Showing 27001 words to 30000 words out of 61588 words

Chapter 10 - AGOLA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Nabila Lawan Zango .txt

har Allah yadauki dayan, sede Falak kawai tayi saura. Kuma itace Hajiya ta maidata kamar baiwa agidan, datana da ikon kasheta kamar yanda tayima mamanta da kaninta itama da tuni takasheta. Nadade ina tunanin hanyar dazan bi inga Falak tabar gidan, sede kafin mutuwar hajiya tabar mata wasiyar komin rintsi kada tabar gidan Alh, har se idan aure tayi.


Nima haka tabani wannan wasiyar, duk da yanzu Falak ba abakin komai take agurin Alh, ba, kuma ba aikin kowa bane sena Hajiya Zarah, kwata kwata yanzu Alh, yamanta da wata Falak agidanshi, shi kanshi yazama shanyayye agidan.


Ina cikin neman mafita segashi Allah yakawo mana Sameee, tun ranar da yafara temakon Falak naji inama ace yazo yanemi auren Falak, alokacin hajiya bata lafiya anrasa wane irun ciwo take, Sameer yabama Falak wata addu,a cikin ikon Allah ana fara yimata ita tasamu sauki, hakan yasa muka dawo gida akacigaba dayi mata addu,a.


Sede alokacin da ciwaonta yakara tsanani Sameer. Yakoma makaranta, kuma wannan ciwon shi yazama ajalinta. Ajiya naje kaima hajiya abincinta naji wata magana data firgitani,......... Anan Baba mairo tafada masu irin wayar dataji Zarah tanayi ajiya.


Ina gama jin wayar nan narasa yanda zanyi intemaki Falak, kawai senayi amfani da abinda nafada maku nashiga gurin hajiya da maganar, cikin ikon Allah tayarda da abinda nafada mata, kasancewar mafita take nema, kuma dama hajiya duk wani makiyin Falak to ita masoyinta ne.


Shine nataho domin infada maku shawar danazo da ita. Goge kwallan idonta Halima tayi, shima Sameer tunda yaji irin abinda akeson ayima Falak dinshi yafara kuka. Halima tace lallai wannan mata batada imani, kuma zata iya kashe Falak, damane kawai bata samuba.


Yanzu wace shawara kika kawo? To kamar yanda mukayi da ita, azuwan nataho tasha ne insamu Asid wanda haka kawai nafada mata sunan, domin acan garinmu akwai wani dan kwaya haka ake cemashi, toganin sunan yayi kama dana marasa da,a yasa nima nace mata sunanshi kenan.


Sameer kaida Falak duk sekunyi hakuri idan har kunaso mucima burinmu, Halima cewa nayi meze hana Sameer yayi basaja yazo amatsayin Asid danace zankawo. Ammafa seka canza shigarka, dole kasamu kaya irin na yan iska, da kuma sarkar dazakasa awuya, domin hajiya tayarda kayi dede dawanda takeson bama Falak, kaga idan har Allah yasa mukaci nasara, shikenan Falak tazama taka, kada kadamu da maganar hajiya dan tace shekara 1 kawai takeso Falak tayi agidan aure asaketa. Mude burinmu tabar gidan, kaga idan har igiyar aurenta tazo hannunka, kaine kake da saki, kuma nasan duk inda za,aje babu mesaka kasaketa, tunda ba ita ta haife taba.


Halima tace agaskiya Baba mairo wannan shawara tayi, koko yakace Sameer? Goge idonshi yayi yace hakane Umma , ashirye nake dayin duk wani abu daze fitar da Falak daga rayuwar datake ciki. Insha Allahu gobe zanzo gidan amatsayin Asid kamar yanda kikace Baba mairo. Allah yayi mana jagora.


Suka ce ameen. Halima tace toyanzu Sameer dole mufara shirin biki, dan nasan baze dau lokaci ba, anjima zansamu kawunka, infada mashi halin da ake ciki, nasan shima zebamu goyon baya, danshima mutum ne me gaskiya kuma gashi malami. Bab mairo tace Kada ku takurama kanku kuyi abinda zaku iya, daga baya komai zeyi dede, nasan ai anan gidan zata zauna ko?


A,a gaskiya Baba mairo nide nafison yaje yakama masu haya mesauki suzauna, idan Allah yasa yasamu aiki ko kuma kasuwancin dayakeyi ya kara kwari tunda yanada filinshi se yafara gini, wlh, banason zama gida daya da sirika, kinsan ance yau da gobe se Allah.


