Showing 15001 words to 18000 words out of 61588 words

Chapter 6 - AGOLA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Nabila Lawan Zango .txt

dole su raina malamai ko, Falak tace to aide ajinmu basa raina ka, ko? Murmushi yayi yace mace daya ce tagama rai nani , zaro ido tayi tace wacece? Yace Falak ce, da gudu yashige gida tana dariya. Shima dariyar yakeyi, shide harga Allah yanason Falak, sede yana tsoron yafada mata abinda ke ranshi taki amincewa.


Wanene SAMEER?


Sameer dan asalin garin kaduna ne, suna zaune a tundun wada, shi kadai Allah yabama iyayenshi, tunda yagama secondary school mahaifinshi yarasu, daga shi se ummanshi Halima suke zaune agidan, yan uwan babanshi bawani karfi garesu ba, hakan yasa suka kasa daukar nauyin karatunshi tunda result dinshi yafito, duk da mahaifinshi bawani kudi gareshi ba, amma yanada rufin asiri, tunda yanada gidan kanshi, dan karami, aciki suke zaune da Ummanshi, tanayin kosan saidawa da kuma markade, dahaka ta tara kudi tabiyama Sameer kudin makarantar dayasamu A Zariya, cikin ikon Allah yafara karatu cikin sa,a hankalinshi kwance, yake karatunshi, domin Sameer beda hayaniya,mutum ne me natsuwa, ga kokari.


Idan anyi hutu yana koyawa a islamiyya kuma yana zuwa shagon wani abokin babanshi yana aiki, da haka yake tara kudin komawa, Ummanshi tahada mashi da nata.


Dahaka haryakusa gama karatunshi, yanzu haryana shekarar karshe a jami,a wannan karin ne daya dawo bangaren yanmata da koyawa aka bashi ajinsu Falak, tunda yadora idonshi akanta yaji yana sonta sosai, sede ganin daga gidan fatake fitowa yasan tafi karfinshi, amma duk da haka yakasa cire sonta aranshi, Sameer kyakkyawane nakarshe yanmatan makarantar dayawa suna nuna suna sonshi, sede yaki basu fuska, baya magana da kowa, dalilin fara maganarsu da falak akan ciwon Ummanta ne, tundaga nan yasamu damar yimata magana.


Wannan kenan.


Bayan sati biyu da samun saukin Hajjo takara tashi da wani zazzabin, haka kullum Falak take yimata addu,a data sha ciwon yake sauki, bayan kwana 2 kuma yadawo, Ameer kullum ciwonshi kara fitiwa fili yake yanzu kowa yagane Abnormal ne, Hajjo duk tarame tayi baki, Falak ma tarame saboda abu 2 yahade mata, ga ciwon Ummanta ga Exam, damma sunkusa gamawa,


Alh, yarasa yanda zeyi gaba daya beda nutsuwa, sbd ciwon Hajjo, Zarah ma afuska kullum cikin damuwa take, hakan yasa tace ma Mairo takoma gurin Hajjo harseta warke, koda yaushe cikin turama Asabe kudi take domin akaima boka.


Ameer ma yarame saboda baya shan nono sosai, hakan yasa Alh, yace adena bashi nonon sbd zafin zazzabin datakeyi, madara yasiyo mashi Mairo tana bashi, abin yayima Fakak yawa ga malam Sameer takoma makaranta, ko no wayanshu batada.
Ahaka ciwo yayita cin Hajjo addu,a kam tana shanta, Aranar da su Falak zasu zana jarabawar karshe, dasafe tafito cikinshirinta, tashiga dakin Hajjo, kwance taganta, sede ayau setaga tayi haske, sosai.


