Showing 15001 words to 18000 words out of 48594 words

Chapter 6 - Kyandir Book Complete By Ameenat Umar Faruq.txt

yafidda tsammani cewa yanada wasu yan uwa aduniya.


"Sosai daddy yatarbesu cike da jin dad'i domin harga Allah yai matukar farincikin ganinsu", inda yaketa kiran sunansu d'aya bayan d'ayan boda Tajuddin boda Fataye boda Biyola, tareda rungumarsu yana fad'in ashe zan sake ganiku?...suma cikin farinciki suke bashi amsa.


Saida sukayi sati biyu sannan sukai haramar tafi inda ya had'ama su shatara ta arziki, tareda damkama kowane ma'kudan kudi yaja jari sannan suka koma ibadan.




"Abinda daddy bai sani ba wani d'an abokin kasuwanci mahaifinsu ne" me suna malam Barau, yaje har ibadan yafad'a masu "cewa aid'an uwansu" yanacan yai arziki sosai, kuma bayada kowa mahaifiyarsa tuni tadad'e da rasuwa, hakan yan'uwanta duk sun rasu sai wani baffansa kwara d'aya shima yatsufa sai ko d'anshi kwara d'aya, wanda shikuma kurma ne bayada wani amfani dan haka suzo suci dukiya haka ne yasa sukazo.


"*""**""""****
"Sai kuma sunnu ahankali sai su boda Tajuddin suka kama zuwa gurin daddy" wanda ba'a rufe sati biyu ukun sunzo, hakan kuma zayai masu shatara ta arziki yabasu sai kuma suka fara shawarar kauda daddy adoran kasa, domin su cinye dukiyarsa wanda kuma malam Barau ne yakawo wannna shawaran, cewarsa mutum me matukar kyashi da bakinciki had'eda hassada wanda dama yadad'e yana bakincikin dukiyar da Allah yabawa daddy.


Dan haka yana kawo "masu wannan muguwar shawara batareda bata lokaciba suka d'auka", tunda damasu dinma suna bakin ciki da dukiyar da Allah yaba d'an uwan nasu nasu gashi kuma duk abinda sukace yaimasu yanayi amma, ahakan sukai kokarin ganin bayansa.


"Saboda haka sai suka fara aika masa da barazana ba tareda sun bari yagane cewa sud'in bane, abinda basu saniba tuni yasan sune shidai dayaga haka sai yasamu lokaci yadauki *TAUFIQ* sukazo kwantagora, inda suka sauka awani gida wanda *TAUFIQ* bai ta'ba sanin cewa daddy yana dashi ba sai aranan.


"Bayan sun huta sai yadauko wasu takardun yace babana wannan gidan nawane bayan megadi babu wanda yasan inadashi, dan haka na mallaka maka shi duniya da lahira duk lokacin dakatashi kazo kazauna.




"Ga takardun gidan nan sannan wannan takardun dakagani takardun dukkan kadarori na ne dana mallaka, nan yabashi yakumace karyasake yabawa kowa, kodasu kawunnasa ne wato su boda Tajuddin, sannan yabashi wata laptop yace akwai sauran dukkan wasu bayanai nasa nasirri acikin nan, da yayi tunanin nasake ba lauyana Lawai to amma sai yaga kamar yafara yima zagon kasa dan haka yabarsa da takardun gidajena guda biyar kawa.


Sannan yasake sanar dashi cewa amma akwai wani "abokinsa tsohon sojaye kuma lauya ne zaya sake sanar da shi sauran komai nashi danke gurinsa, domin shikam yayarda dashi dari bisa dari kuma ya tabbatar bazaya ta'ba cutar dashi ba, yace kaji ko?....Babana inda *TAUFIQ* yad'aga mashi kai domin tuni yake gane dukka maganar daddy nasa fiyeda na kowa.


