Showing 21001 words to 24000 words out of 48594 words

Chapter 8 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

yaga yadaina saidai kuma sai yakasa,


domin kuwa dazaran yayi kamar yadainan kwana biyu to kuma kwana biyu sai kaga ya cigaba, wanda hakan yana faruwa ne da taimakon hudubar *T J* wanda yakan ce masa malam kashana, tunda kana da kudinka kuma sud'in suna maganin komai.


Dan haka ne *TAUFIQ* yake biyema hud'ubarsa yaita neman yana rage zafi dasu, wanda wani lokacin karama kashi zafi yake domin kuwa daga baya idan yagama sai yaringa jin haushin kansa, yaji kamar yakama kansa yaita bugu dan bakin ciki abinda yake aikatawa wanda sannun ahankali irin mutan nan masu sama mutane ido,


suka fara gane me yake aikatawa don hakan yasa suke masa kallon *KYANDIR* wato me kyan banza, yayinda marayun dayake taimako kuwa ko kad'an basuyi masa kallon *KYANDIR*, balle har su daukesa me kyan banza.


"Asalima Kyakkawan bango sukari suka daukesa wanda kowa yajingina dakai sai yalasa, sannan shidin bayane agurinsu wato me goya marayu lallai kam yad'aukesu yagoya inda harda zani yasa yadauresu ram, saboda karsu fad'o wannan kenan.


Haka yaita lafilfili idan yayi yazauna yai tasbihi inda sanun ahankali yakejin zuciyarsa tana sanyi, ahaka har saida aka kira sallar farko sannan yazauna yai addu'o'en masu yawa, sannan yamike yashiga toilet yasake dauro wata alwala. Sannan yafito har zaya wuce sai kuma yadawo, yakwankwasama *T J* kofa daga can cikin barci *T J * yace wanene?...yace bansani ba malam katashi kayi sallah ko bakaji ankira bane eye?....yace naji.


Sannan yanufi part dinsu *Momma* dan yatadasu duk aransa yanada tabbacin sun tashi, domin yasan *Mommansa* ma'abociya ibadace dan haka sallar asuba ko kad'an bata wuceta,wanda zaya iyacewa agurinta yadauki hakan sabo dayin sallar asuba akan lokaci.


"Akam koda yashiga ya'iske sun tashi, dan haka yawuce masallaci inda nanma bai fitoba saida yaga gari yai haske sosai misalin karfe bakwai sannan yafito, bayan sun gaisa da ma'aikata da secuirity gidan sai yanufi part din *Momma*, bayan sun gaisa da'ita dasu Hassy sannan yanufi part dinsa yakwanta inda cikin abinda baifi minti uku ba barci me nauyi yadaukesa.


*******
Aban garen *TASLEEM* kuwa itakam tayi barcinta saidai cike yakeda tunanin ahalin da *Abbanta* yake ciki, yayinda misalin karfe ukun dare ta tashi kasan cewar itama ma'abociyar tsayuwan darence, saida tayi addu'ar neman tsari sannan tafito tsakar gidansu tadauki buta takewa bayi.


Bayan tafito sai ta tsugunan akan baranda tayi alwala sannan takoma d'aki, inda tahau kan abin sallah tafara gudanar da lafilfilita cikin natsuwa kamar yanda tasaba, sai misalin karfe hudu sannan ta zauna tana ta tasbihi.


Wanda tadauki tsawon lokaci sannan tad'aga ahannuwanta sama tana addu'o'en, wayanda yawancin duk akan iyayenta ne da kuma "mutumin da yasadaukar da rayuwarsa domin cheto nata rayuwar, wanda dukkan sallolin farilla datakeyi guda biyar dakuma tsayuwan daren da takeyi saita masa addu'o'e kala kala masu yawa, tareda rokon ubangiji yanuna matashi taimasa godiya abinda yaimata.


Dan haka kamar yanzu hakan takasan cewa bayan tagama yima *Innata* da *Abbanta* addu'o'en tayima kanta sannan shima tayi masa, sai karfe hudu da rabi tamike taje tad'an kishingid'a inda kiran sallar farko yatayar da'ita, tafito ta kwankwasama su" *Innata* kofa sannan tashiga bayi to kewaya bayan tafito tasakeyin alwala, taje tagabatar da sallar asuba bayan ta idar zama tayi tana lazumi, kasan cewar bata saba kwanciya bayan sallar asuba ba dan haka sai misalin bakwa saura sannan tafito.


