Showing 27001 words to 30000 words out of 108344 words
Chapter 10 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
Nuna min sama yayi haka nabi step ɗin har sama, naje naga dakuna. Da yadda Tsarin gidan. Wani daki da nashi na fahimci na yaran shine, tunda na shiga nake kallon yadda aka tsara d'akin.
Jingina yayi da kofar yana kallon yadda nake bin dakin.
"Wani mature ne yayi gina gidan zai zauna sai ya mutu wancan wata shine iyalanshi suka zo suka sa gidan a kasuwa."
Murmushi nayi tare da kallon shi, zamewa nayi na kwanta a saman gadon.
Kokuwa nake da zuciyata, karta sani aikata kuskure.
Zuwa yayi ya daura kanshi a bisa cinyata, tare da rungume cinyar, d'agowa nayi na zauna ina kallon sumarshi masu laushi da tsantsi.
A sannu na kai hannuna ina shafa kanshin, sake k'amk'ame Ni yayi, "Muhammad!!!"
"Hmm"
Sake luma hannuna nayi cikin gashin, ina yamutsawa.
D'ago kai yayi yana kallon fuskana da yake dauke da damuwa yace.
"Ina jinki!"
"Hmm! Har yanzun kana nan da halin ka da nasani bakasan darajar Abu ba, baka kuma san darajar talakawanka ba, tunda ka iya barinsu, zan fama maka sharudd'ana, dole idan zaka Aureni kafita niman kudin aurena, bana son Wanda kake dashi kafita kaga irin rayuwar da talakawa suke yi, sannan na baka kwana 90 bana son kudin masarautarku, bana son kudin Nannah, bana son kuɗin Sana'arka. Kai nake so kaje kanemi guminka idan ka samu kazo zan aurekan"
D'aga kanshi nayi daga cinyata.
"Kuma idan zaka zauna dani ba a cikin gidan nan bane.......🙄🤔😒
Zata kashe musu Sarki fa
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
13.
Wani mugun kallo na wurgata mishi da nasan nazo gida ba, na fito daga motar shi tare da shigewa gida da sauri, kifa kanshin yayi akan motar yana sauke ajiyar zuciya. Shi yanzun bai san yazai da Ammyn shi ba.
.......
A hankali nake takawa, ina tafiya a nutse dan har tsoron karan takura nake ji, hango haske a falon Ummi ya tsinkar min zuciya tabbas duk D'ana gari dole ya kiyaye batawa iyayenshi, duk sai naji kunyar kaina da kaina lokacin da na isa falo babu kowa, cire takalmin kafana nayi na fara tafiya a hankali har na samu na shiga dakina, turss nayi ina sosai goshina dan wacce nake gudun fadar ta ce nasamu tana zaune tana jirana. Duk sai kunya da tsoro ya kamani. Diriri cewa nayi cikin inda inda na fara magana. Dakatar dani tayi ta hanyar d'aga min hannu.
"Na yarda da tarbiyya da nassmu daga iyayena SAFINAH, kuma na yarda da tarbiyya da nake bawa yarana da na kishiyoyina, sannan kece babba a cikin yaran gidan nan, kuma akanki aka fara samun matsala a gidan nan, SAFINAH bansan me zan miki ki fahimci kuskure da kike aikatawa ba, ban san yadda kika dauki kanki ba, Safinah abinda kike aikatawa ya fara jure tunanina, yanzun dan Allah kin min adalci. Tun karfe nawa kika bar gidan nan keda Gimbiya Asma'u, sannan baki tashi dawo min gida ba sai sha daya, gidan Uban waye kika tsaya? Sam kina shirin mai da kanki bola mara daraja da kima, wai me kike nima a duniya. Allah Ubangijin ya kawo miki sauki ya kuma shirya min ke da sauran yaran Al'umma musulmai baki daya, amma ki bi a hankali dan duk rana da kika shiga hannuna zan gwada miki iyakar ki, wawuya shashesha kawai "
Tana gama fadar haka ta raba gefena tabar dakin zubewa nayi a gurin na fashe da kuka. Me cin rai da zuciya.
