Showing 84001 words to 87000 words out of 96302 words
Chapter 29 - Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel By Zainab Abdul Mom Ahlan.txt
hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai yace
"Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa,
"Haba jaruma, karki bani kunya mana" mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce
"Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce
"Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin
"Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce
"To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da Aziza.
A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin azaba tana fadin
"Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba.
💞💞💞💞💞
Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi.
Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.
Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.
Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace
"Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi murmushi yace idan ka so haka"
"Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce
"Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima" mom ta karba tana masa sannunsa da aika.
Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci.
Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju.
Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya rubuta wasika yayi aike sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a tsakanin aljani Banju da Baffa bisa umarnin gayyatar sarkin yankin kwana wato sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja'i da yankin tudu da yankin ja'o da yankin gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna.
Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a tsakanin Magaji bawa da Maciji Banju, wanda ya yi b'arna da ta'adi a yankin kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama macizai irinsu jarman macizai dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da aljan,duk da wannan ba sabon abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa Arɗo.
Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma asalin cikakkiyar mutun ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har zuwa yanzu suna bacci, goshin Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara hamma, wani farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki haka, daga nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne kawai yake iya ganinta dan kuwa mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan Baffa kashe mata Yayanta Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar da kai Baffa yayi, daga haka Bahula ta b'ace, muryan mom Baffa yaji tana magana
"Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?"
"In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu san a ya zai farka ba shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar abunda ya faru kar a boye mata duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sume amma zata iya gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da Banju,jikin ma kuma nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya haifar mata da wani matsala, mom ta gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen.
🍃🍃🍃🍃
Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi
"Kina lafiya?" Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce
"Azima? yar uwata?" ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin
"Azima?" daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa suka shigo, juyowa Azima tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce
"Aziza?" wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam
"Me ya faru Aziza?" Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka
" zan gaya miki" cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara kisa da yaƙi da komai da barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin
"Ni....ni....ni....ban.....ban....ban...kashe....kowa....ba.....Baffa.......bana....da niyyar kasheka...Hajja ban miki rashin kunya ba.....Aziza...banyi faɗa dake ba.....dan Allah kuyi hakuri..... Ban kashe kowa....ba..." duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta ringume tace
"Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba, kwantar da hankalinki, ba ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju shine ya kashe" ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci gaba da kuka, duk da zafi da ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja da kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da hannu tana fadin.
🍃🍃🍃🍃
GARKUWAN MACIZAI🐍
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣
"Aziza?" Azima ta kira sunanta itama murya a sarƙaƙe, Nawaz ne yace kawayen Sultana su fita, da sauri kuwa suka fice,suna fita Al'mazeen ya sawa kofar key, wani kallo Azima ke bin Aziza da shi har ma dasu Mom, Mom ce ta tunkari Azima tana shirin yi mata magana da sauri Aziza ta ce
"A'a Mom!" tsayawa cak mom tayi, Aziza ta mata ido a kan taja baya, Al'mazeen ne ya matso kusa da ita ya ce
"Azima zan iya ce miki wani abu?" shuru Azima tayi kirjinta na bugawa,
"Azima Ina sonki! Kuma na au...." maganar da Al'mazeen bai karasa ba kenan Azima ta saki ihu tana toshe kunne, matsowa kusa da ita Aziza tayi ta duƙa a gabanta tace
"Azima? Ohh ina nufin Banju! Ka sa kunne da kyau, yanzu haka yola zamu tafi, yau sai yankin kwana In sha Allahu! zaku haɗe da Baffana! dama kasan karonku dashi ba dadi" wani dariya Azima ta hauyi marar dadin sauti tace
"Ke a tunaninki zan yarda na koma ne?"
"To taya zaka iya guduwa? Albishirinka! Yanzu haka da aure a kan Azima!" wani zaro ido Banju ya yi yana fadin
Sun ci amanarsa sai ya kashe miji waye mijin, Al'mazeen ya amsa da cewa
"Ni ne mijin!" wani kururuwa Azima ta saka ta miƙe da karfinta da niyyar zama macijiya dan ta saresu da sauri Aziza tasa hannu da wani farin haske ta tokari goshin Azima nan tayi ɗiff!.
