Showing 87001 words to 90000 words out of 108344 words

Chapter 30 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt

Ni da duka. Tsabar ranshi ya ɓaci, ya juya zai fita. Ƙasa ƙasa nace.
"Wallahi ka dawo ka shafa min lafiya dan na gaji da zama da kai."
Girgiza kai yayi ya dauki kayan shi tafi daga d'akin, tabbas da ace ya iya duka da babu abinda zai hanashi zane SAFINAH, wallahi ko Natashah bata isa ta mishi rashin kunya ba, amma Safinah da ta ga gadon barcin shi.


Haka yaje ya shirya, sannan ya dawo dakin saboda kuma Ablah, ina zaune ko kallon inda take makiyin b'allo yayi tunanin sabida yaran nake zaune dashi.


Ɗaukar ta yayi ya fita, ina son zuwa Masallacin Manzon Allah, amma tunawa, bai bani izinin fita ba yasani kwanciyata.


Kartan yunwa tasani mik'ewa zanci abincin da yayi sanyi, ina fitowa falon naga wayam, shiru nayi. Kwafa nayi na shige d'akin na kwanta ganin zan cutu da yunwa tasani mik'ewa na biyu zuwa falo na dauki wayar tafi da gidanka, na kira dakin girki na fada abincin da za a kawo min.


Zama nayi dan jikina har rawa yaƙe, buga kofar akayi, naje na bud'e sannan na amsa abincin, nayi godiya tare da rufe kofar,( bari ba shegiya nace da Ubanta)

Dakyar na wanke hannuna nazo na fara ci, hannu baka hannu ƙwarya, kan kace me tuni na cinye har zare ido nake ga gumin dake karyo min, kiran sallah naji daga masallaci Manzon Allah, na tashi tare da mik'e, sannan na wucce cikin na wanke hannuna sannan nayi alola na fito.
Ina fitowa na ɗauki abin salla na tadda nima, bayan na idar, na zauna ina azkar sai gashi ya dawo da ita, ajiye min ita yayi akan cinyata, sannan ya fita sai nono take nima sai naji ban kyauta ba, ciro nonon nayi nasaka mata a baƙi.


Sauran kwanakin da suka biyo baya, zaman mu ba dad'i. Wallahi domin kowa abinda yake so yake yi, ya ki kuma magana dan ya fahimci nima shi nake da magana, dan haka sai ya bawa isa ajiyata.


Kwanakin mu biyar muka wucce Makka domin umra, a can nayi addu'a sosai da niman zab'in Allah akan zamana da Ashraf.

Kwanarmu huɗu Ghaniyu ya wucce, Oman, washi gari muka dawo Jordan bayan mun gama ibadarmu.


Ranar da muka dawo mun same Fadar, an gyarata fiye da, bayan shashin mu kuwa yafi ko ina had'uwa, a tsohon shashin sa muka zauna, dan yace. Nan ne mafarin komai, dan haka bazai bar shashin. D'akin da bazan manta ba, itace ya bar min a matsayin nawa shi kuma ya ɗauki d'aya, bayan nayiwa Ablah wanka nima nayi, ina zaune sai naji ina son cin abinci dan haka na tashi na mai da Ablah na kwantar da ita sannan na fita. Yana zaune shi d'aya, yana shan tea, nazo na wucce shi. Bina yayi da ido.
Dake blue jeans ne a jikina sai farin shirt me ratsin pink, nayi kyau sai dai na rame, saboda matsalar da muke fama Ni da shi, sam a yanzun abin yafi yawa, dan ko a gaban shi zan yi tsirara, wallahi bai dame shi ba, nima da na dauka da zafi na watsar da komai sulhu nake nima yaki yarda ya saurare Ni, na kira Ummina tace babu ruwan ta, Nanah Asma'u ce ta bani hakuri da kuma na cigaba da binshi.

Maqbool na dafa, sai fruit juice da nayi nazo na ajiye mishi, sannan na dauki nawa na wucce d'aki dashi, Ni nada Amma sai nakasa ci, sabida tunanin zai ci ko bazai ci ba, kad'an na tsakura sannan na fito zan kai kitchen naga baya falon, duba table d'in nayi naga babu abinda yaci, zama nayi tare da fashewa da kuka.
Nasaka abincin a gaba ina kuka, cikin shirin fita pada ya fito, ganin yadda nasaka hannu na tallebi fuskana ya sashi jin ba dad'i, har ya wucce sai kuma ya dawo ya zauna, jan kujera yayi ya zauna, sannan ya gyara hannu rigarshi yana kallon kular abincin.
Jikina na rawa na mike na fara kokarin saka mishi amma na kasa, mik'ewa yayi, nazata tafiya zai yi sai naga ya rike hannuna yana daban abincin, kuka nake har da shasheka, na kalli fuskar shi nace.
"Kayi hakuri Wallahi bazan kuma ba."


