Showing 105001 words to 108000 words out of 108344 words
Chapter 36 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
Kwanansu Ummi biyar suka dawo, ana gobe zasu dawo Abba na yakirani, naje inda yake duk suna zaune na zauna a gefen Umma. Kallona suka yi sannan Abba yace.
"Kuyi hakuri! Allah zai baki wanda suka fisu! Sannan na fahimci kina cikin damuwa, kiyi hakuri ki cinye jarabawarki, Insha Allah komai zai zo karshe."
Nasiha suka min, mun jima muna hira, kafin muka yi sallama, har zan fito naji Muryan Ummi tana cewa.
"Alhaji idan zaman ba me yuwa bane ta dawo gida kawai, na gaji da fitina, nima ina son Y'ata, ta bar mata D'anta."
"Amma Mariamah me yasa zaki d'aga murya ne! Idan kuma taji fa"
"Ai gwara taji, lokacin da nayo cikinta waye ya tayani sai wasu banzaye su samin yarinya a gaba."
Ni dai nabarsu ban san ya suka kare ba, sai da asuba da zasu tafi. Dake jirgin biyar da rabi na asuba, suka samu, ta shigo min, munyi magana sosai wanda naji du duniya bani da sama da Ummina.
Iyayen Natashah sun zo sun dauketa, inda suka tafi da ita domin sai da suka yi uwaka ubanka da Y'ar Uwarsu. Tunda Yaran suka rasu Ashraf ya fidda min wani iskanci, da bakar magana idan yazo shashina, sai ya wucce dakin yaran yaje ya zauna, yayita tuna yaran. Idan naga ya jima sai na biyo shi, koran kare yake min.
Yau ne dai da ya fara min na dakatar dashi.
"Ban san laifin da nayi ba kake min wannan tozarcin, Ashraf ban maka dole ba, kuma kai baka min dole na zauna da kai ba. Dan haka rayuwa yana da zab'in shiga ko fita. Amma ba damuwa gani na da kake a rayuwarka ya saka ke ganin na cutar da kai idan na fita daga rayuwarka, sai kayi farin ciki."
Ina gama fad'ar haka na fita na bar dakin na koma nawa nayi kuka sosai, yanzun nake jin mutuwar yaran, had'a kayana nayi dana Ablah. Sannan na dauki wata memo na rubuta mishi sako.
_Nagode sosai da irin abinda ya faru_
Daga haka na ajiye biron na dauki Ablah,na goya sannan naja akwatina nafito bayanan, duba agogo karfe goma, na koma na duba jakata, na debi kudi na zuba, sannan na fito na bar cikin gidan a hankali na bar Masarautar baki d'aya.
★★★
Oman.....
Tunda suka dawo da ita sai yau Allah ya nufa ta bude idanunta, akan likitan da yake dubata. Sake lumshe idanun tayi kafin ta bud'e tare da juyar da kanta gefe.
"SAFINAH!! Ki koma zasu kashe miki yaranki, SAFINAH ki koma zasu kashe miki yaranki."
Alluran barci suka mata, sannan likitan ya fito, ya sami Iyayenta yace.
"Wacece SAFINAH? Toh ita mara lafiyar take kira ta koma zasu kashe mata yara."
Shiru duk gurin akayi sannan ya kara da cewa.
"Insha Allah zata tashi, sai dai kamar taci wani abu wanda ya haifar mace da kumewar jini a cikinta bayan ta haihu jinin ya taru, mun same nasarar fidda jinin."
Yana gama musu bayani ya fita.....
★★★
A cikin ɗakin ya kwana, har ya makara ma, fitowa yayi bai ji motsin ta ba, dan haka yayi wuccewar shi. Abinda Ya bashi mamaki yana murɗa kofar yaji shi a bude, juyawa yayi ya kalli kofar ta. Sannan ya fita zuwa masallacin sai da garin yayi haske, sannan ya dawo gidan a gurin Ammyn shi ya tsaya suka gaisa, shiru yayi kan a sunkuye kallon shi tayi cikin kulawa tace.
"Kayi hakuri! Allah zai maida maka masu alkhairi."
D'ago kai yayi ya kalleta sannan ya mik'ewa yayi, ya bar falonta. Halayyar shi na baya yake son dawo da ita, duk yadda kaso mishi magana dakyar yake cire kai ya kalle ka, koda ya shiga gurin Zoyah ya sameta tana ta barci fita yayi ya koma gurin SAFINAH, koda ya shiga ya samu bata fito ba, dakin yaran ya koma, ya kwanta a kan gadon su.
