Showing 15001 words to 18000 words out of 108344 words

Chapter 6 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt

kaini gurinsu Ummi, tunda muka shiga Ummi ke cewa.
"Masha Allah!"
Zuwa nayi na zube a jikinta, ina sauke ajiyar zuciya.
"Sannu gajiya ko!?"
Gyada kai nayi tare da gyara kwanciyata. Nace,
"Khalilah matsa min karama ciwon suke min."
Cikin tausayawa, ita ta kama daya Batul ta kama daya suka shiga min, tausa.

Cikin jin dadi barci yayi gaba dani....
***
"Ayya! Ku duba min beauty."
Yadda ya damesu da beautyn yasa Ashraf barin shashin dan wani baƙin cikine ya cika mishi zuciya, gudun kar yayi abinda zai yi,
Yana shiga dakin shi, ban daki ya wucce, dunkule hannunsa yayi ya kaiwa Madubin cikin ban dakin naushi, haka suka fashe tare da tarwatsawa a cikin banɗakin, haka yayi ta naushin Madubin da hannunsa duk ya jima kanshi ciwo. Idanunshi sunyi wani mugun ja, ga azaba Ben kishin da yake damunsa.
Sai da ya gyara ciwon hannunsa sannan ya fito, hannun daure da bandaji.




Tunda Dudu ya zo yasamu ina barci, yaje ya gayawa Dr, ban tashi ba sai bayan awa ɗaya sannan na farka wanka nayi da alola. Na fito na gabatar da Salla.

***
A cikin kwana uku da muka yi idan kaga Ashraf ya zabge sosai tare da mugun rama, duk da nasan dalilin ransa sam bai wani dame Ni ba, sabida babu wata alaƙa a tsakanin mu.

Yau aka shirya dinner kuma a cikin babban filin masarautar, za ayi dan haka Kowa zai.


Karfe tara aka fara hidimar, dukkanmu mun shirya cikin wasu gown Ni bawa dark green, sai Dr da yasaka suit ashe colour, muka fito.
Hannunmu sarke da juna, muka je inda aka ajiye abin zama muka zauna. Amarya ta riga Ango fitowa.
Yana can ya saka tarukan hannunshi, a fuskar shi yana tunani. Sau uku Nannah tana zuwa da kanta, Amma yana kin buɗewa. Duk wandaake tunanin zai masa magana yaki fitowa, ba dan me Dudu ya gayawa Dr ba sai dai ya tashi ya riko hannuna, muka nufi part dinsa.
Umarni Dr ya bani na buga, amma yaki budewa sai da nakiya aunanshi sannan ya bude kofar, ya fito cikin shirinsa.
Mikawa Dr hannu yayi, suka gaisa sannan muka fito, ina manne da Dr. Kamar bai ga abinda muke ba, nan kuwa idanunshi na kanmu yake. Ranshi na kara ɓaci sam baya jin zai iya yafewa zuciyarshi akan katsalanda da tayi mashi na rabashi da abar kaunarshi,
Har muka zo inda zamu zauna, shi kuma ya wucce gurin zaman shi, hankalin mu kwance muke hira da Dr tare da Dr. Kowa yaga yadda muke cikin farin ciki sai mun burgeshi.


Anyi nisa a shagali na zare jikina zanje ban daki.
....


Har na isa na gama uzurin nafito, a baƙin kofa na ganshi tsaye, tamke fuskana nayi cikin sauri, yayi maza yasha gabana.
"Meye laifina! SAFINAH! Kawo hannunki kiki, SAFINAH mutuwa zan."
Matsowa nayi zan wucce yayi sauri zai tabani nayi, na matsa cikin zafin nama ya kai hannu zai tabani a karo na biyu kafin yayi yunkurin tabani na Kifa mishi mari, wanda yayi sanadin zubda kwallana, shi kuma hancinsa ya fashe har yana zuba da jini.
D'ago kai yayi cikin izza hadi da mugun mulki, jinin sarauta na yawo a jikinshi, chafko wuyata yayi ya matseni a bango, kafin yayi kokarin haɗa jikina da nashi na kuma zuba mishi wani mari, na kuma marin shi.
Zare hannunshi yana kallona, zuba gwiwarshi muryanshi na rawa, yace.
"Ki min kome SAFINAH! Kawai ki dawo garemu"