"Bayan yin hakan da kwana biyu daddy yakwanta yarasu batareda wata rashin lafiya ba, wayyo zokuga tashin hankali agurin *TAUFIQ* yai kuka kamar me domin alokakin yai matukar shakuda daddysa fiyeda tunanin me karatu, wanda har saida hakan yasa yakwanta rashin lafiya sosai kamar zayabar duniya saida yai sati biyu yana jinya.


"Wanda alokacin *Mommace* tayi jinyarsa kasan cewar tazo gaisuwar daddy, wanda itama sosai taji mutuwar tayi kukan rashin ubadan d'anta tareda shiga mugun tashin hankalin, ganin halin da *TAUFIQ* din yake ciki narashi jin dayin magana, kasan cewar tun lokacin da tayi auran tayi fushi daddy batasake bin takansu ba, duk da alokacin taji labarin abinda matar baban *TAUFIQ* din tayi masa sai ko kad'an batayi tsammani abin yaka hakan ba.


"Alokacin tayi kuka sosai inda tayi nadamar barinshi, to amma sai tadangana hakan dacewa hakan Allah yatsarsa mata musamman data kalli yan biyun yarata, kasan cewar alokacin tana goyonsu Hussy wanda ta tabbatar rabonsu" ne yarabata da mijinta uban d'anta, wanda taso fiyeda kanta".


Saidai tana cikin jinyar *TAUFIQ* din aka aiko mijinta bayada tafiya sosai, wato babansu Hussy din wanda ashe dama tabaro bayada lafiya saidai baiyi tsanani ba, kasan cewar tanada "yar'uwar zama sai batayi wani damuwa sosai ba to kuma bayan zuwanta kwantagoran ne ciwon yai tsanani.


Bayan ta tabbatar *TAUFIQ* yaji sauki sosai sannan takoma kano, badan taso barin *TAUFIQ* din ba saidan babu yanda zatayi saboda yan'uwan daddysa sunan nan, wato su boda Tajuddin wayanda sune ke da hakkin rikeshi amatsayinsu na yayanni ubanshi.


"Bayan kwana biyu da tafiyar *Momma* sai su boda Tajuddin, sukace* da *TAUFIQ* yashirya sukai shi chan ibadan yaga sauran dangin daddysa, kai ya gyad'a masu alamar to inda suka shirya suka tafi saidai suna fita garin kwantagora, dai-dai shiga wani kauye da'ake kira rafin gora suka shiga cikin dajin kauyan suka tsaya tareda fito dashi,cikin maganar kurame yake tambayarsu ina ne nan suka kawoshi?....


basu bashi amsa ba sai suka rufesa da duka tako'ina suke dukansa, su shidda boda Tajuddin boda Fataye boda Biyola da yarasu biyu Abdussamad da Kayode,


wayan da suma suna jin mugun haushin *TAUFIQ* din, sannan wani abin mamaki harda Alh Barau hakan sukaita dukansa tun yana ihu har yadaina, inda sukai masa jina jina suka tabbatar yamutu sannan suka tafi suka barshi nan yashe kasa.


****"*"*"**""*
Har yamma lis *TAUFIQ* yana yashe akasa, sai gawani bawan Allah yadawo daga gona yaga mutum kwance magashiya, salati yai tareda daukarsa yatafi dashi gida nan yaimasa wasu yan dabari har yafarfad'o, saidai yaitayi masa magana amma bai tanka masa ba hakan nan dai yayita jinyarsa har tsawon sati biyu.


"Inda yaita samun sauki sosai saidai har lokacin baya magana hakan yasa yafara tunanin kila kurmane, mutumin me suna malam isah yanada yara uku maza biyu audu da sale da mace d'aya ramma wacce, tareda Ita da babansu sukai ta kulada *TAUFIQ* din wanda tunda taganshi taji tana kaunarsa aranta.


"Hakan shima babansu sosai yaji yana kaunar *TAUFIQ* din har cikin ransa, domin yakula yanda natsuwa hakan ne yasa yake bashi kulawa sosai har yasamu sauki sosai, saidai kuma agurin su sale da audu tunda sukaga babansu hankalishi yakoma gurin *TAUFIQ* din sai sukaji sun tsanesa sosai.