Ina zaune a gurin har karfe sha biyu ina kuka, sai da naji idanuna na zafi na tashi na shiga ban daki nayi alola sannan na fito na fara gabatar da nafilla, Najima ina gabatar da kuka na ga Ubangiji na. Kafin na juya na kwanta.
***
Washi gari kuwa Ashraf sammako zuwa asibiti. Yana shiga ya dame su zaune sai shiryawa Nannah tsiya Natasha take. Dake yau ya tashi a basaraken shi ne sam baya son magana asalima, zama yayi tare da mikar da kafanshi sosai ya samu balance da kujerar.
Shiru suka yi dan sun fahimci yau maganar ce ba yaso kuma bayajin a ranshi yayi magana.
Ko me zasu yi abu ɗaya yasani kuma idan suka takurashi toh dole ya fada.
Ganin haka Natashah da gigin ciki ke dibanta ta kalle shi sannan tace.
"Ka shirya mana kayan mu ne!?"
Kamar bada shi take ba, asalima, hankalinsa yana kan wayar, yana niman Safinah.
Ganin wayar taki shiga dan bai san ya suka kare da Umminta ba jiya, kuma ya kira layinta user busy, wato dai ta manna shi a bakar jadawalin blacklist.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mike zai fita.
"Baka ji bane ka shirya muku kayan ku dan zamu wucce Oman ne."
Cak ya tsaya shi bai gaba shi baiyi baya ba.
"Na shirya amma jordan zan koma."
Yana fadar haka yasa kai ya fita, ya barsu cikin tashin hankali da firgice, dan maganar shi ya girgiza su.
.... Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan su SAFINAH, horn yayi me kula da get din gidan, ya fito da yaga Ashraf ne sai ya koma yayi zamanshi.
Sake danna mishi horn yayi amma yaki buɗewa.
Sai da ya fita da kanshi ya buga get din, ya buɗe masa ta ƙaramin kofa ya shiga.
Cikin harshen turanci mutumin yace.
"Yallabai zaka iya tafiya dan dan Dr yace kar na kuma barinka shigo gidan nan."
Mamaki ne ya kama shi toh meye matsalar shi da Abdullahi, yaga dai ba wani rashin jituwa suka ba. Amma ya fahimci sam Abdullahi baya kaunarshi.
Hannunshi ya mai da cikin aljuhun wandonshi ya fidda yan dubu ya mika mishi.
Jikinshi na rawa ya amsa har da godiya, sannan ya shige cikin, bai bi takan godiyar da ake mishi ba ya shigo gidan, Ummi tana zaune hankalinta na kan tv.
Ina zaune a kujeran gefenta, kaina a sunkuye sai share kwalla nake, sam bai lura da Ummi bane ko menene ganin ina kuka kawai tsintar kanshi yayi da daburcewa, da sauri ya iso inda nake.
"Ummu Marhus! Make faruwa? Innalillah! Kar dai wani abu ne ya same ki"
Tashi Ummi tayi tabar falon safe goshina nayi cikin jin sabon kuka nace.
"Don ALLAH ka rabu dani, kaje Ni bana son ganinka."
Duk yadda yaso yayi min Magana fir naki kuma na bar mishi falon, dan bansan me Nannah ta gayawa Ummi ba, da safe nan Dudu yazo yayi ta min rashin kunya, har da cewa idan Ashraf ya kuma zuwa gidan nan yan sanda ne zasu rabasu.
Jiki a mace ya fito daga gidan, ya rasa inda zai cusa kanshi yaji dad'i meye Ammyn shi ta gayawa Iyayen SAFINAH yayi musu zafi haka.
Zama nayi a bakin gado na fashe Da kuka, sosai domin ji nake kaman zuciyata zata fashe, kome Nannah ta gayawa Ummi ban sani ba.
..... Itama Ummi tana shiga d'akinta, kwanciya tayi rigingine kalaman Nannah na dawo mata a kanta.
"Mariamah ki shiga tsakani Ashraf da SAFINAH! In ba haka ba Ni zan ɗauki tawa matakin, banda rashin tsoron Allah, ta kaso aurenta ta makalewa yaro karami ta nemi miji dai dai da ita mana, koda ta lika mishi yara mun amsa toh wannan karon kar tayi tunanin idan ta dubi Datti zamu amsa dan mu ba sakarkaru bane, dan haka tun wuri kika mata kunne ta bar min yarima tunkan nasa a baddata."
