Showing 48001 words to 51000 words out of 108344 words

Chapter 17 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt

da hannu da kafa, da bulala, Abba bai dakatar da ita ba, sai ma dage goshinsa da yayi duka ta kai min ciki, wanda ya sani sake wani irin kara tare, da kifawa, ina girgiza mata kai na riƙe bulalar. Dai dai shigowar Ashraf a birkice, ya rike bulalar. Sake masa tayi ta saka hannunta ta cigaba da dukana, rungume Ni yayi, ta janyo recieve ta kwala mishi.
Tana fadin " ka matsa min tun Kafin na illataka."


"Bazaki Illata min da ba, akan wata yarki da ta gama lalatacecciyar yarki. Da ta gama yawo kororo kororo tana bin maza, shine zaki taba min kash."

"Ammyn!!!" Ashraf ya fada da karfi, d'ago Ni yayi yaga bana numfashi, sai jinin dake zuba.
D'ago kai yayi cikin sanyin murya yace.
"Babu ruwanta! Ni nasara komai, Ni na bata shawaran muyi aure da zaran mun tasamu ciki dole ku hakura ku barmu mu zauna da juna. Shekaru Ashirin da shida nayi ban taɓa samun wanda ya gyara min kuskurena da soyayya ba sai ita! Ta ciro Ni cikin Mugaye mutane ta kawoni cikin mutanen kirki, ta kuma nuna min cewa ita bani take so ba sai Hameeed wanda ba sanya shi yayi aiki a matsayin yana sonta. Ta zauna dashi har suka rabu Abdullahi ya gaya mata irin abinda na mata bata damu ba, dan dan tana sona, kuma bata hukuntani ba. Na yarda SAFINAH tana sona so na hak'ik'a. Tunda Sadakin da zan bata turani tayi naje nayi aikin sati uku ban kai ga haɗawa ba, nace mata bani da lafiya."


Kwalla ne ya zubo mishi daga idanun ya goge sannan Yace .
" Ce min tayi ta hakura komai na bata, me yasa kuka ki bata Abinda take so, sabida kuna tsoron Ammyn karta kwace dukiyarta ko!?" Hawaye ne suka. Zubo mishi, ya cigaba da cewa.
"Tun ba yau ba, duk abinda zata aikata sai ta zubda hawaye tare da kiran sunan Umminta! Tsabar sonki da take kiyi. Ban tab'a ganin mace me kawa zucin iyaye irinta ba. Ki gaya min abinda zan yi dan na fanshi hukuncin da zaki mata Don Allah."

Duk wannan bayanin Nannah bata fahimta ba, kafin Ummi tayi magana tace.
"Indai nice na haifeka ka rabu da Ita."
Kallon Ummi tayi sannan tace.
"Kayi yadda kace. Kuma don Allah ka fita a rayuwar mu, Yaran ma kaje mun bar maka su, duk Allah karka kuma dawowa Rayuwata."


"Wallahi ke haihuwar ta kika yi Ni kuma mab'alin zuciya ta ce, zan iya yin komai na mallaketa daga cikin har da sadaukar da abinda na mallaka."


"Toh wallahi sai ka rabu da Ita kuwa." Inji Nannah, har da wasu maganganu,
"Ka saurari Mahaifiyarka"
Duk yadda yaso Nannah ta fahimta amma abin yaci tura. Gani a kwance jini na fita, kallon Ummi yayi ya dauke Ni har zai fita, yace.
"Ina me rikonku yafiyarku, zan tafi da ita Asibiti"

Duk sonda Nannah takewa Ashraf sai gashi tana marin shi, tare da gaya mishi cewa ya ajiye Ni. Ko tagaya mishi magana, ganin haka Ummi tazo zata janye Ni daga jikinshi, ya kara runguma na yana fad'i.


"Don Allah! Karki rabani da ita, ita ce gatana! Ita ce duniyata! Ita ce Alfarma ta! Ita ce suturata! Sirrnina da halayyata ya gurinta! Na had'i da wanda rayuwar mu da mutuwarmu ke hannushi ku hukuntani amma karku ce bazan zauna da ita ba."

Kura mishi idanu Ummi tayi jikinta na tsuma, ga Nannah ita ma, tana jan Ashraf. Tare da kifa mishi mari,
"Dole ka rabu da Ita! Yarinyar da bata ji maganar iyayenta ba yaushe zata ji maganar ka!? Yarinyar da bata ɗauki zina a bakin komai ba yaushe zata zauna iya kai ba tare da tafita niman wasu ba!? Me zakayi da mace mara daraja ga mata bila adadin idan don mata kake muje ka nemi a gidajen alfarma."


