Showing 60001 words to 61588 words out of 61588 words

Chapter 21 - AGOLA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Nabila Lawan Zango .txt

dana sanin abun ba.


Shiru yayi Baba Mairo tace gsky Alh, nima ina maka sha,awar auren Halima, nina zauna da ita kuma kasan bazan zaba maka abinda ze cutar da kai ba. Amma me kace? Alh, ya sosa keya yana murmushi. Kawu yace shikenan nagane, kuma naji dadi daka amince, insha Allahu kasamu wadda zata share maka hawayenka, Allah yabada zaman lafiya, kuma insha Allahu nan da asabar mezuwa za,a hada dana mal. Garba, kaga tsohon sirukinka da kai zaku Angwance arana daya. Dariya Alh, yayi yace kai kawu. Godiya yayi masu.


Haka Baba mairo tasamu Umman Sameer da maganar, amma da kyar ta amince, dan cewa tayi tana jin kunyar Zarah, Baba Mairo tace bakomai zanyi mata bayani kuma nasan zata amince. Zarah wadda take jin duk abinda suke fada dan tazo zata shiga falonsu taji suna magana. Kuka kawai takeyi tana kara tsanar Asabe da kuma irin halinta, share idonta tayi, tayi sallama tashiga, bayan tazauna tace Baba Mairo kuyi hkr naji duk abinda kukace, nazo shigowa naji kuna magana amma wlh ba labe nayi maku ba. Umma kada kidamu babu komai, koma menene nina jama kaina, kuma zanfi son ace kece kika auri Alh, akan yaje waje yasamo wata, Allah yabaku zaman lafiya. Fita tayi tana kuka. Baba mairo tace tokinji abinda tace, Halima tace shikenan, Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi.
Baba Mairo tace amin, dan haka kinga saura kwana 5 daurin auren kuma da an daura zaki tare, dan haka dole ingyaraki dan bawai tsufa kikayi ba, kawai rashin gyarane, murmushi tayi ta tashi tafita. Kowa yaji dadin wannan hadi da akayi, duk da Jalila bataji dadi ba, amma kuma taji dadin da akace Umma Alh, ze aura dan tasan halinta.


Haka akayita shirye shirye Umman Sameer cikin kwana 5 tayi kyau sosai tafito mace me kyau, dan komai yana son gyara. Sameer se tsokanarta yakeyi yana cewa dama Ummanshi tana da kyau amma batason yin kwalliya, itade sede tayi ta murmushi. Sameer yazo gurin baba Mairo shida saleem yace gsky Baba ana daura auren su Umma nima zandau matata mukoma gida, dan gsky abun da kunya. Saleem yace hakane Baba dan Allah kibarsu su koma. Tace to ai shikenan, dama ita nake tausaya mawa, tunda kace ku koma se kutafi amma wlh karika dawowa dawuri, yace angama Baba Mairota. Dariya tayi, sukayi mata godiya.


Ayau asabar aka daura auren Alh, Abba Bala da Halima kan sadaki dubu 30, se Mal. Garba da Samiyya suma sadaki dubu 30, kuma aranar aka kai kowa gidanta, Kawu yayi kokari na gyran gidan Mal. Garba, gashi Alh, yabude mashi babban provision store, haka aka kai amarya Samiyya sede ance yaranta sedaga baya za,a kawosu.


Halima ma Alh, yasa mata kaya adakin Zarah, ita kuma aka maida mata kayanta can part dinsu, akace idan su Falak suntafi seta koma dakin falak, aranar zarah ko abinci bata ciba, tana dakinta takasa fitowa, kuka kawai takeyi, seda tabama kowa tausayi, amma kuma ita tajama kanta.


Bayan kwana 2 da biki Sameer yadauki matarshi suka koma gidansu, wanda yakara shan gyara kamar wata sabuwar amarya, tayi mamaki sosai ganin irin gyran da yayima gidan, haka suka bude sabuwar rayuwa.


