Showing 108001 words to 108344 words out of 108344 words
Chapter 37 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
Nannah basu bar gurin ba sai da Ashraf ya dawo gidan, sannan suka bar gurin.
....... A dakin Natashah tana can tana fama da ciwon tun jiya, idan ciwon yayi mata sai ya saketa, har ta fara barci, wayarta ta ciro takirani, ina bakin kofa naji karar wayar dakyar na mike naga Natashah, da sauri na dauka.
"Natashah lafiya?!."
"Maman Ablah! Bani da lafiya kizo."
Kashe kirar tayi, idan hankalina yayi dubu ya tashi, a hankali na mike sannan nacewa yarana.
"Ku nutsu karku fita yanzun Zan dawo."
Gyad'a kansu sukayi na fita da sauri. Na same su, duk suna falon a zaune, ciki na shiga naga itama Natashah ta fita hayacinta, da sauri na fito na gaya mishi, amma yayi banza dani. Sai da nace mishi.
"Toh wallahi idan wani abu ya same yar mutane sai na gayawa Iyayenta"
Ina gama faɗar haka ya biyo NI da sauri, kayanta na ciro nasaka mata. Sannan na ciro duk abinda zata bukata, sannan muka nufi waje da ita, yana sakata a mota ta riko hannuna.
"SAFINAH!!"
Da mamaki na kalle ta sabida bata taɓa kirana ba, sannan ta cigaba da cewa..
"Don Allah idan na haihu! Ki rike abinda na haifa na bar miki duniya da lahira, idan kuma Maah ta karba don Allah ki saka ido akan babyn, SAFINAH ki yafe min."
Fincikoni Nah tayi na fito daga cikin motar, gaba na faduwar, ina ji ina gani suka tafi da ita Asibiti, wanda yake cikin masarautar, sabon Fad'uwar gabana ya kamani lokacin da na nufi cikin gida naga kofana a bude. A hankali nake jin nauyi a kirjina har na isa falon abinda idona ya gane min ne ya bani tsoro da tausayin kaina da rayuwata
Allah sarki Ashe ganina dasu kenan na karshe, rungume su da nayi dazun shine na karshe......✍🏼
Kuyi hakuri Don Allah, rashin wuta muke fama dashi