Showing 27001 words to 30000 words out of 48594 words
Chapter 10 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt
na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
""""""""Iya habi kina nufin nan ne gidan *Alh TAUFIQ RASHIN TAFIDA*, hamshakin me kudin nan da sunashi yai fice gida da waje?...tace aikuwa dai nan ne kika samu aiki, wani murmushi *TASLEEM* tasaki mekama dayake tace ikon Allah kice gidan arziki nafad'a?...,tace "eh kedai wlh aimutanan Allah yaimusu arziki sosai mu madai Allah ya azirtamu, cikin sanyin murya tace ameen tareda ciro lemon kwalin da ayaba nono d'aya da abarba gida d'aya tabata, tareda cewa iya Habi ga wannan kema kita'ba hajiyarce tabani nayi bud'e baki kinsan yau alhami.
"Cike da jin dad'i tace "eh haka ne kuma kai madallah *TASLEEM* nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi yabada ladan bauta yakuma ba "mahaifinki lafiya tace ameen iya Habi nima nagode sosai, da hanyar dakikai mun nasamu aikin da zamu ringa samun abinda zamuci, harma musamu kudin siyawa *Abbanah* maganin, wanda yana d'aya daga cikin abinda yasama na nemi yin aikatau din domin murufawa kanmu asiri tunda Allah ya jarabi me tallafe damu da lalura.
Cike da tausayi iya habi tace hakane ai insha'allah zaki samu, kilama idan kika fad'ama "hajiyar ta taikama maki da kudin maganin, shuru tad'anyi kafin tace a ah! iya habi kinsanfa halin masu" kudin nan bakowa suke taimakamaba sai wanda sukai niyyi, tace "eh haka ne kumafa yauwa to kingani saboda haka bazan fad'a "mataba kedai kawai bari nayi aikin idan tabiyani, sai mu siyi magani kawai ko?.. tace "eh to hakan ne tace yauwa to ni natafi tace to sai anjima asha ruwa lafiya kigaida *Abban* naki dajiki zayaji insha'allah.
*******
*TASLEEM* kam tana fita tayi tsaye abakin kofar gidan cike da mamaki tafurta tafd'ijam, wato gidansu wannan d'an rainin hankali mutumin da baya kaunar talakawa nasamu aiki?..., kenanma shine wannan mutumin damukai sa in sa ni dashi?...haba shiyasa naji yace" ni yar talakawace humm! idan ko haka ne daga yau nabar aikin nan bazan sake zuwa ba, ko dakuwa shikad'aine aikin dazaya taimakawa rayuwarmu nida iyayena, domin kuwa bazan juri walakaci d'an rainin hankali mutumin nan ba takarashe fadi da jan tsaki mtsw!..,saboda yanda taji haushin *TAUFIQ* din yasake shiga ranta.
"Har tafara tafiya da niyyar shiga gidansu sai kuma ta tsaya chak!, saboda yanda taji wata zuciya tace mata lallaima idanko kikai hakan kin tabbata shashasha,domin kuwa ai aiki agidan nan shine zaya baki damar rama cin mutumcin da "yake shukama talakawa yan'uwanki" cikin ruwan sanyi, "musamman yanda yakebawa su *Abbanki* wahala gurin biyansu albashisu".
"Murmushi tasaki me matukar kayatarwa har saida ushiryarta yabayyana, wanda yake nuna sosai taji dad'in shawarar da zuciyarta tabata hakan yasa tace yes!yes!!yes!!!., *TABID* kake ko *TAFIQ* nema Oho!, koma dai menene sunanka insha'allah sai nagasa maka gyad'a ahannu, badai ka tsani talaka baka kaunarsa ba to ga yar talakawa nan gareka wacce sai tazame maka karfen kafa arayuwa, takarashe dajan kuta sannan tashiga cikin gidansu fuskarta dauke da matsananci farinciki tayi sallama.