Kallon Mahaifiyarshi yayi jin abinda take fad'a.
"Ke Mahaifiyata ce!? Tayani niman auren SAFINAH zakiyi ki bar tozarta min uwar Y'ay'ana Don Allah Ammyna."


Kallon Ummi tayi cike da bakin ciki tace.
"Nawa ne kuka kashe gurin shanye min D'ana!?"


Murmushi Ummi tayi sannan tace.
"Idan shanye shi muka yi, toh bazamu tab'a barin shi ya kalleki ba. Tabbas idanunmu sun rufe da kaunar da muke miki muka gaza fahimtar meye a ranki, wancan ranar! A wancan lokacin da Badar ya barki a can jordan da kaddararta bata sauya ba! A lokacin da kika fahimci in ba ita ba burinki bazai cika ba, da ban bata kwarin gwiwa ba, da haka bazai faru da ita ba! A lokacin da ban barta a jikinki ba da yau baki raye! Amma ba damuwa! Dan Ni a tunanina idan sadaukarwa da tayi zai iya sayan soyayyar da kika mata ashe ba haka bane, dukiyar da kika bamu shine fansar duniyar Y'ata."
Juyawa tayi gurin Abdul tace.
"Kaje kasan gado! Zaka ga jaka ka dauko mata! Karki manta baki da dukiyar da zata fanshi SAFINAH, tuntuni dukiyar ki na zaune, wanda muke ciki rufin Asirinki daga Ubangijin, a lokacin da kika bamu naki a lokacin nima mahaifina ya bamu dan ya rike mu."
Fitowa yayi da jakar ya mikawa Ummi ita kuma ta ajiye a gaban Nannah.
Sannan ta juya ga Ashraf tana murmushi tace.
"Tunda ta tambaye ni Ummi na! Meye Ake nufi da Hulu'e!? Na fahimci ta fad'a komarka, sannan dan ta guje min jin ɓacin rai take niman hanyar rabuwa da kai badan bata sonka ba sai dan soyayyar iyayenta! Ashraf indai Ni da Na haifi Safinah zan zuba mata ido naga gudun ruwanta ai kai da ka mata roman baka me sauki ne!? Ina sane da abinda ka mata ranar da ka aureta, amma dake Ita wawuya ce bata ji zafin ka ba saima kara mika maka rayuwarta da tayi. Duk abinda kake ina kallonku, dan haka yau badan Ni ba badan mun isa ba, kamar yadda ta dawo maka da dukiyar Aurenka, yau ma zan dawo maka da ita, yana cikin takardan da kabata, dan na ɗauki asalin na kuɗin na bar mata wanda babu kome a cikin sai takardun. Karka manta Ni uwa ce."