Yana tuni ana gobe zasu rasu da yazo kwantar dasu suka fara rigima, akan ya goyesu, aikuwa ya dauke su, kowa ya dauka sai daya ta fara ihu, a haka SAFINAH ta same su dams yazo daukar Ablah ce, kuma ba shiri suke dashi ba, har zata fita Aamih tace.
"Ummina kice Appa ya goyi,"
Da sauri na bar dakin tana jin lokacin da suka saka dariya har Aanih nacewa.
"Appa! Ummu tayi nauyi bazaka iya daukar ta ba," cikin dariya yace.
"Ai Ummunku bata da nauyi kamar ku haka nake daukar ta."
Aikuwa suka saka ihu.
"Yeeeeeeee! Appa muje ka dauketa a gaban mu"
Narke fuskarshi yayi dan baya don zuwa gurin SAFINAH dan kartace yazo da laluransa, shine ya lallaba yaran suka kwanta, a jikin shi, sai da ya tabbatar sun yi barci, sannan ya fita a falo suka had'u tana sanye da rigar barci sau daya ya kalleta, ya kauda kanshi, dan ganinta sai haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba.
Kwallar da suke sauka ne ya an karar dashi halin da yake ciki.
*Taya SAFINAH tabari aka kashe mishi yara?!* Wannan shine tambayar da kullum yakewa kan shi, kuma har yanzun bai da me bashi amsa,
A sannu barci yayi gaba dashi, me cike da mafarkai marasa tushe, farkawa yayi yana jin sautin kuka, yunkurin mik'ewa yayi wani irin barci ya kuma ɗaukar shi, dakyar Allah ya bashi ikon farkawa. Tashi yayi zaune yana kallon d'akin yana son tuna abinda ya gani ya manta dan haka, ya tashi ya bar dakin. Yadda ya wucce falon haka ya dawo ya samu, anan ne zuciyarshi ta fara girgiza,. D'akinta ya shiga ya same komai a nutse.
Da azama ya buɗe ban daki, yaga ko dingon ruwa babu, bai gamsu ba, sai da ya fito zuwa kitchen yaga babu SAFINAH babu labarin ta.
Bai tsaya ba ya wucce gurin Ammyn shi, yace.
"Ammyn ina SAFINAH ta tafi."
Baki sake ta kalle shi, sannan tayi sannan tace.
"Ina zan san inda taje, kaine ka yarda da ita ai nasan komai akayi sai ta nuna maka cewa ita din Karuwa ce."
"Ammyn ba shi na tambaye ki ba, ina matata tashiga?! Wallahi wani abu ya sameta dake da Zoyah sai na baku mamaki, ya kuke so nayi ne? Ammyn me kuke bukata na baki ki rabu damu "
Fita yayi daga cikin gidan cikin lokaci ƙalilan kowa yasan Sultan na niman matar shi, cikin awa gudu aka birkita garin jordan, har babu inda ake wuccewa sai ka buɗe motarshi, tashin hankali yayi yawa.
Da farko ya zata tana kusani sai tayi fushi sai yaga ba haka bane abun dan har an dauki lokaci ba a ganta ba, tsabar bai yarda ba da kanshi yaje gidan Ghaniyu da kanshi yaga bata nan, a nan ne fa yasa aje tasha jirgin sama, da ta jirgin kasa. Sai na Safa safe, aka shiga niman SAFINAH, har Airport sai da aka je niman nimanta da hotonta ba a sameta ba, sosai ya gigice tun safiya ake abu d'aya ko ruwa bai saka a bakin shi ba, cikin wuni guda Ashraf ya koma, wani zararre. A sanadin haka sai da yasa aka rufe masu tsaron gidan shi tare da, zuba wasu.
Gidan shi kuwa yaki magana da kowa, karshe da Zoyah ta dame shi da tambayar ganganci, kiran wani daga cikin masu tsaron gidan yace.
" A kai ta gidan su, shi zai nimeta"
Kallon Nannah tayi ko zata yi Magana amma ta wani dauke kai kamar bata gurin haka suka fita da ita ta juya yaje har gaban Nannah tace.
"Wallahi mu zuba dake."
Haka suka kad'ai keyarta....
★★★
"Maah kice SAFINAH ta je karsu kashe mata Yaranta,"
"Toh Natashah za a gaya mata!"
"Maah Ammyn bazata gama da duniya lafiya ba, Ammyn tacutar Da SAFINAH! Maah kice SAFINAH taje kar su cutar mata da Yaranta."
Iya wannan shine abinda Natashah ke fad'a, kuma idanunta na rufe maganar, duk hankalin iyayen ta a tashe, ga jaririnta madara ake bashi, sakamakon bata da ruwan nono, idan kaga ta sai ka zubda hawaye tsabar tashin hankali.