"inda *Inna* ta amsa wacce ke zaune tsakar gida akan kujera yar tsugunne ta rafka uban tagumi, alamar tana cikin damuwa, amma kuma ganin dawowar yar tilon yartata lafiya yasata sakin fuska tareda cewa a ah! yan aikatau ne akadawo?....ciki dariya tace eh *Innata* nadawo, sannun da gida.
Tace yauwa sannun ya aikin?...tace lafiya lau *Innata* yajikin *Abbanah*?...takareshe fadi tareda ajiye laidar hannunta agaban *innan* dai-dai lokacin da *Innar* tace lafiya lau jiki kam saidai ace alhamdulillahi, tace Allah sarki *Abbanah* bari na gaidashi har zatawuce sai kuma tace bari na d'aukar masa ayaba da lemu, nan tadauka tareda nufar d'aki tashiga da sallama ahankali inda ta'iske idansa arufe da alama yai barcine.
"Tsugunnawa tayi gabanshi cike da tausayin halin dayake ciki, ajiye su lemun tayi agefe tareda kama hannusa tari tana kallon fuskarsa datayi fayau irin tamarasa lafiyan dasukejin jiki, ahankali tace sannu *Abbana* yajikin?...ahankali yabud'e idon yakalleta tareda sakar mata murmushin karfin hali, hakan yasa tasake masawa kusada shi sosai fuska d'auke da annuri tace eyya *Abbana* yi hakuri kana barcinka natayarda kai ko?...
Kai ya girgiza mata ahankali yafurta a ah! yar *Abbanta* daman banyi barci ba, tace Allah sarki sannu to yajinki?...da sauki kin dawo?....,fuska sake tace "eh *Abbanah* nadawo kuma alhamdulillahi gidan babu wata matsala matar tanada matukar kirki wlh bakaga yanda tadauke niba kamar yar cikinta,
kaga wannan ma "Ita ce tabani nayi bud'e baki takuma bani dubu daya da dari biyar nahau mashin, kagansu nan taname nuna masa cikin muryar marasa lafiya yace to madallah! angode sai kikaima *Innarki* ta adana, nakuma jidad'in jin hakan domin basan awulakanta mun "ke, ko dai-dai da kwayar zarrane.
"Dan hakama kikaga bansoki da aikatau din nan ba saidan babu yanda zanyi tunda banida lafiyar nemowa, domin kinga aiki agidan masu kudin nan humm! babu dad'i *TASLEEM* musamman idan akai rashin sa'a da "uwayan gida irinsu ubangidanmu Alh *TAUFIQ TAFIDA* shida manajansa, abun babu dad'i domin ko kad'an basusan darajar mutane ba musamman talakawa dasuka mai dasu tamkar wasu bayinsu".
To amma kuma yanzu dakikazo mun da wannan maganar cewa aimatar gidan tanada kirki "takuma kar'beki hannu biyu sai naji dad'i sosai, dan haka kikula dakanki" dan Allah nasan *TASLEEM* din *Abbanta* me kamun kaice sosai to amma inason takara tatsare mutuncinkanta danamu, tajiko?...
Cikin sanyi murya tace insha'allah *Abbanah* zan kiyaye da hakan, yace yauwa to Allah yaimaki albarka tashi kije kiyi shirin bud'e baki, tace to tareda d'aukan ayaba d'aya ta'bare mashi tareda cewa *Abbanah* ga ayaban kaci, tana me nufar abakinsa dashi cikin murmushin yabude bakin tasaka mashi yagutsira, ahankali har yacinye zata kara 'bare wani yace a ah! *TASLEEM* din *Abbanta* ya'isa hakan nagode sosai Allah yayi albarka, tashi kije.
"Tace to tareda mikewa har takai bakin kofar fita sai tajuyo ta kalli *Abban* cikin ranta, tace kayi hakuri *Abbanah* na'boye maka cewa gidansu wannan dan rainin hankali mutumin nasamu aiki, bakuma zan ta'ba bari kasan hakan ba har sai narama maku abinda yaimaku, sannan tafita
tareda d'aukan wata yar karamar kujera akan baranda taje gefe *inna* ta zauna fuska sake tasake fadin *Innata* ya gidan?..
