Showing 93001 words to 96000 words out of 108344 words
Chapter 32 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
Rike shi nayi cikin kuka, "wallahi ba zan kuma ba."
Jikina sai rawan sanyi yake, sai wutsil wutsil nake, ina tureshi.
(🙄) Sai da yayi min wulakancin son ranshi, take zazzaɓin ya kuma dawowa sakamakon kukan da nayi, komawa gefe nayi ina kukan zuci.
Dakyar na sauka a gadon, na nufi ban daki, ina shiga ban d'akin na fad'i a gurin na suma, sabida zafin zazzaɓin da ya rufe ni.
Tashi yayi ya zauna, tare da safe goshinsa, me ya zaiyi SAFINAH ta fahimci gaskiyar shi, wai SAFINAH ke ce mishi dan iska. "Me na tsare miki SAFINAH da kike cutar dani haka."
Shi kad'ai yayi ta surutu, mik'ewa yayi shima dan bai ji motsin ruwa ba, yana shiga ya same Ni kwance, a rikicin ya shiga tare da d'ago Ni jikinshi, yana jijjigani, wuyar hannuna ya rike yaji bugun zuciyata, ajiyar zuciya ya sauke, kwantar da Ni yayi a gurin ya tara ruwan wanka, daukata yayi ya sakani a cikin ruwan, sai ya wanke Ni, sannan ya shiga hura min iskar bakin shi, yana murza hannuna. Cikin ikon Allah na farka da tari, rungume yayi, yana min sannu.
Mai da min gashina baya yayi.
"Kiyi hakuri! Amma don Allah ki daina gaya min magana yadda ranki yaso, SAFINAH ina sonki yasa bana iya hukuntaki sai ta wannan hanyar, Don Allah ki daina tun zura zuciyata aikata abinda zai sani dana sani."
Ni dai ban ce mishi ciki kanka ba haka ya gama surutun shi ya fita Ni kuma na shiga nayi wankar tsarki na fito.
....... Sannu a hankali jituwar tsakaninmu ya kuma ja baya fiye da, bana shiga har kanshi bana mishi magana, abu d'aya na sani nake saka kaina shine bashi hakkinshi, dan na fahimci wannan had'in da nasha ya kuma gigita shi, da zaran ya makale min. Sai nayi da gaske yake kyale ni, shima sabida nakan ce mishi.
"Wannan nacin da kake min shi yake kara rura min k'iyayyar ka."
Toh bai tsayayye ba zai sauka a kaina, dan haka nima nake hutawa, na daina shan haɗin.
Ga baki daya na janye shi a rayuwata, bana shiga sabgar shi.
......... Kallona yayi bayan ya saka agogo, zamu fita cin abincin dare da kuma wayon. Tunda muka fito a cikin lifte muka hadu da wasu turawa, sai cinye kansu suke. Kauda kaina nayi na riko hannunshi cikin nawa, tare da jingina kaina a kafad'arshi.
Kallona yayi cikin murmushi, a hawa na shida suka sauka, suna fita ya juya Ni zuwa jikin liften ya kai bakinshi kan nawa, kauda kai na nayi na ture shi, sakamakon jin abin zai tsaya, aikuwa ya buɗe.
Wata baturiya ce, tsohuwa da ita, tana shigowa ta bude jakarta ta ciro sarkarta cikin harshen France tace ya saka mata.
Wato idan nace muku ban tab'a ganin yar iskar tsohuwa irinta ba nayi karya, dan wani mini jeans ne a jikinta, sannan wata riga da wucce cibiya da kad'an, abin mamaki nonuwarta a tsaye suke kam, tasha kwaskwarimar.
Ture hannunshi nayi na amshi sarkar nasaka mata, dake bana jin yarenta, sai na mata na kurame, sannan na dawo gabanshi na ciro hannunshi na daura akan cikina, na sake mata murmushi.
Itama murmushi tayi min sannan tace.
"Mijinki ne!?"
Cikin English, gyad'a mata kai nayi nima, cikin turancin nace mata eh.
Kallona tayi sannan tace.
"Idan kuka dawo, zuwa gobe ki zo ina hawa na biyar. Zamu fita dake."
Kallon shi tayi cikin niman izini tace.
"Da fatan zaka bani aronta muje mall."
Gyad'a mata kai yayi, sannan muka isa kasa, ta wucce gurin motar da yazo daukar ta, mu kuma muka wucce gurin cin abinci.
..................
