Showing 78001 words to 81000 words out of 108344 words

Chapter 27 - Masarautar jordan Book 2 Complete Document by oum Mufeeda.txt

★★★


Mun fara biyawa ta Ehtophia ne, a babban birnin su Adis Ababa, sannan muka kuma ɗaukar hanya, sai jordan.


Mun isa da karfe daya na rana, sai jaraba layin shi nake ban samu ba.


Wasu mutane naga sunata kallona, wani ya dauki wayar shi ya duba sannan ya kare min kallo.
Can ina cikin jaraba layin shi, sai ga wasu mutane, sun zo kallo d'aya na musu zuciyata ta kusan bugawa.


"Kinzo gurin Sultan Ashraf ne!?"

"Eh! Shi ya aikoku!?"
Gyad'a min kai sukayi sannan d'aya ya ɗauki jakata, d'aya ya amshi Ablah.

★★★
Jikinshi ne yake ji wani iri, kamar wanda yake tare da ita, kallon Ghaniyu yayi cikin nutsuwa sannan yace.
"Jikina na bani, SAFINAH ta shigo Jordan kuma"


Bai kai karshen maganar ba wayar Ghaniyu tayi kara. Ɗauka yayi aka ce mishi.
"Ka bashi"
Mikawa Ashraf wayar yayi sannan aka ce.
"Ka mik'a kanka, ko kuma matar da Yar Me suna Ablah, a same gawarsu."


Kirjinshi ne yayi masa nauyi kamar wanda aka daurawa dutse akai idanun shi sukayi wani irin Jaa a hankali kwalla suka shiga tsatsafowa daga cikin idanunshi bakin ciki da takaici yasa shi sake murmushin dole yace.
"Ku tamb........
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah


3️⃣4️⃣


"Ehtoh ta gaya maka gaskiya, Ni na jima da rabuwa da ita, sannan bani da wata alaƙa da ita, hmm toh bayan haka duk abinda kuka gadama ku mata."


Yana gama fad'ar ya datse kiran tare da kashe wayar baki d'aya ya kalli su Ghaniyu.


"Fahad! Ka kira Sandia! Ka bata Passport d'inta, yau tabar jordan. Ta gama aikinta, Amma tasan yadda zata fito mana da katin gayyata, dan Yau Insha Allah zan fara aikina."


Ganin yadda bai damu da halin da SAFINAH ke ciki bane yasa Ghaniyu yayi mishi magana, yace.
"Sultan! Kamanta jaririyar."


Har ya isa bakin kofa ya tsaya cak, sannan yace.
"Domin samun Farin ciki wasu, dole ka sadaukar da taka farin cikin, dan haka idan ya kuma kira kace ya kashe su."


"Sultan,!!"
Suka ambaci sunansa da karfi, ko a jikin shi, yayi tafiyar shi ya barsu da mamaki.
Yana shiga d'akin ya zub'e a gado, zugi yake ji a ranshi. Shi kad'ai yasan yadda yake ji, domin kuwa ji yaƙe kamar ana hura min shi wuta a ranshi.


Duk kewarta da yake sai da yaji tafita kanshi dukda, yasan dole sai ta shigo cikin wasan amma tayi mishi shiga sauri, bai so haka ba. Yaso shi da kanshi zai dauko ta.

Jin muryan Sandia a gidan yashi mik'ewa da sauri ya fita.


Yana fitowa ya buɗe mata hannu, da gudu ta shiga tana dariya.
"Alhamdulillah! Sultan komai ya tafi yadda ka shirya min, kuma ya baki katin gayyatar, sai dai don Allah kar a cutar da shi, dan bayan umman shi nice mutum na biyu da ya yarda da ita, idan aka cutar dashi zai zama bashi da wanda ya yarda dashi."


"Sandia!"
Fahad ya daka mata tsawa, cikin Kishi. Juyawa tayi tare da isa gare shi. Tana murmushi sannan tace.
"Fahad! Tabbas nice nake sonka! Amma ko sau d'aya baka tab'a bud'e min zuciyarka ba, ka gashi kuwa daga gani na, ya bud'e min zuciyarshi. Kasan me yasa saboda shi yake sona, kai kuma nice nake sonka. Namijin da zai gaya maka gaskiyar shi, ba tare da yayi tunanin waye kai ba shine abokin rayuwa, duk da nasan Sultan Bilal yana gab da rasa mulkin shi, a shirye nake na karasa rayuwata dashi, don Allah kayi hakuri, bai Fika da komai ba sai da kulawar da ya nuna mine, Nagode sosai, Sultan ga katin bazan je ko ina ba, zan zauna a tare dashi. Har me faru ya faru,"


Kura mata ido Ashraf yayi, cikin damuwa yace.
"Idan kuma aka kashe shi fa"