******
"Aban garan *TAUFIQ* kuwa kodaya yafita kai tsaye masallanci yanufa dan yai sallah kasan cewar ankira azahar, bayan ya idar yafito sai yace da direbansa yakaisa d'aya daga cikin gidansa dake fedara lokos, bayan sun isa gidan yafito yanufi cikin falon wanda tsayawa fadin had'uwarsa bata bakine.
Kai tsaye gurin firij yanufa yabud'e yad'ako babban kwalin holandiya milik yabud'e marfin yakafa baki, saida yakusa shanyewa sannan ya'ajiye kwalin akan firij din tareda maida firij din yarufe yanufi kujera two site cike da takaici yafad'a, yana me lumshe tareda sauke ajiyar zuciya me cike da bacin ran akan abinda wannan yar talakawar yarinyar tayi mashi yayinda gefe d'aya kuma yake mamakin karfin hali irin nata.
Sai kuma yabud'e idon abayyane yace a ah! kujimun yarinyar nanfa, ban ta'ba ganintaba sai yau nakuma tabbatar, "ita dinma bata ta'ba ganina ba sai yau" amma tsabar karfin hali ko kuma nace rashin kunya shine tasaki baki tana gayama mun maganganu banza, ko dayake aibata yarba domin 'ya'yan talakawa basuda mutunci yayinda rashin kunya yaimasu kanta.
Humm tabbas ko sai na gyara mata zama yakarasa fadi tareda jan tsaki mtsw!., sannan yasake lumshe ido daniyyar yai barci domin amatukar gajiye yake, saidai kuma me surar *TASLEEM* ce takeyi mashi gizo acikin ido da sauri yabude idon tsawon lokaci, sai kuma yasake lumshewa still "itadin yasake gani hakan yasa cikin masifa wanda yake nuna dakanshi yake yace wai meye haka ne, *TAUFIQ*?....sai kuma yaja tsaki mtsw! tareda cewa mayya aljanar yarinya kawai ni *TAUFIQ* nafi karfinki.
"Sannan yasake lumshe idon wanda saida yai da gaske sannan barci me nauyi yadaukesa, wanda yake cike da mafarkin *TASLEEM* bashi yafarka ba sai misalin karfe hudu darabi na yamma, sannan yatashi aransa yana mamakin mafarkin dayayi da wannan yarinyar.
Tsaki yasake ja akaro na babu adadi yace mayya kawai sannan yamike yanufi wani kayataccan bedroom, wanda yake d'auke da komai tundaga kan gado har zuwa wadrof kayan jikinsa yacire tareda daura tuwul yashiga toilet, yai wanka tareda d'auro alwala yafito yabude wadrof yad'auko wasu kananan kaya riga t-shirt ja me guntun hannu, da wando na jeans sky blue tareda farar vest yasa.
"Bayan yasaka vest din yasaka rigar tareda saka botur dinta sannan yaje gaba mirro yataje kansa da kum tareda fesa turare sannan yafita, yaje yadauki wayoyinsa kan table yanufi masallancin cikin gidan yai sallah yana fitowa kiran *Momma* yashigowa, lumshe ido yana me tsananin kaunarta acikin ransa saida yabari yakatse sannan yasake kiranta, tana dauka sai yai shuru yaname turo baki cike da shagwa'ba kamar yana gabanta.
"Daga chan tasaki murmushin domin jikinta ya'bata yayi fushine, dan haka tace haba d'anlelena fushi kake da *Momman* naka shiyasa naketa kiranka baka d'auka ko?...
