Showing 30001 words to 33000 words out of 96302 words

Chapter 11 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt

sannan ya ce
"Aziza! a da an yi wani mutum jarumi! sadauki! jajircacce! tsayayye! marar tsoro da fargaba!, da tare dukkan wani faɗa! kin san ana cewa ba a faɗa da aljani ko? to wannan mutumin yana yi! wanda a yanzu shike tsaye a gabanki! Wanda wannan mutumin mahaifi ne gareki da kuma 'yar uwarki Azima, kamar yadda kika sani Ardo mahaifina ne wato kakanku! Inna wuro mahaifiyata ce! wasu daga mutanen yankuna suna fadin cewa nayo gadon Arɗo a lokacin yana saurayi, amma kin san me Arɗo ya ce?" Aziza da ta ƙurawa Baffanta ido tana yi masa kallo kamar bata taba ganinsa ba dan gani ta yi gabadaya ya canza mata ya tashi daga Baffanta da ta sani ya koma wani mutum daban ta girgiza kai alamun a'a, Baffa ya ɗora da cewa
"Arɗo cewa ya yi ni daya ne tak a wannan yankin dama sauran yankuna babu na biyuna! domin kuwa baiwata daga Allah ne, tun ina yaro nake mu'alama da aljanu sannan nake taimako! a taimakon da nakeyi ba iyakar mutane ba har ma da aljanun,a lokacin na shiga yankuna da dama dan kai wa wasu dauki! Yankin kwana ta shahara ta yi suna ta sanadina, tun a lokacin nake cin karo da abokan gaba da maƙiya wa inda basu sona sabida farin jinin da nayi a wajan yan mata a lokacin babu wani kyakkyawan jarumi ka ma na, shiyasa na kara yin baƙin jini, mahaifiyarku kamar yadda ku ka sani 'ya ce ga Ƙanwar Arɗo wanda suke uwa daya uba daya, Jumala yarinya ce mai kunya da natsuwa da hankali da sanin ya kamata, tun ranar da naje gidan Inna Kab'o na ganta naji na kamu da sonta amma ban san taya zan bayyana mata ba, Jumala ta ta so ne a babban gida wanda suke da tarin iyalai masu yawa, wanda a yanzu Jumala ita daya ce tal ta rage a danginta duk Banju ya kashesu!"




Kasa hakuri Aziza ta yi ta ce
"Baffa miye dalilin Banju na kashe mutane? Sannan naji Baffa Mandi ma ya ce shi ya kashe masa ahalinsa! Sannan wanene shi Bahula din?"


"Bahula mace ce ba namiji bane Aziza! Saurin me kikayi Aziza? Zaki san komai a yau! duk wani jeji babu wanda bana shigansa da ikon Allah sannan na fito lafiya ba tare da wani abu ya sameni ba, domin nayi imani da Allah da ANNABI MANZON ALLAH S,A,W, nayi karatuna a wajan wani Babban malami a nan yankin kwana mai suna MALAM SHAINI wanda shima ahalin yanzu baya raye Banju ya kashesa! shi da iyalansa!"




"Kenan Baffa yawancin mutane Banju ya kashesu?"


Juyowa Baffa ya yi ya kalli Aziza sannan ya yi wani murmushi ya ce
"Kisan da Banju ya yi ba zai kirgu ba, dan zan iya ce miki a cikin kashi dari na mutanen yankin kwana Banju ya kashe kashi arba'in! Banju mugu ne, na kasance ina shiga jeji dan nemo ganyayyaki na haɗa magani, akwai wani jeji mai sunan jejin 'Bingel, hakika har kwanan gobe ban kara shiga jejin 'bingel ba"




"Kenan Baffa akwai jeji mai suna jejin 'bingel?"


