Showing 42001 words to 45000 words out of 96302 words
Chapter 15 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt
ganin wannan ɗanya ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!" sai sambatu yakeyi a zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin
"Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai" cije baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce
"Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara kalla a rayuwarka"
"E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi" ya fadi yana shirin kai hannunsa kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin
"Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?"
"E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai"
"To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!" ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace
"Dama kafin na tafi ina nemanki!" tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar gidan.
🍃🍃🍃🍃🍃
Kuka Hajja keyi yayinda Inna Wuro da Yawuro suke ta aikin bata hakuri suna rarrashinta,amma pinaa Hajja kamar ba da ita ake yi ba, idonta ya kumba ya yi him sabida kuka fuskarta ya yi jaa! Baffa ne ya duka a gabanta ya ce
"Jumala? Kiyi hakuri,In sha Allah idan anyi duniya DAN MANZON ALLAH S,A,W, Azima da Aziza zasu dawo garemu In sha Allah,kuma yaranki zasu dawo mutane ko da kuwa zan rasa raina na miki alkawari!" ita dai Hajja bata ce komai ba, tun daga wannan rana Hajja bata um bata um-um, idan ta zauna idonta na kan bakin kofa,ta ajiye idanunta har izuwa ranar da yaranta zasu dawo gareta.
🍃🍃🍃🍃
Fitan Azima yawatawa ta ci gaba da yi,dama ita ba sallah take yi ba balle ya dameta, idan kuma wani mai kararren kwana tsautsayi tasa ya shiga hidimarta ta kashesa ta yi gaba, yau kwananta uku da shigowa garin kano bata damuwa da wajan kwana idan dare ya yi duk babbar bishiyar da ya mata zata zama macijiya ta hau ta kwanta tayi bacci ko ta huta, yau ta fito tana cikin tafiya taji ƙaran mota ƙiiiiiii! da sauri ta juyo ta ga wata matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekara ashirin da biyar,fitowa tayi tana zazzagawa Azima zagi, yayinda take binta da ƙaramin kallo
"Ban da hauka taya zaki rufe fuska ki dinga tafiya a kan titi! Sakarya kawai bagidajiya!!" cije baki Azima tayi meyasa ake son ce mata bagidajiya? duk da bata san ma'anar kalman ba amma taji ta tsani kalman, lankwabe murya ta yi ta ce
"Dan Allah ki taimaka mini, ni yar gudun hijira ce an kashe dukkan yan uwana a rigarmu ni daya ce kawai na rage,ban san kowa ba ban san inda zanje ba, dan Allah ko aiki ne a gidanku ki nema mini zan dinga yi" yatsine fuska ta yi tana fadin
"Kuma fa kamar naji Hajiya na neman mai aiki,to amma gaskiya sai dai na sakaki a cikin both dina dan ba zaki shiga mini mota ba"
"Ina ne shi hakan bat din?"
"Banza jahila both nace, nan kenan zo ki shiga" ta fada tana mata nuni da both tana budewa,Azima ta shige tana murmushi tare da fadin
"Matakin farko!" tana rufe murfin both din Azima ta koma Macijiya, shiga motar tayi ta ja tana tsaki.
A kwana ukun nan Aziza ta fito daga bakin titi ita ma,tana fitowa ta zube a kan titi tana sakin kuka tana kiran sunan Hajjanta da Baffanta, Inno Fandi ce ta taimaka mata ta fiddota bakin titi sannan ita ta koma, kuka sosai Aziza ta yi kafin ta tashi ta hau tafiya, tana ganin kamar ta shigo wani sabuwar duniya ne, bata ma san a inda take tafiya ba, shi kuwa da sauri yake jan mota,yana driving yana duba tym, wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Friend 4 Life, dagawa ya yi, ya ɗan yi shuru tukunna kafin ya ce
"Hey Dude bazan maka karya ba,wlh bazan je na dubasa ba,guy din nan ya raina min hankali, jiya banyi niyyar kwana a garin yola ba amma ya sakani kwana, yanzu haka ma nikam gani a hanya ko kwana zanyi sai dai na kwana amma yau din nan sai na kasance a cikin garin Kd in sha Allahu!" yana magana a waya ransa a b'ace sai ji ya yi, ya yi sama da mutum, wani mahaukacin burki yaja ya fito da gudu, yana isowa gareta tana lumshe ido, duk da bai ga fuskarta da kyau ba gashi ya rufe amma daga ganinta a jeji ta fito, kallon gabas ya yi,ya kalli kudu,ya kalli arewa,ya kalli yamma bai ga wani ɗan adam ba, shi a tunaninsa sun fito kiwo ne yan uwanta suka tafi suka barta, to amma idan haka ne shi ya zaiyi da ita? Ga kanta ya fashe yana zubda jini, "No dogon tunani ba nawa bane i need to save her lyf first" ya faɗa yasa hannu yana shirin daukarta, wani mummunar faduwar gaba ce ta riskesa inda yaji dukkan wata gab'a ta gangar jikinsa ya sake, saurin kauda abun a ransa ya yi ya dauketa ya sakata a mota ganin bata motsa, yana addua Allah yasa dai bata mutu ba.