Cikin sanyi murya yace a ah! *Mommana* kiyi hakuri banga kirankiba sai yanzu, kasan cewar nayi barci dana tashi kuma ban duba wayarba nashiga wanka bayan nafito naje sallah yanzuma na fitowata kenan daga masallancin, saiga kiranki amma ni ban isa nayi fushi da *Mommana* ba saidai meyasa kikabawa wannan yarinyar gaskiya akaina eye?, alhalin nasanki" duk wanda yata'ba maki yaronki baki taba kyalesa.
Cikin dariya tace to kayi hakuri d'anlelena nikaina bansan meyasa nayi hakan ba, saidai kawai naji *TASLEEM* tashiga raina sosai kuma naga alamar "yarinyar tanada natsuwa da kamun kai, cike da mamaki yace *Momma* yar talakawan kike yaba gaka?...tace to me mana d'anlelena ainaga abun yabawan ne atareda ita.
Har zayai magana tace yanzu dai kazo kaci abincin domin nasan kanan kana fama da yinwa, kafin yasake cewa wani abin tuni har takashe wayar tana dariya, bin wayar yai da kallo sannan yaje yashiga mota direba yajashi suka wuce yana mamakin *Mommansa*, can kuma sai yaja tsaki saboda tunowa da mafarkin dayai da *TASLEEM* ba.
*Washegari*
******
Takama jumma'a babu islamiya dan haka bayan *TASLEEM* tagama dukkan aikin gidansu takarya, misalin karfe goma da rabi nasafe tanufi gidansu *TAUFIQ* tashiga kayataccan falon da sallama inda ta'iske *Momma* zaune afalo tana kallo ta amsa mata fuska sake.
"Zama tayi kusada kafarta cike da ladabi tace sannu hajiya ina kwana?..lafiya lau *TASLEEM* har kinzo?..."eh, Allah sarki to ya gajiya yakuma mutan gidan?...cikin murmushin tace gajiya alhamdulillahi, mutanan gida kuma suna lafiya sunce agaidake to masha'allah ina amsawa.
Yanzu ga abin karin kumallocan na ajiye maki kije ki karya da sauri tace lah! hajiya nakarya agida wlh, au! Allah?..ciki murmushin tace "eh hajiya to shikenan kije ki gyara d'akin "d'anlele, idan kingama sai muyi girkin ranan dawuri saboda yau d'anlele yace" yanada baki tun d'azuma yatafi gurinsu, nasan insha'allah kafin sudawo mungama ko?...tace in Allah ya yarda hajiya bari naje yauwa.
"Kamar jiyan d'akin *Momman* taje tacire hijab dinta, sannan taje ta fara gyara d'akin tanata gunguni amma kuma tsaf tafito suka shiga kichin din, inda cikin kankanin lokaci suka gama girkin misalin karfe shabiyu da rabi bayan duk sun zuba acikin kuloli, sai *Momma* tace ta d'auka takai part din *TAUFIQ* tajere akan dinning table tace to tareda d'auka tanufi part din, taje tajere tsaf kamar yanda *Momman* tace tayi.
Sannan tajuya da nufi takoma part din *Momman*, dai-dai lokacin da *TAUFIQ* zaya shiga part din nasa kasan cewar yadawo amma sai yafara shiga part din *Momma*, yace mata yadawo yana kuma jin yinwa sosai shine tace masa ai abincinsu" yana can part dinsa ankai masa.
to shine zaya shiga Ita kuma *TASLEEM* din zata fito sukai wani irin lafiyayyan karo, har saida tsadaddiyar wayar *TAUFIQ* din tafadi kan tayis da sauri yad'ago kai suka had'eda ido inda tasakar mashi wani irin shu'umin murmushin, wanda yanuna da alama da gayya tayi hakan fuska yad'aure cikin bacin rai yace ke makauniyace ko?....
cike da gadara tace a ah! saidai ko idan kaine makahon, amma nikam ina gani garau barima ka tabbatar da hakan sai kawai ta taka wayar, dakarfi aiko take tabada sautin karan fashewa jikake 'ka'ka'kas!, da sauri yakalli wayar sannan ya kalleta cikin miliyoyin mamaki me d'auke da azababban bacin rai yace.....
