Showing 9001 words to 12000 words out of 96302 words

Chapter 4 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt

ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce
"Aziza zo mu bar nan wajan"




Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce
"Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu"


"Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun"


Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin
"Aziza! Ke Aziza!? Azi..." Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!.


Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima.


"AZIMAAAAA!" sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba
"MACIJIYA AZIZA LAFIYA!" Azima ta fada cikin halin ko in kula.


"AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?"


kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce
"Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda...." dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme.




🍃🍃🍃🍃


WAI YAU MACIZAI NA FAƊA,NAYI NAN🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


A lallaba chaji wala🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


COMMENTS AN SHARE


BY MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


🍃🍃🍃🍃🍃


🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️
*WANNAN DUƘAWAR NAKI NE SISINA, DAN ALLAH KIYI HAKURI KI HUCE KINJI🙇🏻‍♀️😟 KAR AYI MANA DARIYA, ALLAH YA HUCI ZUCIYARKI🥰 AMEENATUNA SLIMZY BABY🥰 MATAR MIJINTA🥰*




*FREE..*
🅿️==1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣




Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama'ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar'ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa.






@@@@@




Bayan kwana biyu an gama ƙuri'u, inda aka samu sab'anin ra'ayi, jama'ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja'i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja'i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja'i aike da shi.


🍃🍃🍃🍃🍃


Sarkin fulanin yankin ja'i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin
"Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce" wazirin fulani ya ce
"Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?" murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce
"Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala'i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama ce na sun duƙawa wannan yanki tamu"





Sarkin fulanin yankin ja'i ya ce
"Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon"


Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka.




" _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA'I, MUNA FATAN WANNAN SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA'I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA'I WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI ZUWA GA YANKIN JAMA'AR DA SUKE JA'I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN GAMU DA IFTILA'IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA TAIMAKON *INNU MACIJI* MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_"




Wani murmushi sarkin fulanin ja'i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama'ar ja'i suka hau murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja'i ya ce
"Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama gasheshshe!"


Wazirin ja'i ya ce
"Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa" wazirin fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja'i ya kuma cewa
"Ranka ya daɗe kar mu b'ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu" girgiza kai garkuwan fulanin ja'i ya hau yi ya ce
"Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!" garkuwan fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce
"Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato *INNU MACIJI* wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja'i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?"


Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja'i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce
"Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab'ob'in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja'i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, *GWARZON DAFIN MACIZAI!!* ka tuna?" Garkuwan fulanin ja'i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja'i ya ce
"A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja'i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce" Maga Isar da sako ya ce
"Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan"


"Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?"


Maga Isar da sako ya ce
"Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba" Sarki Jawo ya ce "tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka" Sarkin fulanin Ja'i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.








🍃🍃🍃🍃


*YANKIN KWANA*


Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja'i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce
"Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana" mai Unguwa Ori ya ce
"Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja'i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba" Arɗo ya girgiza kai ya ce
"Maganar duniya bata b'uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta'aziyyar jarman macizai"


Sarki Chubaɗo ya ce
"Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce" Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce
"Bana tunanin yankin ja'i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan! Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma mu san ta inda zamu shawota"
Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja'i.






Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-kasa,Arɗo ya ce
"Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?"


"E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza, gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci" Arɗo ya gya ɗa kai ya ce
"Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka" Baffa yace
"Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida"
"To a gaida Jumala da Azima da Aziza"
"Zasu ji" Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama.




🍃🍃🍃🍃




Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la'asar tana zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce
"Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar azahar bare la'asar ki tashi kiyi sallah" ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce
"BANA SALLAH!" 😏
Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce
"Kina fashin sallah ne?" kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce
"Sannu da gida Hajja"
"Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?"
"E Hajja na dawo"
"Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba" murmushi Aziza ta yi a ranta ta ce
"Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena" a fili kuma ta ce
"Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai"
"Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?"
"Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba" Hajja ta kalli Azima ta ce
"Azima kince baki sallah kina fashi ne?" da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce
"Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!" dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b'ata shuru tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin
"Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin haka faɗi kawai take yi" sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah kam Azima baya yi, ta ce
"Hajja ba a gama abinci ba?"
"Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har yanzu ta ƙi nuna" shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce
"To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa"
"A'a Aziza yanzu fa kika dawo daga...."
"Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta" murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce
"Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?"




🍃🍃🍃🍃


COMMENTS AND SHARE


BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login