A sanyayye ta isa gaban shi, cikin tsantsar kaskantar da kai tace.
"Sultan d'in mu! Mutumin kirki ne me rama Alkhairi a bayan sharri, mutum ne da yasan darajar soyayya, sannan masani ne. Akan hakkin al'ummar shi, idan ya kyaleshi yayi tafiyar shi har abada Sultan Bilal ba zai daina d'aga darajar shi ba, ko halin da ake ciki wasu ne suke kaiwa da komowa, da kuma rashin abokiyar hira, shawara da abokiyar rayuwa, ya taso bai san kowa ba, sai Mahaifiyarshi, dole yayi rayuwa irinta wanda bai san meye yake ba, idan Sultan bai manta ba shima yayi dogon rayuwa babu iyayen! Afuwa."


Daga haka ta juya tare da barin gidan, sai a lokacin ta samu kwalla ya zubo mata, tabbas ta fad'a son Bilal ba tare da ta ankara ba, tayi dana sanin zuwa wannan aikin, koda ta isa gida zama tayi a d'akinta tayi, ta fashe da kuka, sai da tayi me isarta sannan ta tashiga wanka dan yau Masarautar zasu yi bikin zagayowar ranar haihuwa Bilal d'in.
★★★
Watsa min ruwan sanyi suka yi wanda ya sani sake ajiyar zuciya, me mugun ƙarfi, a hankali na fara tuno abinda ya faru.


Bayan mun fita daga tashar jirgin saman, abinda na sani, na shiga motar da aka kawo, daga nan ban kuma sanin abinda ya faru ba, sai yanzun.


Kallon kartin dake kaina nayi cikin tsoro tare da fargaban abinda zai iya faruwa ba dan yadda na gansu suna muzurai da ido nayi imani cinye Ni zasu.


Ƙarar bud'e kofa muka ji, na d'ago kaina. Turo keken akayi suka shigo su biyu.

Had'iye yawun tsoro nayi, cikin tashin hankali, sunkuyar da kaina nayi sabida irin kallon da Ukshe ke min ta k'iyayya ce, da tsana.
Cikowa kwalla sukayi ban san zan fad'a cikin wannan tashin hankalin ba da ban zo ba, gashi na kawo kaina cikin tashin hankali da Bala'i, kuka ne ya kwace min, kauuuuu naji kunne da gefen fuskana sun daina aiki na hucin gadi. Sake kifa min wani marin suka yi na fad'i daga kujeran, Ukshe ya ce.


"Bilal! Kasata tayi magana, dan wancan mara mutuncin ba bayyana zai yi ta dad'i ba."


D'ago ni Bilal yasa aka yi, sannan ya koma inda Ablah keta sharar barci, ya d'auketa. Kyau tayi mishi cikin kaya dark purple.


Duk na firgita da juya yarinyar da yaƙe.
"Ku kira min shi."
Har suka kira shi da abinda suka yi da shi ina jinsi, kuka nake sosai dan nasan na kad'e har buzuna.


Mika musu yarinyar yayi sannan ya dawo gaba na ya zauna.
"Kin daiji da kunnenki! Yace kun jima da rabuwa, shin da gaske ne."


Kallonshi nayi idanuna cike da kwalla nace.
"Eh!"
Nayi haka ne dan kare kimarta shi, dan ba dad'i na karyata shi.


"Yana gana kana mata sanya ne!?"


Ukshe ya tambayi Bilal, d'aga mishi hannu yayi, sannan yace.
"Ku shigo min da dr Fu'ad"


Can ya shigo, ya kalleni sannan ya min allura, tattara kayan shi yayi. Sannan ya yi wa bilal bayani, yana gama mishi bayani ya fita.


Bayan wasu mintina, marin fuskana Bilal yayi sannan.
"Meye alakar dake tsakanin ku da Ashraf!?"
A buge na d'ago kaina, dakyar nace.
"Mijina!?"


Shiru duk wajen ya dauka, sake Mari na yayi sannan yace.
"Kafin aure kun tab'a wani mu'amala!?"


Girgiza kai nayi, sannan na fara magana.
"Shekarun baya mun sami Y'ar matsala, a lokacin yana fama da lalurar hauka."
Nan na gaya mishi yadda komai ya faru, sannan na cigaba da cewa.
"Lokacin da Alhaji Nuhu yazo zai aureni, Ni kuma bana son shi, shine Ashraf ya bani shawarar na zo gurin shi, a d'aura mana aure, Ghaniyu ya wakilci shi, Ni kuma Imam d'in masallacin ya wakilci iyayena, kuma aka d'aura auren dan haka bana tunani, Ashraf zai aikata mugu..."
Daga nan dai na dauke wuta, na shiga barcin bugawa.