Murmushi yayi sannan ya zaunar dani, ya fara cin abincin.
Lumshe idanunshi yayi cikin jin dad'i, rabon shi da yaci abinci me dad'i har ya manta, tun shinkafa da wayen da yaci.


Ruwan fruit juice din na zuba min shi yasa ya koshi sannan ya mike tare da rungume Ni dan nima na mike yace.
"Nagode sosai"


Kwallar farin ciki ne ya sauka a idanuna nace.
"Me zaka ci!?"
"Ba komai."
Janye jikinshi yayi na riko hannun shi, nasaka a fuskana.
"Don Allah ka gaya min abinda zan girka maka"


"Duk abinda yayi miki, zan ci."


Gyad'a kai nayi amma bawai na gamsu bane, koda ya fita kuka na zauna nayi har naji Ablah na kuka,


★★★
Kwanan mu biyar da dawowa Su Nannah suka zo, nan na kuma shiga hankalina, dan na fahimci wannan dawowar babu alkhairi a cikin shi, dan daga shigowar ta part d'inmu, ta shiga min kallon ban isa ba, nima sai na kame kaina, tun kafin kimata ta zub'e, dan Natashah itama babu sauki nagani a idanun ta.


Ashe ana can suna shirya mishi, liyyafar dawowar shi, dan har su Ummina dasu Dudu zasu zo.
Bai gaya min ba, sai da nakewa Nanah Asma'u korafi, a nan take gaya min abinda yake faruwa.
Naci kuka har Nagodewa Allah.
Tausayin kaina duk ya kamani, gashi Nannah da Natashah suma basa shiri, kamar da can baya. Ni kuma miji ya juya min baya.

Ban nuna mishi na sani ba, sai ana gobe su Ummina zasu zo, Sannan ya gaya min murmushi nayi sannan nace Allah ya nuna mana lokacin cikin koshin lafiya.


Nima idanu na zuba Mishi, ban san me yasa Nannah bata zama a shashinsu ba sai a namu, idan na tasha ta shigo, ni ina daki sai ta shigo d'akin ta ɗauki Ablah tayi ta renonta. Sai na watsasu a kwandon shata.


★★★
Yau su Ummi zasu iso, dan haka tun safe na fara aikin girki, ina gamawa nayi wanka tare da shiryawa, ina d'aki a zaune ya shigo min, ganin yadda nayi zurfin tunani yasashi zama kusadani, dan abinda na fahimta sun dinke da matar shi, dan har biyo shi nan take, ta kwana ranar da na gani nayi kuka sosai dan wallahi kasa barci nayi dan zaman mu a Lagos bai tab'a zuwa d'akinta ba. Amma wannan karon bata fita sai da safe lokacin ina abin karyawarmu.


Idan nace ban cikin damuwa nayi karya, dafa kafad'ana yayi ya sani dawowa hankalina, ture hannunshi nayi daga jikina, ina kallon shi cikin tambaya nace.
"Lafiya mijin Natasha(Kyautar Allah)".
Murmushi yayi sannan yace.
"Ba wannan bane ya kawo Ni, ki tashi su Ummin sun iso."


Zai kai hannun jikina nayi baya tare da cewa.
"Kul! Karka tab'a Ni"


Murmushi yayi sannan ya fita daga dakin, ina zaune har na fara jin hayaniyar yan uwansa, na kasa mik'ewa. Ina jinsu suka iso kuka ne ya kwace min na fad'a jikin Ummina, wacce ta kasa hakuri ta shigo d'akin.


Isowa tayi inda nake na fada jikinta ina kuka, kamar raina zai fita, nace.
"Ummina ki yafe min."
Dafe kaina tayi cikin tausayina tace.
"Na yafe miki! Maman Fatima Khatoon."