"Kai jahili ina ne? Da aurena kake bina, Muh'd ka gaya min meye nayi maka da zafi haka ka rabu dani mana, don Allah ka barni nayi Rayuwata da mijina."
Tunda muka fara rigimar Dr yake tsaye, bai iya motsawa ba, sai da yaga zan fito ya juya da sauri ya koma inda ya muke, ina zuwa gurinshi na zube a jikinshi ina kuka nace.
"Baby! Mu bar garin nan."
Rintsa idanunshi yayi zuciyarshi na zafi, ji yake kaman ya an cimma mishi wuta, ji yaƙe kamar ya rufe Ashraf da ya fito jikinshi ba laka, yaƙe ya zauna yana goge hanci sa da jini yake.

Kukan da nake sosai nake ganin kamar hankali mutanen zai dawo gare mu ya mike dani muka koma masauki sa, muna shiga cikin d'akin na ajiye Ni. Ya juya abinshi.

Wannan shine karon farko da ya fara jin ciwon akan aurenta, bai ga dalilin da zai bar Ashraf yana tun kara matarsa. Dole yau zasu bar garin dan.

....... Nayi kuka har na godewa Allah, banga Dr ba, har kusan Asuba, da nafito na hango shi zauna a kan kujerar, takawa nayi gabanshi, tare da saka hannuna akan gwiwarshi nace..
"Hameed! Nasan kaga abinda ya faru tunda kaki zama kusa da ni Hameed do.."

"Don Allah karka juya min baya ko? Safinah da tun farko kin nuna min Uban yaranki SAFINAH da ban shiga rayuwarki ba, Safinah abinda kika min baƙi kyauta min ba, amma banga laifinki ba, nine me laif.."
Rufe mishi baki bayi da hannuna, a hankali na shige jikinshi, ina kuka.
"Don Allah ka yafe min wallahi kai nake so, Hameed daka rabudani gwara ace bana numfashi. Don Allah kabar Mutuwa ta rabamu, karka.".

Haɗe bakinmu yayi, nima na riƙe kanshi. Shi kuka Ni kuka dan mun fahimci rabuwa da juna ba abu me sauƙin bane, tun daga wannan kiss din abubuwa suka sauya, sosai ban taba jin dadin kasancewa da Dr ƙamar yau, shima ya fahimci haka, kwantar da kaina nayi a kirjinshi, ina sauke ajiyar zuciya, a hankali yake shafa bayana, a Sannu har barci yayi gaba dani. Leka fuskana yayi a hankali yaga yadda yanake barci, shafa fuskana yayi a hankali don da tausayi, ji yayi zuciyarshi tayi mishi nauyi tausayin kanshi yake ji, wani iri yake ji. Bakin yanayin da yake ji a jikinshi. Musamman mugun ganin da yayi ya kuma karya mishi zuciya.


Lumshe idanu yayi a sannu barci yayi gaba da shi, bamu farka ba sai karfe shida na safe da sauri muka shiga wanka a tare, muna fitowa sallar muka gabatar, sannan muka koma gado Dan barci bai ishenmu ba.
Ina manne cikin jikinshi, kaina yana kirjinshi, dan haka fitar numfashinsa yana sauka a kirjinsane, shafe kaina yayi cikin jin kunci irin na wanda yake jin zai rabu da abinda yafi so a rayuwar shi, damuwa ce ta ƙara mishi yawa. Mikewa yayi zai fita daga d'akin, yayi maza tare da riko hannunshi, nace.
"My Man! Ina zaka je i need you."
Haurowa gadon yayi cikin sanyin jiki. Ya janye bargon ya shiga min tausa, juyar dani yayi ya zuba min ido, ganin yadda nake mika yasashi shiga cikin bargo a sannu ya cigaba da min tausar tare da salon shine me taba zuciya, lumshe idanuna nake ina bud'e su, shigewa jikinshi nake sosai yasashi fahimtar ina bukace dashi........


Kuyi har maneje
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah......


MJ
BOOK-2
19-2-2020


🖐️✌️


"Hameeed! Karka juya min baya, a lokacin da nake bukatarka, Hameeed!"

Cak ya tsaya hannayen shi duk suna cikin aljuhun wandonshi.
D'aga kanshi yayi sama cikin jimamin hukunci da ya yanke, karshe yasa kai ya fita, wacce itace fitar da yayi a rayuwata.