Aha! akafta read *TASLEEM* dinku ta'ballo rufa, to muje dai zuwa yanzu za'a fara gashi...
*MEENAL or LUFHAT*
_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page 2️⃣2️⃣-2️⃣3️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.
_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.
*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,
Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
""""""""Ke! wata iri dabbace mahaukaciya ce eye?....cike da bacin rai tace nice dabba mahaukaciyar?...cikin zafin rai yace "eh ance maki dabba mahaukaciyar, idan ba dabba mahaukaciya ba wanene zayai abinda kikai yanzu eye?...har tai magana sai tafasa sakamakon jiyo muryar hajiya tana fadin meke faruwa agurin nan ne eye?...., tace hum!takasan kacemun dabba mahaukaciya tana gama fad'ar hakan sai kawai tafashe da kuka me sauti tareda cewa hajiya marina yai da sauri tace Subhallahi! me kikai masa yamareki?....,
tace wai dan munyi karo wayarsa tafadi shine kawai yazabga mun mari kuma nabashi hakuri, takareshe fadi tareda tsugunnawa da sauri tadauko wayar wacce screengad dinta ne kawai yafashe. Saidai kuma bahaka *TASLEEM* tasoba, sotayi wayar ta tashi aiki gaba d'aya sannan tasakar mashi wani irin murmushi me kama dana mugunta, tareda tamika mashi wayar tana murzan ido kasa-kasa tamkar me kukan gaske.
"Shikam *TAUFIQ* baki da hanci yasaki cikin biliyoyin mamaki yana kallonta, dai-dai lokacin da *Momman* take kokarin karasowa gurinsu, sai tayi sauri sake mika mashi wayar, cikin wani irin mugun kissa wanda *TAUFIQ* zayace tunda yake bai ta'ba sanin akwai irin shi aduniya ba sai yau, murya very low tace sorry yah! *TAUFIQ*. "Cikin fad'a *Momma* tace haba d'anlele meyasa wani lokaci zuciyarka akusa take ne eye?...d'aga kunyi karo wayarka tafadi shikenan, sai ka mareta kuma tace kayi hakuri amma saboda Allah sai kawai ka daga hannu kashara mata mari akan kyakkawar fuskar nan nata, Tareda da kokarin kai hannunta akan fuskar *TASLEEM* din tana fadin mugani injin dai bai tashiba?..., da sauri tace a ah! tareda du'kar dakai kasa tana rufe fuskar cike da tsoron kar hajiya tagano karya tayi, cikin fad'a tace sannun kinji yanzu haka yadace tana me kallonsa ranta alamar a'bace. "Hakan yasa da sauri yakalli *Momman* aikam yaga 'bacin rai karara akan fuskarta, take yaji ransa yai bala'in baci inda yaji tsanar *TASLEEM* yasake d'arsuwa aransa dai-dai lokacin da *TASLEEM* din cikin sanyi murya me nuna cewa "eh lallai bada saninta hakan yafaru ba, tace Allah hajiya bansan yazaya shigowa ba aidana tsaya tukun har yashigon sannan ni nafito, tace karki damu *TASLEEM* na yarda dake shid'in ne wani lokaci bayada hakuri akan abu kad'an. Cikin tsananin 'bacin rai yace *Momma* nikuma baki yarda dani ba ko?....yakarashe fad'i tareda kura mata idanunsa da tuni suka rikid'e daga fari zuwa ja saboda bala'in bacin rai, yanason yaji me zatace aikam fuska had'e tace aibawai nace ban yarda dakai bace kaid'in ne tamkar me zuciya hannu, kai ya gyad'a alamar gaskiya ne tareda lumshe ido yanaji wani irin zafi aransa. Yayinda cikin kissa *TASLEEM* tasake cewa hajiya kuma fa nace mashi yayi hakuri, amma sai kawai naji saukar mari bazato tafadi