Shafa bayana tayi tayi, har nayi shiru, zama tayi tare da kallona tace.
,"Tun ranar da kika kirani na kasa samun nutsuwa sabida nasan kina cikin damuwa, haka yasani kiran Mijinki na tambaye shi ko ya gaji dake ne, ya sawwaka miki, amma yaci min shi bazai rabu dake ba, kuma babu wata matsala a tsakanin ku, don Allah Kiyi hakuri ki had'iye komai, zan tayaki da addu'a dan dama ina kanyi ba dare ba rana, kiyi hakuri."


Nasiha tayi min sosai sannan muka fito falo, rungume juna mukayi aka hau muna, abinci na ciro musu, shigo Nannah tayi suka gaisa da Ummi da kuma sauran yan uwana, kallon su Aamih tayi sannan ta mika musu hannu dake sun santa suka je gurinta, maganar gaskiya tun shan sambad'e de da Nannah tayi a hannun Natasha, ta dawo rakiyar ta, Ni dai ce bata yina sabida na kwace mata D'anta. Kallon tayi sannan tace.
"Ina Urwah?!"
"Nah tana barci"
Urwa shima duk cikin sunan Nanah A'isha ce.
Mik'ewa nayi naje na d'aukota, sannan ta kama jikinki tayi gaba dasu, murmushi nayi a raina nace.
"Anki cin biri an sha roman sa"
Ba a sona amma ana son Yarana.
"Kuyi hakuri Didi wata rana sai labari."
"Insha Allah,idan tayi hakuri zata ci riba."
Gyad'a musu kai nayi, Tabbas hakuri da wuya amma idan kayi zaka ci riba.


Mu sha hira, sannan na kai Batul da Khalilah da. D'aya dakin da ba kowa, Saphia da Nanah Asma'u, d'akina Ummi kuma tayiwa Nannah kara ta koma shashin ta, yaji dad'i kuwa jikinta na rawa bata shiga hidima da Ummi.


Bayan tafiyar Ummi su Asma'u suka min caaa akan na gaya musu abinda ke faruwa.
"Ai dole ki sane mishi akai, Didih baki jin magana baki iya so ba baki iya k'iyayya ba, sannan mijinki bai isa ya ce karki yi kaza ba sai kinyi, banda zubda kai taya zaki bar wata banza tazo har shasinki ta kwana da mijinki kuma ranar girkin ki."


"Kun nifa kawai ina niman hanyar rabuwa da shine yanzun tunda bai hakura ba, Ni kuma bazan iya zama yana cigaba da share Ni ba, kawai gwara mu rabu."
Buɗe baki suka yi dukkan su, cike da bakin ciki, suna nuna min Annabi ina rintsa idanuna, mikewa Sophia tayi ciki jin haushi tace.
"Kinga Mamankar Sabr nayi nan, dan matuƙa na cigaba da jin abinda Didi take fada zan iya mata rashin kunya, kuma In-law ce Babu reni, sai girmamawa."


Ban d'aki ta shige, kwanciya Nanah Asma'u tayi tace.
"Ranki shi dad'e bani da bakin magana, Allah ya baki Sa'a"


Shiru nayi dan na lura duk na basu haushi (🤣😂😹 Ashansha inji Dan gwari) banda iskanci ana baki shawara kina cewa kashe auren zaki yi
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


Oum Muwaddah


*An sami matsala daga saka number ne amma zan cigaba haƙa*
4️⃣0️⃣
Shiru nayi dan naga sun fusata, kwalla ne ya cika min idanu na shiga gogewa a hankali shasheka na ya dakatar da su, cirko cirko suka yi jikinsu yayi sanyi, zama Sophia tayi tare da dafani tace.
"Didih! Mufa bawai munki baki shawara bane, taya zaki gama shan wahala da mutum once kice wata yar abu kazan uba ta sha gabanki, didih soyayyar da kike nunawa Abbansu yasa yake baki wahala."
Bakina na rawa na riko hannunta, cikin kuka nace.
"Ya zanyi dashi, baya damuwa idan yaga canji"

Dariya tayi Sannan ta gyara zamanta tana kallon cikin ƙwayar ido na, tace.
"Gaya min meye kike a gidan Ni kuma na ciro miki raunin shi."


A kunya nake gaya mata komai, baya niman hakkin shi, sai dai zai ci abinci ko wani irin.


"Zaki ciyar dashi dad'i amma zai sauke nauyin abincin akan wata, daga yau karki kuma girki dashi!"
Zaro ido nayi cikin damuwa nace.
"Toh a ina zai ci!?"