Haka rayuwa tacigaba da tafiya cike da jindadi Alh, yanajin dadin zama da Halima, shikanshi yasan yanzu yana cikin kwanciyar hankali, har mantawa yakeyi dawata Zarah, dan koyaje gaida baba Mairo bata barin su hadu, shima baya nemanta, yana bama Baba Mairo girma sosai kamar ita ta haifeshi, kuma yahanata yimasu girki, yacika masu store da komai na abinci yace suyi iyakar nasu, bayaso ta wahala. Jikin Zarah kam ya warke, har ancire daurin kafar tazama dungulmi, sede haryanzu bata maida jikinta ba, dan kullum cikin kuka take, da tunani, sede kawai bakin datayi ne yaragu amma duk wanda yasanta ada yanzu baze iya gane taba. Malamin da Sameer yasama mata yana zuwa yana mata kari kullum, tamaida hankali sosai gurin koyon karatu.


Bayan shekara daya Jalila tahaifi yaronta me kyau aka samashi sunan Mahaifin Saleem, suna kiranshi da WALEED.Taro yayi kyau, yaran Falak sunyi wayau sosai, kamar sunfi shekara daya, kuma alokacin ne tafara laulayi, bayan suna sukaje asibiti, likita yace bakomai zata iya cigaba dabasu nono, amma tafara basu abinci, idan cikin yayi girma seta ciresu.


Halima ma tasamu ciki wanda haryayi girma, Alh, bakaramin farin ciki yayi ba, ganin zekara samun haihuwa. Zarah ma jiki yayi kyau, tafara dangana, har tafara kiba, kullum Baba mairo cikin kulawa da ita takeyi.


Ayau Halima ta tashi da nakuda sede har Alh, yafita bata fada mashi ba, sede takira Baba mairo, tana zuwa ta temaka mata, cikin lokaci kankani tahaifi danta namiji, Baba mairo tayi mashi wanka ta gyara gurin itama tayi wanka sannan aka kira Alh, akace yazo an haihu, lokacin dayazo yaga abinda aka haifar mashi seda yayi sujada yagodema Allah, har kwallan farin ciki seda yayi. Zarah ma tayi farin ciki, kuma tazo tayi mata barka, dan bata shigowa gidan idan Alh, yana nan.


Bayan kwana 2 da haihuwarta Samiyya matar Mal. Garba ma ta haifi mace, zarah bakaramin jin dadi tayi ba, haka tashirya ita dasu Jalila da Falak sukaje barka, Aranar sunan halima bakaramin kashe kudi Alh, yayi ba, seda ya yanka manyan raguna Biyar, taro yayi taro, yaro yaci sunan Alh, Abba, dan yace sunanshi zesama yaron za,a kirashi da KARAMEE. Bayan kwana 2 akayi sunan Samiyya, itama tasamu alkhairi sosai.


Cikin Falak yana wata 6 ta yaye yan biyu, aka kaisu gurin Baba mairo, haka suka cigaba darenon cikin Falak, harya kai lokacin haihuwarshi, da dare suka nufi asibiti, suna zuwa ta haifi yaronta me cike da lafiya, nan Sameer yarika kiran waya yana fadama mutane, bayan ta huta aka sallameta, suka dawo gida.


Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Sameer Abdullahi ana kiranshi da SUDAIS, Falak ansha kyau sosai, dan takara zama babbar mace, haka taro yatashi cike da farin ciki.


Bayan shekara 2 an maido su Ameer da Ameerah gida, har ansasu makaranta, kowa yagansu yana sha,awarsu, domin suna matukar kama, gasu kyawawa, Jalila takara haihuwa tasamu mace, aka samata Zarah, suna kiranta da AMAL, shima Waleed an saka shi makaranta, hada Karami ma Alhn yasashi makaranta, dan itama Halima wani cikin gareta.