Sosai Baba mairo taji dadin abinda Halima tafada, tace toshikenan Allah yatemaka, kai kuma Sameer banason katakura kanka, kasamu gida mesauk, badole sekunj dadi alokacin da kukeso ba, da sannu wata rana rayuwa take canzawa, kuma duk kudin da hajiya tabayar abaka kayi amfani dasu ka kama haya kuma kayi hidimar bikin dasu.


Sameer yace to Baba mairo, bazace zanki amsar kudin ba, sede kisani bazan yi amfani dasuba, yanda kika bani haka zanba Umma ajiyarsu, banaso in auri Falak da kudin haram, kuma nasan wata rana dole Hajiya zatayi mani gorin abinda tamun duk ranar datasan gaskiya, kuma aranar zanbata kudinta.


Baba mairo tace gaskiya wannan yaron kacika da halak, Allah yayi maka albarka. Ni bara inzo intafi, tunda Allah yasa nasamu abinda nakeso, kada taga kamar na dade. Halima tace to Baba mairo mungode, kema Allah yabiyaki irin jihadin da kikayi. Sameer yayi dariya yace au BabaMairo namanta fa Falak tace idan har badake zamu tafi ba, bazata aureni ba. Dariya sukayi Baba mairo tace haka kullum take cewa. Halima tace ai wannan haka yake, banga abinda zaki zauna kiyi agidansu ba, dama zaman Falak kikeyi, tunda tayi aure ai shikenan. Sede nima ina da tawa shawarar. Baba mairo anan gidan zata dawo da zama,ba gidanku ba. Sameer yace a,a gaskiya Umma kingafa munrigaki. Baba mairo tace kyalesu dama koda tafada nibanyi niyar zama ba, niyata bayan aurenta inkoma garinmu.


Halima tace a,a Allah baza,ayi haka ba kinga babu kowa anan gidan dama diyar kanwata ce nace zata dawo nan idan Sameer yayi aure, tunda kuma gaki ai setayi zamanta, dama ina da almajiri memun aike aike, Allah babu wani abu kidawo nan dazama. Baba mairo tace toshikenan. Allah yamana jagora. Sameer yace wato de anyimana kwace da rana tsaka ko? Sukace ai haka yafi gara abarku kukadai kusan zaman aure kukeyi. Da haka Baba mairo tayi masu sallama tare da bama Halima dubu 10dan tafara ajewa.


Haka Baba mairo tajema Zarah da albishir medadi. Zarah bakaramun dadi taji ba, tace kuma acikin sati daya za,ayi bikin. Baba mairo tace a,a yace yafison nan da sati 2. Zarah tace shikenan, idan Alh, yadawo zanyi mashi magana yabada kudi asai mata kayan aure amma tsofaffi za,a siya mata suma dan kada mutanen gari suce bamu rike amanar da,a bamu ba. Kema zanba kije gurin dillalan nan mata kisiyo mata gado da katifa, se kujeru da yan kayan kitchen, zance mashi cikin kudin dazan bashi yasiya mata kaya kala 3 wanda zatasa da biki.


Haka Baba mairo dashigo daki tasamu Falak tafada mata duk yanda sukayi da Sameer da kuma Zarah yanzu. Sosai Falak taji dadi tajiba, jitake kamar anyi mata albishir da gidan aljanna, itade idan harzata bar gidan nan to ko inama ta tafi.


Jalila tana karatunta hankali kwance, sede akai akai suna waya da Falak, amma Falak bata fada mata labarin aurenta da Sameer ba, da Baba mairo tahana tafadama kowa har Jalila, saboda tace tsakanin da da Mahaifi se Allah, tabarshi idan komai yayi dede taji. Ko maganar auren daza,ayi mata ma sede agurin Zarah Jalila takej, aranar dataji bakaramin kuka tasha ba, tana tunanin wace irin zuciya Umminta gareta.


Jidda kuwa aranar dasuka isa london kwanan Al,amin 2 yayi mata sallama yadawo nigeria, har kuka seda Jidda tayi haka yayita lallashinta, yace nan da sati 4 zezo yadauketa su koma. Tun bayan tafiyarshi suke more rayuwarsu itada abokin Al,amin Joseph, bakananan kudi Joseph yake bama Jidda ba, seda takai har Sallah Jidda tadena yi, rayuwar turai kawai takeyi, idan kaganta sekace baturiya ce, dan takara zama fara sosai.


Yawo sukesha ita da joseph, suk inda takeso yana kaita, domin sosai yakejin dadin harka da Jidda, har fada yakeyi tafi sauran yanmatanshi komai, shiyasa tunda tazo ya sallami yan matanshi, ita kadai yake harka da ita. Duk kudin dayake bata betaba barin takashe koda gwandala ba, shine yake mata komai, shiyasa ma take adana su acikin akwatinta.


