Showing 9001 words to 12000 words out of 61588 words

Chapter 4 - AGOLA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Nabila Lawan Zango .txt

yaja suka tafi.

Suna zuwa aka wuce emergency da ita, Alh, se zagaye zagaye yakeyi, Falak ko se kuka takeyi, shikan shi Alh, tabashi tausayi. Seda suka dauki minti 30 sannan aka fito da ita abisa gado aka nufi, dakin da aka bata da ita, bin bayanta Falak tayi, shikuma yabi bayan likitan.

Zaune suke a office, Dr, yace Alh, sede kayi hkr cikin dake jikinta yazube. Sede bamu samu wani dalilin daze nuna mana abinda yayi sanadiyar zubar cikin ba. Amma alhamdulillahi, babu wata matsala atare da ita, anyi mata wankin mahaifa, kuma anyi mata allurai, insha Allahu zuwa dare ma zaku iya tafiya, semunce Allah yakawo wani me amfani. Zufar data fitoma Alh, agoshi yagoge, sannan yace ameen, Dr, nagode. Sosai yaji ciwon zubewar cikin sede babu yanda zeyi dole yayi hkr da hukuncin Allah, tashi yayi yanufi dakin da suke.

Zauns suke adakin Asabe, Zarah tace gaskiya Inna nagode maki, yanzu nakara tabbatarwa banida sama dake, dana tsaya bin shawarar Karima dayanzu ina can ina tagumi. Kome kenan idan akwai wata matsala, zanyi maki waya sekuje gurin bokan, basena zoba, idan kuma takama dole senazo se inzo din.
Wayarta ce tayi kara, ganin Alh, ne yake kira yasata saurin dagawa, jin muryarshi cikin sanyi, yasa tace lfy de Alh, naji kamar wani abu yana damunka, naji muryar kasa kasa.
Anan yafada mata abinda yafaru, salati tafarayi cike da damuwa kamar zatayi kuka tace Alh, gani nan tahowa, tunda ko la,asar ba,ayi ba. Yace aa kibari se gobe, tunda itama Inna bata da lafiya. Tace a,a ai taji sauki, nide bazan iya zama ba, Hajjo tana da bukatata akusa yanzu, kasan su Falak yara ne, dole asamu wata babba akusa da ita, tunda Mairo aiki yayi mata yawa . Sosai yaji dadin yanda Zarah ta nuna kulawarta akan Hajjo.
Bayan sunyi sallama tayi murmushi tace lallai aikin boka na kyau, Asabe tace meyafaru? Dije tace ai base an fada maki ba, kema kinsan cikin yabi ruwa. Dariya suka sa suduka. Zarah tace dani kike magana Hajjo. Bara intashi intafi, kada yamma tayi. Kudi tafiddo dubu 2000 tamika masu tace ga wannan asayi magi, godiya sukayi mata, suka rakata har mota, tazo shiga kenan Babanta yadawo, yace a,a Zarah ina kuma zaki? Tace wlh yanzu Alh, yamun waya abokiyar zamana tana asibiti, shine nace gara intafi. Baba yace wayyo Allah yabata lafiya, amma kin kyauta. Allah ya kiyaye hanya kidubata idan kinje. Dubu 1 tamika mashi tace Baba ga wannan anyi cefane, godiya yayi mata yanata shimata albarka, har ta tafi. Asabe tace malam kawo indauki kudina najiya, kasande ai baka baniba ko? Kamar zeyi kuka yace haba Asabe wlh koda naje kasuwa babu abinda nasamo, kuma idan nabaki dari 500 dama kuma meshago yana bina dari 300, kinga kudin sunkare, dan Allah kiyi hkr zanbaki. Dije tace a haba malam kabarshi wasa take maka bakomai tabar maka. Godiya yashiga yimata, anan yawuce masallaci, sukuma suka nufi gida.

Dije tace wlh wani lokacin bakida tausayi Asabe, duk irin kudin da kika samu yau, wanda rabon da ki rike irinsu harkin manta amma saboda dari 500 kinemi sama dan bawan Allah hawan jini. Asabe tace kinsanni akan kudi banida mutunci wlh, tunda harna iya kashe mazajena 2 saboda kudi, kinsan banida mutunci akan kudi, shiyasa bazan daga ma Zarah kafa akan kudi ba wlh, kina ganin sabida tsabar rowa dubu 2 tabamu duk irin wahalar damukasha, amma dayake biyan bukatar tane 150 taba boka. Dije tace ki kwantar da hankalinki, ai tunda de zata iya bada ko nawa ne ayimata aiki, mukam kakarmu ta yanke saka. Kinsan konawa boka yadauka yabamu sauran? 80 yadauka wlh, dariya Asabe tayi tace kai amma wannan boka yanada kirki, gaskiya naji dadi, dauko kibani kasona in adana.