*(Tabbas nayi rubutu akala goma sha tara a rayuwata, Masarautar Jordan yasani jin kaina wata daban ban wannan shafin ya ƙaryata min da zuciya ya sani jin kamar nice jikina yayi sanyi, ban taba duban rayuwar macen da ta rasa mijinta da yardanshi ba amma yau naji ina tausayawa matan da aka shiga tsakaninsu,Labarin Sadaukarwa ce garesu)*


Yana fita yaga Ashraf jingine da bangon, murmushi yayi sannan ya dafa kafadar shi, yace.
"Yanzun na sauke nauyin da yake damun zuciyata, na bar maka baiwarka, amma kayi ƙoƙarin janye tunaninta. Iya haka ne zai sa ta fahimceka, Don Allah nan gaba ka gaya mata gaskiya aiki kasani ba yin kaina bane."
Gyada Kai yayi tare da mai da kwallar da yake ciko mishi idanu.
"Nagode sosai Dr Abdulhameed! Tun daga haduwarmu kake taimaka min, sai dai bana jin zan Safinah zata yafe mana, sabida munyi wasa da hankalinta."

"Toh! Wallahi kai da ita nikam aiki kasani, kuma nayi maka, bani da niyyar aurenta kasani. Dan haka ya zama maka wajibi ka."
Cikin tsare gida Ashraf ya kalli Dr.
"Kayi hakuri! Yallabai."
Fita yayi daga ware din zuwa inda motarshi yake, ya zauna tare da kallon Sa'imah wacce ta cika ta batse.
"Ayya na zata kwana zaka a gurin ta!"

"Bazai yi na kwana ba, sabida iya abinda aka dauke Ni nayi da akwai wani abu bayan haka da zanyi."

Cikin jin ba dad'i tace.
"Ban gane ba!?"

"Eh zaki gane"
Nan yaja motarshi ya bar asibitin,
***
Kuka nake me mugun cin rai ji nake kaman na had'iye zuciyata na huta, ina jin aka bud'e kofar ban daina kukan ba, jan kujerar yayi ya zo dab dani ya zauna, yana kallon yadda na fita hayacina, amma dan jaraba shi kukan da nake dad'i yake mishi sai wani lumshe idanunshi yake, tare da gyada kanshi,

Shigowar Dudu bai sashi d'ago kanshi ga kallona da yake ba. Sai ma kura min ido da yayi, da sauri Dudu ya iso gurina yace.
"Didi! Kiyi hakuri don Allah. Wallahi banda Ashraf da yaje gida dazun ba Allah."

Zuwa yayi ya tsaya duba ruwan da aka saka min. Kallon takardan da yake hannuna yayi, a hankali ya zare a hannuna, tare da warwarewa.
*Ni Dr Hameeed nasaki SAFINAH saki d'aya."


Rintsa idanunshi yayi cikin zafin zuciya, yafi minti biyar a haka, Sannan ya buɗe idanu ya,
"Safinah me kulawa Hameeed ya sakeki"

"Sabida yagama yayinshi da ita, kamar Gwanki"

Cikin mugun fusata yayi kan Ashraf wanda yayi fuska kamar bashi yayi magana ba, dan dama tsakanin dudu da Ashraf bawani jituwa bane, kawai suna dan zumunci ne sabida, yaran dashi suke tsakani.


Kwalar rigar Ashraf ya cukumo ya kawo shi bakin kofa ya watsar cikin gargadi yace.
"Kar na kuma ganinka a rayuwata, ka kyalemin yar uwa ta huta."


"Idan zaka wulakanta Ni sau dubu bazan daina ba, sabida ita ta koya Min kome, zaka iya sawa ayi min kome Ni dai don Allah ko sau ɗaya ne kabarni na dinga ganinta"
Banka mishi kofa yayi tare da komawa gurina. Zama yayi yana son sanin abinda ya faru.
Amma na kasa cewa kome sai kuka, Banda kuka.
Har dare Dudu yana tare dani, duk wani kulawa shi yake bani.