"Bayan tagaida *Inna* shima *Abba* tagaidashi tareda tambayarsa yajikinsa, inda ya amsa mata dasauki tace Allah yakara sauki, amma dai *Abbana* yau bazakaje aiki bako?...cikin murmushi karfin hali kasan cewar har lokacin yanajin jikin, yace *TASLEEM* din *Abbanta* me zaya hanani zuwa gurin aiki?...da sauri tace saboda bakada lafiya mana.


Dariya yai yace a ah! *TASLEEM* naji sauki sosai saboda haka insha'allah zanje kinji?...cikin sanyi murya tace to *Abbana* sannan tamike tafita sharan tsakar gida tafarayi, sannan taje azaure tashare tad'orama *Abbanta* ruwan wanka, bayan yai zafi sai tajuye tasake zuba ruwan kunu, sannan tasirka ruwan takai mashi bayi bayan sai taje tafad'a mashi yace to tareda samata albarka.


Inda nan da nan ruwan kunun yatafasa tadama sauran ruwan kunu tasaka sauran tuwon jiyata,ta d'umama, sannan tazubawa *Inna* da *Abba* kunun takai masu sannan tazo tasha nata, lokacin tuni har tuwon yayi zafi tasa miya bayan shima yayi zafin yatauke tad'ora ruwan zafin wankanta.


Sannan tad'ibar masu tuwon takai masu sannan tazo itama tazuba taci, bayan duk sun gama tad'emo kwanonin tawanke sannan tajuye ruwa taje tayi wanka tafito tashirya cikin shirta tsab nazuwa islami kamar yanda tasaba, lokacin karfe takwas saura minti goma shabiyar.


"Dai-dai lokacin da *Abbanta* yafito shima cikin shirinsa nazuwa aiki, inda yafita da mashin din yagoyata kasan cewar dama duk ranan dayake da aikin safe shike ajiyeta islamiya sannan tafi gurin aikinsa, ko yanzuma hakan ne bayan ya sauketa sannan yawuce gurin aiki.


*********


Aban garen *TAUFQ* sai misalin karfe goma da rabi nasafe yatashi yashiga toilet yai wanka, sannan yafito yashirya cikin riga da wando nawani d'anyan yadi dark brown me shara-shara, domin har ana ganin farar vest dinsh yay matar kyau cikin yadin saida yagama feshe jikinsa da turare sannan yadauki, wayoyinsa tareda saka farin takalmi halfcover yafita.


dai-dai lokacin da *T J* yake shiga falon da alama tuni yatashi har yai wanka yafita, domin sanye yake shima da wani d'anyan yadi amma baki nasa kasan cewar fari sai yadin yaimasa kyau.


Cikin dariyar zolaya yace good morning gwauro tazuru, shima dariyar ransa kuma yana fad'in kai yakamata yasaba da halin *T J*, wanda idanma yace zaya ringa 'bata rai dashi to yayi aikin banza ne, domin shid'in hakan Allah yayisa da barkwanci sosai. Sannan shima cikin zolayar yace morning gwauro tazuru lamba d'aya, dariya yai kai kuma lambarsu biyu ko?...eh to zanyi iya d'auka haka, fatan muntashi lafiya?...


lafiya lau yau baka tashi barci dawuri ba gashi tund'azu *Momma* ta aikosu twins sis, suka kawo breakfast ni har nayi nawa ganaka yanachan yana jiranka.


Fuska dauke da annuri yace *Mommana* godiya nake, wlh yau nagaji ne sosai shiyasa da sauri *T J* yace kai yallabai koni Dana kwana ina aiki banji nagaji ba saikai, da sauri *TAUFIQ* ya kalleshi cike da mamaki yace aikin meka kwana kanayi?...


saida yad'aga masa gira d'aya sannan yace ah! shan zuma atukunyar zaki mana, duka yakai masa kafad'a tareda cewa *T J* Allah yashirya mun kai nida muje nayi breakfast karakani kamfani, domin natashi naga miss call din MD guda goma yace har goma "eh wlh to lafiya?...eh to saidai munje tukunna mugani, bayan yayi breakfast sai yashiga yasallami *Momma* sannan suka tafi.