Tunda Zarah ta isa gida wanka kawai tayi, taci abinci tawuce asibiti, lokacin dataje, har Hajjo ta farfado. Tea ta hada mata, takamata suka je bandaki. Seda tayi wanka tagyara jikinta sannan, Zarah tamika mata kayan da Alh, yakawo mata, sawa tayi tafito. Falak ce tashiga bandakin domin wanke kayan data cire.
Bayan tasha tea taci abinci sannan tasha magungunanta. Zarah tace sannu Hajjo, Allah yabaki lfy, ya kuma kawo wani me amfani. Hajjo tace ameen. Zarah tajuya taga Falak bata nan, kuma Alh, yaje yin sallah. Tace amma Hajjo meze hana kibari sekin warke sosai sannan ki kara samun ciki, ina nufin kizo inraka ki gurin likitana asa maki robar hana daukar ciki, amma kada kibari Alh, yasani kinga seki huta sosai, daga baya se acire maki, nasan Alh, beda hkr ko baki warke ba, yana iya zuwa karbar hakkinshi, kinga niyanzu na huta. Hajjo takurama Zarah, ido harseda ta tsargu.
Zarah tace kinyi shiru, murmushi tayi tace ai likita ma yace kozan kara samun ciki senan da shekaru sbd barin dana samu. Ajiyar zuciya Zarah tayi, batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba, tace wayyo gaskiya na tausaya maki, amma ai bakomai wata rana zaki samu. Kallonta kawai Hajjo takeyi, aranta tace ai idan mutum yanuna baya sonka daga farko, koyazo daga baya yace yana sonka kada kayarda dashi.

Segurin karfe 8 aka sallamesu. Bayan sunkoma gida, Alh, yace mairo tarika shiga tana taya Hajjo aiki kafin tasamu sauki. Zarah tace ai bakomai ma taje tayi mata sati 2 harta warke, Hajjo tace a,a Ummin Jalila ai za,a barki da aiki, idan tagama maki tunda nawa babu yawa setazo tamun. Alh, yace shikenan hakan ma yayi.

Tundaga wannan ranar Mairo take shiga part din Hajjo tana taya ta aiki, sosai mairo takejin dadin aiki agurin Hajjo, sbd tana da kirki, kuma bata kyamarta kamar Zarah, gashi tanayi mata alkhairi akai akai, harcewa takeyi dama Alh, yasamoma Zarah wata ita abarta anan, idan ta tuna aikin sati 2 kawai zatayi takoma can dazama batajin dadi, Sosai suke zama da Hajjo suyi ta fira, shiyasa ma seta gama aikin Zarah take tahowa gurin Hajjo. Duk wani labari na Hajjo babu wanda bata sani ba, sbd hakanan Hajjo taji mairo ta kwanta, mata gatade dattijuwa, amma tana bata girma, shiyasa ma bata iya kiranta da mairo sede tace mata Baba mairo, hakan bakaramin dadi yakema Mairo ba, Falak da Jalila ma haka suke cemata, amma banda Jidda.

Jidda ce kwance adakin saurayinta Al,amin, bayan sungama aikata masha,arsu, Al,amin yace Dear nah yakamata fa kitashi kiyi wanka inmaida ke gida, kinga ankusa tashi daga islamiyya, tunda nagama dora maki nawa karatun. Murmushi tayi tace wlh, dande Dady yana gari da anan zan kwana, banason tafiya inbarka. Al,amin yace nafiki son haka Jidda, shiyasa naso ace kinbari nazo gidanku muyi aurenmu mu huta kikace bakison aure yanzu. Jidda tace wlh, Al,amin rayuwar aure takura ce, duka yanzu shekarata nawa dazanyi aure, ai gara inbarai sena kai irin 27 ko 28 haka, yauwa lokacin nakara girma. Amma kawai yanzu da kuruciyata inshiga sahun manya. Murmushi Al,amin yayi yace shikenan ai nima bawai auren ne yadameni ba, tunda de inada kudi na nasan bazan rasa yan mata ba, duka Jidda ta kaimashi yana dariya yace, kemafa bani kadai kike kulawa ba, abinda nasani de nida ke muna son junanmu sosai, amma kowa yana kula duk wanda yasamu, ko kin manta da kaina ina hadaki da aboka naina masu kudi, kuma ni seki hanani kula wasu, aikinsan harakar bariki kowa yanada yanci. Jidda tace naji de amma aikasan kai na dabanne tunda kaine kafara sanina ,ya mace, yace wlh Jidda akanki nafara wannan sana,ar. Shiyasa nake bala,in sonki Jidda na. Murmushi tayi tace bara inyi wanka.