Zama tayi akusa da ita tace Umma zantafi, kuma yau zamu gama makaranta, kinga se indawo inrika kula dake sosai, kinga Baba mairo aiki yayi mata yawa. Murmushi Hajjo tayi, kamo hannun Falak tayi ahankali tace, Falak bazan dena fada maki akowane hali kika tsinci kanki kiyi hakuri da irin rayuwar da tasameki, kuma inaso duk rintsi kada kijuyama Alh, baya, kome zeyi maki kidaukeshi tamkar mahaifinki, kamar yanda ba,a iya canza uba, haka nakeso kirike Alh, ko bana gidan nan banbaki ikon kibar gudan nan ba, sede aure ko mutuwa, ki kula da kaninki, banaso koda wasa rashin kunya tashiga tsakaninki da Zarah, ko Jidda, nasan aduk gidan nan sune basa sommu, amma Jalila Allah yayi mata albarka, banaso kirabu da ita, itace kawarki kuma yar uwarki.


Kiyi hakuri da rayuwa Falak, zakici ribarta wata rana, inaso kirike Baba mairo, domin nadauketa amatsayin uwa, banida abokin shawara se ita, kema inaso kidauketa haka, nasan bazata iya cutar dake ba. Allah yayi maki albarka, tashi kije kada ki makara.
Hawayen dasuka zuboma Falak tagoge tace Umma insha Allahu zanyi aiki da duk abinda kika ce, kuma zaki samu lafiya kidena fadar haka. Hajjo tace bani biro da takarda, bayan ta aje mata tajuya harta kai bakin kofa takara juyowa, kallonta daga Hajjo nayi, kwalla nafita daga idonta. Shigowar Jalila yasa Hajjo tagoge idonta, Jalila tace Umma yajikin, tace dasauki, Harzakutafi? Tace E, to Allah yabada sa,a.


Kama hannun falak tayi suka fita, biro tadauka tacigaba da rubutu a takardar, tana gamawa mairo tashigo. Hajjo tace Baba mairo duba cikin drowar can zakiga wata zaka baka kimiko mun.


Bayan tabata ne tamika mata takardar data rubuta tace tasaka ciki. Baba mairo, inaji ajikina ciwon nan bana tashi bane, zantafi inbar yarana 2 agurinki, duk da nasan kema bakida karfin rikesu, sede inaso Ameer da Falak sucigaba daza agidan nan, matukar ba, Alh, ya koreta ba, dan Allah ki kularmun da Falak marainiya ce, inaso wannan jakar kiajemun ita harse ranar da aka kai Falak dakin mijinta sannan kibata, idan Allah yasa tayi dacen miji kice kada tazama meboye sirrinta agurinshi.


Duk abinda Zarah zatayima Falak Kibata hkr, tashi kilekamun ko Alh, yashigo, goge kwallan idonta mairo tayi tace Allah yabaki lafiya Hajiya ciwo ba mutuwa bace, tashi tayi tafita.
Tare suka dawo da Alh, danshigowar shi kenan gidan. Kwance suka sameta tana kallon silin bakinta dauke da murmushi, kusa da ita Alh, ya matsa, hannunta yakamo gani yayi yakoma, dasauri yadora kanshi bisa kirjinta, nan ma babu numfashi, jijjigata yashiga yi yana kiran sunanta, amma ina rai yayi halinshi.
Kuka yasa kamar karamin yaro, mairo ma kukan takeyi tana fadin shikenan Hajiya wayyo. Yadade ahaka, kafin yadauki waya yafara kiran kawunshi sannan yakira Farouk da sauran mutane, fita yayi domin kiran Zarah.


Tunda driver yakaryo kwanar gidan taji faduwar gabanta ta karu, tunaninta ne yatsaya alokacin dasuka tsaya kofar gidan taga taron mutane, wasu sunata alwala, da gudu tafito tanufi cikin gidansu, ita da Jalila.


Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[7/13, 09:40] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)


@ ( H,O,N,A)


Part 50....... 55


Alh, tafara karo dashi yana goge idonshi, zeshiga part dinsu, kusa dashi ta matsa tana kuka, tace Dady shikenan narasa Umma ko? Kasa kallonta yayi saboda wani irin tausayinta dayaji, wani sabon kuka yaki yataho mashi.


