Showing 45001 words to 48000 words out of 96302 words
Chapter 16 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt
Kamar yadda Nawaz ya fada haka kuwa ya kasance 30mins ta farka, tana buɗe ido ta hau bin inda take da kallo, ba dai har ta mutu bane yanzu haka tana lahira? Take tambayar kanta,kallon hannunta ta yi ta ga wata budurwa zaune kusa da ita, ga wata dattijuwar mata zaune hannunta dauke da carbi tana lazimi, budurwar kuma hannunta da waya tana dannawa,saurin janye hannunta Aziza ta yi ta matsa baya, tana dafe kanta da kafarta da ta ga an daure mata shi,nan abunda ya faru ya dawo mata kai, Sultana ta ce
"Sannu kinji! Ya jikin naki?"
"Sultana kira yayanki mana" cewar Mom
"To Mom" Sultana ta faɗa tana ficewa.
Tare suka dawo da shi, a lokacin Aziza na maqale can jikin gado tana wani irin kuka kanta a sunkuye tayi mayafi da gashin kanta, jin magana yasata dagowa kaɗan ganin mutum na matsota ya sakata fashewa da sabon kuka tana fadin
"Aradu karka matso kusa dani" a yadda take magana zaka san babu hausa a harshenta,banza da ita Nawaz ya yi yasa hannu zai tabata ta saki ihu tana kiran sunan Baffa, haushi ne ya kama Nawaz ya daka mata tsawa
"Keeeee!!! Bana son hauka!! Ki natsu!!" Mom tace
"Haba Nawaz!? Miye haka? Ka mata a hankali mana" wani tsoro ne ya kama Aziza,ganin haka yasa Mom matsowa kusa da ita ta ce
"Ɗana ne! Ba zai cutar dake ba, wancan kanwarsa ce, shi kuma likita ne, ya bugeki ne bisa tsautsayi sannan wannan asibitinsa ne yana kula dake,alhamdulillah kin farka, yanzu haka kina garin kaduna ne,munji kina ambatar sunan Baffanki, da kinji sauki zamu maidaki gida kinji ko? Karkiji tsoronsa zai duba ki ne uhum?" Mom ta faɗa tana bubbuga Aziza, dubata Nawaz ya yi ya fice cikin haushi.
🐍🐍🐍🐍🐍
Tun shigan Azima dakin munir da niyyar gyarawa ba a sake ganin mai kama da ita ba, har dare, kuma cikin wani ikon Allah babu wanda ya nemeta,dan sun manta da ita,tunda sun san mai aikinsu ta gudu sun manta sun dauki sabuwa, sai wajan karfe tara Munir ya dawo shi da Baby, bayan sun yi magana da Zuby da Hajiya Baby ta wuce dakinta,Munir ma ya wuce nasa,yana shiga ya yi turuss yana ganin ikon Rabba, Azima ta yi ɗaya-ɗaya a kan gado ta bararraje an samu gado mai laushi bana kara ba, sai kwasar baccinta take cikin salama hankali kwance, gashinta da ya sha wanki sai kyalli yake yi duk ya baje ya rufe mata fuska, wani yawu muqut Munir ya hadiye yana fadin
"Kai daga ina wannan balarabiyan?" ya fada yana yin kanta ba tare da yayi dogon tunani ba shin aljana ce ko mutum.
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️==3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣
Hannu yasa jikinsa na rawa yana lashe baki yana kwashe gashin da ya rufe mata fuska cikin bacci Azima ta ji mutum a kanta, bata gama tabbatarwa ba sai da taji saitin hannun mutum a wajan dukiyar fulaninta, nan da nan ta farga da abunda ke wakana a kanta, idonta ne ya sauya, da tafin hannunta ta tokari kirjin Munir kamar kiftawar ido da bismillah sai ga Munir ya yi sama ya bugu timm da kasa!! Saurin tashi Azima ta yi,ta dauki mayafinta ta yi lullubi sannan ta yi kan Munir,tana zuwa ta shaƙosa da hannu daya ta haɗasa da bango,nan idon Munir ya yi waje yana so ya yi ihu amma baya so kannansa suji su rainasa, lallai yau ba shakka ya yi gamo da aljana a garin ɗan banzan son matan tsiya tun bai tsaya ya ga wacece ba ya afka mata ga shi tana neman kashesa, lokuta da yawa Munir ya sha yiwa yaran aikinsu fyaɗe,da anyi kara kuwa uwarsu zata zuba kuɗi ta karbo ɗanta tace an masa sharri.