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*
4️⃣2️⃣
Tausayin da soyayyar da na nunawa Ashraf ita ce, ta jamin komai. Domin da ita yayi ta amfani yana min iskanci son ranshi, dan haka nima na farka a giyar son shi dole na rama abinda yayi min.
Sai da nagama had'a kayana sannan na shiga wanka, ina fitowa yana shigowa.
Kauda kaina nayi, na shiga shafa mai, zama yayi yana kallon yadda na tsuke fuska. Sai duk ya diririce ya shiga inda-inda, ganin zaman shirun ya dame shi sai ya fara magana.
"SAFINAH! Ko zaki takura ne akan tafiyar na tafi da Zoyah."
Juyawa nayi na kalle shi na wasu mintina, sannan na cigaba da abinda nake yi, kallon bag d'ina Yayi, sannan ya dauke su ya fidda su falon sannan ya dawo ya same ni a kwance, daga Ni sai towel zama yayi a bakin gadon, yana kallon cinyoyina da suke masa dakuwa (🤣😂 Su Malam Ashraf an jima ba a haɗu ba)
Had'iye yawu yayi, yana jin abu na taso masa. Ƙoƙarin danne Kwadayin shi yake, hannunshi ya kai tsakanin cinyoyina yana shafa su. Banza nayi da shi a raina ina cewa, *zaka ji dashi*
Jin yana shirin wucce iyaka, bansan lokacin da na mike zubur ba, fuskana a daure nace.
"Don Allah ka rabu da ni, kaje ka tafi da matar ka, Ni da kake zaman banza dani ka barni na zauna lafiya."
Rike hannuna yayi cikin damuwa yace.
"Kuyi hakuri! Naga kamar na takura miki ne shi yasa nace ko zan tafi da Zoyah ne! Bawai dan na b'ata miki rai bane."
K'asa-k'asa nace.
"B'acin rai na nawa kuma! Hmm dake Ni ba yar dangin nace shi yasa ake nuna min iyakata kaje bani zuwa."
Duk sai ya shiga damuwa, ya rasa yadda zai dani, ga lokacin sai tafiya yake dan haka ya mike waje ya fita, ashe Dudu yakira ya gayawa abinda ke faruwa..
Ina kwance wayata ta fara kara ina dubawa naga Dudu .
Tunda muka gaisa ya shiga kawo min kabili da ba'adi, na dakatar da shi.
"Dudu kenan kace ya kiraka, toh bari na gaya maka wani abu, wallahi babu inda zanje ya tafi da matar shi, na tab'a gaya maka abinda yake min? Ko na tab'a kawo maka karan shi, tunda kaji nayi magana toh ya kure nine dan. Haka bani zuwa ko ina."
"Toh kiyi hakuri Didih ya gane kuren shi wallahi ya damu sosai."
Kashe kiran nayi dan shima haushi yake bani, shigowa yayi ya zauna tare da narke min kamar zai fasa kuka a raina nace.
" Baka ga komai ba"
Ciro wayar shi yayi ya, can ya manna a kunne yace.
"Ummi gata nan"
Mik'a min wayar yayi na watsa Mishi harara sannan na amshi wayar, tun kafin tayi min fad'a na fashe da kuka. Shiru tayi bata ce min komai, jin ina sauke ajiyer zuciya tace min.
"Ki tashi ku tafi Allah ya jibanci al'amuranki"
"Toh Ummi shi baza a mishi magana sai dai idan ya cuce Ni, Ace nayi hakuri.,"
Murmushi tayi wanda naji sautin shi sannan ta ce.
"Waye ya gaya miki ba a mishi magana!? Kina so na mishi fad'a ko!? Toh share hawayenki zanfi mishi fad'a shikenan."
Kamar tana gabana na gyad'a mata kaina.
"Ummina! Kawai kice ya dawo dani gida na gaji da nan d'in."
"A'ah SAFINAH! Ki zauna a d'akin ki."
Cikin wani irin kuka nace.
"Wallahi Ummi bana kaunar zama kusada shi ne."
Shiru tayi ta rasa yadda zatayi dani, kuma ta fahimce halin da nake ciki Indonesiya samu ne na samu sarari.
"Ki cigaba da addu'a, zaki ji saukin halin da kike ciki."
Nasiha tayi min sannan na mika mishi wayar shi.
Fita yayi daga d'akin, ya jima kafin ya shigo ya same Ni, ina saka kayana, zuwa yayi ya rungume ni ta baya yana fad'in.
"Kiya hakuri! Nasan nayi laifi amma Insha Allah zan gyara."
