Showing 60001 words to 63000 words out of 108344 words
Chapter 21 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt
rabu da D'anta naki, ta sauko ta fara shiga jikina.
Sosai abin ya tab'a Natashah musamman da taga Nannah ta mik'a min wuya, lokacin gud'a itama ta shiga niman shiga jikina.
Kai tsaye Ashraf ya shiga cikin alakar ya hanani, yarda da kowa dake Ni d'in wawuya ce ban san me sona ba, musamman da naga sun miƙa min kansu babu tunanin kome, sai nima na yarda dasu, shi kuma da ya fahimci akwai abu a karkashin sulhun, sai ya raba Ni wasu.
***
Ina kwance nasaka aya a gaba Ina ci, ya shigo min falo ganin yadda nake like idanuna, yayi murmushi tare da zama kusadani ya amshi bowl d'in ayar yana kallon ciki.
"Karki yarda da kowa sai Ni!? Ni d'in ma sabida, duk duniya da yarda kowa ba sai ke!? Sabida kece rayuwata, SAFINAH Ammyn Mahaifiya ce, ban yarda ko ruwa ta baki kisha ba. Na gaya miki ki rufa min asiri, ina bukatar ki da abin cikin ki."
Sai naji ba dad'i sabida Uwa ce like me! Bazan yafewa kaina ba idan har Yarona yayi min haka, kuma zan ji ciwon haka dukda ban san meye hujjar shi nacewa haka ba, amma Uwa wucci haka. B'ata fuskana nayi sosai tare da janye hannunsa akan cikina da yake shafawa, na tashi daga kwancen da nake, na shiga niman rigar barcina na saka, zan fita yayi maza ya sauka a gadon tare da shan gabana.
"Don Allah ki saurare Ni! Zan miki bayani!"
Cikin ɓaci rai nace.
"Matsa min ko na zabga maka tijara! Tunda naga kai ba damuwa kayi da sab'awa Uwa ba, sannan ka ajiye Mata a gefe idan baka yinta ka sallame ta mana, Ni nagaji da wannan shirmen naka wanda yake cike da yaranta."
Kura min ido yayi ranshi a b'ace, make min baƙi yayi da hannunshi, yana ƙoƙarin b'oye bacin ran shi.
Tura ni gadon yayi ya kare min wulakancin, sannan yajani zuwa ban d'aki, ina ganin ja'iba a hannun Ashraf. Duk yadda naso na nuna mishi uwa ba abar wasa bace. Sai ga Mu guy yana fushi dani, once suka d'inke da Natashah.
Sosai suka d'inke, kamar wasa suka shiga tsakani na dashi, duk yadda naso share su kasawa nayi. Ina kallon zai kwashe Yarana su fita su barni kamar mayya a gidan.
Haka ya kuma fito min da halin Nannah sosai dan lokaci da ta fahimci yaronta yana fushi dani ya koma gurin Yarta sai ta same nutsuwa, bazan iya kwatanta muku halin da na tsinci kaina a ciki ba, amma wallahi uwar mijina tana jin zafina da ciwon kasancewata rijiyar D'anta.
A sannu ciwon kai ya fara sani a gaba, me had'e da jiri. Ranar da bazan manta ba, sun dawo daga yawon shakatawa, shine a gaba table da yaran a kirji ko nauyin su baya ji, ya shigo gidan,
D'akina ya kaisu sannan ya shigo nawa ya dame Ni ina kwance a kasa jini ya b'ata ko ina, d'aga Ni yayi yaga na koma. Da gaggawa ya fito dani zuwa asibiti, wanda yake a lekki d'in.
Kamar zautacce yake tuki har ALLAH ya kaimu asibitin, nan dai aka shiga Bani kulawa cikin aka samu bai fita ba.
Kwanan mukayi Ni dashi, washi gari basu san zai dawo ba, a lokacin yazo ya same Natashah ta zane yaran tare da sheka musu ruwan sanyi, Nannah kuwa tana d'aki tana barcinta wai dan sun tashi suna kiran Didih dake yaran sun bi bakin Yaran gidanmu suma Didi suke kirana da shi da, shine suka yita kuka daga fitowanta ta zane su, da wayar Usb kuma ta watsa musu ruwan sanyi, shine Uban yana zuwa.
Bai bi ba'a si ba, ya rufe ta da duka, yadda yake shiga banan yake fita ba, sai da Nannah ta mare shi ya Kyaleta.
Sukan yaran ganin yadda babansu ya haukace yasasu komawa guri guda jikinsu na rawa, dan dama matsorata ne.
Kwashe yaran shi yayi ya kaisu sama ya musu wanka, daga nan ya wucce dasu Our daily meal, inda ya saya musu abinci har dani ya kawo min asibiti.