"Na kafar da ita zamu iya tafiya" Aziza ta faɗa jiri take ji amma ta rasa yadda zata yi, Mom tace
"Nawaz Al'mazeen ku kama matayenku ku saka su a mota, bari na yiwa Umma magana (Umma yaya ce ga Mom wanda itace zata tsaya a karasa biki a kai sultana dakinta) har zasu fita sultana ta fashe da kuka tace
"Aziza! Za ki dawo? Kiyi min alkawari zaki dawo?" itama Azizan kuka tasa suka rungumi juna, Nawaz zai ja Aziza mom ta daga masa hannu alamun ya barsu, dagowa Aziza tayi tace
"Ban san me zance miki ba Antyna...."
"Shiiiii! Yanzu kece Antyna tunda da auren Yayana a kanki" murmushi Aziza tayi hawaye na zuba a idonta tace
"Ba a canzawa tuwo suna, ke ɗin antyna ce wacce nake ji da ita sosai, da fari zan fara neman gafararki! aurenki guda amma ta sanadina da yar uwata ba a miki shi yadda ya kamata ba, kiyi hakuri ki yafe mana, ga shi zamu kara tafiya da mom,mu kuwa me zamu ce muku? Sai dai mu muku fatan Allah ya muku sutura ranar lahira, dan kuwa kunyi mana a duniya"
Sake rungumeta Sultana tayi ta ce
"Ni kam alhamdulillah! Naji dadin aurena,dan kuwa an daura tare da Yayuna, sannan karki damu da batun tafiya da Mom, Umma tamkar mom take har ma taso tafi mom, lafiya za a kaini gidana,ni dai fatana dan Allah kiyi hakuri ki dawo a kan lokaci,kinji?" share hawaye Aziza tayi ba tare da tayi magana ba dan bata sa a ranta zata dawo ba, Nawaz ne ya kama hannun Aziza ya jata ya rabasu da sultana suna kuka suna komai, mom ce ta rufe musu fuska kowa ya kama matarsa a haka suka sauko jama'a sai guɗa ke tashi, da manyan motoci biyu zasu tafi wanda zai juri wahala da afkawa jeji mai gudu, mom da Hajiya Luba Maman Beenah kenan ba dan taso ba haka aka sa ta shiga mota,Maman Hanan kuwa cewa tayi wlh ba zata je ba, da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami da Malam Yunusa abokin Mahaifin su Nawaz.
Al'mazeen da Azima suna zaune a bayan mota Nawaz da Aziza suna zaune a gaba,mota daya suke su hudu Nawaz ke driving, Azima tamkar gunki haka ta koma, lokaci zuwa lokaci Al'mazeen zai waiga ya kalleta, sunyi nisa Al'mazeen yace
"Aziza? Hope dai Azima lafiya take?"
Gya ɗa kai Aziza tayi a sanyaye tace
"Lafiya take Hamma Mazeen, kawai na kafar mata da dafi ne idan ba haka ba sunanku gawa dan Banju zai kasheku! Ni ba zata iya kasheni ba, kuma kafin ace nayi kokarin yin wani abu dan dakatar da ita zata iya kashe ko da mutum daya ne ba zan so hakan ba, zamanta a haka shine mafi alkairi har mu isa" jinjina kai Almazeen yayi yana kara maida idonsa kan Azima.
Basu isa yola ba sai yamma lilis, dan haka Aziza tace ba zai yu su afka jeji ba su bari su sake yin asubanci gobe, dan haka suka kama hotel inda zasu kwana.
A gida kuwa karfe biyu Umma tayi oya-oya aka dauki amarya sultana aka kaita danƙareren gidanta da Khalil dinta ya gina aka ajiyeta, Umma ce tayi mata komai tamkar Mom tana nan, Umma ce ta wakilci mom a komai aka sallami baki da wasu daga cikin yan uwa.
Sadda aka ajiye sultana a gidanta za a watse a barta tasha kuka, duk hankalinta da adduarta Allah yasa Aziza ta dawo.
Kamar yadda suka ce da washe gari asubanci sukayi, sallar asuba kawai suka yi suka yanki cikin jeji inda zai sadasu da ƙauyen yankin kwana, Aziza ke nuna musu hanya, Nawaz ya kalleta yace
"Zamu iya isa a yau?" tace
"Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa"
"Kai har yamma?" Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin.
🍃🍃🍃🍃
Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da mafarkin ba sabon abu bane a wajanta.
Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji, yayinda hawaye ya b'alle mata, hakika yanayin al'karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi abun sha'awa ma sha Allah,