Juyawa tayi taje d'akinta ta ja wani durowa ta ciro farin ma kunshi kudin ta fito dashi sannan ta kai mishi, cikin wani Irin yanayi amsa yana kallon Nannah da Abba, sannan ya kalli Dudu, a sannu ya cire ni daga jikinshi.
*(Hulu'e kuɗin fansar kai ne ko nace kuɗin wanke muni da kotu take niman mace ta biya idan tace bata son mijinta! Sannan wasu sukan biya idan zama yaƙi dadi sabida rabuwa! Sai dai a wannan rayuwar ina son nayi jan hankali gare mu mata, sam ba dad'i kam amma shi rayuwar aure dukkanshi ibada ce, idan muka dauke shi a hakan zamu rabauta, sannan idan kika ce sai abinda mijina yayi min ke naki mijin zai miki wallahi kin fad'i ba nauyi, sannan bamu amfanin kiran Namiji da suna mara fahida, su kanin Ajali, su buhun kaya, su hankaka, Wallahi a wannan rayuwar kina zaune cikin gidanki kika b'allo aurenki ko!?🙄🤔 Wallahi sai kin yi dana sani, bawai nace ki zauna ayita cutar ki ba ki nazarci rayuwarki meye yasa Bawan Allah yake miki wani abu!? Idan kuskuren nakine better ki gyara, zaki samu kwanciyar hankali. Wallahi ina Alfarma da Iyayena, dan lokacin da aka zo niman aurena, abinda suka ce shine sai kayi hakuri da ita dan fitinanniya ce, amma tana saukin hali idan Kabi da Ita sannan tana karanta labarin kanzon kureje dan karka sameta tana karatun tana wasu dabi'u kayi tsammanin haka muka tarbiyyar ce ta. Alhamdulillah now ina niman 10yrs, ba yaji ba raba faɗa. Har mahaifiyar ta rasu ban taɓa kai mata matsalar aurena ba, abin mamaki a wannan duniyar aure yana fuskarta barazana, su iyayen suna jiran giredi ita ma yarinyar haka, shima mijin haka, yau abin haushi namiji dan ashirin da daya zai fito ya nuna aure yake so ki hana, Shin zaki hana shi matse yar mutane a lungu!? Haka ma yarinya ta nuna tana son auren kin hanata zaki iya hanata bada kanta a matseta ki kuma fad'awa lesbian. Don Allah domin kare kananun yaran mu daga sharrin fyade, luwadi, madigo, muyi ƙoƙarin bawa mutane kirki aurensu, Heeeeeeyeee Sai kuma Matan auren kina Ruwa idan kika ce baban yaro sai yayi miki irin cin da Ashraf yayiwa SAFINAH 🤔🙄😂 kin kama gaibu, wallahi kin fad'i ba nauyi. Dan Ni mijina kullum kallon zaki nake mishi ba mijin novel ba, saka sex ko Romance bawai dan a kwadaitar daku haka yake a zahiri, a'a akwai ƙalilan, amma rashin sa yafi yawa, ki kalli mijinki kamar Tiger shruff ko sharukhan ko Ashraf sai kin wahala, amma kika mishi kallon abokin rayuwarki sai kinfi samun nutsuwa. 😏😏🙄 Banda lalacewa kina tare da shi kina tunanin ai ba haka mai lucky yayiwa Maryam Sajida ba,🤔 bayan Itama a cikin labarin sai da ta hadu da kaddararta, wallahi mu ji tsoron Allah...... Sannan nasan maza biyu da suka sayi wannan book ɗin kuyiwa kanku adalcin da matayen ku. Ko sau daya ne ka nuna mata so zatayi alfahari da haka, bawai dan kun tara Yara soyayya ya kare ba, Yana daga cikin soyayyar da bazai kare ba shine soyayyar gidan Abu Alkassim Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, don Allah ku sanya mu a hanya idan.mukayi kuskure duk abinda zamu aikata duk sabida kune ku k'iyayye nuna mana abinda idanunmu bai gani ba, sannan ku girmama soyayyar mu. Yanzun da zaka taɓa wata rabonki da mijinki yace yana sonki tun yaushe Allah sai kaji tace i heard that since 1948 Why sabida bamu daraja kanmu ba mun maida kanmu wasu dabbobi zamu hadu a Next pag)*


Ku gafarce ni Ni yarinya ce dan ban rufa 27yrs nasan kuma na tara iyayena da yayuna a cikin grps ɗin ga kanena yan mata da matan aure, sa'o'i na dole sai da tunatarwa ku gafarce ni abisa kurakurai na🙏🏽🤧
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah......


2️⃣2️⃣
Gaggara motsawa yayi hannunshi daga nawa, yana kallon Ummi.
"Tashi ka tafi amma ya batun sakinta fa."


"Wallahi bazan iya ba! Bana kuma fatar haka, Ni na saki mata ta! Matar da nake So! Nake kuma alfahari da samunta a matsayin mata ta! Wallahi gwara na mutu da naga wani ya rab'e mata ta, wallahi bazan iya ba! Gwara na mutu da na saketa."


Yana fadar haka ya juya ya fita, juyowa Ammyn tayi zatawa Ummi tijara, ta nuna mata hanyar fita dole tafi.


Sannan suka dawo kaina, Dudu ya dauke Ni da sauri, suka fita dani Abba ne ya tadda motar, aka nufi asibiti dani.


Abin mamaki Dr Hameeed shi ya karb'eni amma Dudu ya hana shi min kome karshe Dr Muhsin da Dr Azeemah.


Cikin gaggawa suka shiga bani taimakon, sai da suka shafe awa d'aya cur sannan Dr Muhsin ya fito shida Dr Azeemah, suna share gumi. Dafa Dudu yayi cikin damuwa yace.
"Am sorry Dr Kyari mun rasa babyn."

Lumshe idanu Ummi tayi cikin damuwa.
Hawaye ne ya zubo mata tace.
"Ya ita SAFINAH! Da fatan babu abinda ya sameta"


Girgiza kai Dr Azeemah tayi cikin sanyin Murya tace.
"Babu Wata matsala Mah idan ta farka zata warware."


Hawaye ne ya shiga zuba ita tayi dukar ne bawai dan ta daki cikin. Tayiwa Yarta Asarar gudan jininta, ba zata kuma barin SAFINAH zubda hawaye ba, goge kwalla tayi tace.
"Zamu iya ganinta!?"

"Eh! Mah zaku iya ganinta amma banda hayaniya."