Suna isowa suka zo guna da gudu, tare da fashe min da kuka, kallon shi nayi yadda yake cikin rashin walwala. Ga fuskarshi a daure.
Ina cikin damuwa sosai, domin fushin da Ashu yake yana tab'a zuciyata, ina son sanin meye matsalar na kasa, kwana na uku aka sallame ni, tare da gargad'in banda aikin ƙarfi banda dogon tafiya. Banda Sex!?
(🤗😂🤣) Wallahi a take Ashraf ya dallawa likitan harara yace.
"Ina zan kai bukata ta! Ko ce maka aka yi Ni d'in mazinacine!? Tun wuri kusan abinda zakuwa cikin, dan tabbas sai na sauke nauyin dake kaina."
Kallonshi likitan yayi cike da damuwa yace mishi.
"Me Oyinbo! Zakayi hakuri har cikinta ya shiga wata shida!"
Tsuke fuska yayi cikin masifa ya riko hannun yaranshi.
★★★
Koda ya bar gidan da Yaranshi, zuwa Nannah tayi ta d'ago Natashah daga ƙasa tace.
"Matuƙar kika ce zaki saka kishin ki a kan yaran zaki wahala! Ni dai kisan yadda zaki yi ya dawo gare ki dan matuƙar yana tare da SAFINAH! Shima zai iya bada rayuwarshi dan ita da Yarantaka! Domin haka Kakansa da Mahaifinsa sukayi.,"
Kura mata ido tayi cikin kuka tace.
"Ke bata Ni ma kike ba!? Ta d'anki kike! Sai dai SAFINAH ta gama da shi amma ba makawa bazan kuma taimaka miki ba, dan nima mijina nake buƙata. Kuma sai na haifi Yaron da narasa."
Tabbas rayuwar da ka ganshi nan, a shirye kome yake. Musamman idan ya shiga zanen Kaddara, toh haka zaka ga komai na zuwa maka ba zato ba tsammani. Zaka ga komai na faruwa da kai, tunda muka dawo Ashraf ya tsiro min iya shege, dan ban san meke faruwa ba, sai dai zai gayyato min Natashah zuwa falona suyi rashin kunyar su, dake cikin ya sanya min rashin son magana ko kallo basu ishani ba, ban kuma tab'a gayawa koda Ummina, dan ban ga abinda zan gaya mata ba, kusan me yasa sabida ita d'in Mahaifiyata ce! Zata iya yuwa na manta abinda aka min, amma ita har duniya ta tashi bazata manta ba, shi yasa wani lokacin bana son nace Ummina wane ya min kaza ya min kaza( wallahi akwai kuskuren da muke aikatawa, dangane da iyayen, Yarone yayi miki laifi sai ki hukuntan shi, indai akwai Fahimta da iyayen shi, karki fad'awa Iyayen shi laifin sa, ba dan kome ba sai dan ita Uwa takan ajiye duk wani kalubalen D'anta a cikin wani cantainer na daban, a duk lokacin da ta gana zata bud'e tana jiran yau ma dame kazo dashi, idan alkhairi ne ta saka a ciki ta rufe, idan sharri ne ta addana a ranta, a duk ganinka da ita zatayi toh da wannan tunanin ne a ranta, ta riga cewa toh yau wane da mai yazo, kai wane baya ji! Don Allah ko sau d'aya ne karki kai yaro kara gurin Mahaifiyarshi, ki kai gun Mahaifinsa haka zai ragewa Uwar damuwar da take ciki Allah ka bamu ikon tarbiyyarta da yaranmu takan dai dai 🙏🏽Amin Ya Allah)
Dan haka naji a raina zan iya fuskarta abinda yafi haka idan takama na kuka da bakin ciki ne, zan had'iye saboda gidan Aurena. Babbar matsalar da muke fuskanta, shine na ƙarancin zaman lafiya a gidanjenmu sabida munyi imani wani zai iya haifar mana da matsala bayan mun manta cewa a kowace rayuwa akwai mujarabbi, dan haka na dauki mahaukaciyar soyayyar da nakewa Ashraf ta zame min rawa Jarabawar, shi kuma Mahaifiyarshi ta zame mashi jarabawa, domin duk abinda yake min daga Mahaifiyarshi ce, itama kuma ban ga laifinta ba, dan na fahimci halin da take ciki, A duniya kowa yasan Balarabe ana iya kashe shi sabida abu uku, Matar su! Yaran su! Dukiyar su! Sarkin Yasir Alhashmiyya, an kashe shi akan mulki ba mulkin nace tasa aka kashe shi sai dan sun nemi ya sadaukar da Matar shi da kuma Yaranshi, sai ya tafi bayan ya bada mulkin shi kuma ya duge yaki shine suka sukayi ta saranshi har sai da ya mutu. Sarki Abdullahi Alhashmiyya, shima Marhum ya nemi ya bar mishi Nannah yaki, amincewa har ya kai ya fitar da su ta bayan gidan suka kashe su, dan sunyi imanin duk wani sarki baya auren macen da bata da juriya da tsayawa akan gaskiyar ta, sai gashi duk na had'a juriyar da kafiya, uwa uba soyayyar mu, ta gaskiya da take gauraye a cikin zukatansu.
