Showing 18001 words to 21000 words out of 108344 words
Chapter 7 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
itace ta kirkiro shi, amadadin ta tsaya kome yazo karshe sai taki, Nima kuma ban fahimci ma'aukin abun ba, sai yanzu dan haka ku barni da su."
"Amma naga dai, kana da Matarka toh ka rabu da Safinah mana."
"Hmm! Dr Fu'ad bai gaya maka waye Ni bane? Ni ba a bani umarni, umarni na iya haɗawa."
Kura mishi ido yayi sannan ya janye daga gareshi. Dan shegen kwarjinin Ashraf yake dashi kana ganinshi kaga jinin sarauta, amma ba daga nan abin yake ba, sai ya kalleka kukayi ido biyu dashi anan zaka fahimci karfin mulkin a idanun sa, domin. Tsakarka yake babu tsoro a cikin ta sai tarin izza. Kome girmaka da zaran kunyi ido biyu toh gabaki d'aya dole kayi ladab, mafi akasari da idanunshi kawai yake horasu Ghaniyu.
***
Tunda na dawo gidan zancen da sauki kenan, amma batun aljanu nan fa,
Ga Ashraf da ya binciko inda nake. Baya tashi zuwa sai dare, hmm mutum ya zama kaman aljani shima.
Wani abu da yaƙe dabi'ar larabawa, su a can gurbinsu dare lokacin shakatawa ce, rana kuma ana juyawa ce, dan haka ba wani abu bane a gurin su yawo da dare.
Da mota yashigo unguwar, a can gefe da unguwar, shida Ghaniyu da kuma Fahad,.suka ajiye motar a can.
"Sultan! Me muka zo yi a cikin unguwar mutane da dare!?"
Cikin rashin damuwa da abinda zai fito harshen shi yace.
"Na kawo kune a kashe min ku"
Dariya Ghaniyu ya gimtse dan yasan halin ubangidanshi , da iya bakar magana.
Ciki dariya Ghaniyu yace.
"Akwai wani shaidani da ya sami Gimbiya SAFINAH, shine Sultan yazo su san nayi."
"Shaidanin Mutun ko na Aljanu."
"Ehtoh, nan ne ban sani ba, amma tabbas yazo ganinshi ko yana nan ne ko kuma ya barta dan tsaf Sultan dinmu ya shirya sun kunce Sultana SAFINAH."
Shiru duk sukayi har suka isa gidan, ta baya suka kewaye, kamar marasa gaskiya, wani abu suka saka a hannunsu da kafarsu sannan, suka shiga bin bangon har dai suka samu nasaran hayewa katangar, a dai dai window dakin suka hangoshi zauna bak'ikirin dashi.
"Ghani! Ka daiji abinda nace maka, kafin zuwan mu, sai kai kuma Fahad ka koma inda muka ajiye motar, koda an rutsani zai kaini gun Yan sanda, kai da Gani zaku zo, zai maka bayanin kome.
"Umarni ka kawai muke jira"
Murmushi yayi sannan ya dira!
Nasani Wannan page akwai Question sosai a bakinku......
Fatan alheri.... Allah ya biya mana bukatar mu na alkhairi.
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
MJ
BOOK-2
20-2-2020
Page 4×2
Komawa suka yi yayinda shi kuma ya dirka a gidan juyawa. Juyawa baƙin karen yayo kan Ashraf da mugun gudu, kafin karen ya iso ya fidda wani k'olba a gefen cikinsa tare da ɓalle bakin k'olban, sai ga karen yabi iska ya shiga cikin k'olban shi kuma ya rufe.
Sau da dama wannan ita ce hanya mafi saukin da wasu Malam ruki'a sukewa aljanu ko ifiritai masu shegen taurin kai.
Dake aikin yazo mishi da sauki, sai dai wani irin kara tare da tsawa ya tadamu, Dudu da yake d'akin shi yaga inuwar mutum na zaga gidan.