Cikin zafin zuciya Azima ta kamo hannun Munir wanda ya taba mata kirji da shi, matse hannun tayi jikake ƙashi na haɗewa yana bada ƙaƙassƙasssƙass!! Ihu Munir ya sake na azaba, Hajiya da Zuby dake parlour suka ji ihun Munir da gudu sukayi dakinsa, a lokacin da ya yi ihu Azima ta sakesa ta koma gefe jin kafar mutane da gudu, kafin su shigo Azima ta duƙa kasa a gaban Munir, Hajiya da Zuby suna shigowa Munir ya yi saurin maida hannuwansa baya, Hajiya tace
"Munir ihun me kakeyi haka?"
"Ha...ji....ya...wa..ce..ce...wan...nan...yarinyar.." sai a lokacin suka maida kallonsu ga Azima da take duƙe tana murmushin mugunta ta cikin mayafi, tsaki Zuby tayi tace
"Mtswww Munir amma dai wlh kaji kunya,duk iya shegenka amma wannan yarinyar kake yiwa ihu? Sabuwar mai aikin da hajiya ta dauka ne fa, wlh nikam har na manta da ita a gidan,ke dan uwarki miye kikeyi a dakin nan tun rana har yanzu?" matse hannu Azima tayi tana cije baki, da kyar ta ce
"Da na shigo na manta abubuwan da Inna Lantana ta gaya mini nayi ne,kuma da nazo fita ban san ta inda zan fita bane shiyasa na zauna, shi kuma da ya shigo ya ganni sai ya tsorata" Hajiya ta ce
"Ba dole ba!, fuska a rufe kina dukar da kai, banza kawai maza ki tashi ki gyara masa dakin yanzun nan idan kin gama kije ki gyarawa Baby da Zuby nasu, sannan ni kuma kije ki wanke min toilet, ohh ina nufin bayi ko kewaye ku ke cewa oho,dalla tashi!!" Hajiya ta faɗa da tsawa suna ficewa a dakin ita da Zuby, Munir ya ce
"Kee dan ubanki! Dama ke mai aiki ce shine kika shaƙeni! Kin san waye ni kuwa?" waigowa Azima ta yi ta ce
"Kamar yadda kaima baka san wacece ni ba! Ka kiyaye! Bana gargaɗi sai dai zartar da hukunci!" tana gama fadi harta juya zata fita ya ɗan sake ihu yana maqale hannunsa, juyowa Azima ta yi ta dawo ta cafke hannu yayinda ta sake matsewa ta ware hannun ya sake sakin kara, hannun nasa ya dawo dai-dai ta ce
"Ban taba lalata abu na gyara ba! Sai dai idan aka gyara na b'ata!" tana gama fadi ta fice, wajan Lantana a kitchen taje Lantana tana ganinta ta ce
"Ahh Azima tun rana ina kika shiga haka?" abunda ta gayawa su Hajiya shi ta kara nanatawa Lantana daga nan ta hau tayata aiki suna girkin Azima taji tana bukatar watsa dafi a cikin abincin,amma kasancewar tasan Lantana zata ci yasa ta hakura da watsa dafin,bata taba jin bata son kisa ba sai a kan Lantana ko meyasa hakan oho, bayan sun gama kowa yaci abinci suka gyara kitchen har sun kwanta Hajiya ta kwalawa Azima kira, cike da takaici da haushi Azima ta dauki mayafinta ta fice tayi dakin Hajiya, ko sallama ba tayi ba ta shiga Hajiya na zaune a gefen gado,tana ganin shigowar Azima kamar an bankota yasa Hajiya miƙewa da masifa
"Ke wace iriyar jahilace! Ƙidahuma bagidajiya! 'yar can cikin jeji kawai! ban gaya miki ki zo ki wanke mini bayi ba?" Azima na shirin magana Munir na kwala mata kira, Hajiya tace
"Maza je kiji me yake da bukata ki gama masa ki zo ki wanke min toilet dina yau din nan, ai babu ke babu bacci" fita Azima ta yi ta nufi dakin munir yana tsaye daga shi sai gajeran wando,kallonsa tayi ko gizau bata yi ba balle taji dari-dari dan ta gansa a haka
"Keee!! Banza 'yar jeji, gyara min gadona"
"Kaiiii!! Banza shanu ɗan iska ban gyarawa!" ta juya zata fita Munir yasa hannu ya fizgota ya ɗaura mata sannan ya tureta gado ya bita ya danne, wani gurnani Azima ta yi tare da rikiɗewa rabinta mutum rabinta macijiya! A haukace Munir ya tashi a saman kanta ya yi baya-baya ya faɗi a gado jikinsa na rawa, gashinta ta kwashe blue eye dinta ya bayyana ya ƙare rinewa
"Ban ce maka ka kiyayeni ba! Baka san wacece ni ba ko!?"
