haka bataji sallamar saba balle taji dogon tsakin dayai, saidai kamshin turaransa kawai tajida yadaki hancinta kasan cewar tuni tasan kamshi.
Hakan yasa tayi saurin mikewa tareda daukar hullarta da yacire gurin dariya,tafara kokarin sakawa akai cikin sanyi muryarta me cike da natsuwa tace sannu da dawowa "yayana kasan cewar hakan *Mamma* takoya mata taringa kiransa.
Baki yatabe tareda dauke kansa daga barin kallonta yana saita bugun zuciyarsa, wanda har yanzu yarasa meyasa duk lokacin dasuke tare sai yaringa jin bugun zuciyarsa yana tsananta, take wata zuciya tace dashi karka manta aljanace kasani ko tanayi maka siddabarunsu na aljanune, sai kuma da sauri daya zuciyar tace no! aikafi karfinta balle har tayi maka siddabarunsu.
Tsaki yasake ja mtsww!dai-dai lokacin datasake cewa "yayana sannu da dawowa, ahankali yajuyo yanai mata kallon kasan ido aransa yake tambayar kansa da fadin "ni narasa ta inda nazama yayanta, datake tafaman kirana yayanta", take yaba kanshi amsa da fadin ta karere mana,tsaki yasake ja mtsww! wanda tuni yabi masa jiki yayinda har yanzu mugun haushinta yakeji musamman idan takirasa da yayanta.
Batare da ya amsa sannun taba tasake cewa "yayana ina sweets da chocolates din dakace zaka siyo mun?...fuska hade yace "to uwata" ban siyoba, sai akoreni daga kasata kwantagora ko kuma ashafeni adoron duniyar gaba d'aya kinji ko?...ita dai bata fahimci inda zancasa yasa gaba ba, saidai tafahimci fada yake dan haka cikin sanyi muryar tace sorry tsaki yaja yace nabi sorry dagudu dallah can ina *Mamma* take?...da sauri tace tana ciki tana wanka.
juyawa yai zaya fita da sauri tarike hannunsa tareda cewa "yayana zanje, cikin tsawa yajuyo yace zuwa gidan ubanwa eye nace zuwa gidan uban wa eye?....yakarasa fadi cikin tsawa tareda zabga mata harara, da sauri tasaki hannunsa jikinta narawa ta tsaya tana kallonsa tana turo baki cike da sha'gwa'ba tace yi hakuri, har zaya rufeta da masifar dayasaba yimata musamman idan *Mamma* bata kusa.
Sai kuma yafasa saboda ganin *Mamma* hakan yasa yana shafa lallausan gashin kansa yana dariyar yake cikin faduwar gaba yace ah! *Mamma* kinfito?....wani mugun kallo ta watsa mashi, wanda yasake jin matsananciyar faduwar gaba fiyeda farko, cikin bacin randa bai ta'ba ganinsa akan fuskarta tace?....
Aha! wasa farin girki
Alhamdulillahi!
_*Anan nakawo karshen littabin KYANDIR ME HASKEN BANZA wato book 1*_
SAI MUN HADU A BOOK 2
*_Muje zuwa book 2 wanda anan wasan yake saidai fa nakudi ne amma akan farashi me sauki wato 300 kacal, bayan nagama free pages wanda in sha Allahu daga gobe free page zaya fara, idan kana bukata zaka biyane ta wannan acc no 0047769671 Amina Abdullahi gt bank, to masoyana gareku ta hanyar siyan wannan littafin nawa KYANDIR ME HASKEN BANZA ne zangane irin kaunar da kuke mun musamman yan group dina na ZUCIYATA CE nagode sai najiku_*.
_Ya ALLAH kasa mucika da imani ameen ya ha hayyu ya kayyu mu_