Kamota yayi, suka shiga ciki, kwance tasamu Ummanta anshiryata cikin lakafani se kamshi takeyi, gefenta Mairo ce da Zarah, se Ameer abisa cinyar Mairo yana ta kokarin jan zanin da,aka rufe Hajjo, kowa kuka, yakeyi, Zarah kamar uwar ta ce ta mutu.


Fadawa tayi bisa gawar Hajjo tana wani irin kuka neban tausayi, seda tabama kowa tausayi, bude fuskarta tayi, gani tayi kamar tana mata murmushi, ahankali tace Allah yajikanki Ummana, shikenan ni kuma haka Allah yashiryomun rayuwata zankare cikin maraici.


Kuka sosai takeyi, Jalila wadda itama kukan takeyi tamatso takamata tana bata hakuri, Alh, yace ku gyara za,a shigo adauketa domin yimata sallah akaita makoncinta,


Daki Falak tashige dan bazata iya ganin tafiyar Ummanta daga cikin gidan ba, haka aka fita da gawar Hajjo, akayi mata sallah, sannan aka kaita makabarta. Tunda suka tafi Falak tafadi asome, su Mairo suka samata ruwa da kyar ta farfado, kafin sudawo Asabe, Dije, Baban Zarah da Jidda suka iso.


Zaune suka samesu afalo, Falak tana gefe guda zaune ita da Jalila hawaye kawai ke fitowa daga idonta, bayan sungaisa sukayi masu gaisuwa. Jidda ta matsa kusa da Falak, tunda ta kalleta, hawaye suka cika mata idonta, bata tabajin tausayin ta ba, seyau, gaisuwa tayi mata, ta tashi tana kuka tawuce part dinsu, dan ita tunda take bata taba ganin abinda yabata tausayi kamar Falak ba, dan zata iya cewa rabonta da ta zubda kwalla tun tana yarinya, batasan zafin mutuwa ba, tanade jin anayinta, shiyasa takasa zama agurin tawuce part dinsu.


Haka aka cigaba dazaman gaisuwa, gaba daya kulle part dinsu Falak akayi, Alh, yasa Jalila da Mairo suka kwaso duka kayan Falak dana Ameer takoma dakin Jalila, Ameer kuma yana gurin Mairo.
Seda akayi sadakar 3 sannan su Asabe suka koma, ita ko Jidda cewa tayi bazata koma ba, don tunda akayi mutuwar gaba daya hankalinta yatashi, ko Al,amin yakirata da sauran samarinta bata dauka, gaba daya tsoron mutuwa takamata, sallah ma yanzu akai akai takeyi, wanda rabonta dayin hakan harta manta.


Bayan sadakar 7 ne Alh, yatarasu afalonshi, Kallon Zarah yayi yace to Hajiya, kema nauyi yakara hawa kanki, duk dade Falak tayi wayon dazata rike kanta, amma duk da haka, dole se anrika nuna mata yanda rayuwa take, inaso kamar yanda kika dauketa ada yanzu ma ki kara daukarta fiye da haka, saboda yanzu, tadawo gurinki, banaso ki nuna bambamci tsakaninta da su Jalila.


Shikuma Ameer tunda Baba Mairo tace abar mata shi, shikenan Allah yabaki ikon rikeshi, amma duk da haka inaso shima kirika lura dashi, Allah yabamu ikon rike marayunshi.


Kema Falak banaso kisaka wani tunani azuciyarki, dan kinrasa Ummanki bayana nufin kinzama marainiya bane, idan baki manta ba, tunda nadauko ku, nayi alkawarin rikeki amatsayin diyata, to haryanzu kina nan amatsayinki na yata, duk wata damuwarki banaso ki boyemun, ko Hajiya, kuma insha Allah idan jarabawarku tafito, zakucigaba da karatunku kafin Allah yakawo maku mazaje, dan bazan ce sekun gama karatu zakuyi aure ba, dakun samu miji zan aurar daku, Jidda tunda Exam dinki batayi kyau ba, naso inbiya maki kiyi acikin su Jalila, kika nuna bakiso, ina tunanin kila aure kikeso, sekiyi kokarin fitar da miji.