Agurin ajiye motoci katafaran kamfani sukai fakin, bayan security sun bud'emasu kofa sun fito sannan suka nufi office dinsa inda sauran ma'aikata sai gaidashi sukeyi, yana d'aga masu hannu har suka isa office zamanshi keda wuya wani bakin mutum kakkaura, yashigo gaisawa sukai sannana *TAUFIQ* yanuna masa guri tareda cewa zauna MD kafad'a mun meke faruwa ne naga miss call dinka har goma.


Cikin girmamawa yace yallabai gaskiya malam buzu me gadi yana damun mu, haba dan Allah sai kace shikad'ai ne yake aiki akarkashi wannan kamfanin, kuma gaskiya idan bai daina ba zaya'bata mana sauran mutanansa kamfanin, fuska *TAUFQ* yahad'e tareda cewa akan me yake damunku?...akan kudin gadi, cikin bacin rai yace kira munshi yanzu nan aikam.


Aikam da sauri yafita chan sai gashi tareda *Abba* sun dawo, zubewa *Abba* cikin bugawar zuciya, domin yasan tsakaninsa dasu" talakawa kyaratane da hantara musamman su dake karkashinsa.


Wanda inbadan da Allah yakaddara cewa abincinsu" ajikinsa yakeba, to da babu abinda zayasa yadaukesu ayanda yakeji tsanarsu aransa, cikin girmamawa yace yallabai gani ance kana kirana fuska *TAUFQ* yasake yahad'ewa, sannan cikin kakkausan murya yace.....




Muje dai zuwa


*MEENAL ro LUFHAT*


_ALLAH kasa mucika da imani Ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️


🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page1️⃣6️⃣-1️⃣7️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,


sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.


_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.


✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


""""""""Malam buzu wai meyasa ka ke haka me eye?...da sauri yace yallabai me nayi?...cike da takaici yace malatsar malam ba haushe kenan tambaya cikin tamba, shidai *Abba* yana nan gurfane zuciyarsa sai aikin bugawa take, fatanshi dai kar ace yaiwani laifin da za akoresa.


"Cike da bacin yar yasake kiran *Abban*, cikin kakkausan murya da fadin malam buzu saida yakirsa har sai uku hakan yasa *Abban*, cikin bugawar zuciya yai sauri amsawa da na'am yallabai.


Cikin hassala yace agaskiya banason abinda kakeyi acikin kamfanin nan, da sauri yace ayi hakauri yallabai duk dadai bansan abinda nayi ba, tsaki yai mtsw! tareda cewa haba dan Allah wai "kai kad'an ne ke aiki akar kashin kamfanin nan ne eye?..,cikin kwantar da murya *Abba* yace a ah! yallabai bani kad'ai bane.


"Da fad'a yasake cewa to kafi kowane dazaka ringa damun mutane akan albashi eye?....yace a ah! yallabai banfi kowa ba asalima nid'in bakowa bane acikin kamfanin face meganinta.


"To akan me koda yaushe kaine ake samun matsala dakai akan kudin albashi eye?...yace to ayi hakuri yallabai, cike da bacin rai yace ko ba'abaka albashin nakane eye?... a ah! yallabai ana bani sai dai ba'akan lokacin ba, kuma gani talaka me karafin karfi hakan ne yasa kofin abanin duk nashiga wani hali, shiyasa dazaran naga watan yakare har anshiga wani nake tambaya.


"Ko yanzuma abinda yasa har akaga na tambaya wlh 'yata" nakeson nasiyama takardan shiga makarantar aikin asibiti ne, sannan nikaina kwana biyun nan banida lafiya, inason nasiyi magani ne shiyasa na nemi alfarman abani.


"To amma tunda baza'ai mun alfarma ba shikenan, wanda naga alamar hakan tahanyar tambayar danayi cewa naga ta'bata "maku rai, to ayi haku insha'allah bazan sake tambayaba har sai ranan da akayi biyan, na tabbatar yanda Allah yayini talaka me wadatar zuci insha'allah bazan taba, tagayyara ba arayuwa.


Nakuma sannan ubangijina bazaya ta'ba tozartani ba, yakarasa fadi tareda mikewa yana cewa idan kuma maganar danayi ta'bata maku rai, "amatsayina na talaka wanda bayada wata kima da daraja agareku" to kuyi hakuri.


