Showing 60001 words to 63000 words out of 96302 words

Chapter 21 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt

idan na mata abu a rashin sanina, haka ma dan Allah ki nema min yafiya a wajan Hamma Nawaz, sannan kema ki yafe mini" Aziza na gama faɗi ta fashe da kuka ta tashi da sauri zata fita,sultana tace
"A yau kin ceci rayuwata, da ace ba dan ke ba, abunda nake yiwa gidan mijina tanadi da yanzu an karbe shi, bani da sauran wani mutunci da kima, da na koma matatta ko da ina raya, a yadda naji labarinki ke abun tausayi ce ba abun gudu ba daga ke har Baffanki da Hajjanki da kuma yar uwarki! Ai ke ba abun a gujeki bane Aziza, dan ke din mai tausayi ce, idan har kin yarda dani kuma kin yarda munyi miki halacci ba ki so ki saka mana da butulci to ki biyoni gobe mu koma kaduna,nayi miki alkawari zan tayaki neman yar uwarki gari ya gari, idan har kin yarda dani fa amma" wani kuka ne ya sub'ucewa Aziza ta ce
"Anty Sulty?" rungumeta Sultana ta yi ba tare da tsoro ko fargaba ba,
"Dama akwai mutane irinku a duniya? Tabbas duk lalacewar mutanen duniya na Annabi basu ƙarewa" cewar Aziza tana kuka, Sultana tana bubbuga bayanta ta ce
"Ni dai ki min alƙawari ba zaki gudu ba,kuma karki kara tunanin guduwa,Mom mutum ce mai zargin kanta a koda wani lokaci zata dinga zargin kanta da bata miki riƙon tsakani da Allah bane shiyasa kika gudu, dan Allah karki saka mata da haka"
"In sha Allah Anty Sulty babu inda zani" daga haka Sultana taja hannun Aziza suka fice a gidan ga dare ya tsaga ana neman gaff kiran sallan assalatu, fitowa bakin titi sukayi, Sultana ta ce
"Muna waya da Khalil yan iska sun bugeni wayar ta faɗi, na san za a nemu kam kuma hankalinsu zai tashi" Aziza ta ce
"Nima takalmina kafa daya ya fadi, yanzu ya za ayi kenan?"
"Kawai ki daukemu mu b'ace muje gida" zare ido Aziza ta yi ta ce
"A'a Anty Sulty,mu nemi wani hanyar dai" suna nan tsaye har aka kira assalatu, Aziza tace mu zauna a nan mu jira har ayi sallar asuba nasan a lokacin motoci zasu fara wucewa sai mu wani wanda zai kai mu gida, tunda bamu sallah ba da sauki ai"
"Yan iska mutanen banza! Da yanzu sai su mana fyaɗe muna period ko?"
"To suna tsoron Allah ne, ai basu tsoron Allah" zama Sultana ta yi a kasa tana fadin
"Ai shikenan" itama Azizan zama ta yi, nan kuwa aka yi asuba kafin motoci suka fara gilmawa da kaɗan-kaɗan har suka tare mai taxi, Sultana ta gaya masa unguwar da zai kaisu ya daukesu.




A gate din gidan mai taxi ya ajiyesu, suna fita suka samu harda yan sanda, mutane ana tsaye cirko-cirko daga ciki kuwa harda amarya da ango, wanda jiya da aka tashi a wajan dinner amadadin ayi gida ai sai hankali ya tashi, kuma ga wayar Sultana da suka samu a gate din da kafar takalmin Aziza guda daya, shiyasa suna gani suka sa a ransu ai kawai an sace su Sultana ne, sai kuma ya haɗe da Khalil da yake ta faman zabgawa wayar Sultana kira dan yaji lokacin da Aziza ta kwala mata kira sadda aka buga mata katako a kai wayar ta fadi kasa,kuma yaji sadda suke cewa a dauko da Aziza, itama aka dinga buga mata katako, sannan sun ga jini a wajan, jinin kan Aziza wanda ya fashe.