"Bilal"


. " Toh tunda yace basa tare mu kashe su mana."


Wani irin kallon Bilal yayi mishi, sannan ya mike tare da barin, d'akin har ya isa bakin kofa.
"Kar wani abu yasame uwar da yar."


"Toh."


Sai da Ukshe ya tabbatar da yaji karar motar Bilal sannan ya, yace.
"Ku saka ruwan kankara ku zuba mata har sai ta farka, sannan Yarinyar kuma, itama a tsomata cikin ruwan"


"Toh"
Suka amsa mishi sannan ya fita shima, sannan suka shiga aikinsu, akan jaririyar ce suka kasa yin komai, sai tausayinta ya kama su, Ni kuma suka shiga cin Ubana. Ƙamar Allah ya aiko su.


★★★
Jiki a mace Sandia take shiryawata, kayan da Bilal ya bata ne, mermaid gown tasaka kalar golder, sai Whiter gold wanda akayi mix d'inshi da diamon, light makeup tayi sannan ta fito daga gidan su, ta samu motar da zata kaita masarautar tazo, a hankali take tafiya har ta isa gurin motar Bud'e mata drvn yayi ta shiga ta zauna, rike pouse ɗinta tayi, tana kallon gefen titin. Tare da jin ba dad'i, sai dai bata ji zata iya barin Bilal a wannan lokacin, kuma tasan bata da ikon dakatar dashi, da zata iya dakatar dashi.


Har suka isa tana zance zuci, a hankali take takawa, kamar wata d'awisu, har ta isa gurin da ake taron. Daga nesa ta hango Bilal. Tare da manyan mutane,


★★★
Lokacin da Ukshe ya fito aka sanyashi a mota, ya shiga ya zauna, sannan suka nufi hanyar da zai zai kasu masarautar, tsayawa sukayi a Traffic jam, kafin su bar gurin, akayi yar hayaniya, bai damu ba ya cigaba da kallon jaridar hannunshi.


Sai da yaga tafiyar taki ci taki cinyewa, ya d'ago zai magana, ya ga suna shirin barin garin baki d'aya cikin fad'a yace.
"Waye ne"
Ba a kula shi ba, ya sake magana. Yaji shiru lek'awa yayi, idanunshi ya sauka a fuskar


★★★
Masifa take sosai tare da cewa.
"Gobe zaki bar shashin nan, wannan haukar har ina, kin zo kin zuba min ruwan lemo a kayana." Inji Malika.
Ji tayi an bude kofar ban d'akin, d'ago za tayi magana, aka rufe fuskarta da wani hanky dole barci yayi gaba da ita.


★★★
Lokacin nata tafiya babu Ukshe babu Ummanshi dan haka yasa aka shiga nimansu, magana na gaskiya babu su babu labarinsu, Abin nufi an sace su kenan. Kutt lokacin guda aka hana kowacce mota fita daga gidan, aka shiga nimansu lungu da sako na gidan.


Wayar Bilal ce tayi kara, bai cikin nutsuwa amma dole ya bud'e.....
Kome zai gani 😎🤨 dole ku kira Next page
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah


3️⃣5️⃣


*Ya kaga wasan!? Ya tafi yadda ka tsara ko asake buga wani! Ni ban damu da Uwar da Y'ar ba, sabida hankalina baya tare dasu, kawai abinda na sani harina yana kan Mahaifiyarka da na hannun damar Kabila*


Bai damu da ya duba sakon ba, kawai yana tsaye sai masifa yake wa Masu kula da tsaron gidan.
"Taya kuna zauna za a zo a sace mutane ba tare da kun duba shiga da fitar mutane ba! Wallahi idan wani abu ya same mahaifiyata sai na saka an datse muku kai."


Sake turo mishi sako akayi.
*Kai! Bar samun mutane da haushi, Mahaifiyarka tana hannuna amma kafin nan ka fara duba email dinka da kuma Whatsp d'inka tayu abin ya bada citta*


Sam bai saka ranshi ya duba sakon ba, dan haka bai tunanin sakon me muhimmanci ne ba, ya dai cigaba da bala'iron shi, tare da alkawarin sauke kawunan kowa, indai Babar shi.


Kira ne ya shigo wayar cikin masifa ya d'aga, yace.
"Hey! Sarkin jordan easy! Ba dai Mamankar kake nima ba tana Hannuna ita da Ukshe, yanzun ka duba wayar ka, zaka ga video ya had'u da"


"Kaiii" ya fad'a da karfi,


"Shhhhhi! Karka d'aga min murya dan Ni nafika hauka, kana son Mahaifiyarka a raye kuwa!? Indai kuwa haka ne toh kuwa baka san yadda ake kula da ita ba, domin na d'auki video na turo maka."


