Showing 66001 words to 69000 words out of 108344 words

Chapter 23 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt

mik'ewa nayi a tsorace na bud'e kofar glass d'in da zaka fito ka sauko kasa.

K'ak'arin Nannah naji sosai na karasa saukowa, basa falo dole na karasa bakin kofar, nasaka hannu zan bud'e, dake a tsorace nake, sai ji nayi an dafani ta baya. Ban iya juyawa ba, na yanki jiki na fad'i a gurin.
.......
A can Ikeja kuwa gudu sosai Ashraf yake, kamar zai tashi sama. Yana ce musu,
"Safinah tana cikin matsala naji haka a jikina, zuciyata tana girgiza. Duk yadda akayi wata matsala,"

Sosai yake bawa Motarshi wuta, suna isowa ko parking me kyau bai yi ba, ya fita a motar, zuwa cikin gidan.


Turus ya tsaya sakamakon hango Ni da yayi kwance cikin ruwa, da sauri ya karasa, ya d'ago Ni zuwa sama, sannan ya dawo, yana kallon ruwan yadda yake komawa d'akin Nannah, wacce take daure sama gadonta.


Kunce yayi ya fidda ita falo, sannan yaje dakin Natashah ranshi ya b'aci sosai, yana shiga ya damko gashin kanta, yana janta har falon sannan ya wurgata gaban malamin ya kalli Ghaniyu yace.
"Kuyi abinda ya dace zan koma jikin SAFINAH ina ga zan kaita Asibiti."


Juyawa yayi ya bar gurin, zuciyarshi kamar ya fito shi ba damuwar shi Abin cikin ba Rayuwar SAFINAH, koda ya hauro yaga yadda nake, zuba min ido yayi sannan ya dauke Ni zuwa ban d'aki ya wanke min jikina, gani ba kadan ba, dan cikina ya kara girma.


Haka ya gama min sannan ya saka hannu zai dauke Ni na buɗe idanuna nayi akan shi cikin sanyin murya nace.
"Ashuu!?"


Rungume Ni yayi sosai ina jin saukar kwallar shi a gadon bayana, tare da shafa bayana.
"Me yasa baki jin maganata!? Kinsan yadda naji kuwa Ni nayi kamar bani da sauran amfani, SAFINAH badan Ni ba, kodan cikin jikin ki, guji abinda zai sanya ki damuwa dan nine a dame.....



🤸🤸 Gaba dai gaba dai Yar Abu Uwar Abu, Kanwar Anas da Sama'an, Yayar Hauwa'u da Abbas,Uwar Muhammad, Matar Usman Zunnur,Yar Manga jikar Musa da Abdullahi, Kanwar Habiba Kanwar Zainab, Kanwar Bara'atu Kanwar Rajja'b, Turmin tsakar gida shaluguden Mahassada 😂🤭🤣 Kowa Ya iya ya huta, kaji dodon su, me farin jini masoya me farin jinin makiya, nagaida Asbari a daura Dole ko a daurani dan ruwa ko a daurani dan rana, kuturwan Uwa zama dani ya zama dole, nakiyar kan kabari maganin me kwalama, wujiji motar gawa ya dauki masoya ya dauki Makiya, makiyana fadawana Ya Allah mai da min su abin tinkawo da alfahari yadda sara da sukarsu bazai hanani isa bakin gabb'a ba.🤭🤗😂😆


Kirari naji sha'awar yiwa Kaina.......
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah


2️⃣9️⃣


"Yau da wani abu ya same ki ya kike tunanin zaki, don Allah ki rufe min asiri. Ka sauka lafiya naga abinda Allah ya bamu."


Nayi laifi sai dai daga yau nasaka a raina zan gyara, zan gyara kuskurena da nayi zan daina rashin jin maganar shi.
Kwantar da kaina nayi a kafad'arshi cikin kuka nace.
"Ashu bazan kuma ba, kayi hakuri na daina."

Shafa kaina yayi yana goge fuskarshi.
"Good Girl! Ki nutsu zamu fita yanzun."


Gyad'a mishi kai nayi,muka fito. Doguwar riga da unders d'ina ya ciro min, da gayya ya ciro min bra, hararar shi nayi tare da tura mishi baki. Murmushi yayi yana shafe beard d'inshi. Vaseline lotion ya shafa min a ƙafana da hannuna, sai ya lakuta min na goga a fuskana, sannan ya taimaka min nasaka kayana. Mika min tozali yayi na zizara a idanuna, sannan ya dauko roll on, na murza a hammata na na tashi nasaka ka kayan,


Tsayuwa yayi yana kallon d'an kwalin, ya dauka yana juyawa. Kafin ya mai dani bakin gado, ya daura min kamar yadda nake yi, d'ago kaina nayi. Ya sumbaci goshina, tare da jan kumatu na. Sannan ya juya gurin da nake ajiye man baki ya miko min na shafa, tare da mika mishi.