★★★
Zama yayi yana kallona, bs tare da yace komai ba. Kafin yace,
"Ba zaki sunan Matar Dudun bane!?"
Murmushi nayi cikin nutsuwa nace.
"Zani mana! Amma dole sai an bani izinin ko zan tafi babu izinine!"
Kauda kanshi yayi sannan yace.
"Kwana nawa zaki yi "
Cikin son jan hirar nace.
"A ranar ma idan kace na dawo zan dawo."
Kallona yayi a kaikaice sannan ya maida hankalin sa kan tv falon kafin yace.
"Me kika fuskanta a zamanmu na kwanan nan!?"
Murmushi nayi sannan nace.
"Me kuwa na fuskanta bayan kana jin mulkin ka, sai yan damuwar da baza a rasa ba, kuma kaga Ni ina fama da cikina! Bazan aro damuwar wani na kara da nawa bazan indai ba son nake zuciyata ta buga ba, dan kasan yanzun ina fama da......
✋🏽✋🏽 Assalamu alaikum
(Yana da kyau da Muhimmanci mu nunawa Yaran mu, Darajarmu ta iyayensun Mata har da Mazan ma! Dan nayi Imani duk cikin ku babu wacce zata so ace wancar yarinyar Y'arta ce, don Allah mu nunawa Namu yaran mu iyayensu mata muna da daraja da kima! Dan duk Yar da tasan Wahalar daukar ciki da Wahalar Shayarwa toh bazata tab'a zagin Uwa ba, Toh Allah ya shirya mana yaranmu baki d'aya ya bamu ikon sanin meke cikin rayuwar su, dan matuƙar mace tayi irin wancan shirmen, kamar Yadda wasu suka ce wai Yar tasha ce toh Tabbas ta fad'a d'imuwar Rayuwa, dan abinda kayi a kuruciyar ka itace Tsufarka, kuma duk rayuwar da babu, Tarbiyya toh akwai nakasu a cikin sa, Ya Allah Ka shiryar mana da zuri'anmu baki daya don Allah Auntys Mummys, ku kula da kanena Yan matan nan kar asamu wasu daga cikin b'ata garin Kawayen masu halin banza su b'ata mana su🙏🏽🙏🏽)
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah....
2️⃣7️⃣
"Kuma naga abin naku na dangine, kaga aba ni da ikon shiga hurumin kowa gwara na tsaya a matsayina na baiwarka"
Hannunshi ya tura cikin rigana, yana shafo cikina. Lumshe idanuna nayi sannan na buɗe akanshi.
"Me yasa baki damu da halin da nake ciki mu, don Allah ki saka ido sosai akan abinda yake faruwa."
Yana gama fad'ar haka ya bar Ni zaune a gurin ina tunani, abinda ya gaya min, tabbas akwai abinda ke faruwa wanda Ni ban sani ba, kuma ban tab'a zarginshi ba, dan duk macen arziki bazata tab'a zargin mijin ta ba, dan haƙa bana zargin Ashu dan nayi a manna da son da yake min. Ba zai tab'a cutar dani ba,
Fitowa yayi zai sauka kasa, yaga yadda na zurfaffa tunani, dafani yayi tare da cewa.
"Karki manta da halin da kike ciki karki takura kanki da damuwar wasu."
Tun daga rana na zuba idona sosai, sam bana gane kome tunda ban san abinda ke ransu ba, sai dai rashin fahimtar da na gano a tsakanin Nannah da Natashah.
Abin ya bani mamaki taya haka ya faru ban sani ba, karshe na tattarasu na watsa gefe, sabida yawan tunani akan su ciwon kai yake sani.
Dan haka da na tashi tafiya Abuja daga Ni sai yarana sai Shi, dan ya zame min jela. Duk inda zabi muna tare, har takaici yake bani.
Tunda muka shiga gidan Sunan ake min tsiya Musamman Nana Asma'u, har cewa take.
