Showing 51001 words to 54000 words out of 108344 words
Chapter 18 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
daga mishi riga dole yayi shiru suka fita daga motar, a motar su Ghaniyu suka tafi, Shi kuma ya tura mishi sako.
A rikicin ya zo gurin tare da yan sanda, tun kan su iso su Ghaniyu suka bar gurin.
.......
Dukar Babban barayin yake zuciyarshi na ta fasa.
"Mata ta! Zaku tab'a saboda wata yar iska."
Shigowa da Kidaya akayi suka watsar da ita kamar kayan wankin.
Takawa yayi har gabanta ya take ƙafarta ihu tasaka, sannan ya durkusa yana tauna toothpit, kallon irin shigar jikinta yayi, ya kauda kanshi.
"Wato kika ce idan suka kama Safinah su keta mata haddi sannan su saka a intanet, yadda sunan ahalinta zai ɓaci, Mata ta da igiyar aurena, mata ta mace me daraja da kima zaku lalata min Ita saboda son zuciyar ki, ki godewa Allah ina da yara mata, da wallahi sai nasa yarana sun miki wulakancin da ko biyanki akayi ki tab'a sunan Safinah gudu zaki yi dan mata ta."
Gyara suit din jikinshi yayi bayan, ya cigaba da gyara button ɗin, rigarshi tafiya ya fara Ghaniyu da Fahad suka rufa min shi baya, kamar bazai magana ba, ya isa jikin window ya dafe hannun damansa yana kallon waje.
"Razana min ita Yadda ko sunan Safinah aka kira sai da suma, so nake naji ihun da taso SAFINAH tayi, ita nake son jin tayi."
Kwashe mazan Ghaniyu yayi shima ya dawo, Fahad tsaye A gabanta.
Yana ɓalle rigarshi, tsorone ya cika mata ciki shiga ja da baya jikinta na cikin harshen turanci ya.
"Abinda kika saka a mata shine Ni zan miki kiki irin ciwon da kike so taji kunga gobe koda kuɗi aka had'aki bazaki cuci kowa ba"
Gashin an daure ta, ba halin gudu. Duk ya taso kaucewa barazanar sai da Fahad ya gigita mata lissafi, bata kara fita hayacina ba sai da ya fisge hannun rigarta, taga yayi mata runfa. Nan ta kara kidima taba basu hakuri, a zuciye Ashraf yazo yayita kifa mata mari sai da suka riƙe shi yace.
"Irin kukan da kika so tayi kenan ta gigice ta firgice tayita baku hakuri kuna mata dariya, ashe mutunci bai fi mutunci, koda yake idanuna suna kanki ko a mafarki kika ga fuskar Safinah ki nemi tsari da ganinta."
★★★
Barcin kwana uku nayi sakamakon shaka min cocain, sabida rashin karfin jini na, a hankali na bud'e idanuna akan Ummina, mik'a naso yi amma na kasa, dole na koma na kwanta a hankali nace.
"Ummina! Lokacin Sallah ya wucce ni!"
"Eh SAFINAH! Yau kwananki uku kina kwance, dan ma Allah ya taimaka kin fad'a hannun na gari da bamu san me zasu miki ba."
"Ummina!?
Taimaka min nayi wanka!?"
Haka Ummina ta taimaka min nayi wanka da sallah, sannan ta bani abinci na tab'a ina kara zurfaffa abinda na gani lokacin da suka watsa min abin.
"Ummina!?"
Na kira sunanta a hankali, kallona tayi cikin nutsuwa.
"Ummi! Na ganshi! Yana raye."
"Waye!?" Ta jefeni Ni da tambaya,
Sunkuyar da kaina na yi,nace.
"Shi d'in!"
Ta fahimce Ni sarari so take taji daga bakina.
"Abban su!?"
"Toh waye kenan! Kin sani a rud'u."
Sunkuyar da kaina nayi tsabar kunya kamar zan fashe da kuka nace.
"Ashuu!?"
Sam na manta ita ce na ce mata Ashu.
"Amma na maida mishi kuɗin Aurenshi, ɗan haka ki bar kawo min zance shi."
"Amma Ummi aka ce min bai amince"
D'aga min hannun tayi cikin fusata tace.
"Karki dawo min hannun agogon baya"
"Ummina!?
"Zaki dawo da halinki!?"
Girgiza mata kai nayi,
"Good girl"
Tace min,
Mikewa nayi na shiga ban daki na fashe da kuka bayan na kunna panpo.
Tana sane da kuka na shiga yi, ko a jikinta. Koda na fito biris tayi dani, washi gari aka sallame mu.