Ina fatan kuma zaku cigaba da zuwa islamiyya dan nasan wasu dasunyi candy shikenan sunyaye islamiyya, kunga gab kuke da sauka, sekudage ku hada karatunku gaba daya, Jidda kedama tunkafin kigama makaranta naji labarin kindena zuwa islamiyya agurin shugaban makarantarku.


Inaso infada maki duk wata tarbiyya nabaki amatsayina na uba, duk da naksance ba mazauni ba, amma nasan hajiya zata iya, kula daku, sede nasan yaran zamani, ina shawartarki dakiji tsoron Allah, kina ganin de yanda muka rasa Hajjo, agidan nan, kuma shikenan, bazata kara dawowa, ba sede alahira, naso ace mata suna zuwa makabarta kai gawa, dakunga yanda aka gina rami dan karami aka saka Hajjo aciki, babu komai acikinshi, daga ita se halinta zasu zauna aciki, idan tayi hali mekyau, Allah zekara buda mata kabarinta, idan kuma sabanin hka , Allah zesa kabarin yakara matseta, har hakarkarinta suna shiga cikin yan uwansu.


Wlh babu abinda yafi kabari duhu, sallarka ce kawai zata zama haske acikin kabarinka, idan kana yinta da kyau, ina kara tunatar daku kuji tsoron Allah, domin duk abinda mutum ya aikata zeje yasamu abinsa yana jiransa. Alhamdulillahi, ina kyautata zaton Rahma agurin Hajjo, saboda takasance mace tagari, kuma tana ibada sosai, batada abokin fada, bata taba batamun ba, aduk zaman damukayi.


Allah yajikanta da rahma, Allah yasa sanadiyyar mutuwarta yazamo mana shiriya akan halayen mu marasa kyau. Zaku iya tafiya, hawaye ne kawai suke zarya afuskar Alh, shima yakasa tsaidasu, kowa agurin kuka, yakeyi, Jidda kuwa jitayi kamar tafada ma Dadynsu abubuwan datakeyi yaroka mata Allah shiriya,sede tanajin kunyar fadar irin laifinta agaban mutane, sede tayi alkawarin komawa islamiyya, domin neman ilimin dazata tuba dashi.( ni kuma nace Allah yasa ba tubar mazuru zakiyi ba Jidda, nasan dan adam da mantuwa).


Haka suka cigaba dazamansu acikin gidan gwanin ban sha,awa, Baba Mairo tana kokrin kula da Ameer dan yanzu yayi wayon sede kullum doloncinsa kara fitowa yakeyi, haryanzu ko zama befara ba, sbd kanshi baya tsayawa.
Falak da jalila sukeyi taya Baba mairo aiki dan surage mata wahala, Jidda kuwa dama bata iya girki ba sede gyran daki da falo, kuma shine aikinta. Zarah kullum cikin jin haushin irin yanda Alh, yakeyima Falak da Ameer take, gani take yanzu ,ya,yanta ma sune wararru agurinshi, kome yasamu yace Ameer, akwai wani katon mall daya bude. Suna Ameer yasa, bakaramin jin Ameer yake acikin ranshi ba, gani yake kamar yajawo girmanshi koze fara fita dashi yana tayashi aiki,


Hakan dayakeyi bakaramun kara wutar kiyayya yakeba azuciyar Zarah, kuma tayi shiru ne, kawai tana jiran dan lokaci, mutuwar takara nisa. Jidda andage dazuwa islamiyya duk da ba ajinsu daya dasu Falak ba, amma batajin kunyar shiga cikin kannanta.