Share shi nayi nasaka d'an kunne na, abinda na Fahimta Ummi tayi mishi magana dan naga jikin shi Yayi sanyi.
Ina gamawa na saka gyalen rigar da nasa, na nad'e shi. Sannan na durkusa zan dauki takalmina ya rigani dauka, sannan ya ciro min, tare da d'aga kafana ya samin, yana gamawa ya mike tare da riko hannuna, a hankali na zare hannun fuska ba walwala nace.
"Ba sai ka rike min hannu ba nagode"
A raina kuwa jin haushin rantsuwa da nayi ne nake gashi nan zan bishi, muna fitowa falo naga Mujaheeda tare da Ablah sai kuka take, amsar ta nayi na zauna na bata nono muna gaisawa da ita, ina gama bata muka wucce part din Nannah, tana zaune jikokin suna kwance a jikinta, dan yanzun wani irin so take musu ko Natashah da take da cikin bata damu da ita ba, sai biyun.
Muna shiga duk muka zube a capter, muna gaisheta, kallon agogo tayi sannan tace..
"Kai da zaka fita karfe biyu sai yanzun zaka fita biyu da ashirin."
Raina nace.
*Allah ya haɗa shi da dai dai dashi ce*
Sosa kanshi yayi sannan yace.
"Na tsaya saka hannu ne a wasu takardun da aka kawo min ne, insha Allah yanzun zamu tafi."
A raina nace.
*Ji karya*
Shigowar Natashah wacce tayi fayau sai uwar kayan nono da uwar hanci, a hankali ta taki har inda nake, ta zauna tare da kallon shi tace.
"Maman Ablah! Baki da kirki rabonki da kizo duba ni har na manta"
Murmushi nayi mata sannan nace.
"Ran gimbiya ya dad'e! Nima ina cikin hidindumu ne amma ya jikin naki, ku ai matan so ne kuma y'ay'an dangi duniya tasan daku mufa yan karere ne dan haka idan Allah ya nufa zamu dawo tare zanzo na duba ki."
Tunda na fara magana Nannah da Ashraf suka zuba min ido, suna jin maganar da nake gaya musu magana a wasa.
"Kai Maman Ablah! Ai kinfi karfin karere, tunda ina ganin shigar Sultan shashinki tun karfe d'aya bai fito ba sai biyu da ashirin, ko Sultan"
Shiru yayi kamar baya gurin, a raina nace.
*Ikon Allah! Ni ina rena kulawar da nake samu ashe idanun wasu na kaina*
Mik'ewa yayi yace..
"Ammyn zamu tafi."
Nima mik'ewa nayi sannan nace.
"Nah zamu tafi, Tashah zamu tafi."
"Allah ya dawo daku lafiya! Hmm SAFINAH, dan tsaya."
Fita sukayi da Natashah, Ni kuma ni kuma na zauna.
"Kiyi hakuri, da abinda ya faru dukda nasan mun miki rashin adalci, amma Don Allah karki ce zaki guje shi, a yanzun tallafawarki yake nima, idan kika juya min baya, duk wahalar da akayi ya tashi a banza, a cikin mata dari dakyar ake cire goma masu Irin halinki, idan da za a cire goman nan ayi tankad'e dakyar za asamu d'aya me irin halin sak, SAFINAH badan Ni ba kodan Yaranki Don Allah ki zauna da shi mana"
Shiru nayi ban ce mata komai ba, dan itama haushi take bani, duk damuwar su yara da shi Ni babu wanda ya tab'a tunanin ina cutuwa ko bana cutuwa, ban san me yasa a duniya sai namiji yaci karen shi ba babbaka da zaran an ga, kafara yunkurin zaka kwaci kanka sai kowa ya fara cewa yaranka da kai kanka, bayan kai ma basu maka adalci ba, babu wanda zai dakatar da ni, dan lokacin da yayi min babu wanda ya dakatar dashi.
Mik'ewa nayi cikin sanyin murya nace.
"Sai mun dawo."
Haka na fita nasame shi da Natashah, tana mishi rigima. Kanta a bisa kafadar shi, yana ganina ya zame kanta a kafad'arshi, yana kallona ina zuwa muka rungume juna, nace.
"Gasu Ablah! Koda ban dawo ba ki rike min su da amana, shine iya abinda zan baki."
"Insha Allah, zaki dawo kuma zan rike su kafin ki dawo."