***
A hankali sauki yake samuwa, gefe kuwa Dudu. Na kaftawa Ashraf wulakanci, kuma yaki ya barshi ko sau daya ya ganin, har ofishin Dr Dudu yake, sukayi fada sosai karewa ya ajiye musu aikin su, babu abinda ya ƙarya musu zuciya akan Dudu sai kukan da yake tare da cewa.
"Nan ka bada lokacinka akan SAFINAH, ashe shigo ba zurfi kamata, tare da cutar da zuciyarta. Meye laifin yarinya da ta mutu akan ka, ban taba jin tsanar kowa a duniya sama da kai ba, yarinyar da ta hadu da jarabawar Rayuwa zaka wulakanta. Ba kome mun gode sosai ai kayi namijin kokarin, ga takardanku. Na ajiye muku aikinku."


Yana gama gaya musu haka ya juya yabar Office ɗin, yana zuwa d'akin da nake, yaja kujera ya zauna yana kallona, na cusa kaina a cikin cinyata.


"SAFINAH! Haka zamu cigaba da zama baƙi ce min kome ba, aiko sau daya ne zaki ce min wani abu."

Duk maganar da Abdullahi yake naki d'ago kaina, banda zubda kwalla da nake bana kome, sam bana iya cewa kome.
"Toh tashi mutafi gidana."
A sannu na d'ago kaina. Na sauko daga gadon, na dauki hijabi na nasaka sannan na jira shi ya gama hada kayanmu, haka muka fito jikin Dudu na koma tare da rike rigar shi, ina b'oye fuskana a jikinshi.
Muna zuwa gun motarshi ya buɗe min na shiga tare da kira kaina.
"SAFINAH!!!"
Muryar Ashraf naji, sake rintsa idanuna nayi, yazo da gudu zai buɗe Kofar, tureshi Dudu yayi ciki masifar da dama abokin mutuwa yake nima.
"Wai kai wani irin masifa ne haka? Ka rabu da ita dole."
"Don Allah ka barni na ganta ko sau ɗaya n"
Wanka mishi mari Dudu, bai damu ba ya kuma zuwa zai buɗe motar, Dudu ya sake tureshi. D'ago kai nayi naga yadda dudu yake dukan Shi.
Wani irin tashin hankali naji ban san lokacin da na buɗe kofar motar Ba.
Zuwa nayi na riƙe hannunsa, ina girgiza mishi kai hawaye na zuba daga idanuna bakina na rawa nace.
"Toh meye amfanin haka, kamanta waye shine? Ko dan baka san irin Daular da ya fito bane, masu tsaro dari biyar suke tsaron lafiyar shi, kartine majiya karfi, yafito ta gidan da ko karar sautin faduwar abu akaji mataki ake dauka, shugaba ne na al'umma guda. Kabilu uku ne a karkashin mulkinsa, kimanin yan majalisu dari da goma ke, bashi goyan baya, hatta manyan attajiri da yan kasuwa suna bayan shi, shine zaka dake shi, yaushe ka zama mara tausayi da, da zaka dake shi, badan Kowa ba kodan su Mariamah da Husnah Zaka daga mishi kafa, kazo mujee yanzu ba lokacin rigima bane."


Jikinshi yayi sanyin yabi bayana, muka shigo motar, kauda kaina nayi dan bana son na cigaba da ganin jinin da ke zuba a fuskar shi. Tunda muka fara tafiya, babu wanda ya iya cewa kome. Banda kwalla da ya ɓalle min a idanuna babu abinda nake, tissue ya mika min na amsa a hankali.
"Kiyi hakuri! Amma wallahi matukar zai zo inda yake zan wulakanta shi, gwara ya nisanceki shine zaman lafiyar shi"
"Toh meye yayi maka?"
Na tambaye shi muryata na rawa.
"Didi na tsaneshi! Sabida shine mafarin matsalolinki"
Murmushi nayi dan ya bani dariya da tausayi.
Ban kuma ce mishi kome ba, sai dai fuskar Ashraf yaƙi fita a cikin idanuna, ina masifar jin zafin digar jininshi, kurawa hanyar ido nayi.
Wasu abubuwan na tuna kuka ya kwace min, yama rasa tacewa.
A haka muka isa gidanshi, dan yasan koda ya kaini gidan mu akwai matsala.


***
"Amma me yasa ka bar shi ya dake ka haka?"
Goge fuskar shi yayi. Sannan yace,
"Bazan rama ba, sai dai nafison duk lokacin da zai min haƙa yayi akan idanun ta, so nake na suna girma matsayina a zuciyarta, kamar yadda ta same matsuguni a zuciyata so nake naga haka a cikin idanunta, duk abinda ya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login