Sameer yazo gidan su Falak cikin irin shigar da babu wanda zeganshi yace mutumin kirkine, sosai Zarah taji dadin ganinshi haka, kuma tabashi kudi masu yawa, tace idan Alh, yadawo nan da jibi zata kirashi yazo sugaisa. Amma inaso aranar kadan saka manya kaya, idan ma baka dasu ka aro, duk da zancema Alh, me aikina ce zatayi aure kuma shine ze zama waliyinta, kaga bazeji dadi yaganka cikin irirn wannan shigarba. Anan sukayi sallama yatafi.


Halima tasamu kawun sameer tayi mashi duk bayanin abinda akeciki agame da auren da Sameer zeyi, shima ya tausayama Falak sosai, kuma yace babu damuwa zeje yayi yanda sukace.
Bayan Alh, yadawo Zarah tayi mashi bayani akan auren dazatayima me aikinta, dakuma abinda takeso yayi, babu gardama ya amince, kudi yabata naira dubu dari 500 yace gatashi gudummuwar asaya mata kayan daki, godiya tayi mashi, sannan tace anjima Sameer da kawunshi zasuzo gaisheshi. Alh, yace sunan yaron sameer tace E, dan shima haka yafada mata, amma yace ba,a kiranshi da sunan, sede Asid, dan Sameer cewa yayi bayaso adaura auren Falak dawani sunan banashi ba. Alh, yace Allah yakawosu lafiya.


Haka su Sameer da kawunshi sukazo suka gaisa da Alh, sosai kawun Sameer ya tausaya ma Alh, gashide cikekken mutum amma yana ganinshi yagane akwai sihiri ajikinshi, dan kawu malamine sosai, haka su kawu suka bada kudin aure da kayan sa rana akasa biki sati 2.


Zarah tabama Baba mairo dubu dari da hamsin tace tayima Falak siyayya, daga can awuce dasu gidan dazasu zauna bataso akawo matasu, Baba mairo tace hajiya bazakije ganin gidanba? Zarah tace Allah yakyauta, ai naji dadi tunda kina nan, sekiyi komai.


Sameer yasamu dan karamin gida yakama haya, har fenti seda yasa akayi, sannan su Baba mairo suka kawo kayan daki akayi jere, gado ne da kujeru, se katifa dukansu tsofaffine, sede basosai suka tsufa ba, dan hada kudin Baba mairo aka hada akayimata siyayya, kayan kitchen ma, ansai mata rishow da tukunya 2 se kula 2, jug 2 da plate da ludduwa se cokali. Gidan balaifi yayi kyau. Ana saura kwana 2 daurin aure aka kawo kayan da Falak zatasa , suma acikin bakar leda ne, kala 3 kananan atamfofi se takalmi 1. Zarah kamar zatayi rawa dan murna, su asabe da Dije duk sunzo, amma babu abinda suka kawo.


Aranar asabar aka daura auren Falak da Sameer akan sadaki dubu 20, ba laifi mutane sunzo yan unguwa, dayake Alh, yasa anyi sanarwa amasallaci za,ayi daurin aure agidanshi, yan uwan Sameee ma sunzo.


Da dare gurin karfe 7 aka kawo mota daya somin daukar amarya, Zarah tacema Dije da Mairo suje sukai amarya se sudawo. Haka aka fita da Falak, dan babu wani fada da Zarah tayi mata, Falak taso taga Alh, amma Zarah tahana, dan boka yace duk ranar dasuka hada ido da Falak da Alh, asirin ze karye. Haka Falak tafita tana kukan rashin Uwa. Mutanen unguwa se gulmar Zarah sukeyi suna cewa takasa rike amanar da,a barmata. Su Baba mairo basu dade ba, suka juyo, Falak kuka kawai takeyi. Bayan tafiyarsu Jalila ta kirata awaya, tana kuka tana bata hakuri, tace. Wlh Falak bazan iya zuwa inga irin auren da Ummi tayi maki ba, kiyi hakuri Falak, insha Allahj wata rana komai zewuce. Falak tace bakomai Jalila nagode, haryanzu de kinkasa zuwa gida ko? Jalila tace Falak banason abinda Ummi takeyi agidan nan, shiyasa nafison zama. Makaranta akan gida. Falak tace banason Haka Jalila, da kunsamu hutu kidawo gida, ko kin manta wa,azin da Malam Sameer yayi mana akan muhimmancin uwa? Kome Ummi tayi dole kibata hakkinta amatsayintana Uwa, idan har kinaso mushirya to da kunyi hutu kizo gida. Jalila tana kuka tace shikenan Falak zanzo, nagode da tunin da kijayi mani. Allah yabada zaman lafiya, yasunan mijin naki? Falak tace nimade Ummi tace mun sunanshi Asid. Jalila tace dan Allah jiwani suna, kiyi hakuri Falak nasan Ummi tasakaki kowace rayuwa kika shiga. Sallama tayi mata takashe wayar. Murmushi Falak tayi tace Jalila Umminki tabiyani tunda hartayi sanadiyyar sama mun farin cikina.


Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[7/13, 09:41] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)


Part 85.....90


Zaune take ita kadai tana ta tunanin irin rayuwar da tayi, addu,a tayi Allah yasa aurenta yazamo karshen yankewar wahalarta. Sallama taji anyi, Sameer ne yashigo bayan ya kulle gidan sannan yanufi dakin da Falak take.


Zaune take da ganin idonta taci kuka, harta gaji, zamayi kusa da ita tare da cire mayafin data rufa, hannu tasa tarufe fuskarta, murmushi yayi yace Falak yau kuma rowar fuskar akemun? Ai yanzy munzama daya, nazama ke kin zama ni. Cire hannunta tayi tana kallonshi tana murmushi.


Falak nagaji dayawa, tashi muje muyi wanka, kafin muzauna ko? Aini nayi wanka sede kaje kayi, uhm bawani nan banyarda ba, to koma kinyi zaki sakene, ai bance kiyi ke kadai ba, tashi tayi tashiga bandaki ta hada mashi ruwan wanka sannan tafito, kokarin cire riga yake yana fadin da gaske fa nake tare zamuyi, ai tun kafin yakarasa fadi tayi waje.


Dariya yayi yace matsoraciya, wata rana zamuyi ne, shiga yayi bandakin yayi wanka, seda yagama shiryawa sannan tashigo itama tawuce bandakin, daga cikin dakin yake mata magana, kiyo alwala kafin kifito fa.


Bayan tagama tafito tadauki diguwar rigarta a durowa takoma bandaki tasaka sannan tafito, turare kadai tashafa tashimfida masu abin sallah, shiyajasu sallah har suka, gama, sannan yayi mata tambayoyi akan addini, dayake Falak akwai kokari duka ta amsa tambayar da yayi mata,


Tashi yayi yadauko ledar daya shigo da ita, kitchen ya koma ya dauko plate sannan yazuba masu, shiyarika bata shima yana ci, harsuka koshi, Falak de kunya takeji takasa sakin jikinta. Kwashe kayan yayi ita kuma takoma bandaki tayo brush, abandakin yasameta tana shirin fitiwo, hannunta yakama, seda yagama sannan suka fito tare, rigar jikinshi yacire dagashi se gajeran wando da vest, saurin rufe idonta tayi, jitayi itama yana kokarin cire mata riga, tace sanyi fa nakeji.


Dariya yayi yace ai bargo zamushiga, haka yacire mata riga daga ita se under wear da vest yabarta, bisa gado yajata, bayan aun kwanta yajawota yadorata bisa kirjinshi, yanata shafa mata kanta, tuni jikin Falak yafara rawa. Murmushi yayi yace Falak sarkin tsoro, ni babu abinda zan maki, magana zamuyi, kuma nafiso injiki ajikina shiyasa.


Ajiyar zuciya tayi dataji kalamansa. Falak, Sameer yakirata, na,am. Dole mugodema Allah daya nuna mana wannan rana, bazan iya kwatan tamaki irin farin cikin danake ciki ba, Allah yasani duk da ga yanda akayi aurenmu. Wlh banajin haushi kokadan, nasan dayawa mutane suna gulma akan aurenmu, amma ni beda meni ba.


Nasan Falak zakiji haushi da irin yanda na aureki, kiyi hakuri, komai ze canza, duk da kinfi kowa sanin yanda aurenmu yakasance amma dole inbaki hakuri, insha Allahu gobe tela zekawo maki dinkunanki, akwatinanki kuma suna gurin Umma, suma gobe zan daukosu.


Nayi hakane saboda banaso Umminku ta fahimci wani abu, shiyasa nakawo kaya marasa kyau, inaso kidaukeni abokin rayuwa na har abada, banida niyar cutar dake, kuma insha Allahu zan zamo maki abin alfahari, idan komai yayi mana dede zaki koma makaranta kema kiyi karatu kamar kowa,


Banaso idan kina da damuwa ki boyemun, yanzu bakida kowa seni, Baba mairo tayi maki nisa, yanzu nine makusancinki, idan har muka gina rayuwarmu ahaka, tabbas zamuji dadi kuma wani abu baze shigo ya tarwatsa zamammu ba.