Lumshe idanu Ummi tayi sabida zafin maganar da Nannah tayi mata, ko ba komai ai SAFINAH bata cancanci haƙa daga Nannah ba, yau tana tare da D'anta ne sabida SAFINAH, kuma tayi Imani da Allah bata gayawa D'anta ya rabu da SAFINAH ba, ita kuma bazata taba gaya mishi haka ba, kuma bazata sauya mishi fuska ba, balle yayi tunanin akwai wata magana a kasa, Allah ya gani ita bata taɓa zaluntar abokin zama ba, amma sai gashi Sabida SAFINAH tana biyar bashin da bata ci ba, abinda bai faru ba a shekarun baya ba shine yake faru da ita a wannan shekaru.
....
Asibiti ya koma yaje ya samu Nannah tafita Natashah na crush candy, fauce wayar yayi tare da shake wuyarta yace.
"Me kuka gaya musu!?"
Zaro ido tayi cikin kaduwa, take cewa.
"Wallahi Ammyn ce tace musu."
Rintsa idanunshi yayi tare da ture ta, jikinshi na rawa. Tabbas Ammyn bata kyauta mishi ba.
Saka yayi ya fita. Zuciyar shi kamar ta fado kasa, dan bakin ciki da ɓacin rai.
Wayarshi ya danna ya kuma kara a kunne yana cewar.
"Ka sama min gurin aikin."
Kome aka ce mishi kawai ya kashe kiran, ranshi na kara ɓaci.
.......
Koda Nannah ta dawo kuka Natasha tasa mata tana gaya mata, abinda Ashraf yayi mata hakuri ta bata, sannan tace zata gamu dashi.
🤔🙄 Ashraf ɗin....
***
Bayan barin shi asibiti sai ga Ghaniyu da Fahad, suka saka su Nannah a gaba har Airport, duk yadda taso ganin shi amma ba hali shi kuma yana airport ɗin kawai gurin sune yaki zuwa, yana zaune har jirgin Oman ya tashi,
Sannan suka koma tun da ya kwanta a jikin kujera bai kuma cewa kome ba.
Gurin aikin da aka nima mishi suka kai shi, gini ne na wata ma'aikata, fita yayi cikin motar da wasu kaya, yana zuwa suka gaisa da wanda yake lura da gurin sannan ya gabatar da kanshi a matsayin sabon lebura.
Nuna mishi aikin yayi yace.
"Yanzun dai ka dawo gobe sai mu fara da kai yau mutane sha biyar ake nima, sannan na gayawa yan uwanka kazo da wuri."
Mika hannunsa yayi sukayi musabaha, sannan ya koma mota.
***
Ina durkusa gaban Ummi ina kuka tare da mata alkawarin bazan kuma ba.
"Toh SAFINAH! Kefa ba yarinya bace! Sannan ban san meye haɗin ki da Yaron nan Ashraf ba, Mahaifiyar shi tace bata sonki, nima kuma naga dacewar haka don Allah ki bar sani Cikin damuwa kece zaki lakato karshe Ni ce zan biya laifinki don Allah ki min adalci nima nasamu yancin."
Gyada kai kawai nayi ina kuka dan gaskiya Ummi ta faɗa duk laifina ita ke dauka kuma nayi alkawarin bazan kuma yin abinda zai bata mata rai ba, tunda bai zama dole ba taya kenan!? Dole sai na rabu da Ashraf.
Wani irin bugawa kirjina yayi sai dana dafe kirjina. Sakamakon tuna ta yadda zan rabu da Ashraf.
Ba sauki! Toh me haka ke nufi.
★★★
Nannah sun sauka lafiya ita da Natashah, tunda suka koma ta shiga narkewa,ita tana da ciki karku manta ciki fa da ita, toh ba karamin bidiri akayi ba, dan Uwarta har da tambayar shin meye shene abin cikin.
(🙄🤔 Ni kuwa nace Katon baby boy 🤣😂)
Tun yana sati shida ake son sanin magajin jordan ko yaya.