Haka rayuwarsu tacigaba datafiya, hanakalin Zarah bakaramin kwanciya yayi ba jin Hajjo bazata haihu yanzu ba, arizikin mijinsu sehabaka yakeyi, shiyasa yabiya ma Hajjo da Falak da su Jalila hajji, yace ma Zarah tabari tunda ita taje wata shekarar se sukara tafiya tare, baya son abrshi shi kadai. Bakaramin dadi taji ba, za,a barmata mijinta.

Lokacin da Mairo tacika sati 2 tana aiki agurin hajjo, ranar data dawo bangaren Zarah sallama takeyi amma jin shiru yasa tawuce dakin Zarah, taje zata kwan kwasa taji Zarah kamar tana waya, har zata juya taji Zarah tana dariya tana cewa, ai wlh, Inna Asabe, yanzu hankalina akwance yake, tunda mukayi nasarar zubar da waccan cikin na hajjo likita yace kozata kara haihuwa senan da shekaru, shiyasa nace dole inyima boka babbar kyauta sabida yabiyani, yanzu Alh, yabiya mata hajji ita da yara, harda wannan AGOLAR banzar akabiya mawa, narasa meyasa Alh, yake son maidata kamar kowa agidan nan. Ai kede kibari da sannu zankoresu subar gidan nan, toshikenan sekinjini. Mamaki ne yakama mairo jin abinda Zarah take fadi, saurin komawa tayi tanufi dakinta, tana tunanin hanyar dazata bi domin. Kare Hajjo daga sharrin Zarah.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/8, 4:02 PM] YAYA HAYAT: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Fita Mairo tayi tashiga kitchen tacigaba da aikinta, tana tunanin maganganun Zarah, hakade ta barma cikinta, danbazata so afara jin wata magana abakinta ba, amma tayi alkawarin zata sa ido sosai aharkar Zarah, tunda tagano tacanza halinta.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, harsu Hajjo sunje hajji sundawo, sosai tayima Zarah da Baba mairo tsaraba, bayan kwana biyu suka shirya zuwa Abuja ita da Alh, domin kaima matar farouk abokin Alh, tsara barsu, dan bayan bikinsu akayima Faruok transfer yakoma can. Kwanansu 2 acan, bakaramin bacin rai Zarah tashiga ba, anyi tafiya banda ita.

Bayan dawowarsu, Mairo tashiga part din Hajjo, tana zuwa ta isketa abandakin falo tana ta amai, temaka mata tayi, bayan tagama suka dawo falo, mairo tace sannu Hajiya, amma inaganin kamar ciki ne dake ko? Hajjo tace nima haka nake tunani, dan tunkafin muje hajji nadena ganin al,ada ta, sede yaune nafara amai. Mairo tace aikinsan yanzu ba cikin farko bane, kila ma yayi wata 2 shiyasa baki fara laulayi dawuri ba.

Amma zankawo maki wani magani, inde kinsha zaki dena amai kuma zakiji kwarin jikinki. Hajjo tace aiko nagode Baba mairo, wlh bansan da abunda zan saka maki ba, Allah yasani nayi rashin uwa, amma gashi yanzu Allah yabani ke, inajinki tamkar uwata, babu abinda zan iya boye maki. Kwallan da mairo take boyewa suka zubo mata, Hajjo tace Baba mairo meyafaru kuma? Mairo tace bakomai, kawai naji dadin kalamanki yata, tunda nake bantaba haihuwa ba, banida me kirana mana, segashi yau kinbani babban matsayi wanda bakowa ne yake amsa shiba. Hakika yau ina cikin farin ciki wanda. Nadade banji ba. Allah yayi maki albarka keda diyarki Falak.

Sede inaso infada maki wata magana, ada ina shakkun infada maki, sbd bansan yazaki daukeni ba, kila bazaki yarda da maganata ba. Amma ayanzu dakika bani matsayin uwa agareki, nasan zaki yarda da abunda zan fada maki, dan kinsan uwa bazata fadama yarta karya ba.