Nan suka fara tunanin yanda zasuyi yabar masu gidansu dan haka sai suka bari, bayan baban nasu yaje daurin aure wani kauye, itakuma Ramma taje raka mamasu unguwa sannan suka shiga d'akin da *TAUFIQ* din yake kwance suka fito dashi, cike da tashin hankali yake kallonsu kafin duk yayi wani yinkuri suka rufar mashi da duka, da sauri cikin lallausan muryarsa yafurta kalmar innalillahi'wa'inna'ihaiharraju'um! menayi maku zaku hauni da bugu eye?...


"Cike da mamaki suka kalli juna tareda fad'in shege wai dama kana magana?...,shine sai ayitai maka magana amma kayi banza da muta ne saboda kai ga d'an iskan birni ko?...domin wlh daganinka birni kafito dan haka yau zakaci ubanka,


suna kokarin cigaba da bugunsa ciki zuciyar da takulesa, yace wai kuma kasheni zakuyi kamar yanda "wayan can azzaluman sukayi yinkurin yi eye?...kallon juna sukai sukace au akwai wayanda suyi yinkurin kasheka kenan?....,


banza yai dasu hakan yasa sukace kaga malam mu bazamu kasheka ba zadai mu jibgeka ne koshi saboda ka mallake mana babanmu, yanzu baya kula mu saikai dan haka mukeso ka tattara naka da naka kabarmana gidanmu, ko audu inji cewar sale inda yace kwarai kuwa idan ba haka ba kuma wlh mudin ma saimu kasheka ne.


"Ido yazaro cike da tsoro yace ku kasheni kunsan koni wanene?...sukace mu ina ruwan mu dako kai wanene mudai kawai kabar mana gidamu, cikin sanyi murya yace to zaya tafi amma subari baba yadawo yaimasa godiya sannan yasallame shi, sukace bazasu yarda ba dole sai yatafi domin idan har "baban yana nan zaya hanashi tafiya ne, dan hakan yad'auki d'an abinda yasan nashine wanda baban ne yabashi, har yafito zaya tafi saiga baban yadawo.


cike da mamaki yakallesa yace a ah yaro meyai zafi haka har zaka tafi ba tareda kajira nazo munyi sallama ba eye?...,cikin sanyi murya yace kayi hakuri baba tafiyar tazama dole ne agareni nagode sosai da kulawarka agareni, Allah yasaka da alkhairi insha'allah zan dawo yace to shikenan yaro Allah yasa, amma kafin katafi kafad'a mun sunanka, sannan kasanar dani ko kai wanene.


"Yace baba sunanan *MUHAMMAD TAUFIQ* sannan nidin bakowa bane, nafito fataucine sai na had'uda barayi suka kwace mun d'an abinda ke gareni, sannan sukai mun duka shine katsinceni yace Allah sarki Allah saka maka, Allah kuma ya albarkace ka yatsareka daga dukkan sharrin mutum da aljani, yace ameen, sannan yaciro kudi acikin aljihun rigarsa yabashi yace yahau mota yakarba tareda sakeyin godiya sannan yatafi.


***""*****
"Aban garen su boda Tajuddin kuwa bayan sun tafi sun bar *TAUFIQ*, komawa gida sukai inda suka tsara shirinsu sosai akan duk wanda ya tambayi *TAUFIQ* din, sannan suka fara shirin tattara dukiyar daddy dan su handame, lauyansa suka nema wanda dama daddy yace yana ganin yafara yimasa zagon kasa, inda suka bukaci daya basu dukkan takardun dukiyar daddy dayake gurinsa.