Kafin na saka hijab dan tsakanin da Allah ya hanani yafa gyale. Shi ba d'an kasa ba amma yafi yan ƙasar tsantsena. Wani lokaci haushi yake bani saboda ina son saka gyale da wasu kayan amma ya hanani.


......... A hankali muke saukowa, yana rike da hannuna yaran na bin bayanmu, wato tun shigar shi ake fama da fatalwar. Yaki fita yana ganina kuwa, ya koma ya makura Nannah, yana likata da kujera,(🤣😂✋🏽🤭🤔 K'iyayyar ku da Nannah ya shahara Queen Hafsy Allah ya nuna min ke da tsanar Nah da kika yi)



Abin tausayi, rike shi nayi gam sabida goyo guba, duk lalacewar uwar goyanka sai kaji tausayinta. Balle ni da Nannah ta lalata min rayuwa, tabbas ita ce silan komai da yake faruwa dani. Ba karamin wahala take sha ba, a hannun Natashah.
Tunda muka fita na d'aura kaina a kafad'arshi, ina sauke ajiyar zuciya. Ciwon nake ji kad'an-kad'an, bana son na gaya mishi hankalin shi ya tashi. Shi yasa nayi shiru. A hankali yake jan motar, kaina a jingine da sit nayi tare da lumshe idanuna, abinda nake ji kamar haihuwa ce. Amma bani da tabbacin ita d'ince, har muka isa country mall. Nannah muka je ya kai Ni layin kayan baby. Nan na shiga Baby, dukda kullum naje awo sai na tsinto wasu. Haka na shiga kwasa, durkusawa nayi zan dauki wani set d'in kayan Baby, bayana ya amsa, salati nayi da tare da zubda kayan ina rike bayana, da sauri yazo bayana ya tsaya duk ya rud'e.


"Sannu! Meke damunki!?"


Ganin ciwon ba me, tsananin bane ya sani b'oye masa nace.
"Babu komai."
Mik'a min shi hannu nayi ya d'aga Ni yayi, dakyar na mik'e ina cizon lips d'ina.
Ihun Yara muka ji, sai muryan wata Balarabiya na fad'a, da sauri muka isa gurin, Aamih matar takewa fad'a Yarinyar ta wani dagwadagwa da fuska, alamun zatayi kuka.
"Mariamah!!"
Na kirata da sauri, musamman da naga matar tana zungure mata goshi. Ashe tun isowarmu Ashu cak cike da bakin ciki. Ya juya zai bar gurin, naji wani mutumin yace.
"Sultan Ashraf!!"
Da sauri ya bar gurin bayan ya dauki yaran, kallon mutanen nayi naga suma sun bi bayanshi, dakyar nabi bayan su, har yasasu a mota. Ya dawo riko hannuna yayi tare da bud'e min kofar motar ya sani. Zai ja motar Mutumin yace.
"Sultan Ashraf! Ka saurari muryan Al'ummar Jordan."


Ganin da gaske ba kula shi zai ba, kuma yana ƙoƙarin tadda motar.
Shima ya shiga nashi, suka shiga wasan tsere a garin Lagos. Ga ciwon da ya turmushe Ni.


Juya kaina nayi, a wahale na riko rigarshi nayi cikin tashin hankali nace.
"Ashuuuuuu!"


Zufa neke zuba daga jikina ko ina, a rud'e ya kalle ni. Duk ya firgice.


"Asibiti"
Hmm Allah ne kad'ai yayi mana jagora, inda muka isa wani asibitin kud'i.
Muna isa ya fito ya bud'e min, yaran sai kuka suke. Nayi nayi na fito na kasa, nace mishi.


"Fitar da Yaran, ka kira nurse dan basai mun,cire min pant"


Abin dariya duk ya rud'e, fita yayi da yaran, kafin. Ya dawo na fara nishi, yana dawowa tare da Nurse da matar muka had'u a mall, ka ai dole ya koma gurin mutumin, yaki masa magana hankalinshi na kanmu.
Mu kam muna cikin fama dan yanke pant d'in suka yi da almakashi, ana yankewa Allah cikin ikon shi sai ga d'an baby ya fad'o. Ajiyar zuciya na sauke tare da jingina da jikin sit d'in motar.


D'aga babyn sukayi tare da ce min, kinga abinda kika samu.