Cikin shiɗewar numfashi sabida tsananin tsoro da firgici Munir ya ce
"Dama ke ba mutum ba ce!!?"
Murmushi Azima ta yi ta ce
" *RUWA BIYU!* Mutum Macijiya!"
"Dan Allah kiyi hakuri karki kasheni!"
"Duk wanda ya ga kwayar idon Azima baya sake ganin wani!" tana fadin haka ta koma macijiya ta saresa a bayan wuya nan munir ya faɗi ya hau murkususu yana birgima har ya dai na! rai ya yi halinsa, sai da Azima ta ga ya mutu kafin ta zama mutum ta fice a dakin taja ta rufe shi, ta koma dakin Hajiya da take ta sababi, Azima ta ce Hajiya
"Ki ɗan jira a parlour na gama gyara miki dakin"
"Saura kuma karki gama da wuri ki ga yadda zanyi dake a cikin daren nan 'yar can cikin jeji kawai!" Hajiya ta faɗi tana ficewa, Hajiya na fita Azima ta kulle kofa ta hau gadon Hajiya ba daɗewa bacci ya kwasheta, Hajiya kuwa tana parlour tana jiran Azima ta gama gyara da fito yau ne gobe ne shuru,har bacci ya fara kwasar Hajiya, ta farka taje ta tura kofar ta jita a gangame! Bugawa Hajiya ta hau yi amma a banza har ta gaji, tana bugawa tana aunawa Azima zagi, dakin Zuby taje ta buɗe mata Zuby tace ita ba zata tashi ba ta riga da ta kwanta,haka ma Baby ita kam har da yiwa Maman tsawa ta tayar da ita a bacci, haka Hajiya ta dawo parlour ta kwanta a kujera nan ta kwana.
Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta nufa taje ta sameta zaune tana karatun al'kur'ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce
"Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma garinku,ke yar wace gari ce?"
"Ni 'yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?'' cikin tsawa Azima tace
"Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?" jin haka yasa Lantana karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce "ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana" bata jira amsar Azima ba ta fice, ta kai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce
"Hajiya me ya faru haka?" cikin kumfar baki Hajiya ta ce
"Wannan 'yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?"
"A parlour kuma?" cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe mata fuska
"Ke ba magana ake miki bane?" cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce
"Ya ri ga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi" Azima ta faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya.
A tsawace Azima tace
"NA CE A CIKINKU WA ZAI BISA NA BIYU!!?" cikin kuka da tashin hankali suka hau fadin tayi hakuri karta kashesu basu so su mutu, Azima tace
"Akwai abu daya da zan muku, ruwa zaku sha? Ko abubuwan da kuke sha a robobi zaku sha?" cikin kuka da majina da zufa suka ce ruwa, Azima tasa hannu ta janyo ruwa ta zuba a kofi uku ta ce
"Duk wanda baya son mutuwa ya sha wannan ruwan!" jikinsu na rawa suka dauka suka kafa baki suka kwankwaɗe suna kan bata hakuri, kamar da minti biyu tsakani Hajiya ta hau tari tana rike wuya, da sauri Zuby ta tashi tana fadin Hajiya meya sameki,nan ita ma ta hau riƙe wuya tana tari, Baby ma haka, tari sosai suke yi jini na fita baki da hanci, Azima ta miƙe ta ce
"BANA MANTUWA! BANA YAFIYA! NA RIGA DA NA ZUBA DAFI TA YATSAR HANNUNA!" tana gama fadi ta shiga ta dauki kayanta na fulani da Lantana ta wanke mata ta saka ta fice ta bar gidan.