Nan yace zaya basau amma sai shima sun bashi wani abun, basuyi musuba sukace "eh zasu bashi, inda cikin lokaci kankanin akasa gidanje akasuwa har an siyar da gida biyu da motoci uku, sun fara bushasha dakudi.


sai ga sammaci daga kotu ankawo masu, cewa ana tuhumarsu da kashe d'an d'anuwansu sannan sun na saida gadonshi.


Alokacin da suka samu sammaci sunyi mamaki, sannan suka isa kotu kuwa sunyi matukar tsorata wanda yasa saida sukayi matukar girgiza had'eda shiga tashi hankali saboda gani *TAUFIQ*.


Wanda shikan alokacin da yabaro kauyan da suka tsincesa mota yahau yace akawoshi kwantagora, inda yahau mashin kai tsaye yakaishi gidansa wanda daddy ya mallaka mashi megadin yabud'e masa, Kallon d'aya yaganesa bayan sun gaisa yashiga ciki.


"Kwana biyu yai yagama abinda zayai agidan, sannan yasallami megadi bayan yace mashi sai bayan kwana biyu zaya dawo, sannan yafito inda yahau mota yatafi Minna yasauka ad'aya daga cikin gidajensu, baije wancan gidan ba domin yasan suka chan washegari yanemi gidan lauyan da daddysa yafad'a masa,


cikin sa'a kuma yagane inda yaimasa bayanin koshi wanene yace koda baka fad'iba nasan ko kai wanene, duk da cewa ban ta'ba ganinka ba amma naga kamar dakai Alh RASHIDI TAFIDA saidai kuma nayi mamakin yanda akai naganka darai sannan kuma kana magana, alhalin yafad'a mun cewa kazama kurma haka ne ko?


yace "eh haka ne saidai kasan Allah almusauwuru ne me sauya Al'amurasa alokacin dayaso, shine yadawo mun da maganata kamar da.


Yace haka to amma ya'aikai gaka darai amma yau tsawon sati biyu KENAN anata nunaka a t-v cewa ka mutu, wanda kuma tuni mutane sun tabbatar da mutuwar taka, cike da tsananin tashin hankalin*TAUFIQ* yakallesa cikin tsoro yace?....




Muje dai zuwa har yanzu fa ba'a fara komai ba ahaa


*MEENAL OR LUFHAT*


_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[8/10, 8:41 PM] Amina Frnd: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️🌹
🕯️🌹🕯️
🕯️


🕯️ *KYANDIR*🕯️
( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_


*Free Book 1*


Page 1️⃣2️⃣-1️⃣3️⃣


WRITTEN BY


🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
_Kwantagora_


Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)


*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.


_*SADAUKARWA GA*_
Iyayena abin alfararina wayanda banida kamarsu duk duniya, kasan cewar sune silar zuwana duniyar nan, ina rokon Allah yakara maku lafiya da tsawon rai me albarka, yabaku abinda kuke nema na alkhairi duniya da lahira, ina kuma yimaku fatan gamawa da duniya lafiya ameen ya rabbi.


*_KYAUTA_*
Wannan littafi na DAYA gaba dayansa na kyautar dashi ne, ga dukkan masoyana inayinku over kamar yanda kukeyi na, godiya marar IYAKA na irin kaunar dakuke gwada mani, wanda kalaman bakina sunyi kad'an gurin gode maku, saidai inai maku fatan alkhairin aduk inda kuke afadin duniyar nan tamu,


Dan hakan ne na kyautar maku da wannan littafin na 'DAYA ina fatan zaya nishad'antar daku ya ilimantar tareda fad'akardaku, domin kuwa yana dauke ne wata iri yar *SADAUKARWA* me matukar ban mamaki da al'ajabi, sannan ga wata rikitacciyar zazzafar soyayya, inda wani shahararran matashin me kudi da yatsani duk wani *TALAKA* dake duniya tsana me *MUNI*,


sai gashi kwatsam yafad'a matsananci so da kaunar *'YAR* me gadin company sa, wanda yakasance talaka *FUTIK* yayinda Ita kuma duniya ba wanda ta tsaya irin mutumin nan aha! shin yakuke gani tafiyar zata kaya?..,hmm! akwai rikici had'eda chakwakiya is a very romance love story ne aha akwai shanawa fa kar kubari abaku labari, dan haka kudai ku biyoni insha'allah bazan baku kunya ba, Allah yabar kauna.