Alhamdulillah book 2 ya kare, cikin yardan Allah,
Ga dai abubuwa sun faru ba a san yaushe suka faru ba,
Tsakanin Nannah da Zoyah akwai alaka me karfi!?
A cikin Nannah da Zoyah wacece tayi nasaran bawa Yaran SAFINAH guba?
Me Natashah ta sani! A pagen baya Natashah ta rike hannun SAFINAH zata mata Magana Nannah ta fincikota! Me take son Sanar da Safinah?
Kalmar dake Yawo a bakin Natashah, SAFINAH taje karsu cutar mata da Yaranta, iya shi take fad'a, kenan Akwai wani kulli da tasani.
Na cire muku Abinda baku yi nazarin shi ba.
Duk abinda ke faruwa Sabida Ashraf ne! Sannan Nannah da Zoyah sun taimakawa juna..... Meye silar taimakon......
Book 3 na hanya......
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*
4️⃣8️⃣+4️⃣9️⃣
Juyawa nayi zan bar gurin dan ban ga alamun faduwar da tayi ne ya zubda cikin, kawai dai akwai abinda ta shirya ne kuma zai koma kanta.
Fincikoni aka yi lokacin guda aka sauke min wani mari akan idanuna, sai da na daina gani baki d'aya na tafi zan fadi akan cikina.
"SAFINAH!!!!" Ya kwala min kira, lokacin guda ya ture Zoyah a cinyarsa, kafin ya iso na fadi akan gwiwata, na dafe kasa da hannuwana biyu.
Wani irin b'acin rai nake ji, lokaci guda. Mik'ewa nayi tare da juyawa zan bar gurin, ta kuma fincikoni zata mare Ni ya shiga tsakaninmu.
"Ammyn ki Kyaleta! Ba ita kadai bace da ciki a jikin ta."
Cikin fusata tace.
"Ita Zoyah ba cikin ne da ita ba, ta zubda mata, Muhammad ka farka Yarinyar nan bata kaunar cigaban ka, amma baka fahimci haka ba, kamar yadda ta zubda mata cikinta itama sai na zubda nata, idan kuwa baka son faruwa haka sai dai ka saketa na gaji da ganin SAFINAH a karkashin inuwarka."
Zubawa Nannah ido nayi cikin bakin ciki nace.
"Wallahi Nannah ke butula ce ke, idan Ashraf ya sake Ni sai ki zau.."
"Shuuuuu" abinda naji kunne na na cewa kenan, yayinda na taune harshena. Sabida karfin marin Ashraf yayi min. Sauka kwalla yayi daga idanuna na dama, inda ya mare ni na kura mishi ido bakina yana rawa nace.
" Ni ka mara?!"
Kallon hannunshi yake kamar yaga sabon halitta.
"ASHRAF Ni ka mara?!"
Dan duk abinda muke yi akan idanun Yaran, lokacin da ya mare ni, k'amk'ame juna suka yi tare da fashewa da kuka. Suna kirana,
Lashe bakina nayi cikin murmushin takaici na taka gaban Nannah na tsaya, har numfashinmu yana dukar juna na kalli cikin ƙwayar idonta nace.
"Ki zuba ruwa kisha! Abinda kike son gani ya faru ince muyi rigima, Nah ya mare Ni sabida ke! Hmm zaki girbi abinda kika aikata."
Sake fincikoni yayi, yana hucci bance mishi komai ba. Na saka kai zan koma cikin shashina, naji Muryan Nah tana ce mishi.
"Ka rabu da ita, dan wallahi bata da mutuncin."
Nakai makura bana wasa ba, iya geji na kai, bana son na tanka mata har mu sake samun matsala da ASHRAF. Ga kuma Zoyah a gurin, shima barin gurin yayi har na shiga, na rufe koma na manta da yaran suna waje a dunkule guri guda.
Ganin Ablah ce kawai akan kujera yasani kiran su, basa ciki. Komawa nayi da nasan komawar zata iya zame min matsala da ban fita kiran su ba, dan da na barsu a gurin rayu suke gurin Natashah ina fita naji suna saka dariya tare da magana.
"Ai karuwa ce! Sai da ta gama lalacewarta, sannan suka nacewa Ashraf. Suma Yan biyun shegune, dan haka Ablah ce kawai aka same...."