Inaso kiboye cikin dake jikinki har lokacin da zaki haifeshi, ko Alh, banaso kifada mashi kina da ciki harse yayi girma, nasan shi baza,a iya boyemashi ba. Hajjo tace meyasa kikace haka Baba mairo, nasan dole akwai dalilin dayasa kikace haka, dan Allah kifadamun koma menene, nayi maki alkawarin bazan bafadama kowa ba.

Anan mairo tafadama Hajjo duk abunda taji Zarah tana fadama Asabe awaya. Hajjo tagoge kwallan idonta, tace wlh jikina yabani Zarah ba sona take ba, kawaide tana yimun fuska 2, lokacin da aka kwantar dani asibiti take cemun wai inzo tarakani asakamun robar hana daukar ciki.

Anan jikina yabani wani mugun nufi take nufi dani, kawai sena fada mata likita yace kozan haihu senan da shekaru, wlh Baba mairo ina gama fada mata bakiga wani murmushi datayi ba. Tun daga nan nagane abinda take nufi dani.

Kuma insha Allah Zarah bazatasan ina da ciki ba sede taji haihuwa ta. Shima Alh, bazan fada mashi ba harse yayi kwari, shima sena rokeshi kada yabari kowa yaji, Mairo tace bara inje inkawo maki maganin.

Haka Hajjo tacigaba da renon cikinta babu wanda yasani daga mairo se Falak, su Jidda anyi graduation duk da bawani kokari tayi ajarabawarsu ba, su Falak kuma sunshiga ss3 karatu sukeyi sosai dan sunaso sucigaba da karatunsu idan sungama.

Jidda yanzu duk inda Al,amin zeje tare suke zuwa, ko da kwana nawa zeyi tunda Alh, baya zama gida yanzu sosai, Zarah kuwa tunda Jidda tana wadata ta da kudi babu abinda yadameta, abinda Jidda tagane ma Zariya tamaida gurin zuwanta, tunda taga Asabe bata kwaba mata duk inda taje kotayi dare bata cemata komai, kuma Baba bashida katabus agidan, hakan yasata yanzu tafi zama Zariya akan gidansu, koda Alh, yaji tana zuwa Zariya dadi yaji saboda yaga umminsu ita bata zuwa.

Lokacin da cikin Hajjo yacika wata 7 aranar Alh, yagane tana da ciki, yace lallai ma Hajjo yanzu nikike boyema abun farin ciki? Dariya tayi tace wlh banso kagane ba, naso kawai kazo kaga jariri ko jaririya, shiyasa ko zanje awo nake cemaka zanje wankin kai. Amma kayafemun da karyar danayi maka. Jawota yayi yace bakomai, aikinsan dama ni ina baku damar fita duk lokacin da kukeso koda bana nan.

Amma gaskiya naji dadi sosai, Allah yasa rayayyene, tace ameen. Amma dan Allah banaso kafadama Kowa har ummin Jalila, nafiso inbata mamaki tunda kai kaganoni.
Yace shikenan angama daukarta yayi suka nufi daki.

Su Falak suna third term a ss3 Hajjo ta haifi yaronta me kyan gaske, babu wanda yasan tahaihu, dan cikin dare nafara nakuda kuma taci sa,a Alh, agurinta yake, haka suka hada kaya suka nufi asibiti, Falak kawai tasan suntafi, gurin karfe 8 suka dawo, bayan ya kaita part dinta yawuce part din Zarah, yanashiga yahadu da Mairo, yace tabar abinda takeyi taje Hajjo ta haihu, sosai mairo taji dadi, tace me aka haifa, yace namiji, barka tayi mashi sannan tawuce part dinsu.

Farin ciki kawai Alh, yakeyi, dakin su. Jalila yaje yace tafito tacigaba da aikin da mairo takeyi, dan taje gurin Hajjo ta temaka mata ta haihu. Jalila cike da murna tace Dady meta haifa? Yace kunsamu kani Jalila bakaramin dadi taji ba, fita tayi tawuce kitchen. Dakin Zarah yashiga, ganin yana cikin farin ciki ga bakinshi yaki rufuwa, tace Alh, yaude lafiya kake kamr wanda aka yima bushara da gidan, aljanna? Yace aidole kiganni haka, Hajjo ta haihu kuma tasami namiji me bala,in kama dani. Dariya Zarah tayi tace amafarkin yau ne kaga haka? Yace wlh da gaske nakeyi, tun dare muna asibiti. Zarah tace karbo yaron kukayi kome, nide nasan Hajjo bata da ciki. Ganin zata bata mashi lokaci yajata zuwa part din Hajjo.