To banda jaraba ya gama aikinsa shine ya shiga niman inda nake, sai akayi rashin dace, yaga dakin sai dai Babu ta inda zai shiga shine yake ta daman zaga gidan (🙄 madalla Allah yasa a kama mutum)
Shi kuwa Dudu ganin ana zaga gidanshi yasashi dauko yar goranshi wanda ake kira da ko kwana,
Ya cigaba da kallon yadda Ashraf yake tsaye, kare mishi kallo yayi, ranshi ne ya ɓaci a zuciye ya fito daga gidan, yayi hanyar backyard, yana zuwa cikin ɓacin rai ya daga sandar zai buga mishi aikuwa ya gocce, tare da juyawa suna kallon juna.
"Wai kai wani irin masiface kake bin yar Uwata dashine? Ko ance maka bansan abinda kuka aikata bane."
Sosai giranshi yayi tare da sunkuyar da kai yace.
"Na fahimci kaine kawai zaka bani matsala. Ni bawani abu nake nima ba! Yar uwarka nake bukata, ita kawai Idan kuma haka bai samu ba zan hakura amma kafin nan ka bari ta nuna bata tayi na sai ka samu damar magana"
Tureshi yayi gaba, tare da gaya mishi kalamu masu zafi, amadadin yaji haushi sai ma kin fitar da yayi. Hayaniyarsu ya tasheni. Ni a tunanina barayi suka zo, ashe rigimar Dudu da Ashraf ne.
Da sauri naka mayafi na fito, shi ya ganni amma Dudu bai ganni ba.
"An zo gurin! Don Allah kabari Ni ka gaya mata gaskiya abinda na aikata mata."
Ingijeshi Dudu yayi ya fad'i a ƙasa.
Aikuwa ya sake ƙara.
"Wai Dudu meye haka ne? Dare yayi fa."
Cikin jinjiki Ashraf yace.
"Safinah don Allah ki saurareni ko sau daya ne, zan gaya miki gaskiya."
Kamo wuyar Rufani Dudu yayi, zai fitar da shi daga gidan.
"Don Allah Safinah ki saurareni! Wallahi iya gaskiya zan fada miki."
Kauda kaina nayi tare da jan isa ga sanyin dare da ke ratsa ko ina.
"Baban Affan! Kyaleshi"
Na fada kaina na gefe,
"Bana gaya maka ya, surukinsa nifa nasan abinda nataka yar uwarka ta mutu a kaina."
"Didih karki sauraren shi! Shine ya sa Dr Hameeed ya aureki! Sannan duk abinda yake faruwa yana da masaniyar akai. Wallahi babu kome a ranshi sai cuta. Bakinsu ɗaya da Hameeed."
Tsabar kaduwa kamar zan kira Lokaci guda tsoro ya kamani.
Jikina na rawa na fito zuwa inda suke.
Kallon Abdullahi nake yana bani labarin yadda ya tsinci labarin a bakin Dr Shabhan.
Hawaye suka shiga saukowa da gudu, gabanshi naje na tsinka mishi mari.
"Meye laifina Ashu? Dan nayi taimako shine ya zama matsala ko me? Kasheni kuke son yi kai da Hameeed ko? Wato You creating the game, and kune player ni kuma ball."
Tafa hannuna mai zuciyata na ta fasa.
"The Game is over! Thank you bazaka kuma break heart na wata Y'a mace ba sai ka biya abinda ka aikata. Kaje nan da wata uku Ni da ina zan nimeka."
Wucce shi nayi ina kuka me cin rai.
" Amma ai da kin ji hujjata"
" Wata hujja ce dakai!!!" Na saka mishi tsawa.
" Na ina sonki mana!"
"SO"
Juyawa nayi cikin masifa nace.
" You don love me"
Da sauri yasha gabana yana cewa.
"Wallahi tallafi"
"Ka min shiru! Macuci azzalumi, mugu."
"Safinah!!"
"Stop calling my name fita kan na baka mamaki."
"Don Allah ki saurareni mana! Ko sau daya ki bani damar kare kaina."
"Hhh kabar gidan nan ko kuma na tara maka mutane."
"But!"
"But What!"
Na tsare shi da ido, sunkuyar da kai yayi, a hankali ya tako gabana.
K'olban da ya saka Anim ya dauko ya bani, sannan yace.