A hanyar mu na komawa muka sake haduwa a Traffic Jam, yana wata Hond new model, kafin na dawo daga tunani ya b'ace min, kalle-kalle na fara sai da Ummi ta rike Ni sannan na dawo hayacina.
★★★
Sannu a hankali kaina ya fara daukar zafi, dan yanzun Zan iya kiran kaina da mahaukaciya eh mana, tunda ga dai Ashraf yana min gizo, yau ma na shiga sahad store. Niman wani mai Ni da yaran, sai Ihu suke sunga wasu toys ya d'aga musu hankali, shine nima suka d'ago min nawa Sense din.
Gabana ne ya fad'i, cike da tsoro na d'ago kaina. Bazan iya cewa shi din ne ba, amma tabbas ina kyautata zargin haka, jan Hannuna yaran Suke suna cewa.
"Didih! Muje ki saya mana!?"
Hankalina na kan shi yana gurin biyan kud'i,
Sanye yake da riga me hula, wanda ya hanani ganin zahiri fuskar shi, takawa nake zuwa inda yake kafin na isa wasu matasa maza da mata sun mana katanga dashi, har ya fita hango shi nayi zai shiga mota na fita da sauri, na isa inda motar yake na bud'e da karfi.
"Hoo! Sorry na zata wani ne da nasani ashe ba shi bane."
Murmushi yayi a hankali na juya tare da barin gurin.
*"SAFINAH!!!?*
Ya ambata bayan ya cire mask din fuskar shi. Juyawa nayi ina kallon motar, da sauri yaja motar wanda nake ji kamar da zuciyata yake gudun.
Jingina nayi da wata mota na kifa kaina na sake wani Irin kuka, tabbas Ashraf ya gama kama zuciyata, irin kamun da bana iya tantance fari da baki, Ni kuma tawa kaddarar kenan.
"Madam kin bar yara suna kuka."
Da sauri na shiga suna kuka, durkusawa nayi suka rungume Ni, nima kuka nake sosai. Hakura nayi da sayayyar nasa kai zan fita, wanda yake zaune gurin biyan kudi yace..
"Madam an biya muku kudi kayan wasan da suke so."
Mamaki ne ya kuma kurmushe Ni.
(Auntys & Mommys... Don Allah kanena yan matan nan wanda shekarunsu bai wucce 20yrs ba a koya musu girki, namiji ya kan iya zama da kazamar mace idan ta iya girki, ya kan iya zama da mummunar mace idan ta iya girki, ya kan iya zama da mafad'aciya idan ta iya girki, ya kan iya zama da mara kunya idan ta iya girki, amma batun gaskiya shine kome kyan mace da nasabarta Wallahi zaman zai sha tangard'a sabida shi yayi imanin da Tumbin sa, ita kuma tayi imani da lalace, kanena da kuke tunanin zaki auri handsome guy, mr right, mr perfect, Yes burin kowacce mace kenan amma shin wani Irin tanadin kika mishi, wallahi yana da kyau mufahimtar da juna mu, shi namiji sak ne shi. Taya zaki dauki Yar 20/19/18/18/16 itace kankanuwar cikin su, amma baki nuna mata yadda zata kilace mishi tummys dinshi ba. Yana son kawo friend dinsa cin abinci amma yana tsoron kawo su, Why Mommys,!? Why Auntys!? Wallahi idan kika koya mata girkin nan, shine bokanta!? Kika nuna mata zaman auren Ibada ce, shine Malaminta!? Kika nuna mata biyayya!? Na rantse da Allah koda d'igo kwalla d'aya yaga ya fito daga idanunta sai ya rikice!? Ku da kanku kuke kalublantar Ashraf, akan SAFINAH!? My Dear wannan story ne, ki d'aura Kanwata a saiti Wallahi tallahi, sai ta juya shi ayita tunanin Ta wanke ta bashi ya sha. Kuma duk bala'in da zasu yi yana manne da ita, Mommys da gaske nake ki gwada wannan shine sirrin rayuwar aurena 🤗🤭🤫 har yau ana tambayata me kikawa kikawa Usman da baya iya nutsuwa idan baki nan 🤭🙄 idan nace banyi kome ba karyatani suke, abinda na yarda dashi mijina yana kokarin ƙare hakkina da sauke nauyin da yake kanshi, Ni kuma ina ƙoƙarin kyautata mishi ba hana idan ya ta bani na ishe shi da fitina ba, Yes amfani auren Babba kenan Wallahi ki gama fitinarki ya kalleki Yace ai Yarinta na damunki Don Allah gobe abinda zan yi ai sai yafi na jiya tunda an kalleni ance min yarinya, haka ya faru ne sabida daukar zaman da nayi a ibada kuma mutu kara ba, bana iya hange Kowa sai shi. Duk zaman da ya lalace toh an bawa zuciya jagoranci ne, idan da zamu bawa Allah jagorancin rayuwar auren mu zamu gyara abubuwa fa Allah yasa mu dace 🙏🏽)
*Har yanzun dai Ni yarinyar ce kamar Yadda yake ce min🤭🤫🤣😂 😆 Allah abin dariya sai ka gama tsiyarka a bika da kalmar yarinta shekaru Goma baya da suka same kakarmu tace musu Ni yarinya ce shine ake bina da kalmar Nagode ma a haka*
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah....