"Toh tsohuwar banza! Tunda nake ban tab'a bin wani namiji ba kuma da kike cewa na nace mishi, toh shi ya shiga rayuwata, Nah wai ke har kina da bakin zagina bayan ke kika lalata min rayuwa, bayan na cika miki burinki kika guje Ni. Wallahi tunda kika iya butulce min har abada babu wanda bazaki butulcewa ba, kuma Nagode da sheganta min Yarana, wacce bata san ciwon kanta ba, ke Zoyah kike idan baki bi a sannu ba wallahi sai kin gane kuranki."
Dariya suka saka sannan Zoyah tace.
"Kee Safinah kike ko? Toh ai bani da ciki, munyi ne dan mu hadaku kuma haka yayi aiki, ashe ana tsoron komawa cikin wahala shi yasa kika ki biye mishi."
Dariya suka saka sannan Nah tace.
"An ce miki karuwa! Ai duk Yar Arziki bata barin gaban Iyayenta ta shiga duniya ba, Yaran da suka san darajar iyayensu zama suke a inda iyayensu suka ajiye su amma kum"
Ji nayi jikina na rawa, ban san, ya akayi ba sai gani na nayi a gaban Nannah, kamar dama sun shirya hakan eh shirine kam tunda sun san nashiga ciki kuma, na fito toh meye ya fito dani? Yarana hujjar ya isa har ina kare kaina? Yadda nake jin kamar na rufe ta da duka, tsakanin Nah da Allah ya dungule hannunta zata daki cikina nayi baya, ta dan gefen shashinmu anyi adon gurin da wasu tukwanen flower, shi Nannah ta raruma ta buga min, a bayana. Lokacin da najuya da sauri dan karsu tab'a lafiyar cikin, ina isa bakin kofar na tura yarana sani duk cikin gidan na jingina da kofar, a hankali nasaka key na rufe. Zamewa nayi na zauna a kasa, wannan bala'in har ina.
Ina son nayi kuka, amma ganin Idanun Yarana ya hanani, badan komai ba sai dan su zama masu ƙarfin zuciya, kar su zama komai na rayuwa tsoro yake basu, amma a zuciyata kuka nake me kona zuciya da ruhi.
Buɗe musu hannu nayi suka zo da gudu na rufe su a ciki.
Wannan tashin hankali da me yayi kama, matan nan ta hanani sakat. Sai naki koda fita bakin barandar tunda na fahimci bazata bar gurin ba, burinta ta zubda cikin.
★★★
Kamar zararre haka ya isa gidan Ghaniyu, yana isa ya fito yana tafiya kamar wanda ya sha abin mayye, buga gidan yake kamar zai balle musu kofa. Ghaniyu na buɗewa ƴa faɗa jikin shi, ya sake kuka kamar ƙaramin yaro,
"Subhanallahi! Sultan!! Me ya faru, ina Safinah meye ya sameta?!"
Cak ya tsayar da kukan sannan ya kalli Ghaniyu ya girgiza mishi kai sannan yace.
"Marinta nayi."
"Akan me?! Kuma me ta maka ?! Har akwai abinda zata ka daketa?!"
Yana kuka take bashi labarin abinda yake faru, kallon renin hankali Ghaniyu yayi mishi.
"Ai haka ne?! Ina ga ka sake ta kawai ta koma ƙasar ta, zai fi saukin wannan cin mutuncin, an hanaka shiga gurinta tayi hakuri, sannan yan, dan nayi magana abisa kuskure shine ka mareta, toh idan kuma fitar da kayi su suka cutar da ita, waye gatanta! Don Allah doka fitan min a gida wallahi idan hakkinta ya kamaki sai kun gane kuranku."
Sai da Ghaniyu yayi mishi tass sannan suka tattauna akan abinda Nannah tayi yace .
"Wallahi bazan b'oye maka ba Ammyn bata kyauta ba! Domin ita Uwace taya zata rike ka da wani abinda babu hujja, sannan dan rashin imani har kana marinta dan tace ka zauna da Ammyn idan ka rabu da ita, kai idan akawa Yarka haka zaka ji dad'i, Wai tukun kama da Imani ma kuwa, kamar yadda ka hana Natashah walwala ita Safinar haka kake son ta zauna karya motsa, a waje kai sarki ne a gidan ka mata biyu sun birkita maka lissafi. Indai har ka iya zaro masu laifi toh wannan karon ina bukatar kayi bincike, abinda ke faruwa zaka yi "
Sun tattauna sosai sannan yayi mishi Sallama, har zai fita Ghaniyu yace.
"Majnun angon layla, idan ka kuma a daina kuka idan aka toshe layla."
Banza yayi dashi, sai da ya tadda motar shi, ya d'aga mishi hannu..
★★★
Wato su