Tsaki Nanah Asma'u tayi tace.
"Kinga irinta ba anan nuna miki Annabi kina rutsa idanunki, dole ya dawo ya risina miki, dole ki rama wulakancin da yayi miki inda hali tsakaninku, sai dai yaji kina dariya da yaranki ba dai shi ba, ita kuma Natasha ki ci mutuncin yar banza Idan ta kuma shigowa ki koreta ki mata diban albarka."


Kallon su nayi ina nazarin abinda suka ce, ajiyer zuciya na sauke, sannan nace.
"Ashraf ɗin da bashi bane ga yanzun. Miskilancin, shariya."


"Ko shine dutse dole yaji a jikin shi."
"Toh ai naga kamar bazai damu ba."
Dariya suka aka sannan Sophia tace.
"Hmm! Muna nan dake zai ji, ai sabida kina damuwa dashi shi yasa ko kinyi fushi ba zai damu ba, koda baki je d'akin shi ba akwai me zuwa, amma idan kika daina kuka daina had'uwa kuma kika daina girki dashi, zai gaji ya sauko nan kuma sai ki gasa shi don ranki."


Shiru nayi ma rasa abinda zan ce musu.
"Allah Didih ki rage soyayyar da kike mishi, ki aro halin da ba ba ki mishi in ba haka ba, zaki ji jiki domin yana da damar kara aure kuma ya cigaba da gasaki."


Dafe goshina nayi ina jin hudubar su, miko min wani bag.


Buɗe bag d'in tayi sai ga kayan mata, kauda kai nayi nace.
"ajiye su no need domin ban sami uban gayyar ba, bani da ikon tura wani abu a jikina ko shan wani abu ba."


"Toh ai sai ki tashi a tsaye gurin kwatar kanki."


Haƙa suka yi ta bani shawara, nima dai ba laifi na ɗauka.
Washegari..
Muka tashi da bikin taya murnan dawowar Ashraf, anyi hidima da rana, da dare kuma akayi dinner wanda nayi dana sanin, zuwana jordan da sanin Ashraf d'in ga baki daya. Dan a daren ya gabatar da Zoyah da Natashah a matsayin matan shi. Kura mishi ido nayi a hankali na zare zoben hannuna, lokacin da muka je taya shi murna, rungume shi nayi sannan na kai bakina dai dai, kunnen shi nace.
"Nagode sosai! Bazan d'aga hankalina ba balle ace kishinka nake, zan Barka da manta amma ba yanzun ba, ga tsiyarka da kabani shekara hud'u baya."


Lallubar hannunshi nayi nasa saka mishi, sannan na bar inda yake na dawo mazaunina, muna kallon juna, ido cikin ido.


Tunda ta bar gurin jikin shi yayi matukar sanyi, shi yayi haka ne dan ya rama rashin jin maganar shi, bawai dan ya wulakanta kimarta ba. Dafashi Natashah tayi cikin jin haushin tace.
"Wacece Zoya?!"
Banza yayi mata idanunshi na kaina, ya rasa abinda zai yi dan wanke kanshi.
Haka taron ya watsa, Inda kabilar banu Hussain, suka tafi da farin cikin aurar da yar su a matsayin matar sarki, tunda dama ya amshi auren tun baya yanzun ne zai cika alkawarin da ya dauka.
A daren yaso ganina amma fir naki zuwa da ya dame Ni da kira na ajiye shi a bakin jadawali. Hankalina kwance.


Washi gari... Su Ummi da yan uwana suka tattara suka barni cikin kad'aici da damuwa,'.


Tunda muka dawo daga raka su, na had'a kan yarana muka shige d'akina, ban kuma fitowa ba, sai da karfe sha biyu naje na daura mana abincin rana, ina gamawa na juye mana na wanke komai sannan na koma d'akina.

Duk abinda yarana suke so zan musu a d'akin, da dare ina jin yazo bakin kofata yana bugawa, Ni kuwa nayi banza dashi.

Dan dole ya hakura, da asuba muka had'u, Ni zan shiga kitchen shi kuma ya fito d'akinshi da Natashah a bayan shi, tsayawa nayi ya wucce tana zuwa zata wucce na riko hannunta, cikin harshen English, nace.
"Wannan ne karo na karshe da zan ganki a shashina, idan kika bari nayi ido biyu dake Next time, wallahi sai na tafasasshen miki fuska da mai me zafi."


Na fad'a a matukar haukace, tsoron yadda na buga mata tsawa yasa ta fashe da kuka, zuwa yayi ya zare hannunta yayi a cikin nawa.
Ya fitar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login