"Kai banza me garkuwa da mace me rauni."

"Hhhh! Ai Ni renonki ne, ƙaramin tantiri, Ni ba fad'a nake so ba, dan maganar da muke ciwon kai yake sani, ka ajiye mulkin da kake kai Ni kuma zan sake maka Mahaifiyarka."


"Wallahi sai na kashe matar da Y'ar!"
Dariya sosai Ashu yayi sannan, yace.
"Ji banza kashe su."

"Ba iya kashe su zanyi ba, zan gwada rigarka, naga yadda yake. Ko shi ma na gwada."


Dariyar renin hankalin ya saka mishi, Sannan yace.
"Ka gwada mana! Idan ya dame ni, sai dai ina maka albashir da a Bud'e jakar dake kofar shiga masarautar."


Kashe kiran yayi, Bilal kamar mahaukaci haka ya koma, sai ihu yake, da gudu ya nufi baƙin kofar fita a masarautar, yana zuwa ya hango jakar kasa isa gurin yayi yasa aka dauko jakar, ganin yadda jini ke sauka a jikin jakar, yasashi niman zub'ewa kasar, sai da aka tare shi, kauda kanshi yayi cikin mugun tashin hankalin yace.
"Ku bud'e jakar!"
Kirjinshi ban da dokawa babu abinda yake, dan ji yaƙe duk wani takun masu bud'e jakar ji yaƙe suna tafiya da zuciyarshi, lokacin da suka isa kuwa cikin hanzari yace.
"Ku dakata"


Cak suka tsaya duk suka juya suna kallon shi, kara wayar shi yayi yaga sakone.
"Haba! Mazaje wannan ba girmanka bane, kasa abu mana har ka karaya da wuri haka, ka ajiye komai muyi magana."


Cikin girman kai ya fad'a da karfi.
"Wallahi baka isa ba, ku bud'e min jakar"
K'in kallon jakar yayi tsabar tsoron abinda idanun zai gani yaki kallon jakar, suna cikin bud'ewa, Ashraf ya kira. Kamar bazai dauka ba, ya dauka a masifance.


"Kai idan na kama ka, sai na shayar da kasa jinin ka"


"Ni kuma na maka Alkawarin idan ka kamani zan tsaya ka shayar da jinina ga kasa."


Cikin wani irin izza Ashraf ya mai da mishi maganar,
Shima Bilal cike da alfahari yace.
"Lallai sai na wulakantaka"


Dariya Ashraf yayi sannan yace.
"Idan ka kamani nima Zanyi alfahari da haka, idan ka isa ka kamani."

"Tabbas sai na gigita rayuwarka" inji Bilal,


"Bazaka iya ba."


"Matar ka zata gaya maka"


" Wannan kuma matsalar kace."
Kashe kiran yayi sannan ya karbi key mota da gudu ya fita, daga masarautar.


Kiranshi Ashraf yayi ya dauka tare da cewa.
"Kana wasa da rayuwarka"
Inji bilal,


"Ai Ni da haka na taso, amma ina tayaka da murna ai da ka tsaya kaga meye a cikin jakar ai zaka gidan da kuka ajiye ta ko, toh ai ba damuwa don Allah ka kara gudu."


"Wai kai waye ya tsaya maka!?"
"Akwai wani ne Bayan Allah! Aini bana komai sai na nemi dacewa, kuma shi ya tsaya min shi yasa na zuba maka ido ka gama tsuma tsiyarka kai da wancan na keken guragun! Nima yanzun lokacina ne, kuma sai na tsuma tsiyar da tadama taka, sai na keta alfarmarka, sai nasaka ka bukaci mutuwa da rayuwa. Kamar yadda kuka tab'a ni sai na hanaka sukuni mu buga wasa nan da sati d'aya mugayen waye zai tashi da sifili."


Kashe kiran Ashraf yayi Bilal sai hucci yake yana isa gidan yasamu masu kula da gidan duk sun kwance kamar an bugar dasu.


Yana shiga d'akin da SAFINAH take yasamu bata nan sai jini, da ya b'ata cikin d'akin shima sabida yaga gawan mutanen su har su biyar, an musu kisar wulakancin.


Zub'ewa kasar yayi tare da fasa ihu, idanunshi sun kad'a jajjur.

Damke gashin kanshi yayi tare da lumshe idanunshi, da ƙarfi.
★★★
Da sauri Fahad ya watsar da kayan kan table d'in aka daura jaririyar da bana tsammani tana raye, Ni kuma ya wucce dani d'akin shi, ya kwantar dani, sannan ya dawo kan Yarinyar, dan Dr Fu'ad ya dukufa ceto rayuwarta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login