Saidai kar kumanta da talaka da me kudi duk Allah yayisu, sannan inason kusaka wannan aciki aranku, wato akwai ranan da me "kudi zaya nemi alfarma gurin talakan wanda kudinsa bazasuyi masaba, idan ba wannan talakan da yaraina bane yaimasa.


"Da sauri *TAUFIQ* yace haba dai malam buzu aikudi sune babbar alfarma ko *T J*?..., yace "kwarai kuwa idan kanadasu" babu abinda bazaka samu ba arayuwar nan ta duniya, yace yauwa nawa fad'a masa kam, dan haka abinda bazai ta'ba yiwuwa bane "ace wai me kudi dakudinsa" yakasa biyama kansa bukata har sai talaka wanda bashida komai ne zayai masa.


"Murmushi *Abba* yai me ciwo kasan cewar shima sosai yakejin zafin yanda *TAUFIQ* yakejin haushin talaka had'eda walakanta shi, aransa kuma mamakin yake nayanda akai yake musayar miyau da "yaran da ahaife yahaifesu, ko dayake ba abin mamaki bane dan akai duba dacewa shidin talaka wanda yakeci akarkashinsu" shine yabasu damar mayar masa da magana haka gatsau kamar wani tsaransu.


"Kuna mamakin hakan bazaya ta'ba yiwuwa ba kenan?...da sauri *TAUFIQ* yace kwarai kuwa, kamarfa kana nufin ni *TAUFIQ RASHID TAFIDA* na nemi alfarma agurinka ko?....*Abba* yace "eh!, dariya yasaki me kayatarwa wacce tafito masa da kyakkawar fuskarsa, saida yayi sosai.


Sannan yahad'e rai tamkar bashine yai dariyar ba, yace haba malam buzu kana meganin kamfanina, na nemi alfarma agurunka?...cikin sanyi murya *Abba* yace "eh yallabai hakan yana iya faruw....cikin tsawa yakatsesa dafad'in a ah! hakan bazaya ta'ba faruwa ba, domin bakada abinda zan nemi alfarma agurinka kayi mun, dan haka tashi kafita karka 'batamun rai.


Ahankali *Abba* yamike cikin sanyi jiki yace ayi hakuri nabarku lafiya, rai bace *TAUFIQ* yace MD kaje abakowa albashinsa cikin rawan jiki yace to yallabai, kuma daga yau wata yana karewa aringa bawa kowa kudinsa ok yallabai angama insha'allah,


sannan yafita da sauri yayinda *TAUFIQ* din yamike tareda d'aukan wayoyinsa da yazube akan table din, yana me cewa pls *T J* tashi muje dan Allah gaba daya mutumin man yagama 'batamun rai wlh, murmushi yai tareda dafa kafad'arsa yace karka bata ranka abanza saboda talakan da bashida wani daraja dakima, ajiyar zuciya yasauke tareda cewa haba *T J* yaza'a yana megadina naje neman abu gurisa?..


shi har meyake dashi dazanje nema eye?....yakarasa fada cike da jin haushin *Abba*, *T J* yace kyaleshi da Allah bashida komai sai tsiya, tsaki *TAUFIQ* din yayi tareda cewa aiko dai dan Allah ni muje annex safara nasake tattaunawa da bakina idan nasallamesu, sai mud'an zagaya gari nayi kewar kwari makwancin riki, yakarasa dasakin murmushi yayinda cikin dariya *T J* yace aha!kwarin da baruwa *TAUFIQ* yakarasa dayaci mutum ba, suka tafa sannan suka fita.


********
Aranan dakyar *Abba* ya'isa gida saboda zazza'binsa dayatashi sosai, inda ya'iske *Inna* da *TASLEEM wacce tuni tadawo daga islamiya, kamar kullum da saurinta karasa gurinsa tanayi masa sannun, dai-dai lokacin da yagama jingina mashin dinsa cikin karfin hali yasakar mata murmushi, tareda kama hannunta yana cewa yauwa *TASLEEM* din *Abba* sannu, ya islamiyar?...da sauri tace alhamdulillahi! *Abbanah* yajiki naji hannuka dazafi sosai.