Haka rayuwar Zarah tacigaba da tafiya agidan Alh, kullum jinta takeyi kamar tana kurkutu, idan tayi tunanin komawa gidan ubanta setaga gara tayi zamanta, dan batada daki agidan, gashi de tana cin abinci mekyau, amma kullum kamar ana dibarta, Baba Mairo harta gaji da lalllashi tasa mata ido, shiyasa yanzu idan zatayi kuka seta shige daki sannan, amma duk da haka da baba Mairo ta ganta seta gane tayi kuka sede kawai ta kyaleta. Ga Son Alh, dayake hanata bacci, batason tana sonshi dayawa hakaba seda tarasashi, kuma taga yayi aure, wani lokacin har labewa takeyi idan yashigo tayi ta kallonshi. Zama tayi bisa gado tace Oni zarah, yanzu wai nice haka, lallai rayuwa ta koyamun hankali, Danasani nayi hkr da Hajjo munyi zaman mu Da yanzu nasan nazama wata babbar Hajiya.


Danasani banyima Alh, asiri ba, dayanzu ina nan da kafata lafiya lau, Danasani ban dauki shawarar Asabe ba, dayanzu bnshiga wannan kangin ba. Ya Allah kaji tausayina ka kawomun karshen wannan zaman danakeyi.
Allah kashirya duk masu irin halina ya Allah. Kwanciya tayi tana kuka me tsuma rai.


Nikam dariya 😄😄nayi nace Zarah ada kenan, dama ai Danasani keya ce.


Wata bakar jaka Falak tadauko taciro wani abun hannu, tadawo
kusa da sameer tazauna, yana kallonta, tace Ameerah zonan, hannunta takama tasaka mata abun hannun, Ameerah tace lah, Momy ke kika siyomun? Kwallan idonta tagoge tace a,a Grandmother dinki ce tace inbaki, Ameerah tace toyaushe zan ganta? Sameer yajawota yace kin kusa ganinta kinji. Ameer yace Dady nito ina nawa? Tashi yayi yadauko wani karamin agogo yace kaima ga naka, yace toni wayace abani? Murmushi yayi yace kaima GrandFather dinka yace abaka, tashi sukayi suna tsalle, sukace Thank you Momy and Dady, waje suka nufa suna murna.


Jawo Falak yayi yace haba my dear kin manta kince bazaki kara kuka ba, tace dole inyi kuka my Luv.


Kawai natuna wani abune, wai yau nida ake kira AGOLAH, nice nake zaune da yarana har 3, suke kirana momy, agaskiya ina tausaya ma duk wata AGOLAH datake AGOLANCI awani gida, Allah yajikanku Umma da Abba, badan narasa kuba da babu wanda ze kirani da AGOLAH, har yau idan natuna sunan nan yanamun ciwo.


Sameer yace banaso kina rike abu aranki, kinmanta kince kinyafe masu? To kibar tuna abun, komade menene yanzu gashi kin daukaka, ayanzu kina sama da ita kuma ita tana kasa dake, kuma kinmata nisa, sosai. Yanzu albishirinki. Tace goro, yace hajjin bana tare za,ayi damu. Tsalle tayi ta rungumeshi tana murna tace wow amma gsky kayimun babban albishir, bansan ma dame zan gode maka ba. Dariya yayi yace ni ai nasan da abinda zaki godemun, kuma Falaka, kinfi haka agurina, kece farin cikina, kin bani kyautar yara har 3 kina kula dani yanda yakamata, nine zance bansan dame zan gode maki ba. Amma yanzu tashi mushiga ciki kibani goron albishir. Tashi tayi tana dariya tashige daki.


ALHAMDULILLAH


Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mesuna AGOLAH.
Kuma ina mika sakon gaisuwa meyawa ga dukkanin masoyana nagode da irin kulawarku gareni. Allah yabar zumunci, abinda nafada da kuskure sekuyi hkr dan dan Adam ajizine.


Nasadaukar da wannan littafi ga mahaifina, ALLAH YAJI KANSHI DA RAHAMA AMIN, ALLAH YAJIKAN DUKKANIN MUSULMAI BAKI DAYA, MUKUMA IDAN TAMU TAZO ALLAH YABAMU GUZURIN TADDASU.






ALLAH YAKAREMU DAKA SHARRIN ZUCIYA YASA MUFI KARFINTA AMIN.




Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login