Showing 42001 words to 45000 words out of 48594 words
Chapter 15 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt
inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
"""""""" _Why_ me eye?....cikin sakin fuska yace saboda lokacin data bude ido "kaine mutum nafarko data fara gani shiyasa", sake watsa mashi mugun kallo yai cikin masifar bacin rai yace shikenan kuma sai nine zan bata abinci abaki kamar yarinyar goye eyeeee?....yakarasa fadi da karfi me nuna tsantsan bacin ransa akan abinda ake shirin sashi ya aikata dole.
Still murmshin likita Lamir yasakeyi cikin kwantar da murya yace eh! saidai "ita din yanzu tafi yarinyar goye ma rashin sani komai, bakaji nace maka ita fa yanzu takoma tamkar jaririya sabuwar haihuwa,
Wanda ahalin yanzu kai ne zataso ta cigaba da gani akusada ita, sannan duk abinda ka koya mata dashi zatayi aiki idan me kyau idan akasin hakan, kuma duk abinda kace tayi shi zatayi shima idan me kyau, idan akasin haka saboda yanzu tana karkashin ikon kane tamkar yanda uwa take iko da d'anta.
"Da sauri yace a ah kam ni ban hada komai da'ita ba balle tazama karkashin ikona, yace to ko daima menene hakuri zakayi kabata, kumama ai ko bakomai aikaga batada lafiya tana bukarta kulawa sosai dan haka gashi kabata.
Fuska hade yace nifa bazan bata abakiba, yace haba yallabai to wai duk saboda me yasa ne eye?.....cikin fada yace a ah Dr wai yahaka ne kaketa kokarin tilastani yin abinda banyi niyya bane haka eye?...cikin sigar lallashi likita yace yi hakuri bawai inason ttilastaka bane, kawai dai inason kagane cewa "itadin tana bukatar taimako musamman naka", wanda tahakan zaya iyasa tadawo cikin hayyacinta cikin kankanin lokaci.
Har *TAUFIQ* din zaya sake magana *Mamma* tayi masa wani kallo kasan cewar tin d'azu duk abinda sukeyi tanajinsu batace komai ba sai yanzu data kalleshi, hakan yasa yad'an saki fuska tareda cewa ok to naji saidai maganar gaskiya bazan iya bata abakiba saidai zan koya mata tasha da kanta, dariya likitan Lamir yai tareda cawa hakanan ma yayi muna godiya.
Sannan *TAUFIQ* yace ok to kawo yafadi ne tareda mika hannun yakarbi cup din tia sannan ya kalli *Mamma*, wacce tahade fuska alamar ranta baiyi dadi da abinda yayiba, cikin yanayinsa nayi mata shagwa'ba yakarasa gurinta tareda ajiye cup din akan table din ajiye magunguna, sannan yakama kunnansa duka biyu yalanga'be kai yace sorry *Mamma* kisake hada wani cup d'aya na tin kinji?
batareda tace komai ba tasake hadawa kamar yanda ta hada wancan ta mika mashi yakarba tareda cewa godiya me yawa my first Love, sannan yakalli *TASLEEM* wacce tin d'azu take tsaye tanata kallonsa, fuskarsa babu wani annuri ya zauna agefen gadonta sannan yanuna mata bakin gadon da sauri taje ta zauna kusa dashi, sosai har saida kafad'arta ya gogi nasa kafard'ar wanda har saida yasashi yarintse ido saboda jin wani abu tamkar maganad'isu,
hakan yasashi d'an matsawa yaname sake hade fuska sannan yadauki wannan cup din da ya'ajiye akan table yamika mata, karba tayi tana kallonsa batareda yakalletaba yace Oya say bismillahi!,
ahankali tace bismillahi! sannan yakafa cup din abakinsa itama hakan tayayi, sannun ahankali sukeshan tia din tamkar yanda yakesha cike da yanga da isa hakan itama take sha har suka gama, tanata kallon *TAUFIQ* din wanda baya kallonta tin kawai yakesha fuska murtik yana danna wayarsa, saida gaba daya kallon datake mashi yanaji ajikinsa, sosai *TASLEEM* tayi gumin alamar tia yakamata karo ko'ina ajikinta.