Yace "eh wlh zazza'bin nan yamatsamun sosai, tace sannu *Abbana* dai-dai sanda suka karasa gurin da *Inna* take zaune akan tabarma, shima *Abban* zama yai tareda taimakon *TASLEEM* wacce itama tazauna agefensa, tanayi masa sannu inda itama *Inna* take yimasa sannun tareda kallonsa cike da kulawa, tace ashe kuma zazza'bin yasake dawowa?...ya amsa cikin jin zazza'bin dafad'in eh wlh, tareda yasaka hannu acikin aljihu yaciro kudi ya'ajiye agabansu tareda cewa yau anbamu albashi.


Cikin sanyi murya *Inna* tace to madallah! Allah yasa masu albarka, yace ameen! yayinda *TASLEEM* take kokarin mikewa tareda cewa *Abba* bari nakawo maka abincinka, da sauri yace a ah! *TASLEEM* bana bukatar abincin nan kunu dai nakeso ki dama mun, da sauri tace *Abbana* bari naje nadama maka kaji?....to yar albarka.


"Nan da nan *TASLEEM* tadamo kunu takawoma *Abba* saida tafiffita masa tukun nan tabashi, har zata tashi yace ta zauna tokoma ta zauna inda yasha kunun sosai sannan yature, inda yace "da'ita tadauki kudin takirga nan tadauka takirga dubu ashirin ne cif!, cikin sanyin murya tace *Abba* dubu ashirin ne, yace yauwa to cire dubu goma biyar abiya sale me shago bashinsa dayake binmu, biyar kuma sai ya'ishemu siyi kayan bincinmu kafin karshen wani watan ko?...tace eh *Abba*, yace yauwa to sake cire dubu uku kiba *Innarki* ta'ajiye dubu bakwai kuma sai kije ki siyo takardan shiga makarantar ai haka ne kudin ko?...


Cikin sanyi jiki tace *Abbahna* nidai dan Allah abar maganan makarantar nan tukun har kaji sauki, yace karki damu insha'allah zanji sauki yanzu kije ki adana kudin har gobe kinji?...tace to jiki asanyaye tareda tashi tanufi d'aki, say tun karin tashiga d'akin taji yinkurin amai dasauri tajuyo inda taga *Abba* tsugunne yanata sheka amai sosai.


Da sauri takarasa gurinsa inda tafara rero masa sannu cike da tsananin tausayinsa itama *Inna* tanayi masa sannu, kai kawai yake d'aga masu saboda sosai yakijin jiki, saida ya amayar da dukkan kunun dayasha har yazoma baya amankomai saidai yinkuri kawai yakeyi, wanda kafin kace wani abun tuni harya galabaitai *TASLEEM* taso suje chamins amma yace a ah! akwai maganinsa tad'auko mashi yasha, nan tad'auko masa yasha inda har yasamu barci.


Saidai cikin dare misalin karfe biyu nadare zazza'bin yatashi sosai, atakaice dai haka suka kusan kwana raye batareda suyi wani barcin kirkiba, saboda sosai *Abban* yakejin jiki domin hattada hannusa baya iya d'agawa,yayinda *TASLEEM* taketa kuka cike da tausayin *Abbanta*, inda cikin kukan tace *Inna* gobe mukai *Abba* asibiti kinji?...cikin sanyin jiki domin gaba d'aya ta tsinke da yanayin dataga mijin mata yana ciki, tace to Allah yakaimu amma kidaina kukan nan haka kinji ko?... tace to *Inna*.


******


Dan haka gari nawayewa sallah asuba kawai *TASLEEM* tayi wanda tana ta'idarwa, batareda tatsaya yin wasu ayyukanda tasaba yiba taje takira me dai-dai sahu suka dauki asibiti, inda cikin cikin lokaci kankani aka bashi taimakon gaggawa bayan anfito yana barci inda aka kaishi d'akin hutawa, wanda take aka chajesu kudi dubu goma ruwa da magunguna hadeda allurai, nan taka *TASLEEM* tadauki dubu goman nan tabayar kwana biyu balaifi *Abba* yaji sauki inda aka sallame su, suka koma gida.


*******
Saidai bayan kwana biyu sai ciwon *Abba* yatashi, inda sannun ahankali ciwo sai cigaba yake gashi basuda kudin siyan magani domin sauran kudin dake hannusu duk yakare, sai aikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login