"A da ina tunanin, ina raye ne sabida Asma'u Husnah da MariamSajidah, sai da ga baya na fahimci na shiga zanen kaddarta, na zata zaki sami farin ciki idan ki same Hameeed, sai gashi hankalinki yana wani guri daban. Dr Hameeed nuna shigo dashi rayuwarki, tun daga ranar da kika samun guba hukumar bincike 26 Jordan Agent code 29, tun farko na fahimci aikin kika zo, nayi ƙoƙarin kar wani abu ya dame ki, ta sanadin, nayi ƙoƙarin kare kimarki, Sannan da kome ya gyaru na fahimci waye Ni sai yawa kaddaran, bansan so ba. Ban san mutumtaka ba, zuwanki Rayuwata na fahimci daraja irinta dan Adam"
"Na gaji da jin tatsuniyarka kaje bana bukatarka"
Juyawa nayi zan koma ya rikone.
"Ina raye ne sabida ke"
"Karya kake! Sabida yaranka"
"Ashu! Ka tafi min da kome ka rabani da kome, Ashu taimako kawai nayi amma kome sai Ni, Ashu."
"Ban tafi da kome ba, tun daga ranar da kika kalubalence hukuncina na ajiye ki a matakin Farko "
"Wallahi karya ne kaje nace ka gama dani "
Riko hannuna yayi dukkan biyu yana cikin nashi hannun, "na barki ki auri Hameeed ne dan kiyi farin ciki, dudduniya Ni nafi kowa cancanta zama dake."
Kauda kaina nayi cikin wani irin ciwon da kirjina yake," baka san yadda nake ji ba! Uban yarana ya ci amanata yasa an yaudareni"
"Safinah nifa ba kome nake so a tare dake ba ke kawai nake bukata."
"Har abada bazaka kuma samuna ba, Please go away🙏🏽 kaje Nagode iya haka ma Nagode, mu a cikin ƙabilarmu na arewacin kasar nan, duk macen da rasa Budurcinta."
"A'ah Didih"
Inji Dudu,
"Barni na faɗa Dudu."
Cizon lebbena nayi kwallar na zuba sosai, sannan na cigaba da cewa.
"Idan mace ta rasa shi kuma kowa yasan da haka zai zame mata abin gori agurin mijinta da danginsa ne."
Takawa nayi har gabanshi, Ashraf na da tsawon sosai, dan sai da na daga kaina, ina juyo sautin numfashinsa tare da bugun zuciyarshi, sannan na cigaba da cewa.
"Ba iya kanta ba, hatta jikokinta sai an goranta musu, kasan girman da darajar da mace take ci akanshi, ba iya shi ba cikin ka da yafito a jikina, korata Abba yayi wurgani yayi waje, amma haka Nannah ta tsallaka tayi tafiyarta."
Kauda kaina nayi gefe wasu Irin hawaye ke sauka masu mugun zafi da ciwon,
Sunkuyar da kai nayi ina kuka, nace.
"Na manta kome, a lokacin da ya dace na gina kaina ka shigo min da Hameeed, amma total confuse bansan Taya kuka gama kome ba Amma Allah ya sani."
Juyawa nayi zan bar gurin, ya riko hannuna.
"Tafiya zaki yi? Zagi, duka, kome ki min zan dauka karki juya min baya."
"Har yanzun baka san kima na d'an Adam ba, kaje zan duba Al'amarin basaraken nan me cike da izza."
"SAFINAH!"
Lumshe idanuna nayi domin naji kiranshi tun daga kaina gangan jikina, zuciyata sai da suka amsa, sake hannuna yayi sannan yazo gaba ya tsaya.
"Ki bani dama na gyaran kuskure na."
"Sai nayi tinani akan haƙa."
"Toh wani hukunci zaki yanke min?"
"Sai nayi tinani akan haƙa"
"Safinah"
"Don Allah ka kyaleta, ka barta zuciyarta ta huta, idan kuma kana son ka ga gawarta ne bismillah."
Haɗa hannunshi yayi tare da kallon Dudu yace.
"Ok Nagode yallabai."