**************
"Bayan su *TASLEEM* sun gama shan tin itada mutuminta sai tamika masa cup din yakarba yamikawa *Mamma* Dr yai tafi tareda yin murmshi yace kai! gaskiya yallabai zuwa gaba aikinka zayafi nan kyau sosai, yanzu sauran abinci hararansa yai tareda cewa pls Dr Lamir left this room nagaji da ganinka kaji ko?,
dariya yai sosai tareda cewa ok sorry i will left now but amma before I left pls try t....., da sauri *TAUFIQ* yace bana bukatar jin koma yace ok" ok" to shikenan yafadi yana nufar hanyar fita, still yana dariya yace Allah yabada sa'a "ke kuma *TASLEEMA* Allah yakara maki lafiya.
Hajiya yallabai yakoreni sai anjima idan yatafi nadawo, Tace humm! aikaga danlele tafadi tareda kama kunnansa Allah dai yashirya munshi, cikin shagwa'ba yace auchhhhh! *Mamma* ameen saidai akwai zafi fa sosai cikin dariya tace to sannu danlele na kaji, shima cikin dariyan yace amee yayinda shima likita Lamir yai dareya yana cewa ameen tareda fita.
************
Nan *Mamma* tasake zuba wani farfesun kajin awani filet din tamika masa duka biyu yakarba, ya ajiye tareda cewa thanks*Mamma* sauran ruwan wanke hannu nan tazuba masu kasan cewar komai dazata bukata takawo, yakarba yawanke hannu sannan yamika mata still tayi yanda taga yayi sannan ya'ajiye yadauko filet daya yabata shima yadauki dayan yasaka hannun,
itama tasaka hannun anata ga mamakinsu shida *Mamma* kafin duk yace bismillahi! ita tace tareda dibar farfesun takai bakinsa, wani murmshi yai me kama dana mugunta sannan yace "yafi maki yarinya" kiyi saurin gane karatun, idan ba hakaba zakici bakar wuya ne aha! dan ni babu ruwana saboda ni bazanyi ta zaman koya maki komai ba, tunda nidin ba bawanki bane kuma ba d'an gidanku bane dazan zauna zaman yimaki wahala kinaji ko me kama da aljannu?... kai! ta gyada mashi batareda tafahimci abinda yake nufi ba farfesun kawai take diba tana kaiwa cikinta.
"Yayinda *Mamma* ta harareshi tareda cewa anya danlele yanzu saboda Allah *TASLEEM* "dince me" kama da aljannu?.., dariya yayi me kayatarwa wacce takarwa kyakkawar fuskarsa futowa saida yasake diban farfesun yakai bakinsa yatauna, sannan yace eh mana *Mamma* tayi kama dasu, kai ta girgiza tace kataba ganin aljannun kenan?....ido yazaro tareda cewa a ah *Mamma* ban taba ganinsu ba kuma bana fatan nagansu" koda amafarki na ne,
tace to shine "ita kake danganta tadasu" yace "eh saboda sune akafada sunada tsananin kyau na fitar hankali.
Tace hum! tunda ita kadaice kataba gani me tsakanin kyau dole kace haka ko?...."eh to *Mamma* gaskiya kusan haka ne domin nidai duk iya yawon danayi kasa kasa wlh ban taba ganin me mugun kyanta ba wallahi, yarinya sai kace jinsin aljannu yakarasa fadi tareda karkare kai spoon din farfesun bakinasa sannan ya ajiye spoon din ya mike tsaye, yana goge baki da hankacif din daya fito dashi daga cikin aljihunsa yana kallon *Mamma* wacce itama kallonsa take saidai fuskarta hade tace danlele wai ni kam dai menene hadinka da *TASLEEM* ne?....
kuri yai mata da lulu eyes dinsa dasuka nuna alamun gajiya da maganar *TASLEEM* din, fuska hade tasake cewa danlele dakaifa nakeyi nace me hadinka da *TASLEEM* ne?....ido yalumshe tareda kauda kai gefe ahankali yanda baza tajiba yafurta cewa *Mamma* tsana ne tsakanin mu da'ita, tsanarma irin me tsananin girman nan domin ita ce mutum tafarko data fara shiga tsakanina dake har kika daga mun murya abinda tunda nayi girma baki mun ba, sai haduwar mu da'ita dan haka ida kuma har zata cigaba da shiga tsakanina dake" tasa kinayi mun fada to ko yanzu nafara tsanarta.
"Afili kuma baice komai ba sai dai yajuyo ya kalli *Mamma* fuska ba annuri, wacce 'itama shitake kallo tana jiran amsar da zaya bata akan tambayar datai mashi, saidai batareda yabata amsarba kamar yanda tayi tsammani.