Duk abinda bata ganeba, su Falak suke nuna mata agida, bata zuwa ko ina daga makaranta se gida. Al,amin bakaramin shiga tashin hankali yayi ba, saboda rashin Jidda, duk cikin yan matanshi, ita kadai yakema so metsanani, idan yakirata bata dauka, gashi dama can tahanashi zuwa gidansu,yarasa yanda zeyi yasameta, har kawarta Ameera yasa taje ta dubo mashi ita, amma koda taje tasamu Jidda ta tuba, tafara kawomata maganganun banza seda sukayi fada da Jidda, Haka tafito ranta abace. Data fadama Al,amin shima beji dadi ba, yasan tunda Jidda tadena yin harka shikenan bazata kara sauraronshi ba, haka yacigaba da kiranta, amma shiru.


Jidda ce zaune adaki, tadauko jakarta zata bama, Jalila kudi tasiyo mata, kati, murmushi tayi aranta tace wai yau nice dasiyan kati, lallai mata sunyi sanyi, dubawa tayi sede babu ko sisi aciki, tashi tayi taje gurin Umminsu tace Ummi dan Allah bani 500 Jalila tasiyomun kati.


Wani mugun kallo Zarah tayi mata, batasan dama cike take da ita ba, saboda wannan sabon halin data sake, gashi yanzu ko kudin datake samu hartana bata yanzu babu, gashi yau dan tabewa kudin kati ma suna gagararta.


Ummi ina magana kinyi shiru, Bazan bada ba, ko dole ne? Tunda rayuwar da kika daukarma kanki kenan, talauci ma yanzu kika fara, wata rana ma se kufin siyen turare sun gagareki, tunda dole se Alh, yazo gari sannan yake baku, suma kuma bawasu masu yawa ba, tunda yace bayason saba maku da kashe manyan kudi wai saboda gidan wani zaku.


Wlh kwandalata bazan baki ba, fita kibani guri. Amma Ummi bekamata kifadamun haka ba, kinmanta abunda nayi maki ada, amma yau saboda nace kibani 500 kike fadamun magana,,, saukar marin dataji ne yasata yinshiru.


Fita tayi tabanko kofar tanufi dakinta tana kuka, lallai tayarda sekana dashi kake zama wani abu agurin kowa. Wanka tashiga, sabulun nata ma yakare, ita kuma tafisonshi, dan Jidda babu abinda ta tsana irin taga jikinta yana baki, duk da bawata fara bace amma da tsiya takoma fara, haka tayi wanka da sauran sabulun daya rage tafito, manta ma saura kadan turarukanta duk sun kare, gashi bata saba da shafa turare daya ba.


Gaskiya bari Dady yazo gobe yabamu kudin siyan kayan shafa, bazan iya zama babu kudi agurina ba, wlh.


Saye suke akitchen suna girki, jalila tace wai ni Falak naji ko maganar Mal. Sameer bakiyi, kode harkin manta dashine? Hararta Falak tayi tace meye tsakanina dashi dazan tambayeshi.
Jalila tace ai naga kedin tadaban ce agurinshi, kozakicemun bakisan mal. Sameer yana sonki ba? Falak tace kede makaryaciya ce wlh, kawai daga muna mutunci dashi zakice yana sona, shida babu ruwanshi, da kowa, kilama yanada budurwarshi yar jami,a mezeyi dani. Jalila tayi dariya tace uhm kede fadi gaskiya gashi nan harkin fara kishinshi, ruwan dake hannunta akofi ta watsa mata, fita tayi tana mata dariya. Rufe ido Falak tayi, ita kanta tasan tayi missing mal. Sameer, ta dade da fara sonshi, sede bata son tafara fada mashi ya wulakantata hakan yasa tahakura.