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️==3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣
Murmushi ya mata ta zo ta rungumesa tana yi masa sannu da hanya, ya amsa da "yawwa sannunki,ina Mom kar dai har tayi bacci?"
"Kai anya kuwa, da muna zaune da ita a nan bata jima da tashi ta hau sama ba"
"Okay bari na dubata" ya faɗa yana maida dubansa ga tv'n ya ce
"Ke da kallon horror ko, sai kin fara ganinsu a gaske zaki sani" murmushi Sultana ta yi ta koma tana zama shi kuwa ya hau sama,dakin Mom ya shiga da sallama tana zaune tana waya, zama ya yi kusa da kafarta har sai da ta gama wayar ta ajiye kafin ta kallesa cikin kulawa ta ce
"Nawaz sai yanzu? Ya hanya an dawo lafiya?"
"E wlh Mom, Alhamdulillah! ina wuni? Ya gida? na sameku lafiya?"
"Alhamdulillahi Doctor, fatan dai lafiya ko? Ko dai gajiya ce dan fuskarka ta tuna,yanzu haka ma da Amminka muka gama waya wai ta kiraka wayar bata shiga nace ba mamaki hanya ce ba netwrk"
"E hakane zan kirata gobe yanzu dare yayi zan shiga part dina,kunyi waya da Son dinki ne Mom?"
"E dazu ya kirani dan albarka"
"Mom muna cikin waya da shi dazu tsautsayi tasa na buge bafulatanan yarinyar mutane"
"Subhanallahi!" Mom ta faɗa tana zabura
"Kwantar da hankalinki Mom tana hospital dina" nan ya bata labarin yadda hatsarin ya kasance har izuwa shawaran da ya yanke na tahowa da ita kaduna idan taji sauki sai a maidata gida, Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Shawaran da ka yanke mai kyau ne Nawaz, Allah ya bata lafiya, ma je mu dubata gobe idan Allah ya kaimu ni da Sultana"
"Allah ya kaimu Mom" ya faɗa yana duba agogon hannunsa
"Dare yayi Mom zanje na kwanta na huta akwai gajiya a tare dani"
"To Allah ya tashemu lafiya a huta gajiya,Allah ya yi albarka" Nawaz ya amsa da amin yana tashi ya fice a dakin, yana saukowa ya kalli Sultana ya ce
"Idan baki kashe tv'n nan kinje ki kwanta ba Allah sai na zaneki" da sauri Sultana ta miƙe ta kashe tv'n kasancewar tasan halin Yayan nata, sai da ya ga ta hau sama kafin ya fice ya nufi part dinsa, wanka ya yi ya gabatar da salloli har da nafila ya jima yana addua kafin ya tashi ya koma gado ya kwanta,har ya lumshe ido ya buɗe ya dauki wayarsa ya kira Amininsa suka hau ɗan taba hira inda yake ba shi labari ya buge bafulatana, Allah ya kiyaye gaba ya masa,sannan ya ce
"Yaushe zaka dawo america?" Nawaz ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Nan da 2wks In sha Allahu,but idan nazo ina shekarar karshe zamuyi mu dawo gida gabadaya?,dan gaskiya na gaji da zaman outside"
Daga can bangaren ya ce
"In sha Allahu, duk da ni bana son zaman nigeria gaskiya"
"To ya zaka yi dole ka dawo,duk lalacewa kasarka kasarka ne, sannan karka damu da abinda Momma take maka, ka ci gaba da yi mata biyayya a matsayin uwa,wata rana zata gane In sha Allah" ajiyar zuciya ya sauke, nan Nawaz ya gane damuwar dake damunsa dan haka ya kau da hiran ya jawo musu wata, sun kai biyun dare kafin suka yiwa junansu sallama, yana ajiye wayar bai jima ba bacci ya kwashesa,yana cikin bacci ya hau mafarkin yarinyar da ya buge da mota, suna cikin wani ƙasurgumin jeji sai faman ihun take zabgawa tana fadin ya taimaketa ya taimaki rayuwarta, tana ihu tana gudu yana binta a baya, da haka har suka je jikin wata babbar bishiya taja ta tsaya kanta a sunkuye tana sanye da kayan fulaninta,ta ƙanƙame jikinta tana ihu, shi kuwa yana riƙe da fitila a hannunsa yana haskawa sabida tsananin duhun jejin, yana shirin matsowa gareta ya ga mummunar tashin hankali dan kuwa gani ya yi ta koma wata zabgegiyar macijiya🐍 fara sol sai ƙyalli take yi,tana ci gaba da ihun ya taimaketa.