Matsa min yayi na wucce, juyawa yayi yana dan dukar kirjinshi, tare da lumshe idanunshi, har muka shige Cikin gidan tare da rufewa.
Sannan yaje Me gadin ya buɗe mishi cike da tausayawa,
Ganin su Ghaniyu yayi da Fahad yaje ya shiga gaban motar tare da kwantar da sit din.
Sannan suka bar unguwar.
***
Ina shiga daki na rufe Kofar na jingina bayana jikin kofar , sannan na fashe da wani irin kuka, yayinda na cusa kaina a cinyata. Ina kuka me cin zuciya hatta su Dudu suna jin muryata, Sophia taso zuwa ya riƙe hannunta tare da girgiza kanshi.
"Barta tayi kuka! Cin amanar ta yayi, amma shima ba yayi bane dan ya cutar da ita yayi ne dan niman soyayyar gaskiya, kuma ya samu kawai tana jin ciwon haka da yayi ne,amma nasan zata hakura,"
Sai da nayi kukan ya ishe Ni, sannan na kwanta a gurin, ina sauke a jiyar zuciya, har barci yayi gaba dani.
***
Koda suka dawo gidan, shiga part dinsa yayi yana shiga idanunshi ya sauka akan agogon bango karfe huɗu da arba'in.
Na tasha ya hango tana barci cikin takura, yau kwants goma da zuwanta amma sam baya kallonta a mace, tsaki yayi tare da ɗaukan pillown ya koma falon ya kwanta, tare da lumshe idanunshi.
*Karya kake!!!*
Itace kalmar da take yawo a cikin kwakwalwar shi, lumshe idanun yayi, amma sautin kukarta bai bar shi ya sarara ba har sai da aka yi kiran sallar farko ya tashi, ya shiga ban d'akin falon yayi alola. D'akin da bakowa yaje ya gabatar da nafilla
Yana idarwa ana shiga sallar asuba, da sauri ya fito. Inda ya haɗu dasu Ghaniyu a hanya, har suka fito basu gane mishi ba, dan yaki cewa kome.
Ya ja bakinshi yayi shiru, ganin haka yasa suka fahimci Akwai matsala dan haka basu takura kansu don bin diddiginshi ba.
Muhammad Ashraf bini Abdullahi Alhashmiyya, ya karanci law, a jami'ar Germany, a degree na farko. Lokacin da ya haɗa karatunsa ya dawo Jordan, Mahaifin Ghaniyu shi yake kula da lafiyar shi. Kasancewar shi shugaban dakarun falon na uku,
Duk lokacin da yaga Ashraf cikin damuwa ya kanyi ƙoƙari bashi shawara da zai fita, dan a lokacin Ashraf bai da wata buri da yafi sanin waye shi, kwantar baban Ghaniyu ya daina zuwa. wato Hakeem, sai Ashraf ya shirya yaje.
Anan ya samu ai Kakar Ghaniyu ce ba lafiya, yana shiga gidan tsohuwar da kwance makauniya tacewa Baban Ghaniyu ya d'agata ta zauna, bata gani ta kalle Hakeem tace.
" Barka da zuwa matashin basaraken, zauna ka bani hannunka."
Juya hannunshi tayi har sau uku sannan ta cire zoben hannunta.
"Dukda musulunci yayi yaki da canfi da kuma duba, amma tun zamanin sarki Yasir nake da jiranka, sai gashi kazo a dai dai zan tafi, amma ga wannan zoben zata zo kamar zuwan ruwan sama a sahara, daga nan zata bud'e maka ganinka, idan ka yarda da ita ka bata wannan zoben. Zaka fahimci abinda yasa.......
Don ALLAH ku tayani warware wannan matsalar😢🤪😜
1.8words kuyi hkr
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
MJ
BOOK-2
21-2-2020
_Kafin na fara zan so na tuna muku kadan daga cikin dabi'ar larabawa wanda dayawanmu mun sani sai dai mun mantane kafin zuwan Muslunci, larabawa sun kasance masu imani da canfe, har takai duk indai zasu kasuwanci su, suka yi gamo da Kaji ko kare sun kasance babu Sa'a, kuduba cikin litattafan fikihu zaku tabbatar da