D'ago kaina nayi naga Yarinyar yar katuwa da ita, abinda na fahimta Ni haihuwar bakwaini shine nawa yanayin, dan ita wannan tafi su Aanih girma, d'an kwalina na ciro aka nad'e yarinyar.


Sannan suka mik'a mishi ita Ni kuma aka gyara ni muka shiga cikin Asibitin.

★★★
Jordan.....
Da sauri Salman bini Abul Bashari, ya shigo tare da rungume Abu Zarri yana dariya yace.
"Alhamdulillah! Sultan yana Nigeria, yau matarsa ta haihu."

"Masha Allah! Toh taya zai shigo! Shine maganar gaskiya, domin kuwa duk yadda kaso ya shigo kasar a sirrice Yadda ba zai isa kunnen Bilal. Shine nake buƙata, so nake ya shigo kasar ba tare da an sani ba, yadda mu kadai ne muka sannan da shigowar shi, taya zamu amshi kasar jordan cikin lumana ba tare da an zubda jinin kowa ba, kasar ta dawo hayacinta."


Wannan labarin ya zaga kunne masu dadin dawowar Ashraf, amma ba a faɗa inda yake ba, gudun faruwa wani abu, amma tabbas magana take kunnen Bilal, nan ya shiga girka jami'an ko ta kwana. Tare da jami'an sirri.


★★★
Bayan a gama gyara mu aka sallame mu, dan nace bazan zauna a asibitin ba. Gida ya dawo damu, tare da mutanen da muka had'u a mall, sai da nayi wanka. Sannan aka kawo min abinci naci, sai ga Ghaniyu da Fahad, suka dauki babyn cikin so.
Kallon shi sukayi tare da kallon Mutumin, wanda yake basu labari da harshen Jew, (Yaren Yahudawa! ) Ashraf ne ya juya harshen sabida Ni, dan yasan matuƙar naji abinda suke tattaunawa akai, (😠😡) Allah bazan yarda ba shi kuma baya son tashin hankalina. Shi yasa ya juya mishi harshen.


"Sultan! Jordan tana cikin wani hali, Don Allah ka dawo ana niman ka."


Gyara zama yayi sannan ya kalli Fahad cikin damuwa yace.
"Ni kaina ina son komawa mahaifata! Ba da sunan sarki ba, dan bazan iya jagoranci haske a cikin duhu ba, bazan iya zama cikin duhun damina magani me Kwadayi ba, taya zan jagoranci Al'ummar kasata bayan bani da gogewa ta kimiyar siyasa! Taya zan zauna a cikin al'ummar da basu san dani ba, kowa a cikin masarautar kanshi ya sani, anyi laifi wanda zan hukuntan shi yake da magoya baya bila'adadin! Ni anyi Ni dan Iyalina ne ban haifu a duniyar damuwa ba, ka koma ka basu hakuri Ni na hakura da Mulkin, sabida mata biyu masu daraja da kima, kuma zuciyar su bata cikin jordan. Mulkin jordan baya cikin maudu'insu don Allah, kaje kace musu, su hakura da abinda da Allah ya basu."

K'arban kariyar yayi ya kawo min, ita sannan ya sumbaci goshinta. Yana kallona yace.
"Nagode! UmmulKhair! Kin bani komai a rayuwata, kin zauna dani a lokacin da nake bahago, kin zauna dani alokacin da nake, dai dai, SAFINAH wacce irin sadaukarwa ce haƙa, wacce irin soyayya ce haka. Da ina Ni d'aya yau kin maidani alkarya me dauke da al'umma guda. Fad'a min me kike buƙata."


Mika min hannunshi yayi ya zauna a bakin gadon. Idanuna ne suka kawo ruwa.
"Kayi min Alkawarin bazaka koma jordan ba"




Rike hannuna yayi cikin nashi yana murzawa, murmusa min yayi sannan yace.
"Idan Jordan kaddaranki ce dole ki jera, idan kuma bata cikin zanen Kaddararmu dole su hakura, bazan miki alkawarin da bazan iya cikawa ba, matuƙar hakan na cikin zanen Kaddararmu, sai dai na baƙi hakuri."