Mutuwar tsaye Zarah tayi ganin Alh, yamiko mata yaro me bala,in kama dashi, kamar an tsaga kara, wata irin zufa ce tarika keto mata ta ko ina, tama rasa mezatayi, takasa karbar yaron, hawayene suka taho mata tayi saurin juyawa takoma. Falo, mamaki ne yakama Alh, ganin abinda Zarah tayi, amma su Hajjo sun harbo jirginta.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
[7/13, 09:39] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Fita Mairo tayi tashiga kitchen tacigaba da aikinta, tana tunanin maganganun Zarah, hakade ta barma cikinta, danbazata so afara jin wata magana abakinta ba, amma tayi alkawarin zata sa ido sosai aharkar Zarah, tunda tagano tacanza halinta.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, harsu Hajjo sunje hajji sundawo, sosai tayima Zarah da Baba mairo tsaraba, bayan kwana biyu suka shirya zuwa Abuja ita da Alh, domin kaima matar farouk abokin Alh, tsara barsu, dan bayan bikinsu akayima Faruok transfer yakoma can. Kwanansu 2 acan, bakaramin bacin rai Zarah tashiga ba, anyi tafiya banda ita.

Bayan dawowarsu, Mairo tashiga part din Hajjo, tana zuwa ta isketa abandakin falo tana ta amai, temaka mata tayi, bayan tagama suka dawo falo, mairo tace sannu Hajiya, amma inaganin kamar ciki ne dake ko? Hajjo tace nima haka nake tunani, dan tunkafin muje hajji nadena ganin al,ada ta, sede yaune nafara amai. Mairo tace aikinsan yanzu ba cikin farko bane, kila ma yayi wata 2 shiyasa baki fara laulayi dawuri ba.

Amma zankawo maki wani magani, inde kinsha zaki dena amai kuma zakiji kwarin jikinki. Hajjo tace aiko nagode Baba mairo, wlh bansan da abunda zan saka maki ba, Allah yasani nayi rashin uwa, amma gashi yanzu Allah yabani ke, inajinki tamkar uwata, babu abinda zan iya boye maki. Kwallan da mairo take boyewa suka zubo mata, Hajjo tace Baba mairo meyafaru kuma? Mairo tace bakomai, kawai naji dadin kalamanki yata, tunda nake bantaba haihuwa ba, banida me kirana mana, segashi yau kinbani babban matsayi wanda bakowa ne yake amsa shiba. Hakika yau ina cikin farin ciki wanda. Nadade banji ba. Allah yayi maki albarka keda diyarki Falak.

Sede inaso infada maki wata magana, ada ina shakkun infada maki, sbd bansan yazaki daukeni ba, kila bazaki yarda da maganata ba. Amma ayanzu dakika bani matsayin uwa agareki, nasan zaki yarda da abunda zan fada maki, dan kinsan uwa bazata fadama yarta karya ba.

Inaso kiboye cikin dake jikinki har lokacin da zaki haifeshi, ko Alh, banaso kifada mashi kina da ciki harse yayi girma, nasan shi baza,a iya boyemashi ba. Hajjo tace meyasa kikace haka Baba mairo, nasan dole akwai dalilin dayasa kikace haka, dan Allah kifadamun koma menene, nayi maki alkawarin bazan bafadama kowa ba.

Anan mairo tafadama Hajjo duk abunda taji Zarah tana fadama Asabe awaya. Hajjo tagoge kwallan idonta, tace wlh jikina yabani Zarah ba sona take ba, kawaide tana yimun fuska 2, lokacin da aka kwantar dani asibiti take cemun wai inzo tarakani asakamun robar hana daukar ciki.

Anan jikina yabani wani mugun nufi take nufi dani, kawai sena fada mata likita yace kozan haihu senan da shekaru, wlh Baba mairo ina gama fada mata bakiga wani murmushi datayi ba. Tun daga nan nagane abinda take nufi dani.

Kuma insha Allah Zarah bazatasan ina da ciki ba sede taji haihuwa ta. Shima Alh, bazan fada mashi ba harse yayi kwari, shima sena rokeshi kada yabari kowa yaji, Mairo tace bara inje inkawo maki maganin.

Haka Hajjo tacigaba da renon cikinta babu wanda yasani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login