Showing 96001 words to 96302 words out of 96302 words
Chapter 33 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt
yarsa suka shige, da gudu Azima da Aziza suka rungume Hajja, bayan an gaisa Baffa ya shigo Azima da Aziza suna hada baki wajan tambayar Baffa wannan abun arziki, nan Baffa yake gaya musu ai Mazeen da Nawaz ne sukazo suka maida garin ya zama birni yanzu haka wasu yankuna suna zuwa yankin kwana kallo, duk ta sanadin Magaji Bawa da yaransa Azima da Aziza,harta jauro ya zubar da hassadarsa arziki yake ci, nan Baffa ya dinga gaya musu abun arziki dasu Mazeen da Nawaz sukayi, hakika sunyi farinciki sunyi murna inda son mazajen nasu ke kara ninkuwa a zuciyarsu, sun zama tamkar wasu super'star a yankinsu na kwana.
@@@@@@
Sai dare can su Nawaz suka dawo suka cewa su Azima da Aziza su zo su tafi gidansu.
Ashe sun gina gida a garin madaidaci idan sunzo hutu nan zasu dinga zama dan zasu dinga zuwa yanzu a kai a kai lokaci zuwa lokaci.
Cikin kuka ko wacce ta rungume mijinta tana gaya masa tsananin so da kaunar da take masa, kamar yadda suma mazajen ta bangarensu hakan yake, daga nan ko wanne ya dauki matarsa da 'yarsa sukayi daki.
🍃🍃🍃🍃
TAMMAT BI HAMDULILLAH
*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFI ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON GAMATA lafiya, YA ALLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH KA BAMU LADANTA,KUSKURENA ALLAH YA YAFE MIN.*
*INA TAYA YAN UWANA MUSULMAI MURNAN SHIGANMU WANNAN WATA MAI ALBARKA, ALLAH YA YAFE MANA YA AMSHI IBADUNMU, ALLAH YASA A MUYI LAFIA MU GAMA LAFIYA, DAN ISAR ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM*
SAI KUNJINI A SABON LITTAFINA BAYAN SALLAH DA SATI DAYA IDAN RAI YA KAIMU IN SHA ALLAH, SUNAN LITTAFIN *AHLAN* AKAN FARASHIN DARI BIYU.
BISSALAM.
MOMYN AHLAN
GARKUWAR MACIZAI🐍🐍