Mikewa tayi ta shiga dakin ta zauna a kujeran. Tana kallon yadda na firgice, duk na zub'e.
★★★
Koda Nah ta fita babu Ashraf babu me kama dani da shi, abin ya kad'ata tambayan Drivnta tayi ya gaya mata ai ya fita a guje.
Haka ta shiga motar aka kaita gidan shi babu labarin shi.

Dole aka nimo mata Ghaniyu, ta saka shi gaba da masifa, dake yaji abinda ya faru kememe yaki gaya mata inda yaƙe.


Kamar zata yi hauka, sai da ta kwana ta wuni sannan tattara ta koma.
........
"Ya jikin Nashi Dr."
Murmushi Dr Hameeed yayi cikin nutsuwa ya kalli Fahad yace.
"Da sauki! Zaku iya ganinsa, amma don Allah karku takura mishi dan ya bugu sosai a kanshi."
Gyad'a mishi kai suka yi, sannan suka shiga yana kwance idanunshi a rufe, zama kura mishi ido suka yi. Duk ya zauce ya koma zararre, a cikin wuni daya ya koma wani irin halin,


Abinda Ya faru bayan fitar shi da mota, a guje garin ɗaukar waya ya kira Ghaniyu ya fitar mishi da Passport dinshi, wata mota ta daki nashi take motarshi ta fad'a cikin rami.


Dr yazo wuccewa yaga lambar motar. Ashu shine ya kawo shi asibiti.
★★★
Bayan awa hud'u na farka, ganin Ummi ya sani razana zan tashi.
"Koma ki kwanta,"
Komawa nayi nayi na kwanta ina lumshe idanuna.
Riko hannuna tayi tace.
"Kiyi hakuri! Na miki asarar babynki"


Kwalla ne ya zubo min, a hankali nace.
"Ummina! Ki gafarceni cin amanar ku da nayi."

"Ni dai da baki sabawa Allah ba shine farin cikina."

....... Haka muka cigaba da jinya kwana uku suka sallame ni, sai dai na kara komawa wata irin, dukda nasami Yarana a gidan, haka ya rage min damuwa sosai, kuma ina ƙoƙarin fitowa ayi wasu abubuwan da Ni, sai dai Aahu ya zame min bugun zuciyata, tabbas ya zame min farin ciki na.


★★★
Shima ya warke sumul, sai dai ya tafi Oman sakamakon kiran da aka yi mishi Nannah ba lafiya.


Ta asibiti ya fara bi, ya sameta da sauki ba wani ciwon da kawai dan ya dawo suka ce bata da lafiya.
Tunda ya shiga d'akin shi ya rufe bai fita sai lokacin Sallah.
Duk sun damu da rashin kulawar da yake nuna musu.
Kara Smartphone dinshi yayi da sauri ya shiga dakin ya haɗa da laptop dinshi.
Sanye take da wani pink towel, tana tsane gashinta ta da Towel Dan Karami, yaran suka shigo da gudu suna faɗa, duk sun rud'ata sai ƙoƙarin kunce mata towel ɗin suke,
Tsawa ta daka musu suka fita da gudu, tana dafe goshi tayi a dame.
A hankali bakinta yake motsawa, murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Madarata ina kewarki sosai."
Kamar wanda aka tsikare shi ya shiga had'a kayansa a cikin jakarshi, ya ɗauki Passport dinshi, ɗaukar takarda yayi dan yi rubutu sannan yasa kai ya bar musu gidansu.
★★★
Kusan wata uku kenan da faruwar rabuwarmu, duk lokacin da begen mijina ya taso min daki nake komawa nayi ta kuka ina masifar Son mijina, a yanzun da baya nan na fahimci cewa nima jarababbiya ce irin shi, duk lokacin da na kwanta sai nayi mafarkin shi, idan zan zauna gizo yake min.


★★★
Yau ake sunan Asma'u ta haihu, ina ta sauri zan je gidan sunan duk sun tafi sun barni tsabar nawa.
Mota ta nake ja da sauri, tsayar dani akayi kamar bazan tsaya ba, dan har na wucce sai na dawo da baya.
Ina zuwa nayi parko tare da sauke glass.


Matsowa mutumin yayi sai a lokacin naga bashi d'aya bane.
Nuna min bindiga, a rud'e na kallesu bakina na rawa, nace.
"Lafiya!? Me na muku!?"
Shigowa mutumin yayi tare da cewa.
"Muje"
Zan bud'e gefen ya jefa min hanky, kifa kaina nayi sai da jera Atishawa uku sannan barci yayi gaba dani. Fitowa yayi sauran suka fito zasu fitar dani, sai ganin mutane sukayi sun zagaye motar, Ghaniyu yace musu.
"Me kuke bukata!?"
Babban zai magana Ghaniyu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login