Kamar yanda Umma tace nan da kwana 2 Baba mairo zata koma gidanta, itama bazata kara zama amatsayin me aiki ba, shikuma Dady insha Allahu zamu sa shi acikin addu,a kawu ma yace zetayamu da addu,a domin tun ranar daya ganshi yagane yana cikin yanayi na asiri.


Allah yanbani ikon rike amanar dana dauko, kuka sosai Falak takeyi, jawota yayi yakara rungumeta yana lallashinta, shiru tayi tana maida numfashi. Dagowa tayi ahankali tace Bansan dame zan gode maka ba, Allah ya..... bata karasa ba, jin yahade bakinsu guri daya, kissing dinta yake sosai, tuni jikin Falak yafara rawa, jin irin abubuwan dayake mata. Daga haka labari ya canza.


Zaune suke adaki suna ta faman dariya, Zarah tace yakukaga irin aikina, ai nafada maku bazan taba barin Falak tayi rayuwa me dadi ba, haka zata kare daga karshe tayi mutuwar wukakanci. Dije tace gaskiya hajiya kema kin iya aiki, yanzu dasunyi shekara 1 ze saketa?


E haka nace mashi, daga farko, amma daga baya nace mashi dayaji ta isheshi ze iya koromun ita, kuma nace mashi yatabbatar yayimata raga raga, kada ya saukaka mata dede da kwana 1, kuma nace karyayi mata riko mekyau, kinsan dangiya akwai dukan matansu, haka ze maidata kamar jakarshi, ga aiki ga duka, kafin tadawo gidan nan setakoma kamar me kanjamau.


Asabe tace, amma inafatan idan tadawo ba,anan zata cigaba dazama ba ko? Zarah tace haba de, nikam mezanyi sa wannan yarinyar, ai dama burina ta wulakanta, idan da halima sonake tafito da ciki. Dije tace duk da haka idan tafito kada kibarta tashiga duniya haka, kinsan mutane akwai tausayi, wasu zasu iya daukarta su temaka mata rayuwarta zata iya yin kyau nan gaba.


Kawai itama ayi mata yanda akayima uwarta, asamata ciwo me tsanani kinga kota tafi acan zata mutu. Zarah tace kwarai kuwa wannan shawara taki tayi, zanjira fitowarta, sekuje gurin boka yayi mata aiki. Haka sukayita fira daga nan Zarah tayi masu seda safe tawuce gurin Alh,.


Jidda da Joseph suna nan suna cin duniyarsu, Jidda tayi kyau hartagaji, lokaci zuwa lokaci suna waya da al,amin shima idan yakirata seta ga dama take dauka, ayanzu yanda takejinta cikin daula, gani take tafi karfin Al,amin, shiyasa yanzu take mashi wulakanci. Tunbaya damuwa haryafara damuwa, ganin abin nata yana kara gaba, yasa yayima Joseph magana akan zezo yadauketa.


Dayake agaban Jidda sukayi wayar tun kafin Joseph yabashi amsa ta anshi wayar, cikw da masifa tace wai kai Al,amin ana so dole ne? Nifa yanzu babu wanda zetakuramun nima inada yancin dazanyi rayuwar danakeso, saboda haka dan Allah ka sauraramun kafita ahanyata, wlh yanzu nafi karfin ace wai kai saurayinane, ko ada rashin wayo neyasani biye maka, amma yanzu kasani ni Jidda nafi karfinka, bani ba kai.


Kashe wayar tayi tacema Joseph kada yakara daukar wayarshi, ita baruwanta dashi, anan zata zauna idan taso tafiya gida zata tafi ita kadai. Wani irin mugun murmushi Joseph yayi, dama yana lallaba tane saboda idan Al,amin yadauketa, idan yakara neman tazo zata iya dawowa.


Al,amin kuwa mamaki ne yakamashi, tsayawa yayi yana kallon wayar hannunshi. Wasu irin zafafan hawayene suka rika zubi mashi, har ga Allah yaso ace Jidda ta saurareshi, yanaso tadawo kodan yafada mata shiyanzu yatuba, yanaso itama ta tuba kuma shize aureta, tunda dama shine farkon lalata ta.


Tunda yaga wani abokinshi agabanshi yarasu, tundaga ranar tsoron Allah yakamashi, kuma yayi alkawarin baze kara aikata zina da duk wani laifi marar kyauba. Hakan yasa yakira joseph dan yaje yadauko Jidda amma tayi mashi rashin mutunci. Kuka sosai yakeyi yana fadin why Jidda, meyasa zakimun haka, kinsan ina sonki, tsautsayi ne, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login