"Saidai kawai yace *Mamma* nifa nafara jin barci dan haka zan tafi gida nakwanta saida safe, idan Allah yakaimu lafiya yakarasa fadi tamkar zaya kurma ihu saboda bacin rai wanda ganin hakan, yasa *Mamma* tad'an rikice domin sosai d'an nata yai mata matukar kwarjini, dan haka cikin sauri tace to to shikenan Allah yakaimu lafiya yace ameen tareda nufa hanyar fita.
Aiko *TASLEEM* tayi saurin rike masa hannu kasan cewar tun lokacin da yamike itama ta ajiye nata filet din ta mike, aikam ciki mugun bacin rai yajuyo tareda daka mata lafiyyayan tsawan dayasa tayi saurin sakin hannusa, yayinda jikinta yadauki rawa tayi tsaye tana kallonsa cike da tsoronsa, nunata yai da yatsa cike da bacin rai yace......
Muje zuwa
_*Assalamu'alaikum masoyana dafatan kuna cikin koshin lafiya Allah yasa hakan amen, ina me baku hakuri dajina kwana biyu shuru kunsan karfan nasara bashida tabbas wayatace taci screen shiyasa, amman yanzu alhamdulillahi na gyara dan haka zaku cigaba dajina in sha Allah nagode sosai da kulawa.*_
_ALLAH yakasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:45 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️
🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_
*Free Book 1*
Page3️⃣7️⃣-3️⃣8️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)
*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.
_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.
*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,
Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,
sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.
_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.
*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.
*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_
""""""""Sai kuma yakasa cewa komai saboda tsabar bakin ciki saidai yai mata nuni da tsaya alamar ta koma, aiko dai tuni tagane abinda yake nufi domin kuwa da sauri tajuya jikinta yana rawa tafara tafiya tana juyowa tana kallonsa, kamar zatayi kuka domin kuwa tuni ta kwa'be kyakkawar fuskarta yayinda shikuma yabi bayanta da harara cike da takaicinta, yanajin aransa kamar yakamata yakarya saboda tsabar haushinta dayakeji cikin ransa saida yaga takai gurin *Mamma*,
"Sannan yaja wani dogon tsaki jikake mtsww! tareda juyawa yafita aransa yana fadin mayyar yarinya kawai.
*TASLEEM* kam tana gamin *TAUFIQ* yafita tasaki kuka tareda hawa kan gadon da sauri ta zauna tareda had'a kai da guiwa tana cigaba da kukanta, yayinda *Mamma* tasauke ajiyar zuciya kasan cewar duk diraman dasukai tana kallonsu sosai take mamakin irin tsanar da "danleleta yama *TASLEEM* din, ahankali tamike daga inda take jiki bakwari tanufi gurinta tayi tsaye akanta tadad'e tana kallonta cike da tausayinta,
sannan tad'ago dakanta inda takurawa kyakkawar fuskarta ido wacce duk tajike da hawaye, murmushi tayi me kamada ya'ke sannan ta tallabo fuskarta da dukkan hannunta, yayinda tasa d'ayan hannu tana goge mata hawayan cikin cigar lallashi tace "Yayanki ne yatafi yabarki ko?...batace komai ba saidai kallonta da takeyi, still hawayan bai daina zubowa akan fuskarta ba yayinda*Mamma* ta cigaba da cewa kyalesa" ai zayadawo ya'iske ni sai nayi masa hukuncin tafiya da yai yabarki kinji ko?....,
dan haka yishuru kidaina kukan kinji *TASLEEMA TA* kwanta abinki kiyi barcinki barima nabaki labari me dadi kinji?...tafadi tareda kwantar da'ita taja bargo ta rufe mata rabin jikinta, sannan ta zauna gefenta tareda sahannu tana shafan kanta ahankali duk datasan cewa ba fahimtarta zatayiba hakan bai hanata fara bata labarin ba, yayinda itama *TASLEEM* din tanutsu tana sauranta batareda tana fahimcitar *Mamman* ba.
Ahaka dai *Mamma* tayi ta lallashinta ta hanyar bata labarai har tayi barci, ajiyar zuciya tasauke sannan tayi mata addu'a ta tofa mata tareda gyara mata gashin kanta cike da kulawa had'eda tsantsan tausayinta, tace Allah yabaki lafiya ameen kidawo cikin hayyacinki kikoma ga iyayanki, wayanda nasan suna can cikin halin damuwar rashin sanin hankalin dakike ciki.