_*TUKUICI*_
Wannan littafin Tukuici ne ga dukkan wani BAWA da Allah ya jarabeshi da TALAUCI, ya ubangijin mu ina rokon ka dakai mana tsari da kuncin TALAUCI, kaimana ARZIKI me albaraka wanda zaya amfane mu duniya da lahira ameen👏ya hayyu ya kayyu mu.


*_TSOKACI_*
Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.


*_GARGAD'I_*
Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.


✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


""""""""Yah! robbi yanzu kana nufin ni *TAUFIQ* ake tanunawa a t-v cewa na mutu, har kuma mutane sun yarda da cewa "eh na mutum?....,yace kwarai kuwa da gaske ni kaina tun ban yarda cewa ka mutun ba, har takaina yarda din saidai kuma yanzu Dana ganka nafara shakku akan mutuwar taka.


"Da sauri yace Barr kadaina shakku nidin ne dai gani agabanka ban mutuba, yace "eh na yarda kam tunda gakanan agabana ina ganinka da ranka da lafiyarka kana kuma maga sa'bani, yanda mahaifinkan yafad'amun cewa baka magana.


"Amma dakam tuni har na yarda,yayinda nafara tunanin mika dukiyar ka ga yan'uwan mahaifin naka" kamar yanda suka bukata, tun wancan lokacin da yarasun cewa duk wanda yasan cewa kudin mahaifinkan yana hannusa yakawo.


To amman kuma sai banyi hakan ban kasan cewar lokacin da yarasun bana kasar, "kai koda ina nanma bazan kawoba tunda munyi da mahaifika cewa" ko bayan ransa karna sake nabawa kowa dukiyarsa dake gurin na, ko dakuwa yan'uwansa ne idan bakai ba, ko "kai din sai idan kaine ka neme ni dakanka dan nabaka idan baka", sai idan naga baka nemeni bane to sai ni na neme nabaka dukiyarka wacce take mallakinka.




"To saidai kuma alokacin dana dawo kasar na tambayeka" sai akace mun ai kana nan kwance bakada lafiya", alokacin naso zuwa naganka sai wata tafiyar takamani cikin gaggawa, dole natafi wanda nayi sati d'aya.


"Aran da nadawo ne naga anata nuna hotonka gidan t-v wai ka mutu", sakamakon mummunan had'arin mota dakai akan hanyarku tazuwa ibadan wanda achan aka birneka, lokacin danaga sanarwar nan hankalina yayi mugun tashi sosai.


"Alokacin har naje gaisuwa inda suka tambayeni wai meye alakata da mahaifinka?...."nace masu makwacina ne aminna wai to yada yarasu basu ganni nazo gaisuwa ba" sai da kurman d'ansa marar amfani yarasu nazo, nace masu bana kasar ne daga nan sai kuma suka sake cewa wai "yana bina bashine?....nace masu a ah ni baya bina ko sisi.


"Nan dai na d'an zauna inda duk wanda yazo gaisuwa sai sun tambayeshi mahaifinkan yana binsa kudi, kasan meye?....kai *TAUFIQ* yagirgiza alokacin zuciyarsa cike da bakinciki had'eda tsanar yan'uwan mahaifinsa, yayinda Barr ya cigaba magana da cewa ko sau d'aya banji su tambayi shiko ana bin mahaifinka bashiba, inadai kallonsu inda cikin nutsuwa nafahimce su" ko kad'an mutuwar ku" bai damesu ba, face yanda zasuyi mallaki dukiyar da mahaifinka yabar maka kawai.