Baffa ya gyaɗa kai
"E Aziza, akwai a wannan jejin ne na tafka babban kuskuren da ban taba yi ba a rayuwata, ko kuma nace ya haɗu min har da tsautsayi! dan a wannan jejin ne tsautsayi ta haɗani da Banju, a da ban san wani abu mai suna tsoro ba a rayuwata! Banju shine mutum na farko da ya fara shuka min tsoro a zuciyata, ba dan komai ba sai dan ikirarin da ya yi a kaina da mutanen yankina a sadda zan kashesa! ba dan komai na tsorata da Banju ba illa ta'adi da b'arnan da ya yi a yankin nan"




"Ranar wata laraba ba zan taba mantawa ba naje jejin 'bingel dan nemo wani ganyen magani da zan haɗawa Inna Kab'o mahaifiya ga Jumala Hajjarku ciwon kafa ya sakata a gaba, a lokacin kuma an gano cewa ina son Jumala ita ma kuma tana sona har an fara maganar haɗamu aure, na shiga jejin 'bingel har na tsinƙe ganyayyakina zan fita, da shike duk inda zanje ina tare da addana kin san fulani da takwabinsu suke yawo ni kuwa harda kifiya nake yawo, kifiyata kuma tana da guba a jiki, sabida shige-shigen da nake yi na saka rayuwata a hatsari dole na dinga tafiya da kariya duk da nasan ni Allah shike kareni, kifiyata ba mutum ba duk wani abu da zan harba da shi sai ya mutu walau na harbi aljanu ko mayu ko wani dabba ko ma me da kika sani, na juyo zan bar jejin bingel ban ankara ba na hangi wani zureren 🐍 jelar maciji mai cike da ban tsoro, dama kafin nan a kwanaki muna samun koke-koke daga maƙotan yankuna a kan saren maciji wanda nike zuwa dubawa,saren macijin kuma ya fita daban da saren macizan da na sani, to ganin wannan macijin ke da zuwa ban tsaya dogon tunani ba sabida na ɗan firgita na ciro kifiyata har uku na saita macijin na harba, kin san wane harba?" da sauri Aziza ta girgiza kai
" *BAHULA* wanda ƘANWA take a wajan Banju, wanda yake haukan sonta yake ji da ita, ban taba sanin suna rayuwa a wannan jejin ba, sannan ban san da cewa aljanun macizai bane,ni dai na ga Babban maciji kuma na harba, ina harbinta nan naga abunda ban taba gani ba, wato nan ta rikiɗe ta zama mutum kifiyar da ma harbeta da shi daya a kirji daya a juya daya a baya, kafin na farga da abunda na aikata nan naji ihun Banju yana furta "BAHULAAAAA!!" wanda sai da jejin bingel ya girgiza, a lokacin da Banju ya zo ga Kanwarsa Bahula ina tsaye ina kallon Ikon Allah, yayinda lokaci daya naji jikina na rawa, ko a lokacin da Bahula zata mutu sai da ta cewa Banju Dan Allah ya gyara halinsa na mugunta bata so a sake koransa a wannan jejin kamar yadda ya buwayi asalin garin da suke a jejin aka koresu ta hanyar yi musu turaren barkono dan tun asalin Banju mugu ne fiye da misali, a lokacin da na ga haka na matso kusa ina bai wa Bahula hakuri, murmushi ta min bakinta na fitar da baƙin jini ta ce min ba komai tasan ba da gangan nayi ba, sannan ta roƙi alfarma a kan cewa na bar ɗan uwanta Banju yayi rayuwarsa a jejin bingel, sun taso tare kamar