Hajiya Habiba mahaifiyar amarya Sulaiha ganinsu yasa ta ta tarosu da kuka tana tambayar lafiyarsu, nan suka tabbatar mata da suna lafiya, aka tambayesu me ya faru,nan Sultana tace daukesu aka yi, yan sanda suka tambayesu waye suka ce basu gane mutanen ba, dan sun rufe fuskarsu,
"Taya aka yi kukayi escaping daga hannunsu?" Sultana ta ce
"Ashe bamu zamu dauka ba, su da kansu suka sakemu, a bakin titi muka kwana kasancewar dare ya tsaga, sai da akayi asuba muka samu mota ya kawo gida"
"Ina dai basu muku komai ba ko" cewar Hajiya Habiba
"E Ammi basu mana komai ba"
"Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya" nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba cewa to jami'an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both, Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce
"Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba"
"Haba Sultana ba dole ba"
"To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan an kwana biyu, a sha amarci lafiya" daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami'an tsaro suka rakasu a baya, har kaduna.




@@@@@@


Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce "MOM!?" da sauri Mom ta juyo tace
"Sultana" rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan ta b'ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?" Mom ce ta shafo fuskarta tace
"Kina lafiya 'yata?"
Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu lafiya, Mom ta kallesu tace
"Bakuyi wanka ba ko?" suka gya ɗa kai
"Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan safe ne" suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta.






Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da Nawaz,sai da suka gama Mom tace
"Kin tashi? Kinyi sallah?"
"A'a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka"
"Yaushe kuka fara?"
"Ranar da muka isa zaria"
"Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi"
"To Mom"
"Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci"
"To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan"
"Lafiya dai ko?"
"Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin" gya ɗa kai Mom tayi ta ce
"Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na'am da abunda yace, dan haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya" shuru Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace
"Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci" ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce
"Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?"
"Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi" Aziza ta ce
"A'a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke kasa daya?" dariya Sultana tayi ta ce
"Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya Nawaz *AL'MAZEEN NE* shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu nace bazan je ba.




🍃🍃🍃🍃


MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


🍃🍃🍃🍃🍃




*PAID.*
🅿️=5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣






Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce
"Azima meke damunki?" ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai
"To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al'Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza tace
Ki fara karkaɗe kura" zunbur Azima ta miƙe tana fadin "muje"


saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al'mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan, shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci.




Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce
"Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa"
"A'a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai"
"Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?" shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace
"Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba" da mamaki Hadiza ta juyo ta ce
"To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?"
"Ban taba shara da tsintsiya ba" Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta goge hoton, nan take fuskar AL'MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana girgiza kai, Hadiza ta ce
"Karki tsorata, shine Al'mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne, amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa" Hadiza ta fada tana matsowa kusa da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce
"Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL'MAZEEN,idan har kika ga Al'Mazeen na fara'a to yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu *ALWAZ HOSPITAL* na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al'Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al'Mazeen yafi haka, amma idaa ya dawo zaki tabbatarwa kanki" Hadiza na gama fadi ta juya ta fice.


Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba, AL'MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne.




Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta ta hau bacci.






🍃🍃🍃🍃




"To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi" ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce
"Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya"
"To wanne kenan Aziza?"
"Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba"
"Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu ina sha tara" ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce
"Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan a al'adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana shiga sha daya za a aurar da ita"
" a shekara sha dayan!?" Sultana ta faɗa tana zaro ido
Aziza ta ce
"Wlh da gaske Anty Sulty"
"Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki, amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku"


"Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi dawowa"🤪


"Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?"


"Idan kikaji dadin rugarmu mana"
"Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?" Aziza ta yi murmushi ta ce
"Ai shiyasa ban baki labarin ni'imar dake yankin sassaninmu ba" Sultana ta yi dariya ta ce
"To naji, kar dai ki shashantar da
maganata"




"To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa" Sultana ta jinjina kai tana fadin
"Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa" ta faɗa tana ficewa a dakin.






@@@@@@@


Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to, amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin).






🍃🍃🍃🍃


Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da Al'mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login