Zaune suke afalon Alh, suna fira, jidda tace yauwa Dady wlh kayan kwalliyarmu sunkare, dariya yayi yace to Mamana yanzu kuwa za,a baku, koda yake kekadai zanba tunda nakine yakare, jalila da Falak sukace a,a Dady hadamu. Wata irin harara Zarah ta watsa ma, Falak jin yanda take wani zakewa kamar ba AGOLAH ba. Tsaki taja har seda yafito fili, kara gyarama Ameer zama yayi akan cinyarshi, ya kalleta yace yade da tsaki, murmushi tayi tace Allah Alh, kai ke kara shagwaba, yaran nan, yan matane fa amma ace haryanzu kaine zaka rika basu kudin kayan kwalliya, ai gara ma abama Ameer dina shine yaro.


Dariyar jin dadi yayi yace a,a ki kyaleni da yarana, suma agurina yarane, kuma hakkin uba baya sauka daga kan yayanshi harse ranar daya aurar dasu, hakan yake hana mata karbar abun hannun samari, wanda yawanci shine yake jansu zuwa ga halaka, kuma da wannan damar samari suke amfani gurin yaudarar yan mata. Dubu goma goma yabasu, yace suje su siyi abinda sukeso, dubu goma ya mikama Jalila yace ansa ki kaima Baba mairo, na ameer ne, shima asiya masa kayan dadi, wata 5 yaciro yace tabata itama tasiyi abunda takeso.


20k yamika ma Zarah yace kema uwargida ganaki, hadiye bacin ranta tayi, ganin yan kudin da yabata, bam bancin 10k ne tsakaninta da AGOLA, da kuma dan karamin yaro, wanda ada Alh, seyabata 50k kawai na kayan kwalliya, gaskiya dole ma tasake tsari, seta cire Falak Da Ameer azuciyar Alh, shima sena maidashi rakumi da akala.


Jidda ce tafito zata kasuwa dan su Jalila sunce se gobe zasuje, gashi driver bayanan, ita kuma bazata bari se gobe ba, tafiya take zataje bakin titin domin tarar abun hawa, se sababi takeyi, yama za,ayi 10k ta isheta siyan kayan shafa, to mema zansiya, 10k ai basu kai kudin man datake shafawa ba ma, bare akai gurin sabulai, da turaruka. Gaskiya dasake wlh,,,,, karar horn dataji ana yimata ne, yasata tsayawa, Al,amin ne yafito har yana tuntube ya iso gurinta fuskarshi dauke da murmushi. Bayan sungaisa yace haba Dear meyasa zakimun haka? Jidda tace muje cikin mota muntsaya bakin titi kada Dady yagammu.


Tafiya sukeyi hannunshi cikin nata, tawani lumshe ido, ita kanta tasan tayi missing Al,amin. Yace ina zakije haka cikin rana? Tace. Wlh kasuwa zanje siyan kayan kwalliya. Murmushi yayi yace haba ba girmanki bane zuwa kasuwa, ina laifinma kije mall aizefi. Aranta tace idan kudina sunkai shiga mall ko. Karya kan motar yayi zuwa wani babban mall, suna tafiya yana fadimata irin yanda yayi missing dinta, har suka isa.


Siyayya yayi mata takusan 100k, duk abinda batada shi seda tadauka, azuciyarta fadi take Allah nagode maka daka kawomun Al,amin dabansan yanda zanyi da 10k ba wlh. Haka suka fito suka shiga mota yakalleta yace Baby muje gidana mana nayi missing dinki fa, kallonshi tayi tace Dady na gari fa, kashe mata ido yayi yace just 1 hour plsssss, yana kamo hannunta, murmushi tayi tace ok badamuwa muyi sauri. ( Wa iyazubilla, Allah katsaremu daga sharrin zuciya, dason kudi, domin abinda yake faruwa kenan azamanin nan, rashin godiyar Allah, mutane basa taba godema Allah, daga abinda yabasu duk mun kadan dinshi, hangen nawasu shine yake kara dulmiyar damu zuwa ga halaka. Allah kacire mana son zuciya, ameen.)


Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[7/13, 09:40] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)


@ ( H, O,N,A)


Part 55.....60


Tundaga ranar Jidda takoma ruwa, fiye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login