yadda aka haifesu tare dan su ma yan biyu ne, a hannun Banju Bahula ta cika, Bahula tana mutuwa Banju ya hau kuka ina basa hakuri dan babu taimakon da zan iya yiwa Bahula dan guba ya shigeta,hakika nima nayi kukan kuskuren da na aikata, nan na dinga ba wa Banju hakuri, amma abunda ya ce min shine, shi *BAYA MANTUWA,KUMA BAYA YAFIYA* a lokacin Banju ya yi yunkurin kasheni amma ya kasa, yayinda ni kuma na gudu,ina zuwa gida banyi nauyin baki wajan faɗawa mutane abunda ya faru ba,tabbas a lokacin mutanen kwana sun tsorata matuka,inda aka yi cincirindo aka je aka ba wa Banju hakuri amma ya nuna sam ba zai hakura ba, bayan kwana biyu da faruwan haka nan yankin kwana ta koma mace-mace na hanyar kisan maciji ko kuma kisan gilla ta sanadin wani gurb'ataccen guba wanda Banju ne ke yi, a kwana biyu Banju ya kashe mutane sama da dari a yankin kwana, nan fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kare mana, ba mu sake yin kasa a guiwa ba muka sake zuwa wajan Banju basa hakuri amma kamar mun sake zugasa ne muna tunzura shi, ba zan iya ƙayyace miki mutanen da Banju ya kashe ba Aziza, haka ya bi dangin Jumala mahaifiyarku ya kashesu ita daya kawai ta tsira, a lokacin Arɗo ya dauketa ya kaita gidansa sannan ya daura mana aure da ita, a lokacin Baffa Mandi shi ne sarkin fulanin kwana, haka shima iyayensa matansa yaransa da duk wani danginsa sai da Banju ya kashesu! a lokacin ko yaro aka haifa yau Banju ya samu zai kashe, babu kalar farmakin da Banju bai kawo min, akwai sadda yankin kwana ya koma zallar ƙura ne ke tashi tare da jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,nan nayi tattaki naje na samu Banju nace masa daukar Fansansa a kaina ne meyasa yake so ya shafe yankina, ina nine na masa laifi to ya kasheni ya kyale jama'a amma nan yace min ko da ya kasheni ya min alkawari babu wanda zai rage a raye a mutanen yankin kwana sai ya kashe kowa! ko da kuwa ɗan da yake ciki ne sai ya kashesa! a lokacin nayi niyyar na miƙa wuyata ga Banju amma na fahimcesa kamar yadda ya faɗi ba zai kyale kowa ba, nan jama'ar kwana aka hadu aka yi tattaunawa inda kowa ya kawo shawara a kan na kashe Banju dan abun nasa yayi yawa,da fari naqi amincewa sai daga baya na amince, a lokacin da zamu gwabza na fahimci ba zan iya kashe Banju kai tsaye ba,kamar yadda shima ba zai iya kasheni kai tsaye ba, a lokacin ne na tafi jejin lore aka bani zare mafi hatsarin gaske, wato zaren saƙar dana, a wajan yanki muka gwabza da Banju gaban dukkan mutanen yankin kwana, kin ga wannan takwabi da shi na kashe Banju bayan na saƙa zaren saƙar dana na naɗe a jiki na sokesa da takwabin a ciki, nan ya fadi yana aman jini amma jinin ba ja bane kore ne, kafin ya fadi kasa shine ya mana alkawarin cewa zai dawo daukar fansa a kaina ta ko wace hanya dani da mutanen yankin nan, to kinji abunda ya shiga tsakanina da Banju!"