Janye hannuna nayi daga gare shi, na juyar da kaina, can gefe kuka ya kwace min, me yasa ban tab'a tunanin wannan lokaci ba, me yasa na saki zuciyata da raina akan bazai taɓa komawa ba! Ji nayi zuciyata tana kin amincewa da abinda da nake cewa, na nuna son kai. Nima zan fara butulcin rahama Ubangiji, rintsa idanuna nayi janyo wayata na shiga niman Ummi, tana d'auka na shiga rera mata kuka, fita yayi daga d'akin, na shiga gaya mata halin da muke ciki, rufe Ni tayi da fada, sannan ta shiga kwarara min gwiwa da cewa.
"Haba! SAFINAH anya kece kuwa!? Yaushe so yayi miki illa haka, ki dawo SAFINAH da da nasani jajjertacciya mara tsoron wannar da nasani me kafiya da taurin kai, ki goya mishi baya. Ki nutsu ki fahimci alkiblan mijinki, ki kuma girmama al'amarin shi, ki sani wata duniya zaki bishi, inda dole ki yaki soyayyarku ki bashi daman zama cikakken shugaba, bawai ki kina nuna mishi gazawar ki ba, idan kika karaya bazai tab'a cigaba ba, SAFINAH duk wani cigaban da namiji zai samu, dole sai da taimakon Y'a mace, haka duk wata cigaban da Y'a mace zata samu sai da taimakon D'a namiji, ki had'iye tsoronki dan koda tsoron za ayi galaba akan mijinki, shi ya kike so Yayi!, Zai ajiye alummar shine yazo kareki, ko zai tare a jikinki ne, wannan kukan banza mara fa'ida ajiye shi za kiyi, kefa uwar Yara uku ce, taya zaki koyar da Yaranki!? Da raunin zuciya, ko da Kuka. Ki nunawa Mijinki da duniya a shirye kike ki tsaya mishi kamar Yadda ya tsaya miki, ko zaki barshi ya tafi da damuwarki ce"


"A'ah Ummina!?"
Nace mata a hankali.
"Yawwa! Sarauniyar Jordan matar Sultan Ashraf, Uwar Asma'u,Maman Mariamah, Yayar Abdullahi, Addar Asma'u, Didin Batul, Auntysu Khalilah da Khalil, murmusa min Yar badaru, D'iyar Mariamah....."


Kwallar da murmushi na sauke lokaci guda, nace.
", Allah ya bar min ke Ummina duk Ni d'aya."




(🤣😂🤭 Allah kufa kusan mutane 700 taya zan muku kirari ki zab'i mutum d'aya na wasata)


🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah


3️⃣0️⃣


Murmushi na sake tare da goge hawayen dake kan fuskana nace.
"Ummina! Allah yaja kwananki Nagode sosai da bani kwarin gwiwa,"


Murmushi ta sake min, tare da kara min haske sosai, sannan muka yi sallama da ita, shigowa Nannah tayi tare da zubawa Yarinyar ido, sannan tace.
"Sannu! Kita cika gida da Yan mata, da zaki tona zuciyarshi d'a namiji."


"Ammyn!!?"
Ya kira sunanta a hankali, dukda haka zaka fahimci cewa ranshi a b'ace yake, juyawa tayi tana kallon shi, ta had'e giran sama da na kasa tace.
"Tsakanin ka da Allah baka fi son D'a namiji ba"


Takowa yayi har bakin gadon ya dauki Yarinyar yace.
"Idan zata haifa min Mata dubu Zan amshe su cikin farin ciki da murna sabida na fison su sama da kome Ammyna, Ni Y'ay'a Mata nake so ba maza ba, kuma Safinah tasani. Ni farin ciki na shine ta Allah ya bamu Y'ay'a Mata, dan haka ki daina tunanin ina da burin d'a namiji."


"Muhammad! Ni kake gayawa magana akan Mace!? Anya kana son karewa lafiya."

Riko hannuna yayi sai ya sake Ni, sannan ya shiga had'a min kayana, a cikin manyan jakuna.
"Don Allah! Ashu ka bari, idan kuma ka had'a min kayan idan na tafi bazaka kuma jin duriyarsu ba, ina tare da kai a kowani hali Ni dai Kabi Abinda ranta yaƙe so, idan ma tace bata son zaman mu, na amince ƙaddara da rabo ya had'amu, amma bijirewa Mahaifiyar ka ba abu me sauki bane, don Allah ka rufa min asiri, kar ka b'ata min zuri'a da mugu fenti."

Juyowa yayi yana kallona, idanunshi cike da kwalla. Buɗe mishi hannuna nayi, ya karaso ya shiga, na rufe shi a cikin jikina, yana kuka sosai a jikina. Jikinta ne yayi mugun sanyi, ta fita a fusace.

Abin tausayi ban masan ta yadda zan kamanta rayuwar da muke ba, amma tabbas akwai jarabawa me girma da ikon Allah, wanda yake tare da zanen Kaddararmu. Ban da rabo babu abinda zai kai Ni jordan, rabo me karfi ma ko nace rabon wahala, dan wannan rabon ya jefani cikin damuwa sosai, shafa bayanshi nayi cikin rarrashin ina maida kwalla na,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login