A mugun gigice Nawaz ya farka yana fadin
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!³" hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin ya rike kansa da karfi dan ji yakeyi kamar kan na shi zai faɗo kasa, gabadaya jikinsa ya jiƙe da gumi, yayinda ko wani kofar gashi ta gangar jikinsa ya buɗe sun miƙe tsaye, jijiyoyin wuyansa duk sunyi waje, jikinsa sai b'ari yake yi har yana jin wani zazzabi, da kyar ya jawo wayarsa ya duba tym ya ga karfe biyar, tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah, yana nan zaune yana addua har aka kira sallah, sai da yayi raka'atul fajir sannan ya miƙe da kyar ya fita zuwa masallacin da yake wajen gate ɗin gidansu, bayan an idar da sallah ya shiga ya gaida Mom bai wani zauna ba yace mata kansa na ciwo zai sha magani ya kwanta dan bai samu bacci daren jiya ba, Allah ya kara sauki Mom ta masa ya koma part dinsa ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake kwasansa amma still mafarkin daren jiya shine ya kara tayar da shi, cikin kiɗima ya zauna a bakin gado yana tunani barkatai.
"To miye haɗina da wannan yarinyar? daga haɗuwa da ita jiya shikenan sai na kasa bacci? ni da ko fuskarta ban gani da kyau ba gashin kanta ya rufe! sannan me hakan yake nufi nake ganinta a macijiya!? ko dai ba mutum ba ce? kai inaa a'a ko dai wani abu ya sameta ne a asibitin?" sauri tashi ya yi ya dauki jallabiyarsa yana kiran nurse's din da ya basu kula da ita,amma babu wacce ta daga a cikin su biyun, tym ya duba ya ga 7:30 da sauri ya zare car'key dinsa ya fice ya bar gidan ya nufi asibitinsa mai suna *ALWAZ HOSPITAL KADUNA.*
Yana isa ko parking bai gama ba ya shiga ciki da sauri,yana shiga reception ya samu nurses ɗin suna bacci, a tsawance ya tayar dasu nan ya hau su da faɗa a kan basu san aikinsu ba, hakuri suka hau ba shi amma bai tsaya ya sauraresu ba illa dakin da Aziza ke kwance,kamar yadda ya barta jiya haka ya sameta tana bacci gashinta ya rufe mata fuska,yana ganin lafiyarta ya saki ajiyar zuciya wanda bai san dalilin hakan ba bai ma san lokacin da ya saki ba, dubata ya sake yi ya ga zata iya farkawa ko da wani lokaci, hannu yasa da niyyar kwashe gashin fuskarta a fili ya ce
"Wai meke damuna ne kam? Mtsww!" ya ɗan ja gajerar tsaki yana fita a dakin, gida ya koma dan kansa ke masa ciwo sosai,magani ya sha cikin ikon Allah bacci ya kwashesa bai farka ba sai daya saura,yana tashi ana kiran sallar azahar, bai tsaya bata lokaci ba ya yi alwala ya tafi masallaci bayan ya dawo babban parlour ya wuce ya samu Mom da Sultana suna zaune suna hira, gaishe da Mom ya sake yi ta amsa Sultana ta gaishesa ya amsa yana haɗe rai da fadin
"Keee me ya hanaki zuwa skull?"
"Brother yau bani da komai shiyasa ban je ba"
"Kin san dai bana son wasa da karatu ko?"
"E Brother bana wasa da karatu ko Mom?" ta fada a shagwabe tana kallon Mom,Mom ta yi murmushi ta ce
"Ai kai ma kasan yadda Sultana ke son karatu,ya gajiyar hanyan da kuma jikin?"