Sannan taje itama tayi shirin barcin bayan tayi alwala tayi sallah shafa'i da wutiri inda ta dad'e tana addu'o'i, musamman akan Allah yaba *TASLEEM* lafiya sai kusan karfe 11:00pm sannan ta kwanta zuciyarsa cike da tunanin tareda tambayar kanta wai meyasa danlele yatsani *TASLEEM* ne haka eye....?,ta dauki tsawon lokaci tana tunani har barci ya kwasheta batareda tasamo amsan tambayar ba.
***********
*TAUFIQ* kam rai amatukar bace yafita daga da'kin yanajin tsanar *TASLEEM* aransa fiyeda tunanin me karatu, kai tsaye yanufi gurin drive shi wanda yakawo *Mamma* kuma dama shine zaya maidashi gidan, dan haka yana ganinsa sai sauri yabude masa gidan baya yashiga yarife sannan shima yaje yashiga yatayar suka bar harabar asibitin yayinda d'ayar motar me dauke da escot dinsa suka take masu baya kasan cewar sun rako *Mamma*.
*********
Saida suka haukan titi sannan cikin ladabi drive yad'an waiga bayasan yace yallabai ina muka nufa...?cikin masifa yace sama muka nufa, jin hakan yasa drive saurin kallonsa ta madubi inda cikin sa'a suka hada ido da drive hakan yasashi zaro nasa idon cike da tsoro gani mugun bacin rai akan fuskar ubangidan nashi, wanda tunda suke dashi bai taba ganin irinsa ba sai lokacin dan hakan bashiri yamaida kallonsa kan tukin.
Ciki girmamawa yace Allah yahuci zuciyarka yallabai dama naga nakan kaika wani gurine, ko majalisa to shine nayi tsammani ko yanzuma zankaika daya daga cikin biyu ne, cikin fada yace ai shine nace sama zaka kaini kaji ko?...da sauri yace ayi hakuro, tsaki yaja tareda cewa idan ina bukatar zuwa bani ke cewa kakai ni ba?....
da sauri driver yasake cewa "eh hakan ne to ayi hakuri nayi kuskere, still tsakin yasake ja mtsww! tareda fadin kaini gida malam jo i need to to rest kaji ko?..da sauri yace ok sir tareda d'an dukawa inda yadauki hanyar ungwarau g r a first 2 ko?....
*********
Koda suka isa gida bai yatsa jiran drive yabude masa kofar motar ba yabude dakansa yafito, fuskana nan babu annuri kai tsaye yanufi part dinsa cikin tafiyar nan nashi me daukar hankalin yammata kai hardama samari, da sauri yana shiga karamin falo ya'iske *T J Turaki* akan kujera three site shi da wata kod'ad'd'iyar yarinya suna romance juna like kamar zasu cinye juna.
Wani mugun tsaki yaja mtsww! cike da takaici yace *T J* wai kai wani irin dan iska yaro ne?….dago kansa yai daga kan kirjin yarinya yakalli *TAUFIQ* da idanunsa dasukai jajir saboda tsabar jarabar dake cinsa, yana murmushi yace to me nayi kuma?...cikin masifa yace ban saniba dan iska yaro namamajo banza kawai, cikin dariya yace kai nawa yanzu saboda Allah bakayi miss dina ba?...
da sauri yace banyi din ba d'an iskan d'an karamin yaro dakai sai shegen jaraba daga dawowar ka, natabbatar ko hutawa bakai ba amma kafara da iskanci saboda kai din jarabbene nakarshe ko?...dariya yasakeyi yace kamar ko kasani wlh ban hutaba saboda amugun matse nake jinake kamar naci babu, shiyasa nafara takan wannan din,
kasan tafiya tareda da "Dad ba dadi domin babu damar kebewa ahole da yammata, masu kayan dadi yakarasa fadi yana dariyan iskanci tareda shafo shafaffan kirjin yarinyar wanda babu wani abin arziki ciki.
Tsaki *TAUFIQ* yasake ja tareda cewa d'an iska yaro kaidai kasani ai Dad yayi mun dai-dai, tunda kai bazaka adana hajiyarka har kayi aure ba, amma saboda tsabar jaraba sai jefata kakeyi duk cikin kazamin ramin da