"Bayan nadawo gida nayi ta tunanin "ayya mutanan nan basuda hannun cikin mutuwar ku"?...,saboda dai duniyar nan damuke ciki cike take da abin mamaki,wato d'an uwankama yana iya halakar daka domin yamallake abinda Allah yahore maka.


Sai kuma ahankali nafara bibiyarsu" kona samu wata hujja akan abinda nake zarginsu dashi, saidai kuma ko kad'an ban samuba, hakan yasa tunanin yanda zanyi da dukiyarka dake hannuna, inda daga baya sai kawai na yanke shawara nakai masu tunda dai sune yan'uwan ku dakeda hakkin cin gadonku, to kaji dalilin dayasa nayanke hukunci kai masu dukiyarka tunda dai an tabbatar cewa ka mutu.


"Alokacin ajiyar zuciya *TAUFIQ* yasauke ransa a mugun bace cikin sanyin muryarsa, wacce take cike da matukar zafi yace barr mutan nan "yan'uwan mahaifina ne amma azzaluma ne, kuma nafara tunanin kilama sune suka kashe mun mahaifina, Barr yace gaskiya nikaina nayi tunanin hakan saidai kuma babu hujja, yace humm barr kasan abinda sukai mun kuwa?...


yace ban saniba amma dai yanzu ka sanar dani har da yanda akai ka kasance araye bayan an tabbatarwa mutane ka mutu.


"Nan dai *TAUFIQ* yafa'a masa duk abinda yafaru, tundaga ranan dasukace dashi yashirya suje yaga sauran yan'uwan mahaifinsa, har zuwa kan dukan da sukai masa suka barshi kwance har zuwa yanda sukai da yayan mutamin da yataimaka mashi.


Barr yace ni nayi tunanin "sunada sa hanun akan lamarika" to saidai tunda banida wata hujja akan hakan dole na kyalesu, nan take yabashi komai na ragowar dukiyarsa dake gurinsa, sannan suka shirya yanda har ka kawo masu sammaci.


***********
Bayan angabatar da wanda ake kara tareda wanda yaikara sai da alkali yabukaci lauyan *TAUFIQ*, yai jawabi, inda yai bayani akan dalilin dayasa yake karansu boda Tajuddin wato sun kama dukiyar maraya sunaci, ko da alkali yatambayesu hakane basu musaba.


Sannan yabukaci da *TAUFIQ* yai bayani, aikam nan hankalin su boda Tajuddin yakaran tashi lokacin da sukaji *TAUFIQ* yai magana, inda "yafad'awa alkali duk abinda sukai masa, kuma dayake bayada hakkisu koda alkalin ya tambayesu" shin hakane?..nan ma suka amsa "eh hakane.


"Dan haka alkalin ya yanke masu hukunci dai-dai da alaifin dasuka aikata, sannan lauyan *TAUFIQ* yace da alkali yanason yashiga tsakanin *TAUFIQ* din dasu, bawai dan araba zumuncin dake tsakanisu ba sai dan kawai bayason su sake yinkurin kashesa, nan alkali ya gargad'esu cewa ko ciwonkai idan *TAUFIQ* yayi akace sunada sahannu sai kotu tadauki mummunan mataki akansu, kunsan bayarabe da tsoro dan haka da sauri suka amsa da sun amince, wanda hakan bakaramin dadi yaima *TAUFIQ* din ba matuka dan haka yabar Barr Usman din amatsayin special Lauyansa.


"Sannan yacigaba da gudanar da rayuwarsa cikin tsananin jarumta yayinda za'ace tana cike da jarabawa, domin kuwa bayan komai yalafa sai kawai yashiga makarantar yan sandan ciki wato *DSS* wanda dama burinsa kenan arayuwa, to amma sai "daddysa yakatsemasa hakan ta hanyan sashi yakaranci business dan hakane sai yashaga school din saboda yacika burinsa nasan zama cikakken *DSS*.


Sannan kuma yafara gudanar da kasuwancinsa da abokan kasuwancin daddysa, cike da kwarewa wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login