"Wallahi Ummi tayi farar dabara da ta barki kika koma d'akin mijinki, da wannan babyn a gidanmu za a dame shi, tunda Sultan ya lalata mana ke da rashin ta ido Didih"
Pillown kujera na wurgata mata ta tashi a guje tana min dariya.
Wato Ni dai ban san ya zanyi da Kanena ba, sun ishe Ni da fitina.
Sai dare muka koma gidan Iyayena, na shiga d'akina na fara had'a kayana da zan koma dasu Lagos, ina cikin haka naga kwalbar da ya bani, ranar da ya shigo gidan Dudi. Kallon kwalbar nayi yana wani irin hayaki, ajiye shi nayi a cikin handbag d'ina na, shirya kayan.
Ina gamawa na shiga d'akin Ummina, nan muka baje hira, har sha biyu sannan ta Kore Ni d'akin sa, yana zaune a bakin barandar shi, nazo na wuce shi.
Koda muka kwanta, hakkinshi ya nima. Kuma ban hana shi ba, dan nima kwana biyu ina yawan jin haka sosai, sai da ya sami nutsuwa sannan yace min.
"Ina son Rabuwa da Natashah, amma ban san ya zanyi."
Nutsuwa nayi ina jin abinda yake fad'a min a zahirance shawara yake nima, dan alamu sun nuna min yana cikin damuwa.
"Idan na fahimta, baka son Rabuwa da ita sabida wasu dalilin, Ni a nawa tunanin ka hakura da ita. Sannan idan ka rabu da Natashah, amadadin ka samu sauki a rabuwar ku zai iya zama tashin hankali, sannan zumuncin dake tsakanin iyayen zai lalace, sai abu na gaba wanda dole ka hakura da ita, shine aurena da kai, Yau kana sake Natashah. Duk danginka sai sun tsanani, sannan k'iyayyar danginka zai iya kasara rayuwarmu, ga kuma Nah ya zakayi da ita. Don Allah kayi hakuri ku zauna da ita ka kuma bata hakkinta. Idan kayi haka tabbas zaka sama min zaman lafiya."
Sumbatar goshina yayi tare da gyara min kwanciyata, dake yana jingina da jikin gado, Ni kuma ina tsakanin cinyarsa.
Shafa bayana yayi cikin jin dad'i yace.
"Nagode da Allah yabi ke a matsayin matata jakadiya ta gari, mace me hangen nesa da tunanin gaba."
Kwantar da kaina nayi a kirjinshi ina shakar kamshinsa.
★★★
Jordan...
"Abu Zarri! Ya kamata Ku sanya mutane na ko ina na duniya, su fita niman Sultan Ashraf. Dan na lura Wancan azzalumi ba kyalemu zai ba."
Inji wani daga cikin manyan Fadar Salman bini Abul Bashari,
Ajiyar zuciya Abu Zarri yayi cikin damuwa, sannan ya koma ya zauna. Yana kallon Salman kafin ya had'iye yawu, cikin damuwa yace.
"Babu inda ban tura ba niman shi, har yau ina alakanta kaina da son zuciyata, dan haka muyi hakuri. Lokaci na zuwa da zamu kwaci kanmu, Insha Allah."
"Toh haka zamu bari yana cutar da kowa, talakawa sun fahimci cewa ba Sultan Ashraf bane, dan yanzun basu da yanchin magana basu da ikon magana kome sukayi sai an azabtar dasu, shima Ukshe ance bai da lafiya dan ya kwace komai na shi, Allah ka kawo mana mafita."
Haka suka yita tattaunawa, har wani lokaci sannan suka bar falon.
★★★
Lagos....
Saukowa muke daga jirgin sama nisa shi sai yaran da yake rike dasu, Ni kuma ina rike da handbag d'ina, fuskana a tsuke nake tafiya kamar zan fashe da kuka, kuma ba kome ya had'a mu ba, sai akan abincin da aka kawo mana ina ƙoƙarin daukar meatpie, kawai ya buge min hannuna, ya dauki cake ya ajiye min, tare da b'ata rai. Ni kuma nace bazan ci ba, shine fa nake ta fushi, shi ko a jikinsa sai murmushi yaƙe, muna fita muka same Ghaniyu da Fahad suna jiran mu,
Kallona Ghaniyu yayi yace.
"Ranki shi dad'e lafiya kike fushi!?"
Aikuwa bahaushe yace.
*Me niman kuka aka jefa shi da kashin Auwal*
Kawai na b'are baki sai kuka,(🤣😂😎🙄😏 saura wata tace hmm Yo haka nake nifa bana rena abin kuka musamman kukan banza✋🏽🤫🤭🤔)
Aikuwa me Ashu zai banda dariya ya d'auka da wasa nake, sai da