"Nagode"
Nace mata, sannan muka rabu, shiga motar muka yi ita kuma ta juya zuwa cikin gidan, tunda muka fita daga Masarautar na sauke a jiyar zuciya, ina ji a jikina na bar Jordan kenan, dole na bar shi kodan nimawa kaina martaba, dole na hakura da Ashraf, dan yana cutar dani da zaran nayi magana ya had'ani da Ummina. Kuma dole tayi min fad'a, idan na nisance shi kuwa zai gane irin son da na mishi babu algus, a yanzun bai san darajata ba, tunda ganina yake kawai babu yadda ya iya dani, a yanzun nafi zargin jikina ne yake so ba wani abu ba, dan ko ya-ya yaga wani part na jikina sai ya nemi tab'awa, shi yasa nake tunanin nisanta kaina dashi dukda nasan zan wahala, amma dole na koyawa kaina nisantar shi, a yanzun da yake basarake dole nayi nisa dashi yadda zan bawa zuciyata hakurin rashin sa, tunda ya zame min wani bangare na rayuwata.
Jin hannunshi nayi cikin nawa, kauda kaina nayi tare da zare hannun daga nawa, sake riƙe Ni yayi na juya na kalle shi, sannan na mai da idanuna gefen da nake.
"SAFINAH! Wallahi da rashin mutunci da rashin kunya kike min zan sami nutsuwa, akan wannan shirun da kike min gaba ki daya kin mai da min rayuwa wata irin, Sabida ke na dauki hutun sati uku, amma naga haka bai lik'aki da kasa ba, don Allah ki dai na share Ni bana jin dadi haka."
Murmusa mishi nayi sannan na cigaba da kallon, gefen da nake. Har muka isa Airport din.
Fidda kayan mu akayi sannan muka nufi inda Asalin jirgin masarautar yake aka aka shigar da kayanmu, nima na shiga shi sai da ya gama abinda zai yi sannan yazo, zama yayi kusa dani, tare da riko yatsar hannuna ya mai damin zoben da na mai da mishi, zarewa nayi. Sannan nace mishi.
"Ka kaiwa Natasha ko Zoyah, Ni kam nagode."
Kallona yayi cike da mamaki baki sake yace.
"Wai me yasa kike min haka ne?! Meye laifina, da na gabatar dake a matsayin matar da nake aure me kike tunanin zaki fuskanta a gurin abokan zamanki, wallahi idan Natasha tana shakkar ki Zoyah bazata tab'a barin ki haka ba, dan duk yadda kika so zaman lafiya sai ta dagula miki lissafi, tabbas nayi abinda ya dace ne, amma kike ganin laifine, na nuna baki da daraja bawai bana sonki bane, kisaka ido ki ga yadda zasu kaya da Natashah, domin dukkanin su larabawa ne kuma basa iya adana kishinsu, shi yasa naki jefa ki cikin damuwa, amma kina ganin laifina dan baki nuna ki a matar da nake so, kiyi yadda yayi miki."
"Hmm" na iya cewa domin ban gamsu da abinda yace min ba......
Alhamdulillah Nagode 🤝 sosai
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*
Oum Muwaddah
4️⃣1️⃣
Mik'ewa nayi na shiga had'a kayana, Ina cikin saka kayana naga jakar da Sophia ta kawo min ɗauka jakar nayi na d'an dib'e wani garin daka, da kuma nakiyar Sudan, sai garin kuka wanda aka had'a har da kanunfari da aya tare da marzan kwaila. Tsimi wanda aka jefa dabino me hula a cikin.
Sai wani d'an karamin abu kamar bushashen jijiya, anyi rubutu a ciki.
_Didih wannan gindin ayi ce, koda ke baki bukatar Abbansu Ablah, ki jika da ruwan zafi yana jika kici ki b'oye dan iskokai suka d'aukewa sai ki sha Insha Allah zaku raya daren cikin amincin Allah_
Wani roba na ciro a kayan naji yana kamshin, ina duba saman robar.
_Didi wannan sabulun tsarkine babu wani abin cutarwa dan Nice na hada, sabulun cussion na baby care, sai garin Jujuba magarya, sai d'an sabulun zaitun, sai lalle, da farin miski dashi nake amfani babu matsalar komai_
'
Shiru nayi cikin raina ina jin kaunar Sophia da Nanah Asma'u, bud'e wata leda nayi naga zunguru (Bani mantawa ina da shekara tara zuwa goma, Kakata tana saka min zunguru idan zata mana lalle sallah, a lokacin kuka nake sabida ina son me yankar salate, wannan zunguru malamai likitanci a musulunci sun nuna