Baffa na gama ba wa Aziza labari tasa kuka tana fadin
"Kenan yanzu Baffa Fansar da Banju yake dauka a kanmu ne? Innalillahi wa inna ilahirrajiun! Yanzu Baffa kashemu zaka yi?" Baffa ya girgiza kai yana fadin
"A'a Aziza! Kin taba ganin Uban da ya kashe yaransa ne? Amma idan ta kama zan iya Kashe Azima dan tsaida wannan bala'in,idan ba haka ba tabbas ba a fara mutuwa ba, ke rabaki da Bahula ba zai yi wuya ba, amma ko da an rabaki da ita ke Banju ya maidaki Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinki ba sai ta jikin Azima, kuma ni bana da masaniyar makarin abunda Banju ya miki, amma akwai wani Babban Malami mai suna Malam Shadi a can yankin ja'o zamu je wajansa dan ya mana bayani,ki kwantar da hankalinki, amma kafin nan muna da bukatar tsaida Azima mu ɗaureta, ki daina kuka kinji? Tashi mu tafi gida" Aziza ta miƙe tana share hawayenta suka nufi gida, a hanya kafin su karasa Baffa ya haɗu da Salti ɗan gidan Jauro mai maganin kwana aljanu sun bugesa, da sauri Baffa ya yi kansa yana dubasa,girgiza kai ya yi yana fadin
"Sai da nace kar wanda ya fito ai ga irinta nan, taurin kan Salti iri daya ne da na Ubansa Jauro" Baffa ya faɗa yana daukar Salti, gida suka nufa suna isa Baffa bai yi nauyin baki ba ya gaya musu ai Banju ne a jikin Azima, Bahula kuma tana jikin Aziza, sannan ko an raba Aziza da Bahula Banju ya maidata Macijiya, wani kuka mai rikita zuciya Hajja ta kuma sakawa, yayinda Aziza ta faɗa jikinta suka hau yi tare, Baffa Mandi ya ce
"Abun da za ayi yanzu shine, ya kamata muje wajan wannan Malamin wato Malam Shadi na can yankin Ja'o mu je zuwa gobe kawai dan bamu ga ta zama ba, amma kafin nan dan Allah kar a fadawa jama'ar gari dan ba a san me hakan zai haifar ba har sai munje an dawo, mu da muka sani ya tsaya a iya mu kawai" aka amsa da hakane, nan Arɗo ya ce
"Magaji? Ana ta wannan maganar ina Azima?"