"Alhamdulillah Mom na warware"
"To Ma sha Allah haka ake so, dama mun gama shiryawa kai muke jira idan ka farka sai mu gaya maka zamu je asibitin duba yarinyar"
"Okay Mom bari nayi wanka sai na kai ku,nima akwai marasa lafiyan da nake son dubawa, gobe kuma zanje abuja akwai aikin da nake da shi"
"Kuma?" cewar Mom,ya ce
"E wlh Mom,ai idan har mun samu sauki sai dai idan mun dawo kasarmu gabadaya,tunda ko kaɗan zuwan nan wan can guy din dan ya raina min wayo ba zuwa yakeyi ba,ya maqale a kasar wasu" murmushi Mom tayi ta ce
"Ka kyalesa mana Nawaz,kasan fa ba jin dadin zama yakeyi dasu Hajiya Lawiza da Hajiya Luba ba, kai mutanan duniya sai Allah wlh,ace kuna zaune karkashin mutum kuna cin albarkacinsa kuna rayuwa da dukiyarsa amma kun tsanesa kuna cin dunduniyarsa,kai Allah shi kyauta" Nawaz ya amsa da amin yana fadin
"Ba ri na shirya nazo na kaiku nima na samu nayi aikin dake gabana a hospital din"
"To a fito lafiya" cewar Mom.
Mintuna sha biyar ya daukesa ya gama shirinsa ya shiga ya yiwa su Mom magana suka fito suka nufi asibiti,ko da sukaje kwatanta musu room din ya yi shi bai shiga ba ya tafi dan akwai cs din da zai yi, su Mom ne suka shiga suka zauna da ita,Sultana tasa hannu ta kwashe mata gashin fuskarta ta ce
"Woww! Allahu Akbar! Ma sha Allah!"
"Menene Sultana?"
"Wlh Mom kyakkyawa da ita, ki ga gashi, wayyo Allah na ni,wlh Mom kamar ba yar nigeria ba" Mom tayi murmushi ta ce
"Baki rabuwa da shiririta Sultana ba bafulatana ba ce"
"Ai wlh Mom ko a fulanin ba kowa ke da kyau ba"
"To anji ki rufe min baki, karki cika marar lafiya da surutu Yayanki ya shigo ya sameki kina zuba zaneki zaiyi kema kin sani" zare ido ta yi tana riƙe bakinta dan tasan sarai zai zanetan sai dai idan bata cika masa ciki ba dan akwai sa da saurin zuciya abu kaɗan ke tunzura shi ransa ya b'aci.
Su na zaune a asibitin sai wajan uku da rabi kafin Aziza ta fara farkawa, farkawartata yazo mata da mugun mafarki Azima ta biyo Baffa da wani zabgegen takwabi tana shirin kashe Baffa bayan sun gama dambatuwa In da Baffa karfinsa ya ƙare ya hau kwalawa Aziza kira ta kawo masa dauki Banju zai kashesa! Ga Hajja a sume a kasa, wani ihu Aziza ta yi dai-dai da lokacin da Nawaz ya sako kafarsa dakin ya zo dubasu ya iske ihunta tana fadin
"BAFFAAAANAAAAA!!! HAJJAAAAA!! KEEEEE!!! AZIMAAAAAA!! KARKI KASHE BAFFAAAA!!" sauri yin kanta suka yi Nawaz ya tallabota kirjinsa ya kalli Sultana yace "maza je ki kirawo min wasu nurses ko Dr duk wanda kika samu su zo yanzu" da gudu Sultana ta fice suka dawo da nurse mutum hudu, nan yace su ba shi allurai, bayan sun miƙa masa ne tana ta faman buge-buge, Mom tana tsaye daga saman kanta tana mata tofi, yana mata alluran ta koma ta yi lamo a kirjinsa tana kan ambatar sunan Baffanta da Hajjanta, kamar da minti biyar abun ya lafa,Mom ta ce
"Nawaz ya dai?"
"Ba komai Mom,nan da 30mins zata farka zata dawo dai-dai In sha Allah" Mom ta ce
"Ka gani ko Nawaz? Gwara da Allah yasa baka barta ba ka taho da ita, Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta" ya amsa da amin yana me leƙa fuskarta ya ga gashi ya rufe,kwantar da ita ya yi ya fice, Sultana ta zauna kusa da ita tana kamo hannunta.