2️⃣3️⃣
Kasaike nayi ina kallon yadda ake zuba musu kayan a motarmu har bayan motar. Muna koda aka gama muka dawo gida, wucce d'akina nayi na zauna tare da cusa hannuwana nayi cikin gashin kaina na,
"Da alamu na haukace ko Son Ashu ya haukatani"
Ni d'aya nayita surutu, Ina cikin jarabawar So, dan bana fahimtar kome na Rayuwata, da Abuja yayi min zafi sai na haɗa kayana zuwa gidan Aunty Yaanah, ko zan same.
Da yaran muka tafi, tunda nazo na same nutsuwa kan, tunda na ajiye tunanin Ashu muna bin dangi da yan uwa, lokacin da nakai Yaran gurin yayansu Ummi Sheikh Hayatudeen ya dauke su yayi musu addu'a sosai tare da sanya musu albarka yace.
"Mahaifinsa! Yana da kirki wancan Satin yazo a nan yayi Sallah Jumma'a. Yaron Akwai nutsuwa a tare da shi ga kamala da zati, kiyi ƙoƙarin kin shiga al'amarin shi da Mahaifiyarshi, ki samu damar da zaki dinke barakar dake tsakaninsu, sannan Kiyi hakuri dashi, ya tashi a bahagon rayuwa, bai fahimci farin ciki ba sai da ya haɗu dake. Basarake ne bai san kome ba sai akanki don Allah ki bashi farin ciki da nutsuwa, dan idan ya rasa nutsuwa dake har abada bazai kuma fahimtar ki ba, kiyi ƙoƙarin gyara tsakanin su Allah shine gatarki Dan Dama ko baki zo ba zan saka a kawo min ke, sannan banga dalilin da Mariam ta rike ki ba ta barki ki koma d'akin mijinki kema zaki nutsu."
Wayyo garin dad'i na nesa wato duk sabida Ashu ake min nasiha, "Allah Nagode maka da ni'imar da kai min."
Koda muka bi sauran zuri'anmu kowa da abinda yake fad'a akan jarumin maza, kowa yabon shi yake, da alkhairin da yake musu.
Gidan Hajja Kaka naje na sameta hakimce tana duba littafin Hadri, da medical glass ɗinta, wani kallon banza tayi min sannan ta maida kan littafin gabanta a raina nace.
*Da alamu aljanun basa kusa yau.*
Shigowar Yaran kawunaina ne yasani dogo kai suma suka shiga murna, tare da cewa.
"Didih Feener! Yau kece a gidan mu, gashi zamu fita zuwa Two days shopping mall"
Inji Meenal,
Murmushi nayi sannan nace.
"Eh nice! Nima ina son zuwa dan naso zuwa Abuja amma ban je ba, ku tashi muje"
Wani kallon da matar nan tabi yan matan dashi yasu mik'ewa, nima kuma na mik'e.
"Ke! SAFINAH ki fita idona na rufe, dan na lura baki san hakkin aure ba, kin dibo jiki daga Abuja baki nemi iznin mijinki ba, kika zo sannan baki zauna waje guda ba sai yawo kike masa da yara salon Mayu da masu kambi baka su tab'a masa yara toh babu inda zaki ki zauna idan ya dawo ki tambaye shi."
Ko kallonta banyi ba na mike tare da saka hijab dina cike da jin haushi nace.
"Idan ya matsu ya bayyana kanshi Ni kuma sai na kare hakkinshi sannan Ni babu auren wani a kaina! Yan mata muje kunji."
Duk yadda take masifa ban kulata ba sai bar mata yaran nayi tare da tafiyata,. Tunda muka isa muka siya abinda ya kawo mu, tunda zuwan mu wani mutum yake like min, duk abinda na dauka sai ya dauki biyu ya saka min.
Tun ina bata rai har na hakura, tsinkewa zuciyata tayi sakamakon hango Ashu hannunshi hard'e a kirjinshi, yana bina da wata irin azababben kallo, wanda yake dafa ruhina da zuciyata.