🐍🐍🐍🐍🐍




COMMENTS BUT PLSS DON'T SHARE BA DAN NI BA DAN ALLAH DA MANZON ALLAH 🥺👏🏻[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)


MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


🍃🍃🍃🍃🍃





*PAID.*
🅿️==2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣






"Azima?" Baffa ya nanata sannan ya kuma cewa
"Tun sadda ta b'ace ban ganta ba" Aziza dake kuka a jikin Hajja ta miƙe tana goge hawaye ta ce
"Baffa bari na dubota na gani tana ina" Baffa ya ce
"To dubota Aziza" rufe ido Aziza ta yi ta shafa hannun damanta da hannun hagunta,amma abun mamaki bata ga Azima ba, saurin bude ido tayi tana fadin "taya hakan zai faru?"
"Menene Aziza?" Arɗo ya tambayeta
"Arɗo bana ganin komai,bana iya ganin Azima amma taya hakan zai kasance?"
"Ki sake dubawa Aziza" Baffa ya faɗa Aziza ta gya ɗa kai tana fadin to Baffa, ta sake rintae ido amma wayam, sake buɗe ido ta yi ta ce
"Wlh bana ganinta, Baffa ya ce zan duba da kaina amma sai bayan munyi sallar magriba fatana dai daya kar ace Azima taje ta yi wani ɗanyen aiki"
"In sha Allahu ma ba zata yi ba" cewar Baffa Mandi, kamar yadda Baffa ya faɗa bayan sallar magriba ya hau duba inda Azima take amma abunda bincikensa ya nuna masa shine kwata-kwata Azima bata yankin kwana ta fice gabadaya daga wannan sassanin, a firgice Baffa ke furta kalman "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATIHI WA AKHLIFNI KAIRAN MINHA!" da gudu Hajja da Aziza suka shigo suna tambayar Baffa menene? "Azima bata yankin nan kwata-kwata,bata wannan al'ƙaryan! ta bar wannan sassanin, Banju ya ja min 'ya sun bar wannan yankin!" cewar Baffa hankalinsa a matuƙar tashe, Aziza ta ɗora hannu a kai tana fadin
"Wlh Baffa ta sha fadin tana son shiga cikin inda yake da mutane da yawa ta tarwatsasu,kenan ina Azima ta nufa!? Duk inda zata je dai ba alkhairi zata shuka ba,dan nasha gaya mata shiganta mutane ba alkairi bane, yanzu miye abun yi Baffa?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Ban sani ba Aziza! Allah ya kaimu gobe asubanci zamuyi mu tafi yankin ja'o dan zuwa wajan Malam Shadi" Aziza ta juya tana kallon Hajja wacce ta kasa tsayar da hawayen da ke zuba a idonta, a hankali Aziza ta fice a bukkar tana sharan hawayen tausayin iyayenta, Aziza na fita Baffa ya matso kusa da Hajja dake hawaye tun tana kuka mai sauti har ta koma kukan baya fita sai ambaliyar hawaye, cikin sigar rarrashi Baffa ya ce
"Jumala kiyi hakuri! Ki dage da addua muna kai wa Allah kukanmu! Dan Allah ki daina wannan kukan kar ya jawo miki ciwo, kinji!?" dago jajayen idonta Hajja ta yi ta watsasu a cikin na Baffa wanda tun tahirin aurensu bata taba kallon tsakiyar idonsa ba sai yau, muryarta a dashe ta ce
"Ciwo? Ciwo fa ka ce Baffan yan biyu? Wani irin ciwo ne ya fi na zuciya? Shin kasan ya nake ji a raina?"
"Ko ma ya kike ji ki yawaita nanata kalman Innalillahi wa inna ilahirrjiun! ya zaki dinga jin sassauci a ranki, sannan....."
"Don Allah Baffan 'yan biyu!" Hajja ta kasa Baffa ba tare da ya idasa maganarsa ba, cikin zafafan hawaye ta dago ta ce
"Ni dai kawai abunda nake bukata a wajanka shine ka dawo min da yarana! Ka dawo mini da Azima da Azizana, ni dai ban haifi macizai ba! mutane na haifa,idan wani abu ya samu Azima da Aziza hakika zan iya mutuwa kawai ka dawo min da yarana!" ta tashi ta fice da gudu a bukkan, Aziza dake maqale a jikin bukkan tana sauraronsu ta riƙe bakinta gam tana kuka itama da gudu ta fice a gida ta yi rafin jimulo, taje ta ci kukanta har ta godewa Allah kafin ta dawo gida, bukkar Hajja ta shige ta sameta zaune ta zauna kusa da ita ta ɗora kanta a kan cinyar Hajja ta ce
"Hajjana! Inaji a jikina kamar na kusan barinki! Ba wai ina gaya miki dan na tashi hankalinki bane, duk duniya babu abunda na tsana kamar na ganki ke da Baffa cikin tashin hankali,abunda yasa nake gaya miki Hajja dan na nemi yafiyarki ne! Hajja ki yafe min idan har nayi miki wani abu a zaman da muka yi dake! Kowa da kalar kaddararsa amma mu wannan shi ne namu kaddara! Ba mu kasance cikin mutane da zamu yi rayuwa dake ba Hajja,dan Allah ki yafeni! Ki yafemini!!" Aziza ta karasa da sakin kuka mai ban tausayi da karya zuciya,tana sa kukan Hajja ta rungumeta tana bubbuga bayanta dan tama kasa magana ko tace zatayi maganar ma muryarta ba zai fito ba dan ya dashe!" su na nan suna kuka har dare ya tsaga kafin Baffa ya shigo ya musu umarni da suyi alwala suyi sallah, hakan kuwa ta kasance, Baffa ne yaja su sallah suna gayawa Ubangiji, da haka har asuba ta yi basu rintsa ba.


Bayan Baffa ya dawo daga masallaci tare suka shigo da Ardo da Baffa Mandi, a lokacin Aziza da hajja suna zaune sunyi jingum-jingum, Baffa ya ce
"Aziza ta shi mu tafi, Jumala ke kuma ki tafi gidan Arɗo" ko uhum Hajja bata ce ba tana riƙe da hannun Aziza,fuskokinsu a kumbure,shima Baffa ɗaurewa kawai yake yi baya so ya kara karya musu guiwa amma da zai samu dama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login