Nan aka bazaka bin Asibiti dan a gano me take dauke dashi.
★★★
Yau kwanaki biyar da ya fara aikin gina, idan ka ganshi a cikin rana sai ya baka tausayi, ga rashin sabo da wahala. Duk yadda Fahad da Ghaniyu suka so hana shi fir yaki,gashi kuma baki buɗe shi.
Rayuwa ya cigaba da garamu, Ni ina ce ina fama da fushin da Ummi take dani shima yana can yana fama da daukar kasa da siminti.
Idan ya koma gida jikinshi yayi ta ciwo duk ya rasa inda zai kai gajiyar shi ya huta.
Dan ma yana cin abinci me kyau, amma ya dishe domin rana bata barshi haka ba, kullum sai yazo amma fir ake hana shi shiga, sosai ya shiga damuwa.
Koda yake ana biyansu kudi me kyau dan akala duk aiki na suka yi ana biyansu nera dubu uku da ɗari biyar.
Wani lokaci yakan hana su Ghaniyu zuwa daukar shi.
A sannu ya fara fahimtar yadda mutane suke rayuwar kunci da niman abinda zasu saka abakin salati.
Wani abin da ya kara bashi mamaki wasu a gurin suke kashe kuɗin a cikinsu dan abinci flat daya kawai dubu da wani abu ne balle ruwan da zasu sha,
Ga matasa bil'adadin babu aikinyi, ga tsofin wanda da suna ake Aikin, ga Ma gidanta duk sai yaji hankalinshi ya koma ga Al'ummar shi, a cikin kwana goma da yayi aikin sai ji yaƙe yayi sakaci sosai gurin barin ana zalintar al'ummar shi, yau ne karon farko da yayi tunani akan Masarautar shi,
Kwance yaƙe yayi rub da ciki Fahad yana mashi tausa, sai lumshe idanunshi yake Ghaniyu na gefe yana haɗa mishi tea me zafi yace.
"Gaskiya Sultan ya kamata kasan abinyi tsakanin ka da Mamansu Husnah, yanzun da ka dawo muna maka tausar nan, da ace tana tare da kai Allah zaka nemi gajiyar ka rasa. Sabida akanta zaka juye tsaf gobe katashi babu inda ke maka ciwo."
Juyawa yayi cikin damuwa kafin ya taɓe baki yace....
_🤔🙄🤣😂 Ghaniyu ashe kai ma shu'umi ne wai dagaske ne?🙈 Abinda Ghaniyu ya faɗa_
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
12.
Shiru nayi sakamakon, jin hannunshi a k'uguna. D'aga kaina nayi ina kallon kwantaccen beard dinsa, idanunshi a rufe hannuna nakai ina shafa fuskanshi. Koda goshinsa yayi a goshina. Kauda kaina nayi cike da ƙarfin hali. Nace,
"Bazan zauna a gidan nan ba! Sabida cike yake da abinda zai iya mantar da mutum Allah, a cikin kwanaki da na diba maka nake son ka haɗa dubu ɗari cif shine kuɗin aurena, bayan nan ko tsinke bana bukatar ka saya min, sannan kana da daman ka dawo gidanka ka kwana, Ni kuma zaka iya nima min haya wannan shine iya abinda zan gaya maka idan ka shirya."
Janye jikina nayi zan fita daga gidan ya riko hannuna. Ya dawo dani jikinshi, tare haɗe goshinmu.
"Haka kike bukata!?"
Gyada mishi kai nayi,
"Idan na kawo a cikin kwana goma fa."
D'ago kaina nayi numfashi na karo da juna, idanunmu a haɗa da juna. Kunya ce ta kamani dan nakasa b'oye sirrin dake raina.
Janye idanuna nayi nace.
"Idan ka Kawo bazan aurena ba, kaje kayi yadda nace."
Hannunshi duk biyu ya saka a k'uguna ya haɗa da kirjinshi, sumbatar goshina Yayi tare da cewa.
"Na shirya amsar koma menene! Amma idan na kawo shi kenan."
Jingina goshina nayi a kirjinshi ina sauke ajiyar zuciya.
"Ehtoh matakin farko kenan ka haye, na biyu sai kayi yadda nace zan gaya maka."