🍃🍃🍃🍃
Kwanan Aziza biyu a asibiti jikin nata alhamdulillah duk da da ace taso zata iya warkar da kanta amma bata so ta sakawa su Mom da Sultana shakku a ransu su fara zarginta, sannan yanzu idan tace zata gudu bata san duniyar da Azima take ba kuma tana ji a jikinta duk inda Azima take bata shuka alkairi, abu biyu ne ya haɗe mata waje guda ya jagula mata lissafi, bata san taya zata fara neman Azima ba tunda basu al'karya daya, sannan bata san wani hali iyayenta suke ciki ba,duk da tana da yaƙini a kan Baffa zai kula da Hajja sosai shima zai kula da kansa, tana zaune tana tunani, wani dabara ne ya faɗo mata, wannan dabara kuwa shine ta fara yawon bin garurruka! duk garin da suka haɗe da Azima idan ta lumshe ido zata iya hangota ta cikin tauraronsu, da wannan tunani ta samu karfin guiwa,lumshe ido tayi ta shafi tafin hannunta amma bata ga Azima ba, a fili ta ce
"Hakan na nufin bamu gari daya kenan, wannan hajiyar (Mom kenan) ta kira sunan wannan yankin da kaduna ko? Ina gani gwara na tambayi wannan yarinyar tata sunayen yankuna sabida naje na dudduba Azima, amma kuma kafin na tafi dole ina bukatar kudi, hakan yana nufin dole na yi musu aiki dan na tara kudin neman Azima? Idan kuwa haka ne Banju ya cuci rayuwarmu,ga shi wahalar a kaina da Baffa yake karewa" ta karasa maganar da sakin kukan tausayi, tana sakin kukan su Mom da Sultana suna shigowa.
Ganin tana kuka yasa suka karaso wajanta da sauri suna tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo ne? ta girgiza musu kai alaman a'a, Mom ta ce
"Yarinya? Kiyi hakuri kodayaushe kina cikin kuka, ina yan uwanki suke? A wani ruga kuke a garin yola idan yaso gobe sai a maidaki" jin haka yasa Aziza kara sakin sabon kuka,inaa ai ba zata so ta koma ba tare da burin Baffa na su dawo tare da Azima ba, mafita daya ne shine kawai ta yi karya,cikin kuka ta ce
"Yan fashi ne suka fada rugarmu suka kashe mana kowa, nima da kyar na sha,dan Allah Hajiya ki taimaka mini na dinga yi miki aiki kina biyana,yanzu idan na barku ban san inda zan hadu da mutane nagari kamar ku ba dan Allah Hajiya!" Aziza ta fada tana kuka sosai,jikin Mom ne ya yi sanyi sosai, Sultana ma kwalla ya cika a idonta ta kalli Mom ta ce
"Mom mu dauketa kawai,tunda dama kinga Haule ta yi aure,ita wannan ma zata jima " Mom ta ce
"To shikenan kira mana wani Dr ya zo ya rubuta mana sallama,dan munyi waya da Nawaz yace sai gobe ko jibi zai dawo,kuma yace idan har jikin nata da sauki mu koma gida, to gwanda gidan dai zaman asibiti ba dadi garesa ba"
"To Mom" Sultana ta fice bata jima ba suka dawo da wani likita ya rubuta musu sallama suka yi gida, dakin masu aiki dake kasa wajan cikin parlour bayan step dakin mai aikinsu na da Haule wacce tayi aure,bama iyakar Haule ba duk masu aikinsu nan ne dakin da suke zama,babban daki ne dasu babban gado da wardrope da toilet da komai da komai, Sultana ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da komai,bayan ta nuna mata Aziza ta kalleta ta ce
"Na gode Anty Sultana" Sultana ta yi murmushi ta ce
"Ba komai mai kyau, amma meyasa kike son rufe fuskarki? Har yanzu baki saba damu bane?"
Cikin in-ina Aziza ta ce
"Inada matsalar ido ne, tun ina yarinya bana son haske, sannan bana iya kallon mutane da idona shiyasa mahaifiyata ta bani wannan mayafin ina lullubi da shi, gashi na kuma na fiddo da shi dan ya rufe min daya idon da zan dinga ganin hanya"
"Ayya Subhanallah! Idan Brother ya dawo zan gaya masa sai ya duba miki idon, watakila idan aka dace sai ya miki magani"
Da sauri Aziza ta ce
"A'a Anty Sultana karki gaya masa halittatace a