Ashe na kai hannun zan dauki, wani set na pant da bra wanda yake zuwa a kwali, ban dauka ba, sabida kallon da yake min, yana waje ne fa amma Tsabar masifar shakkar shi na kasa yin komai.
"Malama! Me kika kallo haƙa!? Tun dazun nake miki magana baki ce kome ba sai kallon waje kike."
Ajiyar zuciya na sauke sannan na buɗe baki zanyi magana makalewa maganar tayi sakamakon jin an zuro hannu ta k'uguna, jan janyo Ni baya, kamshi oud na shaka, na zub'e a jikinshi sharaf. Kallon Mutumin yayi cikin zafin kishi yace.
" Kaci arzikin!? Ina cikin wani yanayi da wallahi sai na baka mamaki, tunda tace maka Ita mallakin wani ne sai ka fita harkanta."
Ina jin shi yajani zuwa inda ake biyan kome, ya biya mana.
Koda su Meenal suka zo, suna ganinshi suka fara murnar, biyan musu kome yayi sannan yaja hannuna muka bar gurin, tafiya mukayi sosai sannan muka nufi wani unguwar tsayar da motar yayi sakamakon cika mishi kunne da nayi da kuka, ya juya zuwa gidan Hajja, koda muka isa ya kai hannu ya zai ta bani aikuwa nasaka mishi kuka, tare da buge mishi hannu ina faɗin.
"Dalla kyaleni, mugu kawai"
D'alle min bakin yayi ba rike ina kuka.
"Na farko ranar da aka zo sace ki! Na biyu a Traffic Jam! Na uku a Sahad!"
Haushi ya bani na d'ago kaina. Buɗe motar nayi zan fita, ya riko hannuna.
"Kiyi hakuri!"
"Eh hakurin kayane mad'e gamo ka dauka Ni ka maida yar iska mara kamun kai, sha-sha-sha, ballag."
Fincikoni yayi yana hucci, tsoro ya bani, sune kaina nayi cikin shakkar idanunshi.
"Kar na kuma jin kin zagi kanki, in ba haka ba toh zanyi bulala wanda yafi duka zafi dan na san ajima bamu haɗu ba, dole kofar takoma ta rufe."
Kwallar bakin ciki ne ya zubo min, banza nayi dashi. Shiga ciki muka yi, sai hira.
D'akin mu a da idan munzo gidan na nufa, ina shiga kamshi turaren shi yayin min barka da zuwa, zama yayi a falon suka cigaba da hiran amma shi da ido yake binsu kasancewa hiran da shuwa suke, sai turanci da suke jefawa shima sabida ya shiga hiran.
...... Gyara dakin nayi dan kome na d'akin zaune yake da ɗuwais dinshi, ina cikin aikin ya shigo, ban san ya shigo ba sai da naji an make min ɗuwais dina na tashi a tsorace, ina binshi da mugun kallo. A raina nace dole na kwaci kaina a hannun d'an renin hankalin.
Ban daki ya shiga, na juya zan fice murda kofar naji gam ya rufe.
Kumbura fuska nayi kama yana gabana na fara kunkuni ina cewa.
"Wallahi ba zan yarda da mulki ba, aurene dai nima nace banayi eyyee!"
Fitowa yayi alamun alola yayi zai tafi share ruwan fuskar shi yayi ya watsa min a fuska.
Fuuu nazo kamar zan bangaje shi na fita, yayi bake nake a baƙin kofar, tare da watsa min wasu mugun kallo.
Tsayawa nayi k'am kamar na rufe shi da duka.
"Kinga ada na rashin Kunyarki anjima zamu raba reni."
Tsaki naja kasa kasa, ya kalleni cikin murmushin mugunta ya d'aga kafadarshi.
"Kar naga kafarki a waje"
"Kutt! Hmm lallai fa! fita zanyi abuna wallahi."
Kaina a sunkuye nake maganar, leka fuskana yayi yaga naki yarda mu had'a eyes sai yasa kai ya fita yana fad'in "idan ban isa dake ba ki fita."
Kwalla ce ta cika idanuna lallai Ashu harda.
Can shashin zuciyata tace.
*Toh meye yayi miki!? Da kike jin haushinsa*
Tsaki nayi a fili nace.
"Kome mana!? Yana sane da komai yake guje min"
*Toh kinsan hujjar shi!?*
"Ban sani ba!!?"
Na saka tsawa, Ni ɗaya nayita shirme nan ina jin haushinsa.
Ina zaune a gurin ya shigo rike da